Hausa NovelsSakayyah Complete Hausa Novel

Sakayyah 38

Sponsored Links

SAKAYAH

 

38

 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

 

 

*Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha’awa.* Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban  lissafa. Sune manyan alamomin infection.

Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.

Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.

KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.

INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.

 

 

Da sauri ya juya baki ɗayansa kana ya nufi hanyar ƙofar masallacin ta waje yana ida fita yaga anja motar dake gefe ta wajen masallacin antafi dashi cikin sauri ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yana maimaita duk wata addu’a da tazo bakinsa.

 

Batare da yace Uffan ba ya juya kansa ya nufi cikin hotel cikin raunin murya yace.

“Meyesa idanuna ke yimin gizo yau kuma J ɗina nake gani”.

Haka yaci gaba da mgnar zuci har ya shiga ɗakinsa.

Baki ɗaya abin ya fara bashi tsoro anya kuwa bai far zaucewa ba. Ya ƙare mgnar zuci tare zamewa ya zauna bakin gadon.

Wayoyinshi guda biyu dake gefen jakarshi ya ɗan juya ya kalla sabida jin ƙaramar tana ruri.

Hannunsa yasa ya zarosu, duk da kiran ya katse. Numfashi mai sanyi ya fesar ganin tarin miss call ɗin Abba, Innayi, Ummi da Malam Arɗo ahankali ya fesar da numfashi tun da yabar masauƙinsa na Abuja gaba ɗaya mancewa yayi da wayoyin suna cikin jaka bai buɗe ba sai yanzu da yaji kiran. Da sauri yayi picking call ɗin Abba da ya sake shigowa.

Cikin sanyin yayi sallama tare da cewa.

“Barka da dare Abba”.

 

“Barka dai Aliyu ya gajiyar hanya tun ɗazu nake ta kiranka, shiru”.

Cikin lumshe ido yace.

“Alhamdullah Abba phones ɗin ne suna cikin jaka”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauke cike da kulawa yace.

“Amma to ya hanya”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Lafiya lau hanya Alhamdulillah Abba gashi har na isa nayi sallar maghariba, yanzu wanka zanyi kafin sallar Isha’i ta gabato”.

Jinjina kai Abba yayi kana yace.

“Alhamdulillah ahuta gajiya amma kafin nan ka kira Innayi da Malam Arɗo da kuma Ummin ka dan hankalinsu ya kwanta”.

Kai ya gyaɗa cikin alamun gajiya yace.

“Toh Abba Insha Allah zan kira”.

 

“Wanne hotel ka sauƙa”.

Abba ya tambaya.

 

Ɗan guntun numfashi ya fesar tare da cewa.

Sofitel Mouley Youssef na sauƙa Abba dan naga  Hotel yanada Kekkyawan tsari kuma a binciken da nayi naga yafi kusa da Companyn’ namu”.

Cikin gamsuwa Abba ce.

“Sosai ma kuwa, anan kusa da shine ma gidana yake inda nake sauƙa in nazo. Kaima dan ba’a gyarashi bane shiyasa”.

Miƙe tsaye yayi da wayar saƙale  a kafaɗarsa yace.

“Amman yanada tsada kam”.

Shi kuwa Abba gyara zama yayi tare da cewa.

“Ka zauna anan zuwa lokacin da za’a gyara gidana dake nan bayan hotel ɗin ƙadan, sai ka koma can, zan turo maka mai gadin gidan zai zo ya kawo maka key ɗin motar da zaka rinƙa zirya dashi, zai kuma nunnuma maka duk abubuwan da suka dace”.

cikin gamsuwa yace.

“Toh Abba sai yazo”.

Daga nan sukayi sallama.

Yana katse kiran yayi dearling number Innayi lokacin da kiran ya shiga Innayi na kan Sallaya bayan ta idar da sallan maghariba tana ganin kiran tace Alhamdulillah kana ta ɗaga tare da kaiwa kunnenta tace.

“Moddibo”.

Lumshe Idanunsa yayi tare da komawa yayi bakin gadon ya kishingiɗa kana yace.

“Na’am Innayi”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin murya tace.

“Fatan ka isa lafiya?”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Lafiya lau Alhamdulillah”.

Numfashi ta fesar kana tace.

“Masha Allah cikin Rabat kake ko kuma  cikin gefenta kake?”.

Cikin alamun gajiya yace.

“A’a cikin Rabat nake a tsakiyar garinma kuwa”.

Kai ta gyaɗa cikin sauke numfashi tace.

“Wace Unguwar?”.

Hannu yasa tare da shafa sumar kansa kana yace.

“Tsetse amman a hotel ne”.

Kai ta jinjina tare da sauke numfashi tace.

“Ayyah Tsetse kuma kai bansan Unguwar ba”.

Ware ido yayi tare da miƙewa daga kishingiɗar da yayi da mamaki yace.

“Dama to kinsan Rabat ne bare kisan Unguwannin su?”.

Cikin sauri ta girgiza kai kana tace.

“Um-um bansani ba amma ban taɓa jin sunan bane”.

Ahankali yace.

“Ayyah yanzu ina so inyi wanka ne”.

