Sakayyah 36
SAKAYAH
36
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Alamomin infection sune kamar haka*. Rashin sha’awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni’ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al’ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni’ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin yana kwaranya. Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA sai ya gama yi miki illah. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni’imomin ki, da sha’awarki, duk kyan kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA’AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha’awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor’s suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin sherrin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi’izinillahi ta’ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa dole kema ki nace masa da maganin mu, set ɗin10k ne kuma maganin kala biyarne nasha kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin indai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma’ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya’ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba dan kun kai mishi amarya a rarake bayan kun san kuɗin sadaki ya ƙara sama. Saboda yanayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi a 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER’N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA’AURATA.
Cikin yanayin ɓacin rai Mommy ta ture kanta dake kan cinyar ta babu walwala atare da ita tace.
“To ai shikenan Khausar hankalinki ya kwanta, zagine da abin kunya kunja min, kukan me kuma zaki zo kina min, in banda rashin hankali dama rashin kunya Khausar yaushe Moddibo yace yana sonki yaushe Moddibo ya taɓa zuwa wajenki?”.
Kasa cewa komai Khausar tayi sai hawaye dake cigaba da kwaranya a Idanunta Shar-shar.
Cike da takaici Mommy ta cigaba da cewa.
“Mutumin da ko Amakaranta tsakaninki dashi sai dai faɗa kyara da hantara. Duk abinda ke faruwa ina sane ai ana bani labari amma saboda tsabar shashanci ki rasa wanda zaki ce kina so sai mutumin da bakwa zama inuwa ɗaya!”.
Kuka sosai Khausar ta fashe dashi cikin sheshsheƙan Kukan tace.
“Wallahi Mommy ba haka bane dan Allah ki tsaya ki saurareni”.
Kai Mommy ta Girgiza tare da tsira mata Ido tace.
“Hmmm Khausar kenan me zan saurara kuma, ai babu abinda zanji daga gareki tunda ke kika haifi kanki ke zaki yankewa kanki hukunci sannan ke zaki zaɓawa kanki miji wai ki kalli tsabar Idanunmu saboda tsaurin Ido kice Modibbo kike so to yaushe yace yana sonki?”.
Girgiza kai kawai tayi cikin matsanancin kuka da tashin hankali tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri wallahi ba rashin kunya bane dolene yasa haka Mommy ki sanya mana al’barka acikin rayuwar auren da zamu yi”.
Cike da takaici Mommy ta kalleta kana tace.
“Toh Khausar tambayar da zan miki Moddibo yace yana sonki ko kuma ke kike haukanki?”.
Girgiza kai Khausar tayi cikin rawan murya tace.
“Mommy I don’t know either he love me or not”.
Miƙewa Mommy tayi tare da jan dogon tsaki ta fice daga ɗakin ta nufi Falon Lamiɗo.
Khausar kuwa kanta ta kife ajikin katifa ta fashe da sassayan kuka tana sheshsheƙa Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da kallon Khausar cikin sanyin murya da rashin fahimta yace.
“Addah Khausi ban fahimci abinda Mommy take faɗa ba wai Malam Moddibo kike so ko kuma wa?”.
Kai ta gyaɗa masa Muryanta na rawa tace.
“Eh shi nake so”.
Zare ido Haiydar yayi tare da sanya salati kana yace.
“Toh shi Malam Moddibo yana sonki ne?,”.
Kai Khausar ta girgiza tare da ɗago Idanunta dake jiƙe da hawaye cikin raunin murya tace.
“Ban saniba Haiydar I really don’t know”.
Cike da matsanancin mamaki da damuwa Haiydar yace.
“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Khausar baki sani ba kuma?”.
Jinjina kai Khausar tayi cikin raunin murya tace.
“Bansani ba Haiydar Bansani ba Haiydar”.
Miƙewa Haiydar yayi cike da takaici yaja dogon tsaki tare da faɗin.
“Wallahi dama nasan hakane babu abinda zaisa in rakoki wajen Mommy”.
Ya ida maganar tare da ficewa cike da takaici da ban haushi.
Cikin rauni Khausar ta miƙe tare da nufar Bedroom ɗinta tana shiga ta faɗa bisa gado tare da sakin kuka mai masifar ɗaci da ƙuna.
Mommy kuwa kai tsaye falon Lamiɗo ta nufa bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zaune ta samu Abba akan 2sitter.
Anutse Lamiɗo ya ɗago kansa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.
“Shatu Ikon Allah mai kuma ya ɓatawa Gimbiya Aysha rai”.
Fuska Mommy ta ɓata tare da narkar da murya kana tace.
“Na lura ma al’amarin Khausar dariya yake baka, baki ɗaya tun jiya Yarinyar nan ta ɓata min rai ta hargitsa min lissafi, sam kakarta bata da kirki tsohuwa ce mai zafi ta saba da iko da gadara akan ƙannenta ta saba da maganar ta kamar yankan wuƙace”.
Kallonta kawai Lamiɗo yake yana murmushi.
Cikin yanayin damuwa ta cigaba da cewa.
“Duk abinda ta faɗa haka ne babu wanda ya isa ya musan ta mata gashi Khausar tazo tayi mata abinda bashi neba ta tafi tana zagina yanzu tana zuwa Rugar nan zata baza sunan Khausar hakan zanji daɗi ne?”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da gyara zaman sa kana ya miƙa mata hannunsa tare da cewa taho nan zo nan Shatuna”.
Maƙe kafaɗa tayi tare da tura baki kana ta narkar da fuska.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
“Ki zauna mana”.
Kallonsa kawai take amma ba tace Uffan ba.
Ahankali ya sanya hannunsa ya janyo tsintsiyar hannunta tare da zaunar da ita agefen sa cikin sanyin murya yace.
“To amma ai akwai abinda baki sani ba”.
Asanyaye ta kallesa tare da cewa.
“Toh menene ban sani ba?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira mata ido kana yace.
“Jiya Hajja Nana bata bani dama inyi mata Magana ba saboda yanda ta ɗauki abin da zafi take ta ihu da kururuwa da Masifa sannan dole mu bita ayanda taso”.
Jinjina Kai Mommy tayi tare da sauƙe numfashi.
Cikin sanyin Murya ya cigaba da cewa.
“Tun da kinga tsohuwa ce sannan tana da ƙarfin iko akan Khausar babu yanda muka iya, amma Baffanta ya fahimta domin yau kafin ya koma Ɓadamaya yabiyo nan munyi magana dashi”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya kalli Mommy da itama shi take kallo yace.
“Sannan yace ba zai mata dole ba kamar yanda idan Mahaifinta yana raye ba zai mata dole ba kamar yanda zai yiwa ƴaƴan sa haka zai mata saboda yana da ƴaƴa mata da yawa kamar yanda bai musu dole ba haka itama ba zai mata dole ba dan mahaifinta baya raye”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.
“Na sani shi yana da fahimta, amma ita tsohuwar ce gaba ɗaya ba zata fahimta ba”.
Lakace mata hanci Lamiɗo yayi kana da murmushi afuskarsa yace.
“Kada ki damu ɗan zai fahimtar da ita, dan yace ya bata haƙuri sannan idan ta huce zai sake dawowa ya bata haƙuri kuma Insha Allah zata fahimta”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da gyara zamanta kana tace.
“Toh naji ta wannan gefen an samu fahimta amma fa Moddibo baya Son Khausar din ita da bakinta fa tace min bata san yana sonta ko baya sonta ba, ka taɓa ganin Moddibo yazo wajen Khausar ne?”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da cewa.
“Eh na taɓa gani mana kwanaki sunzo da Asma’u”.
Girgiza kai Mommy tayi tare da fesar da numfashi kana tace.
“Zuwan da kaga yayi ta’aziyyan Ramadan yazo min domin yace alokacin da suka zo yimin ta’aziyya sun haɗu da Ori da ya muku bayani gawar Jameel toh sun fita bai shigo ya min ta’aziyya ba, shine suka zo da Asma’u yamin amma fa baice yana son Khausar ba hasalima Khausar da Moddibo basa zama inuwa ɗaya”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da gyara zamansa ya fuskanceta tare da cewa.
“Ki nutsu mana Ni nafi so ki nutsu Ayshatu idan kin nutsu sai in miki bayani”.
Marairaice fuska tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.
“Toh ai yanzu ma Anutse nake ranka shi daɗe kai nake sauraro”.
Murmushi yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Jiya ma hargowar Hajja Nana ce ya hana in miki bayani shekaran jiya baki ji cewa nayi baƙi ba?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh naji”.
Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauke kana ahankali yace.
“Toh Malam, Arɗo ne da Alh Bashir mai Dala Mahaifin marigayi Malam Jameel da kuma Malam Ahmad Baban Asma’u suka zo”.
Jinjina kai Mommy tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Ooh sune suka zo!?”..
Kai ya gyaɗa mata still hannunsa na cikin nata yace.
“Eh”.
fesar da numfashi yayi kama yace.
“Toh kinsan me yaka wo su?”.
Kai ta Girgiza kana tace.
“A’a sai ka faɗa”.
Atake yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi zuwa rauni cikin sanyin murya da rauni yace.
“Magana suka zo akan wasiyyar da Marigayi Jameelu ya bari”.
Saurin Kallonsa Mommy tayi cikin sanyin murya da damuwa tace.
“Wasiyya kuma!?”.
Jinjina mata kai Lamiɗo yayi tare da fesar da numfashi kana yace.
“Eh”.
Ahankali tace.
“Wasiyya kuma Jameel ya bari akan me!?”.
Zamansa ya gyara tare da janye hannunsa ɗaya daga cikin na Mommy ya dafe goshinsa cikin raunin murya yace.
“Jameel yabar wasiyya ne akan Moddibo da Khausar”.
Lokaci ɗaya idanun Mommy suka ciko da Hawaye cikin raunin murya tace.
“Wasiyya akan Moddibo da Khausar kuma to akan me?”.
