Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 9

Sponsored Links

9……

Sai kusan karfe biyar din yamma Khaleel ya dawo da boys din, da kayan wasa suka shigo mata ko wannensu baki har kunne, kana ganinsu kasan they are just happy, ta ajiye handout din hannunta tana kallonsu ta nuna masu hanyar bedroom alamar su wuce ciki, basu mata musu ba suka wuce, mikewa tayi ta isa kofa ta sa makulli sannan ta bi bayansu, tsaye ta samesu sun yi tsuru tsuru, ta hade rai tana kallonsu gaba daya tace “Ku gaya min daxun da ku ka je ajiye cup a kitchen me ku ka tsaya yi?” Duk suka ki cewa komai ko wannensu a tsorace, tace “Ba magana nake maku ba?” Sudais ya kalli Shuraim sannan yace “Anty mun ga uncle a waje shine ya xo wajen window yace mu fito, ni nace A’a, sai Shuraim yace xa ki mana duka” daga haka yayi shiru, ta kalli Shuraim strictly tace “Sai me ya far kuma?” Shi ma kamar xai yi kuka yace “Shine sai ya tambayemu inda kike sai Sudais yace kina parlor” shiru yayi shi ma, ta rungume hannayenta ta kalli Sudais tace “What now happened after that?” A hankali yace “He told us to remain in the kitchen he will come pick us…. And, shine kawai muka gansa ya shigo ya tafi da mu” tana kallonsu da kyau tace “Good… Next time baxa ku sake xuwa wajena ba kuma xan fadi ma Mumy duk abinda ku ka yi tunda bakwa ji” hawaye su ka fara yi suna bata hakuri, bata bi ta kansu ba ta yi fitowar ta parlor. Ranar lahadi Khadijah na kitchen tana dama masu custard kamar yanda suka bukata taji an danna kararrawa, kusan a tare da Nanny dake masu wanki a bathroom suka fito, ganinta Nanny ta juya ta koma, ita kuma ta sa hijab ta iso gun kofar, a hankali tace “Waye…” Yace “Kin sani” k’in bude kofar tayi tace “How can I help you?” Yace “In bude kofar kenan da kaina” shiru ta yi na ‘yan sakwanni kafin ta bude kofar, da sauri ta bar bakin kofar ganin shigowa xai yi kuma bai damu da cewar sai ya bugeta kafin ya shigo ba, yace “Where are they” ta hade rai bayan ta bar gun tace “Breakfast xa su yi” lkci daya duk suka fito daga dakin suka tsaya cirko cirko, sakin baki tayi tana kallonsu, arms akimbo ya tsaya kallonsu shi ma yana murmushi, can a hankali yace “Good morning boys” suka washe baki a tare suka ce “Good morning Uncle” yace “We’ve got 2 more places to go… So…” A hankali Shuraim yace “Noo we won’t make it up” ya buda ido yace “Why” duk suka kalleta, Khaleel ya kalleta shi ma sannan yace “What about her?” a hankali Sudais yace “Aunt was angry at us yesterday, she promise not to let us come over again for holidays” Buda baki tayi tana kallonsu, Khaleel yace “Ohk, haka kika ce masu” ta hade rai ta kallesa tace “Ni bance masu haka ba, they misunderstood me” yace “Ohk to fahimtar da su abinda kike nufi ynxu” ta kallesu tace “Oya ku bi sa ku tafi” Shuraim ya kamo hannunta yace “Sure Anty?” Ta dake tace “Yeah” rungumeta suka yi gaba daya da murna suna ce mata thank you aunt, Khaleel ya kama hannunsu suka fita yana murmushi, banging kofarta tayi bayan fitarsu rai a bace. Ba su tashi dawowa ba sai da daddare don ita har ta kwanta sbda takaici gashi gobe xa su koma, wato ba gunta twins din suka xo yin hutu ba wannan karan kawai, Nanny ce ta shigo daki da uban ledoji ta mike xaune tana kallon ledojin, rungume ta boys din suka taho suka yi da gudu ko wannensu na kokarin expressing kansa ya bada labarin abubuwan da ya faru, sai kuma suka sauka kasa suna bude mata ledojin, mamaki duk ya cikata ganin uban abubuwan da ya siya masu har da kaya da abubuwan makaranta, haka ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nanny kam sai yabawa take tana shi masa albarka, ita dai bata samu bakin cewa komai ba har Nanny ta ja su ta masu wanka, bayan ta shirya su xuwa rigunan baccin su tayi masu tayin abinci suka ce sun koshi, daga haka suka kwanta bbu bata lkci bacci yyi gaba da su, Nanny ta wuce dakinta, sae a snn Khadijah ta samu kwarin gwiwar sakkowa daga saman gado tana kallon tsaraban cike da mamakin yanda ya san gobe xa su koma, bata kwanta ba sai da ta gama hada masu duk kayansu da za su koma gida da, taji har ta fara jin kewan yaran gashi bata samu lkcn su yanda take so ba. Washegari kafin karfe takwas