Kai ta gyaɗa cike da kulawa tace.

“Toh shikenan ahuta gajiya”.

Daga nan ya kira Ummi da Malam Arɗo bayan sun gama gaisawa ya shiga toilet, da ido yabi  turaren wanka Maclean brush towel pich colour yana kallo komai na ciki sabone Anutse ya fara wankan lokaci ɗaya yaji tsikar jikinsa na miƙewa sabida wanirin sanyin na ratsa baki ɗaya ilahirin jikinsa, cikin sauri yaja dogon tsaki Aransa kana yace.

Anya wannan aljanar yarinyar zata bar rayuwata ta nitsu kuwa, yarinya sai mata da nacin tsiya.

Towel ya janyo ya ɗaura kana ya ɗaura alwala ya fito dai-dai lokacin aka kira sallar Isha’i jikin Dressing mirrow ya nufa ya shafe jikinsa da mai kana ya fesa turare sa masu daɗin ƙamshi kana ya buɗe jakarsa ya ciro Jallabiya Sky blue me taushi kana ya ɗaura hirami kamar ɗankwali ya riƙe farin carbin sa sosai yayi kyau tun da aka sace M Jameel aka kashe sa bai sake yin wankan daya nutsu irin na yau ba yana fita ya nufi Masallaci akayi sallar Isha’i ana idarwa yayi adduo’i kana sai da aka wawwatse kafin ya fito ya nufi cikin  ƙoƙarin shiga ya haɗu da mai gadin na fitowa.

 

Kallonsa mai gadin yayi cike da girmamawa yace.

“Aliyu Youssef Mouley?”.

Ya faɗin sunan da sigar tambaya tare da duba hoton Modibbo da Abba ya tura mishi ta whatsapp.

Kai Modibbo ya haɗa mishi tare da bashi hannu.

Cikin fara’a mutum miƙo hannunsa tare da cewa.

“Assalamu alaikum Yah Mouley”.

Rumtse ido Modibbo yaui domin tunowa da Jalaladdeen ne kaɗai ke kiransa da wannan suna. Sai kuma ya ƙara rumtse idanun da ƙarfi, sabida tunowa da tsawon lokacin da baiji motsin Jalaladdeen ba, tun kafin a sace. Jameel, ya tabbatar babban abune kaɗai zai iya ritsa Jalaladdeen da har zai iya hanashi nemansu na tsawon wannan lokacin.

Cikin sauri ya buɗe idanunsa tare da gyaɗa tsayuwarsa yana jan Carbin hannunsa jin Mutumin na cewa.

“Sunana Habibullah nine mai gadin gidan Alh Bashir kuma nike kanshi in yazo duk inda zaije nike kaishi kuma nida matata ke zaune a BQ ɗin gidan”.

Kai Modibbo ya gyaɗa masa tare da cewa.

“Eh Abba ya gaya min”.

Jinjina kai mai gadin yayi tare da cewa.

“Ganan abinci  na kawo maka”.

Kallonsa Moddibo yayi da mamaki yace.

“Abinci kuma?”.

Kai mai ya gyaɗa alamar Eh.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da kallon womers ɗin hannunsa yace.

“Toh daga ina aka samu abincin?”.

Murmushi mai gadin yayi kana yace.

“Ai akwai abokin Alh anan lokacin da Marigayi Jameel yazo har ya koma daga can ake kawo masa abinci”.

Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyi yace.

“Ayyah yayi kyau angode”.

Sannan yayi gaba, mai gadin kuma na biye dashi.

 

Bisa kujerar ya zauna shi kuwa Habib kai tsaye dining area ya nufa kana ya ajiye mishi ɗan kondon da kulolin ke ciki, kana ya dawo gabanshi tare da miƙa mishi key ɗin mota tare da cewa.

“Ga wannan da ita zamana fita, in kuma baka son draving ga number’n ta sai ka Kur’ani, zanzo in kaika duk inda kakeso”.

Ya ƙare mgnar tare da miƙa masa hannunsa alamun ya bashi wayarsa ya saka mishi number’s.

Wayar ya miƙa mishi ba tare da yace komai ba.

Shi kuwa Habib number’s sa ya sawa wayar Modibbo kana ya miƙa mishi.

Amsa yayi tare da ajiye wayar.

Shi kuwa Habib sallama yasa kana ya miƙe ya ficee.

 

Shi kuwa Modibbo a hankali ya miƙe jin yadda cikinsa ke ƙugi alamun yunwa.

Dinning table ya nufa, kujerar yaja ya zauna tare da zuba abinci kana ya fara ci bayan ya gama ne ya dawo falon.

 

Lumshe yayi  dearling number Abba.

Bayan Abba ya ɗaga sun sake gaisawa ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da cewa.

“Toh Abba yanzu me ake ciki idan Allah yakai mu gobe dame dame za’a fara?”.

Kai Abba ya Girgiza cikin yanayin sanyin muryarsa yace.

“A’a Moddibo gobe kam ka huta tun da kaga yau  Alhamis gobe kuma jumma’a ne ba aiki a ƙasar tasu dan jumma’a da asabar ne ranakun hutun ƙarshen makonsu, shiyasa dama naso yau ka tafi ka kwana ka huta gobe ma huta sai jibi lahadi in Allah ya yarda zaka fara zuwa Company”.

Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

“Toh shikenan Abba Allah ya kaimu”.

Ameen Abba ya amsa kana sukayi sallama.

 

Miƙewa yayi akan kushin ɗin ya lumshe Idanunsa  a hankali yayi miƙa da alamun gajiya kasancewar yayi doguwar tafiya sannan dan kusan wuni yayi a zaune, da fari  akan ƙarfe tare jirginsu zai tashi. Ashe tun dare sun mishi text sun caza lokacin tashin sun meda sai biyu zasu tashi bai ganiba, saida yazo Airport ɗin, shiko yanaga komawa ciki wani jidaline shiyasa ya zauna anan kawai.

To hakan ne yasa ya wuni a zaune, shiyasa gaba ɗaya gaɓoɓinsa ciwo suke masa ahankali ya gyara kwanciyar sa still Idanunsa na lumshe cikin sauri ya miƙe kana ya tashi ya zauna numfashi mai zafi ya fesar, tsaki yaja kana ya miƙe tare da nufar ƙofan Falon ya fita yana mgnar zuci Mayya jarabebbiya nan ɗinma sai kin adaddabeni.

 

Ahankali ya tsirawa coumpund ɗin  ido zuwa wajen ganin yanda fitilu suka haska wajen kamar rana komai na hotel ɗin abin burgewane da ban sha’awa ne ahankali ya fara taka step ɗin farandar yana sauƙa kallon dattijon mai gadin dake zaune daga can wurinsa ya nufa,

Duk da tarin motocin dake wurin Hausa wurin ya cunkushe ba, yayinda kuma kowa harkar gabansa yake.

Hannu ya mikawa tsohon tare da yi mishi sallama.

Cikin tsananin girmamawa tsohon ma ya bashi hannu tare da zuba mishi ido cikin ƙare masa kallo.

Shi kuwa Modibbo a ya buɗe bakinsa tare da ɗan ɗaga sautin muryansa yanda zaiji yace.

“Baba”.

Miƙewa Dattijon yayi tare da da ɗan rusunawa kana ya ɗan ɗaura hannunsa na dama kan kirjinsa tare da ɗan sunkuyawa cike da tsananin girmamawar da ta fara bawa Modibbo haushi ya za’ayi dottijo kamar wannan yake kishi haka, in Habib ya mishi haka zai iya amsa sabida ya girmeshi.

Numfashi ya fesar tare da ɗan sakin fuska jin dottijon na cewa.

“Na’am Alh ya aka yi?”.

Gyara tsayuwar sa yayi kana yace.

“Baba kana zaune kai kaɗai ne?”.

Kai Dattijon mai gadin ya gyaɗa kana yace.

“Eh Alh gacan abokan aikina yanzu sune a bakin gate, ni sai da safe zan koma can kuma, yanzu anan nake”.

Ya ƙare mgnar yana buɗe wani mutun da yazo shiga, saida mutumin ya shiga kana ya kuma rufewa.

Girgiza kai Moddibo yayi yana kallon kalimin Dattijon numfashin ya fesar tare da cewa.

“Sunana Aliyu Youssef Muhammad Mouley, daga Nigeria amma kakata tana kirana da Moddibo zaka iya kirana Modibbo”.

Jinjina kai Dattijon mai gadin yayi yace.

“Ayyah Alh yayi kyau”.

 

Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin sanyin murya yace.

“A’a ba sai kace min Alh nan ba ka kirani da sunana kawai”.

Kai ya gyaɗa yana jinjina karamcinsa Aransa yace yana nan kamar ƙaninsa Ibrahim Youssef Muhammad Mouley. Ibrahim bashi da girman kai sai dai shi Ibrahim yafi wannan dariya afili kuma sai yace.

“Toh Moddibo”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Yawwa ai yafi sannan kuma akwai abinci da aka kawo min so naci yamin yawa, kaje ka ɗauka mana sai kaci sabida kada ya lalace!”.

Cikin tsananin mamaki da ganin tsananin karancin Dottijon ya haɗa kai, tare da amsar key ɗin ɗakin da Moddibo ke miƙa masa, cike da yarda aminci yace.

“Ngd Ngd matuƙa Modibbo, Allah ya kara girma ya kare zuriyar Mouley baki ɗaya”.

Gyara tsayuwa yayi tare da girgiza kai yace.

“Amin Ya Allah”.

Gefensa mai gadin yabi kana yace.

“Bari na ɗauka to”.

Ya faɗi tare da nufar cikin, cikin nitsuwa Modibbo yabi bayanshi.

Yana shiga falon ya dauko Warmers din sannan ya fita.

Cike da girmamawa Moddibo yace.

“Toh saida safe Baba”.

Mai gadin na fita yace.

“Allah ya tashe mu lafiya ahuta gajiya”.

Sannan ya fice.

 

Ahankali Moddibo ya rufe ƙofar falon tare da kashe wutan falon da Ac kana ya nufi Bedroom ɗinsa Kallon AC bedroom din yayi jin kamar yayi mishi yawa ne yasa hannun ya ɗauki rimot ɗin kana ya rage gudunshi.