Jinjina mata kai yayi still muryarsa Araunane yace.
“Tabbas Mahaifinsa ya faɗa min cewa akwai ranan da suka je shi da Moddibo gidansa alokacin saura kwana uku asace sa har yake faɗa masa yafa zaɓawa Moddibo matar da zai Aura Amma shi kansa Moddibo bai sani ba domin koda Jameel ya faɗa murmushi Moddibo yayi alokacin har yake cewa Alhaji Bashiru. Abba kaji fa wai ni J zai za ɓawa mata kamar wani yaro ko makaho”.
Lumshe ido Lamiɗo yayi cikin rauni ya cigaba da cewa.
“Alokacin Abban sa yace ya faɗa masa wace mata ce sai Jameelu yayi dariya yace sai ya dawo asirri zai faɗa masa to bayan da ya dawo sai yace wa mahaifinsa dan Allah Abba ina neman alfarma acikin kwanakin nan domin wata ƙila akwai abinda zai iya faruwa acikin kwanakin nan wataƙil agaban ido na wataƙil kuma abayan Idona”.
Cikin sauri Mommy ta rintse Idanunta Hawaye masu zafi suka zubo mata ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe kana yace.
“A lokacin sai mahaifinsa yace.
“In sha Allah a gaban idon ka nema Jameeluna ina zakaje”.
Sai yayi murumshi tare da sunkuyar da kansa murya a sanyaye yace.
“Wata ƙil kafin nan na tafi Marocco ko wata duniyar. Dan haka ga mata na zaɓawa Moddibo koda bayan bana nan Abba ayi ƙoƙari ahaɗa auren Moddibo da Khausar sai Abban sa yace to Meyesa kace haka sai yace wa Mahaifinsa shi dai yana fata kuma yana buri ahaɗa auren Moddibo da Khausar domin Moddibo yana ɓuƙatar Aure fiye dashi shiyasa ya fara yi masa zaɓin mata”.
A hankali Lamiɗo ya fesar da numfashi mai zafi kana ya cigaba da cewa.
“Sannan Marigayi Jameelu ya sanar da mahaifiyarsa maganar kana ya sanar da Kakar Moddibo maganar har ta kira Malam Arɗo ta sanar dashi maganar domin wasiyya ce alokacin yake cewa ayi ƙoƙari ayi auren cikin gaggawa domin Moddibo yana bukatar aure shiyasa yake so ayi kokari ayi auren cikin gaggawa koda baya nan babu wanda baisan da maganar ba sai Moddibo shiyasa shekaran jiya suka zo akan neman alfarma ga Uzurin da suka zo dashi”.
Sai kuma ya numfasa kana yaci gaba da cewa.
“Akan wasiyyar da yabari toh na faɗa musu lallai Nine mariƙin Khausar Kuma Khausar tamkar ƴa take awajena, saidai bani da iko da kuma ƴan cin da zan bada Auren Khausar garesu batare da izinin Yayan mahaifinta ba da kuma sahalewar kakarta”.
Gyara zama tayi tare da kallon Mommy da tayi sanyi hawaye na zuba daga idanunta numfashi ya fesar kana yace.
“Toh nace suje bayan kwanaki zasu jini, toh dana niyyata zamu je Jauro yaya muyi wa Hajja Nana bayani sannan mu faɗa mata wasiyya ne duk abinda ake ciki dama nace idan muka dawo zan faɗa musu”.
Kallonsa kawai Mommy take bako kyaftawa tana sake jin tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali aranta cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Kuma tunda kika ji Khausar ta furta haka wataƙil itama akwai abinda ta sani acikin wannan al’amarin”.
Dogon numfashi Mommy taja tare da fesarwa kana ta lumshe Idanunta hawaye masu zafi suka zubo ahankali ta sunkuyar da kanta cikin raunin murya tace.
“Allah sarki toh Ubangiji Allah ya jikansa da rahma idan al’khairi ne Allah ya tabbatar idan kuma ba al’khairi bane Allah ya sauya musu da mafi al’khairi”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.
“Yawwa Aysha yanzu kika gane addu’ar da zaki yi kenan, sannan kada kiyi fushi da Khausar fadan nan dakike yi bashi da amfani zama zakiyi da ita ki fahimci Meye dalilinta na fadar haka”.
Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.
“Toh shikenan Insha Allah zan kiyaye”.
Sai da aka kira sallar azahar Lamiɗo ya fita ya tafi masallaci kana Mommy ta miƙe ta nufi sashenta tana shiga falon ta fara jiyo sheshsheƙan Kukan Khausar abakin ƙofar Bedroom ɗinta ta tsaya tare da ɗaga labulen ta kalli Khausar ba yabo ba fallasa tace.
“Idan kin gama kukan ki tashi kije kiyi al’wala kiyi sallah”.
Cikin sanyi ta gyaɗa mata kai kana ta miƙe tashiga toilet ta ɗaura al’wala ta fito Anutse ta gabatar da sallah.
Mommy ma na shiga Bedroom ɗinta ta ɗaura al’wala sannan ta gabatar da sallah.
Bayan Khausar ta idar da Sallah kai tsaye ɗakin Mommy ta nufa.
Acan ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take akan kujera taji ƙa garin magani da tsamiya da kuma ruwan zafi ta kalli Samira dake zaune gefenta ta zabga ta gumi cikin sanyi tace.
“Gashi ki karɓi maganin kisha dama wannan yace sai da rana-rana zaki riƙa sha wanda kika sha jiya da daddare kuma dare-dare zaki sha”.
Karɓan kofin Samira tayi tare da tsira masa Ido ganin yanda ta tsirawa kofin Ido yasa Hajiya Lami cewa.
“Kisha mana”.
Cikin raunin murya Samira tace.
“Mommy nifa na jiya da daddare nan ma dana sha babu abinda ya ragu saima zubar ruwan daya ƙaru”.
Ahankali Hajiya Lami tace.
“Toh Sokuwa wataƙil ruwan ai zai zube ne ya gama ƙarewa idan ya gama zuba shikenan magana ya ƙare”.
Cikin raunin da tashin hankali Samira ta kalli mahaifiyar ta da Idanunta dake cike da ruwan hawaye kana tace.
“Toh Mommy ruwan fa da ƙarni da wari yake zuba yanzu ma bakiji yanda nake ƙarni ba?”.
Cikin tsinkewar zuciya ta kalli Samira sai kuma ta basar domin bata son bawa ƴartata tsoro amma baki ɗaya hankalinta ya tashi kar dai ƴarta ta samu wata matsala numfashi ta fesar tare da kallonta kana tace.
“Ni dai banji wani wari ba hancin kine dai da shegen jiye-jiye kina nan da hanci kamar na kule ke dai kisha magani tunda yace kisha na tsawon sati biyu kafin mu koma”.
Zare ido tayi cike da tashin hankali tace.
“Mommy har sati biyu kuma?”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa kana tace.
“Eh saboda zaiyi tafiya so koda munje baza mu same shiba”.
Ajiyar zuciya Samira ta sauƙe tare da cewa.
“Toh bari in sha”.
Aɓangaren Naseer kuwa zaune suke afalon Mahaifiyar sa da Addarsa Hindu da kuma Mahaifiyar su Hajiya Kubra yayin da akwatuna ke jere agabansu cikin su sanye da Atamfofi, Leshuna, Shadda, English wear, Turaruka, Mayuka,Takalma.
Gyara zama Naseer yayi tare da kallon Addah Hindu murmushi ya sakar mata tare da ɗage mata gira ɗaya kana yace.
“Insha Allah Addah Hindu burina ya kusa cika”.
Murmushi tayi tare da jinjina masa hannu kana tace.
“Ƙwarai kuwa nan da ƙanƙanin lokaci ma kuwa”.
Gyara zama Hajiya Kubra tayi tare da kallon Naseer tace.
“Toh yanzu me yarage acikin kayan Auren nan ba asaba!?”.
Ajiyar zuciya Naseer ya sauƙe tare da cewa.
“Kayan Aure kam yanzu ai kusan an gama komai kawai yanzu gishiri da goro za asiya sai kuma sadaki i think suka ɗaine suka rage”.
Kai Addah Hindu ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh saura kayan rufi ba ahaɗa ba”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Toh badamuwa yaushe za akai?”.
Kallon akwatunan tayi kana ta kallesa numfashi ta fesar ta da sakin murmushi tace.
“Idan Allah ya yarda nan da sati za akai saura gyalullulka dana aika akawo min daga Kano basu iso ba tukunna”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh ba matsala sai sun iso”.
Bayan Moddibo da Abba sun idar da sallar Azahar Amasallacin Kofar gidan Abba kai tsaye gidan Ummi suka nufa bayan sun isa Moddibo yayi Parking suka fito daga motar kana suka tsaya daga coumpund ɗin Moddibo yayi sallama daga ciki Malam Ahmad ya amsa kana ya fito ganin Abba yasa ya faɗaɗa Murmushin fuskarsa tare da cewa.
“A’a Alh Bashir yau har da kaine agidanmu sannu da zuwa sannu da zuwa maraba lale ku iso mana”.
Kai Abba ya girgiza kana yace.
“A’a nan ma yayi”.
Ahankali malam Ahmad yace.
“A’a bakomai Abban Jameel mu shiga mana ai an zama ɗaya haba dai mushiga dan Allah”.
Murmushi Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh shikenan Nagode”.
Sannan suka nufi falon Ummi Asma’u dake zaune ta miƙe tare da yi musu Barka da zuwa kana ta koma kichen ta dauki Plate ta kawo musu ruwa da drinks da kuma Fruit ta ajiye masu kana ta Gaishe su cike da ladabi.
Ahankali Moddibo ya jingina bayansa da jikin kujera ya lumshe idanunsa baki ɗaya ya tsani garin Gembulan da jahar Taraba ji yake tamkar ana yayyafa nasa garwashin wuta ajiki baiƙi ace ko yaushe yana ɗaki baya fita ko ƙofar takashi ba.