har ta gama shiryasu nanny ma ta shirya, tana kokarin fita kira masu taxi aka danna bell, lkci daya kuma ya bude kofar yana mata kallon cikin ido a hankali yace “Morning” sauke kanta tayi wondering anya yasan abinda yace kuwa, don gaisuwa bai taba hada su ba, “Same to you” ta mayar masa, a takaice yace “Yaushe xa su wuce airport din” tace “Yanxun xa mu wuce” yace “Alryt, ina jiran ku” ta bi sa da ido bayan ya juya. Shi ya kai su har airport din a motarsa duk da bata so hakan ba amma twins suka gwaleta, suna isa duk jikinta yyi sanyi, yanxu fa komawa yaran xa su yi su bar ta, su kansu sai bata rai suke suna shisshige mata, shi ya rakasu daga karshe don ita kam kasawa tayi, sae d’aga mata hannu yaran suke, kasa daurewa tayi bayan tafiyarsu ta hade kai da gwiwa a inda take xaune, bayan kusan minti goma Khaleel ya dawo, muryarsa taji yace “Heyy” ta dago kanta a hankali, ya d’an bude ido yace “Waow, kuka kike?” da sauri ta goge idonta don bata san ma tana yi ba, yyi murmushi yana shafa kai yace “Su ma kinga kukan suke, Ashe sun ji a jikinsu kina kukan ne” tashi tayi da sauri tace “Kuka suke?” yace “Yea but I made sure sun yi shiru before I left, the bond between u and ur Siblings is really amazing….” daga haka ya fara tafiya yace “let get home” bin bayan sa tayi a sanyaye har suka isa gun motar sa, a hankali ta sa hannu ta bude front seat ta shiga, babu wanda yace komai cikin su yana driving, tsaki yyi bayan wani lkci ya jawo wayarsa dake ta ring tun fara driving dinsa yyi silencing wayar ya ajiye, ita dai tayi nisa tunanin da take na su Shuraim, yana gama parking a gida murya can kasa tana wasa da yatsunta a hankali tace “Thank you very much, Allah ya saka da alkhairi” kamo hannunta yayi yace “For?” Ta fixge hannunta hade da galla masa harara daga haka ta bude motar ta fita ta nufi flat dinta ya bi ta da kallo ta madubi. Tun da ta shiga bedroom dinta take bacci har azahar, biyu da rabi ta tashi ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana gabatar da sllhn zuhr ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, ko ba a fadi mata ba tasan ita kadai ce gidan coz everywhere was very silent, ta gama cin abinci ta dau materials din karatunta don rabonta da karatun tun xuwan kids din, gashi yau ma tana da lectures bata je ba, sai sha biyu saura na dare ta hakura da karatun ta kwanta don gobe da safe take da lecture. Washegari takwas saura ta fito xata wuce makaranta, dai dai fitowarsa shi ma, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta kara pace dinta, kafin kuma ya fito da motarsa har ta hau taxi abun ta. Karfe uku da wani abu suka fito school tare da Vanessa da Angela, sauraren Vanessa dake mata korafi ta gama yi kafin tayi ‘yar dariya da halshan turanci tace mata ba wai ta fasa xuwa bane xata dawo gidan nata amma sai during weekend, ko da wasa bata nuna mata su shuraim sun xo ba balle ta sake jin haushin rashin kawo su da tayi, juyawa Khadijah tayi tana kallon direction din da Angela da Vanessar ke kallo, sai a snn ta ga motar da ya tsaya gefensu dai dai lkcn da kuma ya sauke glass, hannu ya daga ma su Vanessa a hankali yace “Hi” suka mayar masa da “Hello” Ya kalleta yace “Are you heading home?” Tunani ta fara yi shi kuma wannan yaushe suka fara yin haka da shi, wani kallo tayi masa tace “Noo thank you” wani murmushi yyi yana shafa millionaires belt dinsa yace “Ohk a gaban kawayen naki xaki ce min A’a” Tace “Ka saba daukata ne?” Yace “Xan fara yanxu, shiga mu je” tabe baki tayi bayan few seconds ta kalli su Vanessa tace “Alryt, see you girls tomorrow” daga haka ta xaga ta bude front seat ta shiga ta kulle kofar, daga masu hannu yyi ya ja motar suka bar gun, basu yi tafiya me nisa ba yace “Twins sun isa lafiya?” Ta gyada kai tace “Sure” wayarsa dake ajiye kusa da ita yyi haske ta sauke kai tana kallon screen din, “Jawahir” sunan dake saman screen din kenan ta dauke kanta, bayan seconds kusan biyar ya dau kiran yace “Am driving baby, xan kira ki when am home” daga haka ya katse wayar ya mayar ya ajiye, suna isa gida yyi parking ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi apartment dinta, xaro ido yyi ya bi ta da kallo.