 

Kwanciya yayi akan gadon tare da lumshe Idanunsa cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da dafe ƙasan  lokaci ɗaya zuciyarsa da jikinsa sunka harba a tare, baki ɗaya ya fahimci wannan muguwar yarinya haka zatayi ta addabar rayuwarsa kenan.

awannan rana dai haka ya kwana cikin wani irin yanayi bacci rabi da rabi yayi.

Washe gari Jumma’a haka ya wani cikin hotel din sai sallan jumma’a da ya fita ana isarwa ya dawo, daga nan ko  bakin titin hotel ɗin bai leƙaba.

masallaci ne kaɗai ke fitar dashi.

 

Hakan yayi kwana biyu yana hutawansa.

Yau Lahadi a bisa tsarin ƙasar Marocco yau ɗin ne forkon sati.

Ƙarfe takwas ya samu Moddibo acikin Company Abba bisa jagorancin Habib.

Yana isa suka fara aiki gadan-gadan aiki ake tako ina babu kama ƙafar yaro domin dama sa hannunsa kawai ake kira da sahalewarsa a matsayinsa na mataimakin MD duk sabbin Injina da aka kawo aka shiga daddasasu da duk wasu gyare-gyare daya kama suka shiga yi domin samun asabunta Company da habaƙashi don har buga atamfofi, Laces, Mayafain laffaya da duk sauran abubuwan buƙata suke so  farawa.

Domin shine Company na farko da aka buɗe sa acikin Rabat wanda aka haɓakasa sannan ake inganta kayyakinsu.

Bai bar cikin Company ba sai shida saura kwata kai tsaye masauƙin ya wuce yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa gate yana Parking suka gaisa.

 

Kana ya wuce yayi ciki. kai tsaye Bedroom ya wuce ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito Masallaci kasancewar ankira Maghariba bai fito ba saida akayi Isha’i kafin ya dawo yaci abinci da Habib ya kawo masa. bayan ya kammala ya ɗauko system ɗin sa ya tura Abba duk yanda sukayi tsare-tsaren abubuwan da kuma hotunan yanda abubuwan suka tafi sosai yayiwa Abba bayanin sannan Abba ya kara masa haske akan sauran abubuwan sai misalin shaɗaya ya tashi yana jin wani irin kasala bini-bini zaiyi miƙa tare da hamma kai tsaye toilet ya nufa ya watsa ruwa.

Anutse ya fito tare da kumtsaawa, kana ya kwanta akan gado tare da lumshe idanunsa tsikar jikinsa na tashi sanyin AC da ƙamshin Roomfreshner da kuma ƙamshin tularensa shi yasake haddasa masa jin wani masifaffen kasala cikin wani irin yanayi ya ƙudundune tamkar yaro lokaci ɗaya bacci yayi awon gaba dashi.

A hankali yake juye-juye yana mai jin da ganin abin kamar a mafarki kamar kuma a zahiri.

Kanshi longwaɓar cikin narkekkiyar murya yace.

“Zakeeh kasheni fa”.

Cikin tsoro tace.

“Ana asped Yah Mu’allim”.

Kai a jujjuya mata tare da cewa.

“Kije keda Allah, kiyi ta dakon zunubi, kina sane dai in har ban yafe mikiba cikin fushin Allah zaki kwana”.

Da sauri ta ƙara kwaɓe fuska, tare da cewa.

“Dan Allah Yah Mu’allim kayi haƙuri ka yafe min, nayi maka al’ƙwari ina nan tafe zanzo gare cikin aminci da rakiyar amintattu a ranar nayi al’ƙawarin gujewa fushin Ubangiji a ranar kada ka ɗaga min ƙafa ka mallaki dukkan ƙudurinka”.

Wani irin mataccen murmushi yayi tare da cewa.

“Yaushe ne ranar?”.

Da sauri tace.

“Nan kusa take”.

Wani irin kallo yayi mata tare da cewa.

“Ranar yaushe ce”.

A hankali tace.

“Raanar larabace ce”.

Cikin wani irin kallo yace.

“Na’amin ce, tunda al’ƙawari kikayi”.

Cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet cikin mawuyacin hali ya ɗago idanunsa dake cike da feeling kana muryarsa na rawa yace.

“Pleaassss Hayatieee kada ki saɓa min al’ƙawarin dan idan kika saɓa min a wannan ranar”.

Girgiza kai Khausar tayi cikin kuka da raunin murya tace.

“Bazaka mutuba”.

Amatuƙar galabaici ya yunƙura da niyyar binta tayi saurin rufe kofar toilet.

 

Akuma dai-dai lokacin ya farka da wani irin azabebben kasala dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yayin da Idanunsa suka cika da ruwan hawaye haka ya kwana cikin mawuyacin hali Allah ya sani ya fara ganin yarinyar  aljana.