Ummi dake Bedroom zaune kan Sallaya ta miƙe ta fito jin muryan Asma’u na gaishe da Moddibo kana tace.
“A’a Moddibo ne”.
Ganin Abba zaune yasa ta tsaya cike da Mamaki tace.
“A’a Alhaji Bashir”.
Cikin sanyin murya Abba yace.
“Na’am Fatima”.
Kallonta Malam Ahmad yayi sanye take da hijabi har ƙasa hannunta riƙe da Carbi cike da kulawa yace.
“Ki ƙara so mana ku gaisa”.
Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa ta zauna daga gefe.
Anutse Moddibo ya daga kai ya kalleta kana yace.
“Ummi ina yini”.
Kallonsa Ummi tayi ba tare data amsa gaisuwar ba tace.
“Babana jiya duk baka leƙoni ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Eh Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Kuma na kira wayarka baka ɗaga ba sai nayi tunanin ko kana bacci ne?”.
Kai ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa yace.
“Kuma Ummi ban kulaba ban miss call ɗin ba”.
Jinjina kai tayi tare da fadin.
“Ayyah”, Kana suka gaisa.
Anutse Abba ya kalleta tare da cewa.
“Fatima ina yini”.
Ahankali ta gyara zamanta tare da faɗin.
“Lafiya”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ya muka ƙara ji da haƙuri”.
Lumshe Idanunta tayi kana tace.
“Haƙuri ya zama dole”.
Jinjina kai yayi tare da cewa.
“Toh Allah yajiƙan Jameelu Ubangiji ya masa rahama”.
Baki ɗayan su suka amsa da Ameen ya Allah.
Gyara zamansa yayi kana yace.
“Fatima kada ki yiwa Jameelu kuka ki tayi masa addu’a shine abinda ya dace kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace.
“Insha Allahu bazan yiwa Jameelu na kuka bai Insha Allah zan ta binsa da addu’a”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Hakan yafi”.
Anutse ya gyara zamansa tare da kallon Moddibo da kansa ke ƙasa kana ya kalli Ummi da itama still Kanta ke ƙasa ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Dama nazo da Moddibo ne inne ma masa uzini awajenki”.
Cikin sauri ta ɗago kanta tare da Kallonsa tace.
“Izinin me kuma?”.
Numfashi ya fesar tare da cewa.
“Dama Abune da yashafi kasuwanci na acan Company mu na Marocco wanda Jameelu ne yake komai na Company nin toh kuma yanzu kin gani Allah ya dauke mana Jameelu”.
Cikin sauri Ummi ta lumshe Idanunta tare da gyara wuyan hijabinta.
Abba ya cigaba da cewa.
“To Kuma Manager company shima ba shida lafiya toh sun nemi da Inje kuma nima bana jin daɗin jikina bazan iya zuwa ba”.
Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da kallon sa gani tayi baki ɗaya ya rame ya zama wani so silent dashi.
Cikin sanyin murya da tausayawa tace.
“Toh Abban Jameel Idan bamu sa haƙuri aranmu ba ya zamuyi ka kwantar da hankalin ka Ubangiji Allah yajiƙan Jameelu shine kawai fatan mu da addu’ar mu”.
Kai ya gyara tare da sauƙe numfashi yace.
“Insha Allah zan kiyaye.
Yanzu mshawan jinin ne baki ɗaya yasani agaba duk kan magungunan da nake sha sai yazama kamar basa min aiki”.
Jinjina kai tayi cikin sanyin murya tace.
“Allah ya sawwaƙa amma ka rage tunani koda kana shan magani idan baka rage tunani ba ba zaiyi aiki ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Toh Fatima ya zanyi idan banyi tunani ba!?”.
Ahankali ta sunkuyar da kanta hawaye na zuba daga idanunta.
Gyara zama Abba yayi cikin sanyin murya yace.
“Toh dama shine nake so Moddibo ya wakilceni yaje shine yake cemin bawai zuwan bane baya so amma baya so yayi nesa da Umminsa”.
Ahankali ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Moddibo murmushi tayi kana tace.
“Ba komai Babana kaje wannan ma ai abin farin ciki da al’fahari ne zaka cika burin da Jameeluna yake son cikawa. Ubangiji Allah yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya Allah ya maka albarka”.
Cikin sanyin murya da tausayawa Moddibo ya amsa da Ameen asaman laɓɓansa.
Ahankali Ummi ta cigaba da cewa.
“Insha Allah zanyi ta binka da addu’a ba komai Babana ai muna tare ina nan ina Marocco amma idan ya gama zai dawo ko?”.
Ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya tana kallon Abba.
Kai Abba ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh zai dawo Insha Allah bazai wuce sati biyu”.
Jinjina kai tayi tare da kallon Moddibo kana tace.
“Badamuwa Babana ai zamu nayin waya”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Shikenan Ummi ba matsala tunda kin amince.
Murmushi tayi still Idanunta cike da ruwan hawaye tace.
“Na amince Babana Allah Ubangiji ya kaika lafiya Allah ya dawo da kai lafiya Allah yasanya alkhairi da albarka acikin tafiyar.
Ahankali yace.
“Ameen Ummi”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da kallonta kana yace.
“Yanzu kuma sai batun kuɗin ku da aka har haɗa”.
Sunkuyar da kai Ummi tayi Atake hawaye suka cigaba da zubowa daga Idanunta cikin raunin murya tace.
“Toni me zanyi da kuɗin nan ne Abban Jameel?”.
Kai Abba ya Girgiza cikin rawan murya da rauni yace.
“Toh nima ɗin idan kun barsu awajena me zanyi dasu ga kuɗin Aliyu ga naki kowa ya karɓi kuɗin sa kowa yana da bukatarsa motar ki da Sarƙoƙinki kika siyar ki sayi wata mota amfani dashi”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo kana yace.
“Kaima Moddibo ka karɓi kuɗin ka ka sayi mota sannan sauran kuɗin kayi abinda ya dace dasu”.
Kai Moddibo ya girdiza ciki rauni yace.
“Abba me zanyi da kuɗin?.
Ai kuɗi na gama abinda ya dace inyi dasu Babu abinda zanyi dasu tun da har basu tseratar min da J ɗina ba wani amfani zasu yimin?”.
Cikin rauni Abba yace.
“Bakomai Moddibo ka karɓi kuɗin nan idan ka barsu awajena kun barmin tashin hankali da damuwa”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da faɗin.
“Kuyi hakuri duk kan tsanani yana tare da sauƙi addu’a kaɗai zamuyi wa Jameelu amma kamar yanda yace ne Moddibo ka karɓi kuɗin nan sannan kema Fatima ki karɓi kuɗin na shine abu mafi a’ala”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.
“Yawwa shine dai ki bani account number inyi Miki transfer”.
Kai Ummi ta shiga Girgizawa hawaye na kwaranya daga Idanunta.
Ganin haka yasa Malam Ahmad ya karbi wayarta tare da fito da account number ya faɗawa Abba Atake Abba ya mata transfer kuɗinta Naira million goma da dubu ɗari takwas kasancewar yana da account number Moddibo Shima Atake ya Masa transfer kuɗinsa.
Anutse ya gyara zamansa tare da Kallonsu cikin sanyin murya yace.
“Nagode da halarcinku agareni musamman ma kai Moddibo Allah Ubangijin ya biya da mafificin alkhairi”.
Atake Moddibo yaji wani irin rauni ya mamaye sa kallon Abba yayi muryarsa na rawa yace.
“Abba akan J ne kake min godiya?”.
Numfashi Abba ya fesar tare da sauƙe ajiyar zuciya yace.
“Toh Aliyu ya zanyi kayi min halarci duk kan inda Aboki na gari ya cika ka cika Ubangiji Allah yasaka da alkhairi Nagode da halarcin ka”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Ameen Abba”.
Kallon Ummi Abba yayi kana yace.
“Toh insha Allah sammako zaiyi ya tafi kinsan akwai tazara tsakaninmu da Adamawa kuma can zai shiga jirgin zuwa Abuja”.
“Toh Allah ya kaimu Allah yakai ka lafiya Babana Allah ya kareka”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ameen Ummi”.
Miƙewa Abba yayi tare da cewa.
“Toh bari mu tafi”.
Godiya suka masa har sun fita Ummi ta miƙe tare da bin bayansu abakin barandar ta tsaya tare da cewa.
“Babana amma ai zaka dawo daddare muyi sallama ko?”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Insha Allah Ummi zan zo”.
Bayan sun fita kai tsaye gidan Malam Arɗo Abba ya ajiye Moddibo zaiyi masa sallama kana Abba ya wuce gida.
Cikin sanyin jiki Khausar ta isa Bedroom din Mommy, a hankali ta zauna agabanta cikin Muryan kuka tace.
“Mommy kiyi haƙuri kada kiyi fushi dani”.
Tsira mata Ido Mommy tayi ba tare da tace Uffan ba.
Cikin raunin murya Khausar ta haɗa hannunta waje ɗaya kana ta fashe da matsanancin kuka da sheshsheƙan tace.
“Mommy dan girman Allah kiyi haƙuri ki daina fushi dani”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da fesar da nunfashi kana tace.
“Khausar to ni me zan ce miki?.
Bani da abinda zan ce miki tunda ai hukunci ne kin riga da kin gama yanke shi baki nemi shawarata ko izinina ba”.
Girgiza kai Khausar tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga Idanunta.
Ita kuwa Mommy kauda kayi tayi gefe kaba ta cigaba da cewa.
“Kawai kin fadi maganarki gaba gaɗi, sannan koda akeɓance baki taɓa faɗa min tsakanina ni dake ba, sai da kika zaɓi cikin mutane sannan kika faɗa saboda ki kunya tani kin bani mamaki ban taɓa zaton haka daga gareki ba”.
Khausar kuwa kai take Girgiza cikin muryan kuka mai gunji kana Muryanta na rawa tace.
“Mommy nima ina tsoron Modibbo bafa, dan nasan baya sona”.
