Noor Al Hayat 7
By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
7…..
Matar farouq ta sakko suka gaisa da Aliyu tayi serving dinsu abinci ta koma daki, farouq na lura da abokin nasa dake cin abincin a hankali, yayi breaking silence din after a while yace “Toh tun yaushe kasan Iman din nan ni dai ka ban labari frnd” Aliyu ya dago yana kallon sa, murmushi yyi ya ajiye spoon din hannunsa yace “Tun tana shekara sha hudu…” Farouq ya wara ido yace “Kace yanxu ta girma kam” Aliyu ya d’an bude ido yace “Uhn” Farouq yace “Kuma yaushe rabon da ka ganta a mafarkin naka” wani kallo Aliyu ya watsa masa yace “Ce maka nayi a mafarki na santa?” Farouq yace “Au, nayi xaton a mafarki ne ai” tsaki Aliyu yyi ya mike yace “Da gaske ka ma mayar da ni mahaukaci wllh” farouq yyi dariya sosai, Aliyu ya dau makullinsa yace “Am full frnd, gobe xan tafi UK in sha Allah” Farouq yace “UK? Ba last month ka dawo ba?” Aliyu yace “Yeah ina da aiki can, beside na fi jin ddin can wllh, ba takura…” Kofa ya nufa farouq ya mike ya bi bayansa, har gun mota ya rakasa Aliyu ya shiga ya tada motar yace “Toh sai na dawo frnd, a kulan min da boys dina” Farouq yace “Toh Allah ya tsare, ya sa ka taho mana da tsarabar mata ko da baturiya ce wllh don na gaji da ganin ka ba aure” d’an murmushi Aliyu yyi yace “Toh Abba….” farouq yace “Allah kuwa, Abban ma da ya gaji ya xuba maka ido ynxu, ni wllh da ma kawai su yi taking dinka unaware kana dawowa sai dai kaji ai an sa ranan ku da Hanan, ga mace har mace tana son ka amma kayi ta mata jan aji kana jiran Iman Aljanar ka, ni wllh ko Salmah ce a hadaku, ka kuma san gwara Hanan sau dubu kan salmah…” Aliyu bai ce komai ba don har ya 6ata masa rai, ya ja motarsa kawai ya bar gun Farouq na dariya.
Tunda Khadijah ta shiga daki ta sa key bata sake lekowa parlor ba kusan awa daya da rabi kenan, ita dai ta ga abinda ya isheta…. Khaleel taji kanwarsa ta kirasa da ko wa?? Kwafa tayi ta juya xuwa daya side din gadon da take kwance, kallon agogo tayi a hankali ta jawo wayarta dake gefenta ta gama dialing number ta kai kunne, Muryar Nanny taji, bayan sun gaisa tace “Umma fa?” Nanny tace “Umma na tare da bakuwa….” Tace “Toh xan kira xuwa anjima….” Nannyn tace “Ga su Sudais….” Khadijah ta d’an buda ido tace “Boy… how you?” Shiru tayi tana apprehending abinda twins din ke gaya mata a waya duk jikinta yyi sanyi sosai, Shuraim yace “Hello… Are you there Anty?” Ta lumshe ido ta bude cikin sanyin murya nace “Yea soldiers, hope ba ku ji ciwo ba” Shuraim yace “Not at all aunt, we where just freaked out, and an Uncle consoled us right there and made sure we where fyn, he was kind aunt….” Tace “That nyc of him, But did you both prayed?” Duk suka ce “We did…” Tace “Good, you make prayer ur daily routine before leaving home and when coming back, clear?” Suka ce “In sha Allah aunt” tace “Hand the phone over to Nanny…” ba musu suka kai ma Nannynsu wayar, ba su dau lkci suna magana ba tayi mata sallama ta ajiye wayar duk da ta so magana da Umma, har lkcn hankalinta ya kasa kwanciya, mikewa xaune tayi a hankali, she can’t imagine loosing the boys, she just can’t….. Tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ta