 

Washegari da sassafe ya tashi yayi wanka kana ya shirya cikin gezner fari ƙal da ya fito da ainihin kyawunsa Anutse ya fito falon hannunsa riƙe da Breafcase a dining area ya tsaya tare da buɗe Warmers din da Habib ya jere Wainar shinkafa ce da miyar taushe sai kuma soyayyan Arish da tea Wainar yaci kana yasha tea bayan ya gama ya mike tare da ɗaukar Breafcase ɗinsa da wayoyinsa da kuma mukullin motarsa kai tsaye Company ya nufa.

 

 

Gembila

 

Aɓangaren Abban sosai hankalinsa ya dan kwanta fahimtar lallai Moddibo yana aiki gadan-gadan bisa tsari da hikima komai na tafiya dai-dai.

Numfashi ya fesar tare da ciro wayarsa yayi dearling number Malam Arɗo bayan ya dauka sun gaisa.

Abba ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.

“Yau kusan kwana shida kenan da zuwan mu gidan Lamiɗo akan maganar Aliyu da Khausar amma har yau bamuji ya sake neman muba amma tunda mu muke da buƙata yakama muji ta bakinsa”.

Ya gyara zamansa wayar akunnensa kana ya cigaba da cewa.

“Musamman ma da yanzu na tura Aliyu Marocco yana rayuwa shi kaɗai ya kamata ace anyi ƙoƙari anyi batun auren nan saboda kaɗai ci da damuwa zaiyi masa yawa”.

Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da gamsuwa yace.

“Nima abinda nake tunani kenan amma Insha Allahu gobe zamuje da daddare idan Allah ya kaimu rai da Lafiya”.

Ahankali Abba ya jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.

“Toh Allah ya kaimu bisa rai da Lafiya”.

Ameen malam Arɗo ya amsa kana suka katse kiran.

 

*Jauro Yaya*

 

Hajja Nana ce zaune ta tanƙwashe ƙafafunta Baffa Garga dake gefenta yayi Murmushi yana kallonta yace.

“Addah Nana ɗazu nayi magana da Hammadu”.

Kallonsa tayi tare da kawar da kai gefe tace.

“Ya masa kyau”.

Murmushin Baffa Garga ya faɗaɗa yana kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska sassauta murya yayi kana yace In gaishe ki”.

Taɓe baki tayi ba yabo ba fallasa tace.

“Idan ya damu da gaisuwar ai sai yazo inda  nake”.

Gyara zama Baffa Garga yayi kana yace.

“Addah Nana ai yace ma zai zo In sha Allahu gobe da safe zaiyi sammako yazo”.

Sassauta fuskarta tayi kana tace.

“Toh Allah ya kawo shi lafiya”.

Ameen Baffa Garga ya amsa tare da ɗauko mata wani hiran.

 

Washe gari:Asuban fari Baffa Jimeta yayi sammako ya ɗauko hanyar Taraba duk da sammako da yayi sai ƙarfe biyar da rabi ya isa Jauro yaya Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar juna koda wasa bai kawowa Hajja Nana maganar Khausar ba sai bayan sallar Isha’i bayan sun ci abinci sun zauna da mahaifiyarsa da kuma Kawunnansa ana hira.

 

Ahankali ya gyara zamansa kana ya tanƙwashe ƙafafunsa agabanta ya karyar da wuyarsa cikin sanyin murya yace.

“Hajja Nana alfarma nake nema awajenki”.

Kallon second ukun tayi masa kana tace.

“Ni kuma wace alfarma zanyi maka ai da har ina da abinda zaka nemi alfarma awajena Umarni na zaka bi”.

Ahankali ya sassauta muryarsa yace.

“Ai yanzu ma Umarnin ki nake bi Hajja Nana Ni dai temako nema”.

Kallonsa tayi kana tace.

“Taimako akan me?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin ƙasa da kansa yace.

“Taimako akan Marainiyar Allah”.

Baki ta buɗe tare da kallon ƙannenta sai kuma ta kallesa tace.

“Ai kowa ma Maraya ne sannan kowa ma zai iya kasancewa Maraya”.

Kai ya gyaɗa yana kallon yanda take jijjiga ƙafa yace.

“Eh nasani amma akan Khausar nake magana Hajja Nana nazo ne in sake Baki haƙuri akan laifin data aikata sannan muyi mata uzuri matsayinta na yarinya ƙarama”.

Kai ta gyaɗa ba yabo ba fallasa tace.

“Shikenan komai ya wuce tunda Ni ban kaiba Ni kaka ce kun nuna min bani da matsayi sannan banida ikon faɗa aji”.

Da sauri Baffa Jimeta ya kalleta amma baice komai ba ta cigaba da cewa.

“Acikin maganar rayuwar Khausar to ba matsala na cire hannuna ta Auri duk wanda taga dama take so Ni bani da damuwa aciki na janye hannu na tunda haka kuke buƙata”.

Numfashi Baffa Jimeta ya fesar cikin kwantar da murya yace.

“Toh shikenan kiyi haƙuri ki sanya Albarka aciki”.

Taɓe baki tayi kana tace.

“Zansa al’barka ai tunda bazan sa tsinuwa ba Ni dai babu bakina aciki sannan babu batub aurenta da wancan ɗan gaba da fatihan kam”.