Kallonta Mommy tayi cikin da mmki ta tsareta da ido tare da cewa.
“Toh kina tsoron Auren Moddibo kuma, akan wani dalili zaki ce zaki Aureshi? Kuma bayan kina sane baya sonki”.
Sunkuyar da kai ƙasa tayi cikin gunjin kuka ta lumshe Idanunta tare da taune Lip ɗinta cikin raunin murya tace.
“Mommy wasiyyar Yah Jameel ne Yah Jameel ne ya roƙi al’farma awajena sannan tun lokacin daya faɗa min yace min wasiyya ya barmin yace koda ya mutu kada in manta ya nemi wannan al’farma awajena”.
Sai kuma ta kasa ci gaba da mgnar sakamakon kuka da yaci ƙarfinta hannu ta sanya ta goge hawayen fuskarta wani na sake zubowa Muryanta na rawa ta cigaba da cewa.
“Aranan da za’a ɗauke Yah Jameel bayan mun taho amota yace min yana neman alfarma awajena in na ɗauka Alfarman da yake nema awajena tamkar wasiyya ce”.
Sai kuma ta kife kanta kan cinyar Mommy tana mai sakin wani irin raunataccen kuka murya na karkarwa taci gaba da cewa.
“Mommy a ranar a gabana Yah Jameel yayi ta kuka kamar yaro ƙaramin ya rinƙa haɗani da Allah da Manzonsa cikin sanyin murya da neman alfarma yace dan Allah kada ince bazan yi masa ba yana so koda bayan Ransa in Auri Moddibo”.
Kallon ta kawai Mommy keyi bako ƙyaftawa yayinda itama hawaye ke zubo mata.
Cikin sheshsheƙan Kuka Khausar ta lumshe Idanunta tana tuna lokacin da suka kasance da M Jameel amota yana faɗa mata magana da sauri ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kana muryanta na rawa tace.
“Mommy alokacin Cike da damuwa na kalli Yah Jameel nace ya Jameel Meyesa kake Fadar haka Meyesa kake magana me karyar da zuciya dan Allah kada kace wasiyya nidai ka faɗi ko wace irin alfarma kake so zanyi maka domin kafi ƙarfin alfarma awajena”.
Taja hanci tare da kallon Mommy da yanayin ta ya sauya Muryanta na rawa kana numfashinta na fusga tace.
“Sai yace min Khausar koda ace kin riski labarin mutuwa ta ki tuna da Alfarman da kuma Wasiyyar da na bar miki ki Auri Moddibo idan kuma Allah yasa ina raye zanfi kowa farin cikin ganin An ɗaura Aurenki da Moddibo”.
Ahankali Mommy ta sun kuyar da kanta ƙasa cikin wani irin yanayi na tsananin tausayawa da kuma tsoron Allah Mabuwayi gagara Misali tol-tol haka hawayenta ke zuba jin Khausar taci gaba da cewa.
“Mommy Yah Jameel ya faɗa min cewa ya fadawa. Kakar Moddibo cewa dan Allah ayi Aurena da Moddibo Mommy dan girman Allah ki tayani cikawa Yah Jameel Wasiyyar daya barmin bani da abinda zanyi masa a wannan duniyar wanda zaisa Yah Jameel farin ciki amakwancinsa sama da in cika masa burinsa naji na gani zan rayu da Moddibo duk da nasan ya tsaneni zan rayu dashi sabida darajar Yah Jameel da wasiyarsa zan juri dukkan uƙubar da Moddibo zaimin koda kuwa zai kasheni zan zan cikawa Yah Jameel burinsa”.
Cikin sheshsheƙan Kuka da fisgar numfashi tace.
“Mommy wannan buri da fatan Yah Jameel ne dan Allah da Manzonsa ku barni in cika masa burinsa, tun da muke rayuwa da Moddibo Amakaranta yace ko yaushe kallon mu yake amatsayin mata da miji yace bashi da buri sama da wannan Mommy yace min da ɗan Adam yana da zabi idan ajalinsa yazo to da zai roƙa ajinkirta masa ajalinsa yaga kasancewa ta da Moddibo a Inuwa ɗaya a gidan aure”.
Sai kuma tayi saurin dafe ƙirjinta jin yanda numfashinta ke fusga.
Ta sauƙe wani irin numfashi tare da dafe kanta kana ta cigaba da cewa.
“Yace min Khausy zanso naga wani irin zama zakuyi keda Moddibon.
Yace min zaiso ace Allah ya bashi Aron Rai ya rayu ya ganni gida ɗaya a Inuwa ɗaya da Moddibo yaga wani irin Rayuwar aure zamuyi koda na wuni ɗaya ne.
Allah sarki ya Jameel ashe bazai ganiba.
Dan Allah Mommy ki barni in cikawa Yah Jameel burinsa Mommy Dan Allah kiyi haƙuri ki barni in cikawa Yah Jameel Wasiyyar sa”.
Taƙarashe mgnar tare da fashewa da matsanancin kuka mai masifar ƙuna da ɗaci sai kuma tace.
“Mommy wallahi ina tsorin son Moddibo har Raina, kawai na faɗa ne domin kada Hajja Nana tace dole sai na Auri Yah Aliyu shiyasa na faɗa alokacin, amma bawai dan in kunya taki bane Mommy kinfi kowa sanin halina banyi hakan da wata manufa ba face cika wasiyyar Yah Jameel”.
Numfashi mai tsawo taja cikin Muryanta da baya fita tace.
“Mommy ina matuƙar girmama Yah Jameel Mommy Ina so in cika Masa burinsa wannan shine wasiyyar Yah Jameel na karshe kuma shine karshen maganarmu dan Allah ki tayani cika masa wasiyyar sa na roƙeki”.
Wasu irin hawaye masu zafi ne suka fara bin kuncin Mommy cikin sanyi da raunin murya tace.
“Insha Allahu Khausar da izinin Ubangiji za acikawa Jameel burinsa…!
*LITTAFIN SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama ba haƙƙin kowa a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In dai baki biyaba kika karanta to na satane, kuma na Allah ya isane*
By
*GARKUWAR MARUBUTA* Runtse idanunsa yayi da karfi, tare dasa hannunsa duka biyu ya matse kansa, sabida yadda ya fara jin kansa yana juyawa tare da sarawa, yayin da kalaman Hajja Nana ke dukan tsakiyar ƙoƙon kansa yana ratsa ƙwaƙwalwar kansa tare da jin suna ratsa kunnuwansa suna yawo tamkar yanda aradu ke yawo asararin samaniya, baki ɗaya idanunsa sun juye sun kaɗa sunyi Jawur, kab ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari cikin wani irin sauri zuciyarsa ke bugawa da kaso Cassa’in da tara cikin ɗari, tana mai wanzar da jini litter-litter a cikin dukkan daƙiƙu yana watsashi wa jijiyoyin jikinsa.
Hakan yasa tuni rigarsa ta fara jikewa da zufa, duda yanayin garin Gembila da ba’a musu zafi.
Sai ga tashin hankali ya sashi tsats-tsafo zufa sabida yadda zuciyarsa ke bugawa da Masifaffen ƙarfi yayin da numfashinsa ke fusga tamkar zai bar ganganar jikinsa, cikin tsanananin tashin hankali da wani irin masifaffen juyi da kansa keyi ya ƙara matse kansa da hannu bibbiyu, da ƙyar ya iya daga ƙafarsa ya sauka daga barandar ya nufi side ɗinsa yana tafiya tare tangaɗi tamkar ɗan maye yayin da kuma jiri ke ɗibarsa.
Yana cikin tafiya tamkar zai faɗi ya tsinkayo muryar Innayi cikin tsananin fushi da takaici cikin zafin zuciya tace.
“Zaki sha mamaki kuwa.
Hajja Nana zan nuna miki ƙarfin iko da isan ɗan shegen da kike faɗi. Zaki gane kinyi kuskure ambatonsa da wannan sunan da yafi ƙarfinsa. Auren nan kuma da izinin Ubangiji tamkar anyi sa angama ma, in dai wannan auren nen kika tashi ki kace zaki yaƙesa sannan kika ce zaki hana toki sa. Aranki anyishi an ɗaura shi angama domin ke dai baki isa ki haramta abinda Allah ya halastaba wlh muddin ina raye toh in Sha Allah kamar ma anyi auren nan an gama zan shayar dake mamaki”.
Wani irin kallon rainin hankali me ɗauke da zafin zuciya Hajja Nana tabi Innayi dashi.
Ita kuwa Innayi. Cikin fushi ta cigaba da cewa.
“Babu wani mahaluki na duniya daya isa ya hana wannan ɗaurin Auren sai Ubangiji daya halicci sammai da ƙassai. idan har kinga wannan Auren bai kasance ba to daga Rabbus Sanawati ne amma ba daga ke Hajja Nana mai kaɗa kai kamar Ƙadangariya ba”.
Wuhuhu ina wuta Hjja na ta faɗa ciki.
Cikin fushi da hatsala Hajja Nana dake ƙoƙarin fita ta tsaya tare da juyawa ta kalleta sai kuma tayi murmushi tare da gyara tsayuwar ta kana tace.
“Wani ƙarfin iko ko kuma isa. Ɗan shege ke dashi? Ai sai dai kuje kunemi watsatstsiya ƴar gaba da Fatiha ku Aura masa, amma dai ba jikata dake da asali da tushe ba zuri’ata tayi miki nisa sai dai hange daga nesa?”.
Afusace Innayi da Idanunta suka kaɗa tamkar garwashi tace.
“Tabbas zaki ga isa da kuma ƙarfin Iko irin na ɗan shegen da kike faɗa agaban idanunki za’a ɗaura Aurensa da Khausar sannan ya ɗauketa su tafi ke babu yanda kika iya, zakisha mmkin ganin tushensa daya girmi tunaninki ya kuma zarta zatonki. domin ke ba kowa bace a kansa, Allah ya wadaran aminiyar da bata mutunta amintaka, kin kasance mara ɗa’a da sanin ya kamata!”.