rike kai tana jin dama ta gansu kusa da ita a yanxu, ita kanta bata san wani irin soyayyan yaran bane ya dirar mata all of a sudden tun daga shekaru biyun da suka wuce, unlike before, kamar yanda bata son mutuwarta until her God is please with her haka bata son su, bata son su kusa da ita but now…. Reverse is d case, Allah yasan yanxu bata da kamarsu a duniyar nan gaba daya, she just love them, she know she love dem dearly… Ji tayi kamar xata yi xaxxabi ta koma ta kwanta, nan bacci ya dauketa, ba ita ta farka ba sai kusan magrib, bayan ta idar da sllh ta bude kofar dakin a hankali tana lekan parlor, bbu kowa parlorn kamar yanda ta yi tunani, ta karasa ciki a sanyaye a ranta tace ae da ka xauna ka jira ni, ta isa gun main door ta sa makulli tana kallon tray din abincin da ta kai ma fatima daxu, toh ko shi ya kawo ya ajiye daxun, ta bude plate din dake a rufe taga da sauran Irish din, da alamar fatima bata ci da yawa ba, ta dau tray din ta wuce kitchen, disposing din abincin tayi, duk da muryarsa da ta ji a baya bata leka ba har ta gama abinda xata yi ta bar kitchen din, Mis cals din Vanessa ta samu a wayarta, ta mayar da kiran bayan sun gaisa Vanessa tace yau ma tana ta jiranta, murmushi tayi tace “Sorry love, I had a visitor today, an unexpected one…” Vanessa tace “Alryt then, good nyt” daga haka Khadijah ta katse wayar ta ajiye, Daren ranan bata samu bacci me tsawo ba, don da tayi xata farka, karfe uku tana ta xaune har lkcn ta kasa baccin bayan ta idar da sallah, tashi tayi ta wuce kitchen don diban ruwan Lipton ta sha ko xata iya karatu, kamar ance ta daga kai suka yi ido hudu da shi xaune da uban textbooks a gaban sa yana sanye da siririn farin glass, ta cikin glass din yake kallonta, a hankali ta sauke idonta ta gama abinda xata yi ta kashe wutan kitchen din ta wuce. Har gari ya waye idonta biyu kamar warce ta sha wani abu, Shayi kadai ta iya sha da safe bayan ta shirya ta bar gidan misalin karfe bakwai da rabi don wucewa makaranta, throughout ranan bata da walwala a makarantar ma, bayan la’asar tare da Vanessa suka taho gidanta kamar yanda ta bukaci su je, suna gama cin abinci khadijah ta tafi tayi wanka ta bar Vanessa parlor tana kallo, bayan ta gama shiryawa ta dau waya ta shiga kiran Umma, a hankali ta gaisheta, bayan yan sakwanni tace “Umma yaushe su Sudais xa su yi Mid term break?” Umma tace “Mid term… gobe ne ai….” Ta d’an yi shiru sannan kamar me tsoron magana tace “Toh, dama Umma don Allah da sai su taho gu na da Nanny suyi hutun a nan plss” Umma tace “Saboda rashin hankali” shiru ta yi bata ce komai ba, Umma tace “Shi hutun kwana hudun ne xa su kwashi jiki su tafi UK” Khadijah ta girgixa kai tace “Toh shkkn Umma kiyi hakuri” Umma ta katse wayar ta, misalin karfe shidda suna xaune waje da Vanessa suna duba wani material na karatu khaleel ya bude kofa ya fito, 3 qtr da singlet ne jikinsa, tun da ta kallesa sau daya ta mayar da kanta kasa bata sake daga kai ba, taji Vanessa tace “Good evening” cikin cool voice dinsa yace “How you?” Tace “Am great” ya saci kallon khadijah sai kuma ya juya ya koma ciki, Vanessa tace “Ur neighbor?” Khadijah tace “Yeah” Vanessa ta wara cat like eyes dinta tace “He is damn cute, a Nigerian also?” Khadijah ta nuna mata kofar flat dinsa tace “You can ask him” Vanessa tayi dariya tace “Sure I can” suna nan xaune har kusan goman dare, Khadijah ta san ba don suna wajen ba da yanxu ya fito, sai taji dadin hakan ko ba komai dai sun hanasa xama wajen, a ranta tace ba don ba don ba ma a nan xata kwana a xaune, sha daya saura suka tattara takardunsu suka wuce ciki, ae kam ko minti takwas ba su yi da shiga gida ba taji fitarsa, Missed calls din Umma ta gani har biyu a phone nata dake daki, ta shiga kiranta bayan tayi shirin kwanciya, Umma tace “Kin yi bacci ne” ta girgixa kai tace “Yanxu xan yi Umma” Umma tace “Tunda ganin yaran kike son yi gobe xa su bi train xuwa Abj su yi boarding plane….” Khadijah ta d’an xaro ido tace “A’a Umma hutun ba yawa ai” Umma tace “Ai kinsan da ba shi da yawa kika ce su taho, so keep shut” shiru ta yi bata iya tace komai ba har Umma ta katse wayar, har ranta taji dadin abinda Umma tace, tayi murmushi ta kwanta hade da lumshe ido.
“Sir ga mu Airport din…” Dago kai Aliyu yyi da sauri daga danne dannen wayar da yake yi, ya kada kai yace “Alryt Bilyamin thank you” daga haka ya bude motar ya fita yana rike da karamin travelling bag dinsa, in 2 hrs and a halve har sun shigo Abj daga kd, ko don yayi gudu ne, “Amin nagode” amsar da ya ba Bilyamin kenan dake masa Allah ya kiyaye hanya ya bar gun ya nufi hanyar shiga cikin airport din, yana jin wayarsa na ring a aljihunsa amma sanin warce ke kiransa yaki fiddo wayar. Aliyu na kokarin ajiye karamar jakarsa sama bayan an shiga jirgi ya ji an taba sa, juyowa yyi da sauri, lkci daya ya wara dara daran idonsa ya durkusa yana kallon Little Shuraim dake masa murmushi yace “Waow handsome we met again” Shuraim yace “Sure!” Aliyu ya juya ko xai ga any of his parent ganin babu yace “So how you?” washe hakora shuraim yyi yace “Am fyn Uncle, and you?” Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace “Same sweetheart… Where is ur twin” nuna masa Sudais dake kusa da Nanny tana bude masa cake dinsa a leda yyi, Aliyu ya dinga kallon matar kafin yace “Is…. that your mum?” Shuraim ya girgixa kai yace “Noo she’s our Nanny, we left mum at home, we r going to meet aunt in UK in sha Allah” Aliyu ya gyada kai yana mamakin sharpness din yaron don da ganin sa baxai wuce shekara biyar ba, ya kamo hannunsa yace “That’s nyc my boy, am also heading there, What’s ur name?” “I am Shuraim Muhd” Cewar Sudais yana wara masa ido, Aliyu yace “Waow, ur twin name?” Shuraim yace “Sudais Muhd” Aliyu yyi patting shoulder dinsa yace “That’s my boy” mikewa yyi ji da yyi ana announcing ayi fastening din seat belt, Tuni Nanny ta taho tafiya da Shuraim, kafin Aliyu yace komai yaron ya daga masa hannu yace “C ya uncle, well’ meet later, may be in UK….” daga haka ya bi Nannynsa Aliyu ya bi sa da kallo yana murmushi, xaunawa yyi seat dinsa, Baturiyar dake wajen tana murmushi tace “You’ve got a lovely son” Aliyu ya kalleta da sauri,