Kai ya girgiza cikin sassauta murya yace.

“Mu dai kiyi haƙuri dan Allah kiyi haƙuri kiyi mana fatan alkhairi aciki”.

Ahankali ta kallesa kana tace.

“Toh Allah ya kyauta ya kiyaye gaba dama maganar data kawo ka kenan??”.

Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yace.

“A’a bashi bane ya kawoni kewar ki nayi shine nace bari nazo in gaisheki”.

Hararansa tayi tare da kallon sauran ƙannenta tace.

“Oho dai”.

 

Akuma dai-dai lokacin Malam Arɗo,Malam Ahmad da Abba ne zaune afalon Lamiɗo bayan sun gaisa sannan suka yimasa jawabi kan cewa sunji shiru shiru bai sake neman suba yasa suka dawo.

Anutse Lamiɗo ya gyara zama cike da dattako yace.

“Badamuwa Insha Allahu dama nima ina shirin zan ne meku ɗin saboda bani da ikon bada ita akaran kaina amma munyi magana da Baffan yarinya yau ɗin nan ma yazo daga can Adamawa zai nemi sahalewar kakar yarinya”.

Ajiyar zuciya suka sauƙe atare Kallonsu Lamiɗo yayi kana ya cigaba da cewa.

“Dake Itace taso kawo tangarɗa acikin al’amarin amma yace zaiji da lamarin duk abinda ake ciki yace min Insha Allahu gobe muyi ƙoƙari muje gamu gashi gata ya zama na munje neman Auren ne”.

Numfashi Malam Ahmad yafesar kana yace.

“To ai wannan duk mai sauƙi ne badamuwa za’ayi hakan”.

Kai Abba ya gyaɗa kana tare da faɗin.

“Bakomai Insha Allah goben zamuje”.

Murmushi Lamiɗo yayi cike da kamala yace.

“Eh zamu bari gobe idan munyi sallar Azahar sai muje kafin nan ya tattauna da mahaifiyarsa idan anyi sa’a abin zai zo da sauƙi dake shi yana da kyakkyawar fahimta sannan bashi da son zuciya”.

Jinjina kai Malam Arɗo yayi idanunsa akan Lamiɗo yace.

“Ba matsala Insha Allah nima ina da ƙafa agarinsu dan Malamin dana ke zuwa ɗaukan karatu awajensa ai ƙanin Kakarta ce kuma sunzo wajena tare shima nasan yana da kawaici, kara da dattako”.

Jinjina kai sukayi tare da tsaida magana akan washe gari Bayan Sallar Azahar zasu tafi.

 

Washe gari baki ɗayansu suka shirya har Mommy da Khausar Lamiɗo yace su shirya atafi dasu Khausar da Mommy suna motar Lamiɗo Malam Arɗo da Malam Ahmad suna motar Abba kai tsaye suka dauki hanyar Jauro yaya suna isa Jauro yaua kai tsaye gidan Hajja Nana suka nufa dai-dai lokacin dasu Baffa Jimeta suka fito daga sallar La’asar Malam Liman na ganin Malam Arɗo ya faɗaɗa fara’ar fuskarsa kana yace.

“A’a Malam marhaban lale sannunku da zuwa”.

Baffa Jimeta kuwa cikin sauri ya nufi Lamiɗo tare da miƙa masa hannu yace.

“A’a Sannunku da zuwa har kuzo kenan?”.

Murmushi Lamiɗo yayi cikin yanayin dattako da kamalarsa yace.

“Eyyy sosai ma ai ba’a bori da sanyin jiki”.

Abba dake tsaye jikin mota yace.

“Aikam dai ba’a Bori da sanyin jiki”.

Baffa Garga da fitowarsa daga masallaci kenan yace.

“A masha Allah harda  Alh Usman mai Dala ne a Lallai sannun ku da zuwa maraba maraba ku karaso?”.

Ya faɗa tare da shigewa gaba kasancewar yanzu shine ƙarami tun bayan rasuwar Baffa Umaru yana shiga ciki yace.

“Addah Hajja abamu taburmai munyi baƙi”.

Miƙewa tayi daga zaune da take da murmushi afuskarta ta ɗauko taburmai ta miƙa masa karɓa yayi kana ya shimfiɗa musu Abaranda.

 

Daga ciki tace.

“Aaa baƙi mukayi sannunku da zuwa sannunku”.

Tana ƙoƙarin fita Khausar da Mommy Kuma na kokarin shiga Atake fara’ar dake fuskarta ya gushe Harara ta watsawa Khausar sai kuma ta maida kallonta kan Mommy tace.

“A Aysha kune atafe?”.

Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

“Eh”.

Sannan suka shiga cikin dakin mazan kuma Baffa Garga ya shimfida musu taburmai daga waje.

Koma ciki Hajja Nana tayi tare da ɗaukan ƙwaryar nono da ƙorron soyayyan Zabbi da aka yiwa Baffa Jimeta na zuwansa ta kalli Khausar dake gefen Mommy zaune haɗe fuska tayi babu walwala atare da ita tace.

“Toh fitsararriya uwar fitsararru zoki kai musu abin taɓawa kin zauna kina zare ido sai kace wata ta Allah rasa kunya ɓerar tanka”.