Ita kuwa Hajja Nana mugun kallo ta watsawa Innayi tare da nuna kanta da tsaya kana tace.
”Ni kika faɗawa haka?”.
Kai Innayi ta gyaɗa cikin tsawa tace.
“An faɗa miki wacece ke?Ko kina tunanin nan ma Jauro yaya ne da kike baza ikon ki da mulkinki kina kaɗa kai uwa ƙadangaruwa, kina abinda kika ga dama? to a hir ɗinki ki sani kece kika shigo muhalli na toh ki sani duk da cewa mu muke neman aure a ƙarƙashin ku ba za ki taka muba in barkiba domin mace bata bada Aure dan haka ki ficemin agidana”.
Wani irin dogon tsaki taja kana tace.
“Ko da baki ce in fice miki agida ba dole zan fita, amma kisa Aranki badai.
Ɗai shegen jikanki da tsarkakakkiyar jikata su haɗa Aure ba”.
Tana faɗin hakan
ta ida ficewa daga ɗakin amma still Idanunta na cikin dakin tace.
“Dama ace ansan tushe ansan asalinku sannan ansan jikan ki tsarka kekkene wanda aka haifa ta sunna, to ba komai amma jikanki da yake Najasa wanda aka haifa ta hanyar ƙazanta ba zaiyu abashi auren jikata ba, zaki ga ƙarfin Ikona da isata sannan kuma da Izzata akan al’amarin auren nan”.
Innayi da zuciyarta ke wani irin tafarfasa tace.
“Toh mu zuba mu gani kada ki fasa idan har ke kin cika mai karfin iko da Izzah”.
Ƙwaffa Hajja Nana tayi tare da sauƙa daga barandar ta juya fuuuu kamar zata tashi sama ta nufi waje.
Moddibo kuwa yana shiga falonsa ya maida ƙofar ya rufe, kana ya zame tare da zama aƙasan daɓas ya jingina bayansa da jikin ƙofan Falon lokaci ɗaya yashiga kokuwa da numfashinsa dake ƙoƙarin ɗauke wa.
Atake wani irin azabebben kuka mai gunji ya kufce masa cikin raunin murya da tsantsar tashin hankali ya shiga furta.
_“Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha Ya wadud³ ya zul’arshil Majeed ya fa’alillima yurid As’aluka bi izzatil lati layura wa mulki kallazi la yurad Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n_”.
Cikin wani irin tashin hankali ya cigaba da karanta duk wata addu’a da tazo bakinsa.
Kana wani azabebben kuka mai sa rawan jiki ya sake kufce masa lokaci ɗaya wani masifaffen zazzaɓi ya rufe sa cikin kiɗima ya fara zantukan zuci. Aransa yace.
Innalillahi Wa’inna ilahi rajiu’n. Shin wannan wace irin Masifa ce? wani irin rayuwa ce take fukantoni! sannan inane tushena.
Ko-ko dai da gaske ne kalmar wannan matar gskyace, cewa bani da asali.”
Sai kuma ya rumtse idanunsa da ɗan karen ƙarfi.
Tare da fara ƙanana mgn a saman lips dinsa dake tsuma.
“Hahhhh da ƙamshin gaskiya acikin kalaman matar nanfa, domin da inada tushe da asali da tuni Innayi ta kaini garesu sannan ta nuna min tushena shin da gskene kenan bata hanyar aure sunnanr Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama aka samar da niba Yah salam.”
Sai kuma ya fara mgn cikin rawan murya.
“Ya Ubangiji Allah kada kasa zargina da zatona na tsawon shekaru ya tabbata ta wajen furucin wannan matar.”
Ya ida mgnar tare da kife kansa bisa guiwowinsa.
Domin shi akaran kansa ya daɗe yana tunanin wataƙil shi ɗan shegene shiyasa Innayi bata taɓa faɗa masa Asalinsa ba kuma bai taɓa ganin wani saba dangi na gefen uwa ko uba, ya kuwa san bazai taɓa yiwuwa ace kab duniya bayi da wani ɗan uwa ko ƴar uwa da za’ace nase sai dai in har shi ɗin ɗan Shegen ne, shiyasa Akullum yake tsoron tambayarta wanene shi domin kada yaji abinda zai tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa da kuma lissafin sa sabida tsoron hakanne yasa baya bincike kan tushensa sabida shi kansa ya fara zargan lamarin.
Lumshe Idanunsa yayi hakan ne ya bawa hawayen ciki damar kwaranyowa da masifar zafi suka zubo masa, cikin ransa yace dama nasani dole irin wannan ranan zai zo ranan da wasu mutane zasu fuskance mu gaba da gaba su tuhumi nagartata. sannan su kirani da shege idan har basu samu gamsasshiyar amsaba. Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.
Hajja Nana kuwa Afusace ta fita daga gida tare da buga Murfin gate din tana zuwa ta buɗe motar tashiga tana wani irin huci na tsananin ɓacin rai da takaici kallon Baffa Jimeta tayi kana tace.
“Mu tafi baki ɗaya mutanen cikin wannan garin basu da hankali basu san abinda suke yiba”.
Cikin sanyin murya Baffa Jimeta yace.
“Subhanallah Hajja Nana kada kice haka kada kiyiwa baki ɗaya mutanen garin nan kuɗin goro sam hakan be cancantu ba”.
Harara ta watsa masa kana cikin fushi tace.
“Rufe min baki kaja mota mutafi bana son maganar banza”.
Kai ya gyaɗa kana yayiwa motar key suka bar kofar gidan kai tsaye hanyar Jauro yaya suka nufa.
Anutse Malam Liman ya juya tare da kallonta kana cikin sanyin murya yace.
“Kiyi haƙuri Hajja Nana ita rayuwar nan na duniya komai sai da haƙuri ake fuskantar sa, abinda fa hakuri bai warware saba tofa rashin haƙuri ba zai warware saba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki koma menene Khausar tayi yarinya ce bazaki sa shi amizani da zai tayar miki da hankali har haka ba”.
Cikin sauri Hajja Nana data tsirawa madubi ido ta juya ta kallesa kana cikin fushi tace.
“Wai Ni Khausar zata dubi tsabar Idona tace bata son Aliyu”.
Anutse Baffa Jimeta dake driving ya dan juya tare da kallonta kana cikin sanyin murya yace.
“Toh Hajja Nana menene aciki dan Khausar tace batason Aliyu ainima kaina bazan yiwa Khausar auren dole ba, duk da cewa Aliyu ya kasance ɗana amma bazan tauyeta in Aura mata shi adole ba tunda bata son shi”.
Afusace Hajja Nana ta buga masa tsawa tare da faɗin.
“Rufe min baki me kake nufi kenan?”.
Ahankali ya sassauta muryarsa cike da girmamawa yace.
“Hajja Nana kiyi haƙuri ki gafarceni Idan har abinda zan faɗa zai ɓata miki rai, amma abinda nake nufi a aura mata wanda take so.”
Sheƙeƙe Hajja Nana ke Kallonsa da Idanunta dake cike da Masifa cike da iko da kuma Izza tace.
“Wannan ne kuma baku isaba ba’a haifi wanda ya isa ya ƙaddamar da wannan abin ba”.
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe tare da kallon Baffa Liman daya tsirawa titi idanu kana ya sake sassauta muryarsa tare da cewa.
“Dan Allah Hajja Nana ki gafarceni Ayiwa yarinya abinda take so”.
“Bafa ku isa ba”.
Ta faɗa a taƙaice.
Kai Baffa Jimeta ya gyaɗa batare da yace Uffan ba ya cigaba da Driving.
Ahankali Malam Liman ya sauƙe Ajiyar tare da juyawa ya fuskanci Hajja Nana da kyau kana yace.
“Adda Hajja to dan tace batason Aliyu shine hankalin ki ya tashi haka?”.
Sake baki Hajja Nana tayi tare da cewa.
“Au don ne ma kake cewa, wato baka ɗauki abinda muhimmanci ba, wannan ɗin bai kai hankalina ya tashi bane?Sannan ma wanda tace tana so ɗin dama ace mutum me tushe ne da asali to ai da sauƙi”.
Dogon numfashi Malam Liman yaja tare da sauƙewa kana yace.
“Toh waye ne tace tana son din ne?”.
Dogon tsaki Hajja Nana taja tare da yin ƙwaffa kana tace.
“Wai wani Malamin Makarantar sune, Moddibo ne ko Momodu ne ohon mata, wannan yaron dai da Malam Arɗo yaje dashi Jauro yaya ashekarun baya sannan akwanakin baya muka je muka sameshi agidan Malam Arɗon tofa wai shi take so”.
Jinjina kai Malam Liman yayi alamun ya gane.
Ita kuwa cike da takaici ta cigaba da cewa.
“Toh Jikan wannan Ƙawar tawa Innare, kuma sanin kanku ne tunda nasha baku labari cewa babu wanda yasan asalinsu, sannan babu wanda yasan tushen su a iya binciken da nayi a iya sanin su da nayi muke zuwa Makka tare yaron nan ɗan shegene”.
Cikin sauri Baffa Jimeta dake Driving ya juya ya kalleta jin furucin daya fito daga bakinta.
Harara ta galla masa kana ta cigaba da faɗin.
“Ɗan shegene bashi da asali ɗane da aka haifeshi ta hanyar zina ta ƙazantacciyar hanya, shin taya zamu haɗa alaƙar aure dashi kalen ya lalata mana sunan zuri’a asamu abin faɗa aciki.
Girgiza kai Malam Liman yayi kana ahankali ya juya da fuskarsa gareta ya fuskanceta sosai yace.
Um-uhum kiyi haƙuri Addah Hajja kada ranki ya ɓaci”.
Girgiza kai tayi tana huci tace.
“Ai dole raina ya ɓaci Liman”.
Gyara Alkyabbar sa yayi kana yace.