Washegari Tuesday da yamma ta shirya bayan ta dawo makaranta don xuwa shopping mall ta yi shopping din turarurruka da man shafa, karamar jakarta ta sakale kafadarta ta fito ta rufe apartment dinta, ganin motarsa a parking space yasa ta gane yana nan don tun da ya ajiyeta jiya rabon da su hadu, babban shopping complex ne wajen ta gama daukan mayuka da turarukan da xata dauka, tayi deciding hadawa da disinfectant da antiseptics, Dettol babba ta dauka bata lura da mutumin dake bayanta ba kamar yanda shi ma din da alamar bai lura da ita ba don backing din juna suka yi, lkci daya suka juyo kusan a tare suka ci karo, pack din Sabulun dettol dake hannunsa ya fadi kasa, da sauri suka durkusa kusan a tare again ta rigasa daukan sabulun kafin ya kai hannunsa tace “Ohh sorry pls, I…i…” dai dai sanda suka mike tsaye ido cikin ido, shekaru kusan hudu kenan rabon da ta ji abinda taji a xuciyarta lkcn, a hankali ta saki dettol din hannunta tana kallonsa bbu kiftawa, wani kallo shi ma yake mata da wani expression, yana son magana amma da alama words din sun kasa fitowa, lkci daya words din yyi escaping lips dinsa cikin wani yanayi yace “IMANN….” Juya masa baya tayi tana ganin turawan da ke d’an nesa da ita doubled doubled, kawai ta nufi kofar fita complex din, tana jin yana kiranta da alamar bin ta yake ta kara saurinta, cikin sarkewar murya tace ma baturen gun ta mance ATM card dinta a gida yana bude mata kofa ta fice fittt without thinking twice ta nufi bayan mall din kamar xata tashi sama, ta xauna nan kasa jikin bango ta kai hannu dai dai kirjinta ta runtse ido, ta fi minti sha biyar wajen xaune, ji take kamar an mata alluran tsayar da Adrenaline ne don komai na jikinta gani take ya daina aiki kamar ba nata ba.

*Haske Writers Association*💡

✨ *Noor-Al-Hayat*✨

Back to top button