Uffan khausar bata ce mata ba ta miƙe ta ɗauki Ƙorran ta fita ta kai musu sannan ta dawo wani ƙorron Hajja Nana ta miƙa wa Mommy kana tace.

“Aysha Bismillah”.

 

Kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska Khausar tayi taɓe baki tayi cikin tsira mata ido tace.

“Hajja Nana Ni kar inci ne?”.

Harara ta watsa mata kana tace.

“Duk yanda kika ga dama kiyi”.

Ware ido Khausar tayi ta kalli Hajja Nana data kawar da kai gefe murmushi tayi cikin sanyin Murya tace.

“A’a Idan kada inci sai inbar miki kayanki”.

Baki Hajja Nana ta taɓe kana tace.

“Oho cikin ko nawa  fitsararriya Mara kunya mai ido atsakar ka”.

 

Fuska Khausar ta ɓata ta buɗe baki da niyyar magana Mommy tayi saurin ɗaga mata hannu alamar kada tace komai hakan yasa ta tsuke bakinta Mommy kuwa kindirmon ta ɗaga ta burga kana tasa sugar.

 

Daga waje Lamiɗo yace.

“Khausar fito mana ki burga mana Nonon”.

Kai Baffa Garga ya Girgiza kana yace.

“Ba matsala bari na burga muku”.

Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.

“A’a bari dai ita ɗin tazo ta burga mana”.

Miƙewa Khausar tayi tare da ɗaukan goran zuwa ta fita ta burga musu Nonon kana ta zuba musu zumar sannan ta miƙe ta koma ɗaki bayan sun gama taɓe taɓe an sake gaisawa Lamiɗo ya kalli Baffa Jimeta cikin sassauta murya yace.

“Toh Alh Muhammadu Hausawa sunce maso ɗan tsun-tsu shike binsa da jifa, mun zo wajenku neman yafiya, afuwa da kuma alfarma sannan da neman iri domin nima ina cikin ƴan neman Auren ne”.

 

Cikin sauri Baffa Jimeta yayi dariya kana ya girgiza kai tare da kallon Lamiɗo yace.

“Haba Lamiɗo ba zamuyi haka da kaiba ai kai mai bada Auren Khausar ne baka cikin masu neman aure kana cikin masu bada Auren Khausar ne”.

Murmushi Lamiɗo yayi cike da jin daɗin karancinsu yace.

“Nagode da karamci”.

Gyara zama Baffa Jimeta yayi da murmushi afuskarsa yace.

“Ka cancanci fiye da hakan Lamiɗo”.

Jinjina kai Baffa Liman yayi cike da kamala yace.

“Ai mu saidai muyi addu’a da fatan alkhairi amma kaine mai bada Khausar”.

Cikin jin dadi yace.

“Nagode da kawaici Allah yasaka da alkhairi”.

 

Gyara zama Malam Arɗo yayi da murmushi afuskarsa yace.

“Toh mu mun yarda mun amince mune masu neman Aure”.

Abba dake Kallonsu ya faɗaɗa Murmushin fuskarsa kana yace.

“Mune masu neman aure da kuma neman iri agareku bisa cika wasiyyar da ɗana ya bari ina fatan zan samu sauki da haɗin kanku wajen cikawa ɗana burinsa koda bayan ransa kamar yanda ya faɗa min”.

Ya ida maganar cikin rauni idanunsa na tara ƙwalla.

 

Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauke cike da tausayawa yace.

“Bakomai Alh Bashir Insha Allah babu abinda zai gagara aida mu daku duk mun zama ɗaya Lamiɗo yamin bayanin duk abinda ke tafiya kan cewa wasiyya ce daga wajen danƙa marigayi Jameelu”.

Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa hawaye na cigaba da taruwa akwarmin Idanunsa.

Cikin sanyi Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.

“Insha Allah bazai gagara ba zamuyi ƙoƙari amma yanzu kuyi haƙuri da al’amarin tsohuwa in Allah ya yarda babu abinda zai gagara”.

 

Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke tare da gyara zamansa yace.

“Allah Ubangiji yasa haka mukam ma da gwaɓin mu muka zo duk da cewa akwai tsoro atare damu amma muna da kyakkyawan yaƙini akanku hakan yasa kafin muzo muka taho da gishiri da goro na neman izini”.

Murmushi Malam Liman yayi yana kallon Lamiɗo yace.

“Lallai kuwa zamu barku da Hajja Nana ku fafata”.

Zare da ido Lamiɗo yayi tare da sanya dariya kana cikin sauri yace.

“Na tuba ayimin afuwa ai Hajja Nana saiku zakuji da ita”.

 

Gyara zama Malam Liman yayi cike da nutsuwa yace.

“Insha Allah itama munyi ƙoƙari mun samu ta ɗan sauko amma duk da haka akwai karin ɗan lokaci da za’a bayar”.

 

Anutse Mommy ta gyara zamanta tare da kallon Hajja Nana cikin sanyin murya tace.