“Dan Allah kiyi haƙuri amma kada ki sake aibanta yaron, domin koda maganar ki hakan take, sam bai da ceba duk da cewa kin bada hujjarki akan cewa shi shegene, tofa koda ya kasance shegen ba laifinsa bane, laifin Iyayensa ne da suka haifesa ta hanyar zina”.
Tallafe kunci Hajja Nana tayi tare da tsira masa ido babu keftawa, Malam Liman kuwa cikin sanyin murya da son nusar da ita ya cigaba da cewa.
“Sannan babu inda Shari’a ta hana Auren wanda aka haifesa ta hanyar zina.
Shari’a bata haramta Aurensa da Khausar ba, bai haramta ba a musulunci sai dai idan har akwai wani na ƙasu atare dashi wanda yake aikatawa shine zai zama lalura, sannan dan Allah irin wa’annan kalaman idan zaki furta su ki rinƙa tauna su saboda suna da nauyi”.
Atsawace ta kallesa kana tace.
“Liman Karka fara yimin wannan wa’aze wa’azen’kan nan masu sauya ra’ayi mutum”.
Cike da ladabi malam Liman ya sunkuyar da kansa ƙasa kana yace.
“Dole ne in fara yimi ki wa’azi, domin kada ki faɗa cikin furucin da zai kaiki ga fushin Ubangiji”.
Salati ta rafka tare da riƙe haɓa kana tace.
“Ikon mai duka Fadar gaskiyar ne zesa in fada cikin fushin Ubangiji, ko kuma yana da Uban ne ai tun yana jariri yana cikin tsumma da ka gani kasan cewa ƴarta ce ko ɗanta ya haifo shege ya kawo mata shiyasa ta gudu dashi saboda abin kunya yau tsawon shekara talatin harda ɗoriya kenan bata da wata ƙawa sama dani amma koni bansan tushen suba, bansan asalinsu ba sannan bansan daga ina suke ba”.
Girgiza kai Malam Liman yayi kana yace.
“Kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki amma. Duk da haka Addah Hajja baki da hujjar shegan tasa”.
Cikin sanyi ya cigaba da yi mata nasiyya yana nuna mata kuskuren abinda take amma firrr Hajja Nana taƙi sauraronsa. Baffa Jimeta kuwa Uffan bai sake cewa ba har sukayi nisa da tafiya.
Ɓangaren Moddibo kuwa wani irin zazzafan zazzaɓi mai zafin gaskene ya lulluɓe sa wanda gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Innayi dake tsaye ɗaki ma baki ɗaya jikinta rawa yake sai Safa da marwa take daga ƙarshe ta zame ta zauna kana ta fashe da kuka cur-cur-cur tamkar ƙaramar yarinya cikin Muryan kuka tace.
“Bansani ba Aliyu bansan wannan abin zai zame maka tabo ba acikin al’amuran kaba, bansan zai zame maka na ƙasu da kuma abin nunawa acikin al’amuran kaba Aliyu”.
Cikin tsanananin tashin hankali da tarin damuwa take maganganu tana zubar da hawaye.
Acan ɓangaren Abba kuwa bayan sun gama waya da Moddibo number Malam Ahmad yayi dearling jin yayi Picking yasa yayi gyaran murya tare da sallama kana suka gaisa bayan sun gaisa Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da gyara zamansa kana cikin sanyin murya yace.
“Dan Allah Malam idan anyi sallar La’asar ko zan samu ganinka?”.
Cikin daddataku yace.
“Toh badamuwa Insha Allah zanzo, Allah dai yasa lafiya?”.
Jinjina kai Abba yayi tare da faɗin.
“Eh babu komai Allah ya kawo ka lafiya”.
Bayan Malam Ahmad ya katse kiran ya juya ya kalli Ummi dake gefensa kan 2sitter sai kuma Asma’u da Bashir dake kan 3sitter cikin sanyin murya yace.
“Abban Jameelu ne ya kirani”.
Cikin alamun damuwa Ummi tace.
“Lafiya kuwa!?”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Lafiya lau”.
Girgiza kai tayi hawaye na taruwa akwarmin Idanunta tace.
“Ka dai ƙara tabbayarsa”.
Ganin bata gamsu bane yace.
“Toh bari in tambayan”.
Ya ida maganar tare da dearling number Abba.
Abba na ɗagawa Malam Ahmad yayi Sallama kana yace.
“Dama na faɗawa Fatima gashi-gashi yanda mu kayi to amma tace wai dan Allah meyake faruwa lafiya kuwa?”.
Kai Abba ya gyaɗa cikin sanyin murya da tarin damuwa yace.
“Eh lafiya lau dama ina so ne kuɗaɗen da suka haɗa na motar ta data saida da kuma na Sarƙoƙinta tunda ga yanda Ubangiji ya ƙaddara to shine kuɗin nake so kazo in baka su sai ka maida mata su, sannan kayi mata bayani tare da kwantar mata da hankali”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa tare da faɗin.
“Toh shikenan bari zan faɗa mata”.
Ahankali ya juya ya kalli Ummi bayan ya katse kiran kana ya mata bayanin duk yanda sukayi.
Cikin rauni ta sunkuyar da kanta hawaye na kwaranya daga Idanunta Shar-shar-shar suna zuba akuncinta cike da tausayawa suke kallonta musamman Asma’u lokaci ɗaya itama Idanunta suka fara zubar da ƙwalla.
Asanyaye Ummi ta ɗago kanta tare da kallon Malam Ahmad Muryanta na rawa tace.
“Kace masa bana son Kuɗin Na yafe me zanyi da kuɗin da suka kasa ceto min Jameel me zanyi dasu?.
Me zanyi da duk wani kayan ƙawa bana so bana ɓuƙatar su nayafe su duniya da lahira bana ƙaunarsu”.
Anutse Malam Ahmad ya girgiza mata kai cikin rarrashi yace.
“Kada kice haka Fatima kiyi haƙuri Jameelu addu’a zaki yi masa, kuɗin nan kada kice ba zaki karɓaba, idan har kika ce ba zaki karɓa ba zaki sake saka Mahaifinsa cikin damuwa da tashin hankali aransa”.
Kai ta girgiza tare da miƙewa ta nufi Bedroom ɗinta still hawaye na bin kuncinta.
Asma’u kuwa kife kanta da jikin cushin tayi tare da fashewa da sassayan kuka me gunji cikin sauri Bashir ya ɗagota tare da share mata hawaye cikin sanyin murya yace.
“Asma’u Yah Jameel baya ɓuƙatar kukan mu addu’ar mu kawai yake buƙata, dan Allah ki daina yi masa kuka kinji, na tabbata Yah Jameel baya son wannan kukan”.
Kai ta gyaɗa masa still hawaye na bin fuskarta tace.
“Bashir ya zanyi idan na tuna Yah Jameel ya barmu bari na har abada nakan ji zafi da ƙuna acikin zuciyata, nakan ji raɗaɗi mai zafin gaske nakanji.
Tamkar zuciyata zata fashe”.
Cikin sanyin murya Bashir yace.
“Toh ya zamuyi da hukuncin Ubangiji Asma’u haka Allah ya tsara Yah Jameel ba zaiyi tsawon rai ba, koda ace basu sace sa sun kashe ba na tabbata ba zai wuce wannan kwanakin ba mu dai kawai addu’ar mu yake buƙata a hankali kuma waɗanda suka aikata masa hakan zasuga SAKAYYAH mabayyaniya addu’a kawai zakiyi ta masa kinji”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Inayi kuma zan cigaba da har ƙarshen rayuwata da izinin Ubangiji”.
Ummi nashiga Bedroom ta zaune gefen gado tare da fashewa da kuka Malam Ahmad na shiga cikin daƙin ya zauna gefenta kana ya sanya hannunsa tare da janyota ya mannata da jikinsa cikin sanyin murya yace.
“Kiyi hakuri ki daina kuka Fatima, ki yiwa Jameelu addu’a Ubangiji ya masa rahma sannan madadin kice ba zaki karɓi kuɗin nan ba ki sake sakawa mahaifinsa damuwa to ki karɓa”.
Cikin rauni Ummi ta sake manna kanta da ka fadarsa kana ta cigaba da sheshsheƙan kuka.
Tafin hannunta Malam Ahmad ya damƙe acikin nasa kana ya cigaba da cewa.
“Idan yaso idan kika amshi kuɗin sai kiyi amfani dasu wajen yiwa Jameelu Sadaƙatul Jariya.
Kamar Gina Masallaci, Ko kuma gidan marayu, Ko Asibiti,ko makarantar addini, ko kuma yin Bohorle rijiya da dai sauransu da nufin Allah ya kai ladan garesa kinji ko Fatima kada ki butulcewa Ubangiji”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana yace.
“Kada kice ba zaki karɓa ba Ubangiji shi yabamu Jameelu, sannan kuma shi ya ɗauke Jameelu bamu da abinda zamu yiwa Jameelu sama da addu’a shine kaɗai soyayyar daza mu nuna masa amma idan kika bar kuɗin ya mahaifinsa zaiyi dasu?”.
Jinjina kai Ummi tayi cike da gamsuwa kana tace.
“Shike nan insha Allah zanyi yanda kace Allah yajiƙan Jameelu Allah ya gafarta tamasa Ubangiji ya jaddada rahma agaresa”.
Malam Ahmad na share mata hawaye ya amsa da.
“Ameen”.
Ɓangaren Hajiya Lami kuwa zaune take afalonta cikin sanyi Samira ta fito daga Bedroom ta zauna gefenta tare da tsira mata idanu.
Kallonta Hajiya Lami dake riƙe da wayarta tayi kana tace.
“Lafiya kuwa Samira?”.
Girgiza kai Samira tayi cikin sanyin murya tace.
“Mommy cikina ke ciwo”.
Ahankali Hajiya Lami ta ajiye wayarta tare da tsira mata Ido kana tace.
“Meke damunki ne kwanan nan kina yawan complain din cikin ki yana ciwo”.
Rau-rau tayi da ido still Muryanta na rawa tace.
“Mommy nikam wannan ciwon cikin ya fara damuna,
duk fa lokacin daya Murɗa Mommy wani farin ruwa ne yake fito min ta gaba na.
Mommy har saina sa Path agabana kamar mai yin period kuma ba jini bane kawai ruwa ne yake fito min mai ƙarni da masifar wari”.
Zare ido Hajiya Lami tayi tare da cewa.
“Ruwa kuma?,Ni Lami wani irin ruwa kenan?”.
Cikin rawan murya Samira tace.
“Ruwane kamar Sparm yake fita sannan da yawa da yauƙi yake fita Mommy ga wari da ƙarnin Masifa yanzu bakya jin ƙarnin da na matsoki”.
Da sauri ta jujjuya mata kai alamun a’a.
Ita kuwa Samira cike da damuwa taci gaba da cewa.
“Nifa idan na sunkuyar da kaina ƙasa ƙarnin da warin nakeji”.
Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da haɗiye wani abu mai masifar ɗaci kana ta kalli Samira tare da cewa.
“A’a Samira nikam ban jiba. Amma tun yaushe ya fara miki haka?”.
Kallonta Samira tayi tare da faɗin.
“Yafi kwana biyar idan naji cikina ya Murɗa ya Murɗa, sai wannan abin ya zubo da fari ya fara zubowa kaɗan-kaɗan, to amma yanzu ya fara zubowa dayawa, sannan ciwon cikin yana ƙaruwa baki daya hankalina ya tashi Mommy!”.
Cikin sauri Hajiya Lami tace.
“To bari zan shirya Inje wajen boka Kar’uzu in Faɗa masa halin da ake ciki”.
Suna cikin magana suka ji ƙaran buɗe Bedroom ɗin Abban Samira.
Ganinsa yasa Hajiya Lami wayancewa da faɗin.
“Eh Samira Insha Allah Idan Daddy ki ya bari zanje induba Aminan Hajiya Bunayya dake fama da ciwon ciki”.
Cikin nutsuwar Kamilin Dattijo dake cike da kamala da nutsuwa ya ƙaraso cikin falon tare da kallon Hajiya Lami cike da dattako yace.
“Ayyah Subhanallah lallai dai naji kuna maganar ciwon ciki ashe Amina ce ba lafiya Allah ya sawwaƙa”.
Da sauri Hajia Lami tace.
“Amin dai”.
Shi kuwa yana gwara zaman hular kansa yaci gaba da cewa.
“Shiyasa na kwana biyu ban gantaba ashe ba lafiya ne?”.
Kai Hajiya Lami ta gyar’ɗa tare da cewa.
“Eh wallahi dama so nake idan ka fito zanje in dubata Idan ka amince”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Ayyah to ba matsala ki Gaishe su”.
Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya na shiga falonta ta kalli Amina dake zaune kan 2sitter gyara zama Amina tayi tare da cewa.
“Mommy wai ɗazu hayaniyar me nake jine ina waya da Uncle Naseer ne yana gaya min tsarin ginin gidansa da ake gyarawa a cikin Abuja yace min in anyi aure zamu zauna a nan na wata ɗaya zuwa biyu kafin mu tafi India, shiyasa ban fito ba”.
Cikin jin dadi tace.
“Alhamdullah kice dai abu yanata kankama”.
Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.
“ Eh Ummah Amman Hayaniyar me akayi ɗazun”.
Taɓe baki Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Ooo Kakar Khausar ce kuma yau tazo tana ta bala’i, banma san bala’in da take ba na dai ji tana cewa Khausar bata da kunya zata kalli tsabar idonta tace batason mijin da ta zaɓa mata tana da wanda take so, to bansan ya ake ciki ba dai. Ni dai tsoro na kaddai Nasseru take so?”.
Gyara zama Amina tayi tare da Girgiza kai kana tace.
“Ba dai Uncle Naseer ba Dan ko magana bata mishi, sai in shi ya mata, shima kuma baya mata magana sosai da nace masa bana so.
Sai dai ko ina wani can daban wayasan mata”.
Cikin jin daɗi Hajia Bunayya tace.
“Ato da sauƙi”.
Ita ko Amina gyara zama tayi tare da cewa.
“Uncle Naseer Kam yanzu ma wayar da muke yine, ya hanani fita.
Kuma cewa yayi anfara hada kayan lefe sannan kuma idan an tashi da kayan lefe da kayan gishi da goro da sadaki da kayan rufi duk za ahaɗa rana ɗaya za akawo”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da Jinjina kai.
Ajiyar zuciya Amina tayi kana ta cigaba da cewa.
“Kuma yace nan da wata ɗaya za’a ɗaura Auren mu sannan ana gama bikin a Abuja zamu tare baza mu wuce wata biyu ba in yayi yawa ne uku zamu wuce India sannan zai nema min admission In cigaba da karatuna”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da ran gaɗa guɗa kana tace.
“Alhamdulillah burina ya cika haka nake son ji da ace mun na cewa batun wannan yaron Jameel gashi ƴan Kidnapping sun kashesa a wofi”.
Kai Amina ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai dai kam Umma Allah ya rufa mnaasa asiri da na nacewa batun Malam Jameel da yanzu na zama matar Mamaci ina takaba”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.
“Aikam Allah ya tsareki yaje can Allah ya jikansa da Rahma”.
Cikin sanyin murya Amina tace.
“Ameen dai tun da yana da kirki Allah ya jikansa Allah yasa ya huta amma dai na kama dahir dana kama Uncle Naseer”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Kin kama dahir kam”.
Asiya ce da bata cika shiga mgnar suba, tunda Hajia Bunayyah tace mata zata tsine mata in tana damunta da batunsuji tsoron Allah, a hankali ta ninke hijabin da tayi salla dashi tare da miƙewa ta fito falo tana maiyi musu addu’ar shiriya.
Ita kuwa Amina da baki ta nunata.
Shashar uwa sai dariya tayi.
Suna cikin hiran wayar Hajiya Bunayya ya hau ruri tana dubawa taga Hajiya Lami cikin sauri tayi Picking tare da kaiwa Kunnenta Hajiya Lami najin tayi Picking batare da tayi Sallama ba ta fara kora mata jawabin abinda Samira ta faɗa mata.
Zare ido tayi cike da damuwa tace.
“Subhanallah toh Meyesa haka?”.
Cike da damuwa Hajiya Lami tace.
“Ban saniba amma ki shirya da daddare bayan sallar Isha’i ki rakani”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh nima zanje dama in Faɗa masa maganar Amina don tuni anfara hada kayan lefe, Gishiri, Goro, kayan rufi, da sadaki duk lokaci ɗaya za’a kawo kinga hankali ya kwanta”.
Jinjina kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“A hankali ya kwanta kam bari sai nazo ɗin dai”.
Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.
“Toh sai kinzo ba komai ki kwantar da hankalin ki”.
Aɓangaren Innayi kuwa har maghariba bata ji motsin Moddibo ba sosai hankalinta ya sake tashi.
Wunin ranan yini tayi tana kuka wanda lokaci ɗaya zazzaɓi ya kamata baki daya tunaninta ya ta allaka akan idan ta mutu ya Moddibo zai kasance awannan gari ya zaiyi.
Wasa-wasa har aka Idar da maghariba da Isha’i har misalin goma ba Moddibo ba labarinsa cikin sanyin jiki da tashin hankali ta miƙe ta nufi sashen sa tun kafin ta ƙarasa hawa barandar ta jiyo sheshsheƙan kukan sa cikin sauri ta ƙarasa hawa barandar tare da Murɗa Kofar falon tashiga kan Sallaya ta hangosa yayi Sujjada yana sheshsheƙa.
Cikin sauri ta zauna gefensa Muryanta na rawa tace.
“Subhanallah haba, Aliyu!, Haba Aliyu!!. Meyesa haka Aliyu ka ɗauki dangana mana kuka shine abinda zakayi ta raka Jameelu dashi arayuwar ka wannan soyayya itace zaka nunawa Jameelu kenan?”.
Anutse ya ɗago daga Sujjada tare da yin tahiya kana yayi sallama yana sheshsheƙa kana ya daga hannunsa biyu sama cikin raunin murya yace.
“Ya Allah Ubangiji kasa mafarki nake, Allah kasa in farka daga wannan hautsinennen mafarkin da nakeyi”.
Ahankali Innayi ta matsa kusa dashi tare da Kallonsa cikin sanyin murya tace.
“Haba Aliyu Meyesa kakeyi yin haka? ka kwantar da hankalin ka babu abinda ya gagari lamarin Ubangiji”.
Domin Ita batasan cewa yaji maganar da sukayi da Hajja Nana ba.
Ahankali ya ɗago idanunsa da suke kada sukayi jawur tamkar garwashi cike da mamaki take kallon yanda idanunsa suka sauya launi Muryanta na rawa tace.
“Aliyu lafiyar ka kuwa?”.
Kai ya Girgiza tare da cewa.
“Bakomai”.
Ya faɗa tare da lumshe Idanunsa domin ya rasa ta yaya zai fara tambayarta shin inane asalinsa shin waye mahaifinsa su waye ne tushensa, yanaso ya tamyan amma ya najin tsoro da fargaba da taraddadin ya tambaye, ya zama cewa kalaman da Hajja Nana ta faɗa da kuma zarginsa na tsawon shekaru ya zama gaskiya hakan yasa yaji tsoron tambayarta kamar yadda ya saba, haka ya meda tambayar cikin ransa, sunkuyar da kansa ƙasa yayi.
Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da rarrashin sa domin duk azatonta mutuwar Jameel ya tuna cikin rarrashi ta cigaba da cewa.
“Aliyu kayi haƙuri kowa da irin ƙaddarar da Ubangiji yake masa Addu’a zamu masa”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi hawaye ya cigaba da kwaranya daga Idanunsa.
Innayi kuwa cikin sanyin murya ta cigaba da cewa.