“Dan Allah Hajja Nana kiyi haƙuri abinda ya kawo mu nazo ne in baki haƙuri naga kin tafi ranki aɓace abinda Khausar ta aikata ba laifi na bane ba kuma da yawuna bane”.

Ta ida maganar Muryanta na rawa tamkar zata fashe da kuka.

Hajja Nana kuwa jin yanda Muryan Mommy ke rawa yasa tayi saurin Kallonta har ranta take Jin Mommy domin alokacin zamansu tasan bata da matsala cike da kulawa tace.

“Kar kiyi kuka Aysha aina zauna dake nasan halinki fitsaran Khausar ba daga gareki bane kuma ba daga Allah bane halitta ce da tayiwa kanta”.

Cikin sauri Khausar ta ɗago kanta ta watsa mata Harara cikin ƙasa da murya tace.

“Inma tsiwarce ai awajenki na gada”.

Harara Mommy ta watsa mata hakan yasa ta tsuke bakinta.

Ahankali Mommy ta sauƙe Ajiyar zuciya kana ta fuskanci Hajja Nana cikin sassauta murya tace.

“Itama kanta Khausar al’amarin yazo mata adolene”.

Baki Hajja Nana ta taɓe kana tace.

“Bangane yazo mata adole ba inace soyayya take da wani can yasa ta kalli tsabar idona tace bata son ɗan Uwanta”.

Kai Mommy ta Girgiza kana ta kwashe duk yanda Khausar ta faɗa mata sunyi da M Jameel aranan da aka sace sa kana ta daura da faɗin.

“Sannan kuma yaron shine ƴan Kidnapping suka sace sa suka ɗauresa har ya rasu”.

Ahankali Khausar tayi ƙasa da kanta hawaye na taruwa akwarmin Idanunta.

Cikin sanyi Mommy ta cigaba da cewa.

“Sai maganar tasa ta zama kamar wasiyya kuma ya roƙi alfarma ya faɗawa kakar Amininsa Moddibo kana Ya faɗawa mahaifiyarsa da mahaifinsa yanzu ma haka da mahaifinsa muka zo kuma yace alfarma yake nema ko bayan ransa acika masa wannan burin nasa, jin haka yasa nima baki ɗaya jikina yayi sanyi”.

Numfashi Hajja Nana ta fesar kana tayi ƙasa da kanta cikin sanyin murya tace.

“Allah sarki shine akace ansace sa a daure sa ya rasu ko?”.

Asanyaye Mommy ta gyaɗa mata kai tare da faɗin.

“Eh shine aka sace aka ɗaure har ya rasu”.

Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da watsawa Khausar Harara ta kalli Mommy cikin raunin murya tace.

“Ayyah Allah sarki Allah yajiƙan sa da rahma ina ma ace yana raye dashi zan bawa Khausar ya aura wallahi koda Khausar bata auri Aliyu ba bazan damu ba”.

Cikin raunin murya Mommy tace.

“Gashi kuma shi ɗin Ubangiji bai nufa za ayi dashi ba, babu gatan da zamuyi masa sai dai addu’a”.

Jinjina kai Hajja Nana tayi cikin sanyi tace.

“Sosai ma”.

Mommy kuwa sassauta murya tayi kana tayi ƙasa da kanta tace.

“Kuma inda hali mu samu mu cika masa wasiyyar daya bari”.

Gyara zama Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar da kanta ke ƙasa kana ta kalli Mommy nunfashi ta fesar cikin sanyin murya tace.

“To aini bani da tacewa acikin wannan maganar sai abinda iyayenta suka faɗa tunda annuna min bani da iko da ita”.

 

Dai-dai lokacin Baffa Jimeta ya shigo Anutse ya zauna gefenta ya tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta da kyau yace.

“Kina da iko da ita mana muma kam mu aike kike da iko damu amma ana neman alfarma awajenki gacan Baban yaron ma awaje sai hawaye yake zubarwa yana neman alfarma acikawa dansa wasiyyar sa”.

Daga waje ta jiyo sheshsheƙan Kukan Abba cikin sauri ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita kusa dashi ta zauna cike da tausayawa tace.

“Kuka kuma kake Alh Bashir?”.

Cikin sheshsheƙa Abba yace.

“Ya za ayi ba zanyi kuka ba burin da Jameeluna da kuma fatan da yake so yana tangarɗa koda aranan da muka rabu na ƙarshe yace min shine babban burinsa daya rage aduniya”.

Cikin zubda hawaye ya cigaba da cewa.

“Yace babban burinsa yaga Moddibo yayi Aure kafin nasa Saboda Aliyu yana buƙatar mace yana buƙatar ayi masa Aure sai dai Allah bai nufa Jameelu na zai gani ba ina tsoro saboda bani da damar da zan cika masa wasiyarsa”.

Gyara zama Hajja Nana tayi kana ta gyara ɗaurin dankwalinta ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ahankali ta ɗago Muryanta na rawa tace.

“Na amince ina dai dan nice. To acikawa yaron nan burinsa Allah yajiƙan sa da rahama na amince Ayi aure…

 

 

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP NUMBER’N 09097853276.

 

 

By

*GARKUWAR FULANI*

Leave a Reply

Back to top button