“Kada kayi kuka Aliyu ko wani irin matsala ka shiga arayuwar duniya kada ka butulcewa Ubangiji da irin wannan kukan, babu abinda zai kawo maka banda tashin hankali da damuwa”.
Ta ida maganar tana zubda zafafan hawaye, kukan abubuwa biyu ne suke haɗe mata alokaci ɗaya kalaman Hajja Nana da kuma halin da taga Moddibo aciki yayi masifar ɗaga mata hankali.
Anutse Moddibo yasanya tafin hannunsa yashiga share hawayen fuskarsa muryarsa na rawa yace.
“Toh shikenan Innayi nayi shiru dan Allah kema ki daina kuka Ubangiji Allah yarufa mana asiri”.
Cikin muryan kuka tace.
“Ameen ya Allah”.
Miƙewa tayi tare da fita ba daɗewa ta dawo hannunta riƙe da Warmers din abinci ta ajiye masa agabansa kana tace.
“Gashi kaci abinci”.
Kai ya Girgiza kana yace.
“A’a Innayi bazan ciba aƙoshe nake”.
Jinjina kai tayi tare da miƙewa ta dawo hannunta riƙe da wani bowl dake ɗauke da Fruit ta ajiye masa kana tace.
“Toh kaci wannan”.
Kai ya gyaɗa kana ya fara ci ahankali.
Ganin ya fara ci yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa.
“Toh sai da safe”.
Sannan ta fice domin bata da nutsuwa atare da ita.
Washe gari Da safe Ganin Moddibo bai zoba yasa Abba yashiga motarsa kai tsaye gidansu Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ya fito daga bakin gate ɗin farko ya tsaya yayi sallama Innayi dake Alwalan sallar Walha ta miƙe bayan ta ida ta nufi ƙofar tare da amsa masa Sallamar.
Bayan sun gaisa Abba ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.
“Dama Moddibo ne nake son ganinsa kuma bai zoba”.
Cikin sanyin murya Innayi tace.
“Hmm Moddibo ai jiya wuni yayi aɗaki yana kuka babu inda ya fita”.
Cike da alhini Abba yace.
“Subhanallah ni kuwa dama al’farma nazo nema Aliyu yamin taimako”.
ya ida mgnar cikin alamun neman al’farmar.
Haka yasa Innayi ta ɗan juyo ta kalleshi da kyau kana a hankali tace.
“Alhji Bashir ai ka wuce haka, kawai Umarni zakiywa Aliyu, kamar yadda kakeyiwa Jameelu da izinin UBANGIJI kuma zai cika maka umarninki. Aliyu ɗan ka ne, kadama kacemin komai kawai ka bashi umarni yamaka duk abinda kakeso ni kam na amince duniya da ƙiyama”.
Cikin jin daɗi kara da kawaicinta gareshi yace.
“Nagode da mutuntaka Allah ya bar zumunci”.
Amin tace tare da juyawa
tayi gaba.
Abba na bin bayanta zuwa falon Moddibo tsaye Abba ya gansa afalon yana ƙoƙarin fita.
Cike da ladabi yace.
“Ha’a Abba kazo ne?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh naga shiru-shiru Aliyu ba kazo ba tun jiya”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da faɗin.
“Eh dama yanzu nake shirin fita zan biya ta gidan Ummi sannan na ƙara so wajenka”.
Ahankali Abba yace.
“Allah sarki to zamu tafi tare”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh”,Sannan suka fita.
Cikin sanyi da
disesshiyar murya yace
“Abba na rasa ta ya zan gayawa Innayi batun
tafiyar nanfa”.
Juyowa Abba ya ɗan yi
ya kalleshi na second uku kana yace.
“Munyi mgnar da Innayi tace, babu matsala duk abinda ya dace in saka kayi min ta amince”.
Cike da mamakin amincewar tan yace.
“Ta yarda”.
Ka Abba ya gyaɗa mishi yana mai ci gaba da tuƙi.
Acan gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyar Hajja Nana Mommy ta fita sabgar Khausar da zaran ta gifta gefen da Mommy take Mommy zata kawar da kanta tare da dauke Idanunta akanta kana Uffan bata ce mata ba ko da safe da Mommy ke haɗa breakfast Khausar na shiga da niyyar tayata ta batare da tace mata Uffan ba ta nuna mata hanyar fita cikin rauni tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri na tuba”.
Cikin fushi Mommy ta nuna mata hanyar fita ba tare da tace komai ba.
Da gudu Khausar ta juya tare da nufar Bedroom ɗinta tana shiga ta faɗa kan gado tare da fashewa da matsanancin kuka.
Haiydar ne yashigo falon jin sheshsheƙan Kukan ta a Bedroom yasa ya nufi Bedroom Cike da kulawa yace.
“Adda Khausi Meye sameki?”.
Ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye tayi tare da Kallonsa tace.
“Haiydar Mommy fushi take dani”.
Cike da Mamaki yace.
“Fushi kuma? to me kika mata?”.
Kai ta girgiza still tana kuka tace.
“Nima ban sani ba amma Mommy fushi take dani”.
Ajiyar zuciya Haiydar ya sauke tare da cewa.
“Toh Addah Khausi muje kibata haƙuri kinji ko?”.
Nunfashi me zafi ta fesar tare da Kallonsa kana tace.
“Haiydar Ina tsoro”.
Kai ya Girgiza tare da sassauta muryarsa yace.
“Toh idan baki bata haƙuri ba so kike tayi ta fushi dake?”.
Be jira cewar ta ba ya riƙo tsintsiyar hannunta suka fita, ganin Mommy bata falon yasa suka nufi kichen still Nan ma bata nan kai tsaye Bedroom ɗinta suka nufa zaune suka sameta abakin gado da alamar bata daɗe da fitowa daga wanka ba ta gama shiryawa tana ɗaure yalwataccen sumar kanta da Ribont.
Tsugunna wa Haiydar yayi agabanta tare da jan hannun Khausar itama ta tsugunna cikin sanyin murya da neman yafiya Haiydar yace.
“Ayyah Mommy dan Allah kiyi haƙuri Addah Khausi tace kinyi fushi da ita tun jiya bakya mata magana”.
Kallonsu Mommy tayi tare da kawar da kanta gefe Khausar kuwa da hawaye ke kwaranya daga Idanunta yayin da kanta ke ƙasa.
Miƙewa Mommy tayi kana ta cigaba da shirinta ba tare data tanka suba ta ɗauki turare ta feshe jikinta.
Cikin sanyi Haiydar ya mike tare da ƙarasawa gaban Dressing mirrow ya durƙusa kana Cike da ladabi yace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri Idan akwai abinda tayi miki mu baki haƙuri”.
Banza Mommy tayi dasu ta cigaba da shirinta.
Cikin raunin murya da tsanananin tashin hankali Khausar ta shiga Girgiza kanta tana sakin kuka, kana Idanunta na zubar da hawaye Shar-shar muryanta na rawa tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri ki yafemin, kinsan fushinki masifa ce agareni”.
Uffan Mommy bata ceba ta koma bakin gado ta zauna cikin sanyi jiki Haiydar da Khausar suka bita da rarrafe suka durƙusa a gabanta, ido ta zuba Khausar tana kallon yadda take kuka,
Ita kuwa Khausar ta kasa ɗago kanta, sai hawaye dake cigaba da zuba shar-shar.
Cikin muryar dake nuna ɓacin rai Mommy tace.
“Toh Kuma kukan me kike yi bayan kinyi abinda ranki keso.
Ai dariya ya kamata kiyi tunda har kin kai matsayin zaɓawa kanki miji, kin iya fetsare idanu gaban manya kice ke ga wanda kikeso. kin jamin tashin hankali da zagi awajen kakarki”.
Haiydar kam ido ya zubawa Mommy don bai taɓa ganin tsananin ɓacin ranta irin na yau ba.
Mommy kuwa cikin fushi ta cigaba da cewa.
“Tsohuwar da kinsan ba kirki da kara bane da ita, ta fita tsakiyar gida tana min ihu da haushi tana tara min mutane, Kina sane da cewa duk abinda kika yi laifinsa kaina yake dawowa, sannan duk abinda kikayi Ni bansan dashi ba bansan yaushe kika tsara ba ban isa ki gaya min sirrinki mu biyuba sai kin bari a tsakiyar mutane”.
Ajiyar zuciya Haiydar ya sauƙe tare da cewa.
“Dan Allah Mommy me tayi miki ne?”.
Cike da ɓacin rai Mommy ta kalli Khausar kana tace.
“Ai ita tasani ta faɗa maka me tayi”.
Ahankali Haiydar ya juya tare da kallon Khausar yace.
“Addah Khausi me kikayi?”.
Kallon Mommy Khausar tayi Muryanta na rawa tace.
“Dan Allah Mommy kiyi haƙuri?”.
Girgiza kai Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.
“Toh me kike nufi da kalmar da kika faɗa?
Kince ba kyason Naseer na gamsu domin Ni kaina bana son Naseer tunda nasan abinda ke tafiya, sannan na fahimci yanzu Ameena yake so”.
Kuka kawai Khausar keyi Allah ne kaɗai yasan me take ji aranta.
Mommy ta cigaba da cewa.
“To amma shi Aliyu Meye lefinsa ɗan uwanki ne sannan zai riƙe da amana da gaskiya kamar yadda ya riƙe yar uwarki. Baffanki bazai bari ya to zarta kiba sannan kinzo min da wata magana wai Moddibo kike so ko kunya baki jiba”.
Ahankali Khausar ta ɗago kanta kana ta rumtse idanunta dake zubar da hawaye Muryanta na rawa tace.
“Mommy dan Allah kiyi haƙuri abar batun Yah Aliyu ayi batun Aurena dashi Mommy wlh ni Moddibo nake…!
Ikon Allah sai kallo wai fa Modibbo takeso.
*Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ki biya ki karanta cikin Aminci yafi ki karanta na sata kuma na Allah ya isa, 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in tura miki littafin*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*