Sannan ya kalli Shuraim sai kuma yace “Ohhh thanks very much” har jirgi ya tashi Aliyu bai daina juyawa yana kallon cute twins din ba har ya lura sun yi bacci few hours later. Da yamma suka sauka Uk, Aliyu ya mike ganin Twins din duk bacci suke ya nufi Nannynsu da ke kokarin tada su gaba daya, yace “Bari in taimaka maki da guda daya Madam” bai jira cewarta ba ya dau Sudais don ya fi kusa da shi, ya rungumesa yana rike da jakarsa ya nufi kofar fita jirgi, Nanny ta bi bayansa da sauri tana rike da Shuraim da har ya tashi, sai da ya jira suka dau luggage dinsu sannan ya samar masu taxi… tuni Sudais ya bude ido yana kallon Aliyu ya wani tsuke fuska, Aliyu ya sakar masa murmushi yana kallonsa a hankali yace “How you Prince?” Sudais bai amsa ba sai ma kokarin sauka da ya fara yi daga jikinsa, hakan yasa Aliyu ya sauke sa yana kallonsa murmushin dake fuskarsa yyi fading a hankali, Shuraim dake rike da Nanny da ke kkrin saka jakar kayansu cikin booth din taxi yace “Uncle are we going the same way?” Aliyu ya kallesa sannan ya girgixa masa kai yana murmushi yace “No love” godiya Nanny tayi ma Aliyu ta shiga taxin Sudais ma ya shiga da sauri, Shuraim kam sai da ya daga ma Aliyu hannu yace “See u some other time” Aliyu ya gyada masa kai har lkcn bai daina kallonsa ba, Shuraim na shiga ya rufe kofar motar, Aliyu ya daga masa hannu shi ma ya daga masa yana washe set of teeth dinsa, har taxi din ya bar gun Sudais kin daga nasa hannun yyi sai ma dauke kai da yayi, Aliyu ya kasa dauke idonsa a kan yaron. A hanxarce khadijah ta gama daukan duk abinda tasan boys din suna so sanin sun kusa sauka ko sun ma sauka, ta nufi counter ta biya kudi ta bar Mall din, taxi ta samu ya kawo ta kofar gida ta fito ta basa kudinsa sannan ta shiga ciki, ko kadan bata ji dadin tafiyar Vanessa daxu ba, tana kkrin bude kofa taji tsayuwar taxi ta juya da sauri tana kallon gate, bayan minti biyu ta hango twins, ai bata san lkcn da ta ajiye ledar hannunta ba ta nufe su kamar yanda su ma suka nufo ta da gudu, durkusawa tayi ta rungumesu gaba daya suka kankameta barin sudais ita ma duk ta fi maida hankali kansa, kisses ya dinga mata a fuska, shuraim kuma ya dinga kyalkyala dariya yana kallon su, ganin ba saketa xae yi ba ta janye sa ta mike tana dariya ganin yanda Nanny ta tsaya kallonsu, Nanny tace “Toh ba mu kudi mu ba mai cab, ba currency din nan tare da ni” Tashi tsaye tayi da sauri ta bude jakarta ta ciro kudin kasar ta mika ma Nanny, kamar ance ta waiga taga Khaleel tsaye bakin kofar sa, tayi saurin dauke kai, Shuraim ya wara ido yace “Aunt you knw what” hannunsa ta kama da na d’an uwansa ta fara tafiya tace “No Darling” yace “We still met with that uncle I told you about….” Tace “Which?” Maimakon ya bata amsa sai ta ga ya tsaya yana gaida Khaleel dake kallonsu har lkcn, Khaleel yyi murmushi ya karaso wajen yana kallon yaron a hankali yace “How are you handsome?” Shuraim ya wara ido yana nuna masa wandonsa da yyi sagging yace “Am fyn, but….” tuni Khadijah ta ja Sudais da shi dama bai ma da niyyar gaida khaleel suka shiga cikin parlor a ranta tana cewa ita kam ta shiga uku da Shuraim, sai a sannan tace “Which uncle was ur brother talking about” Sudais ya yamutsa fuska yace “I don’t think I like him…” Ta d’an bude ido tace “Who?” Yace “The uncle he is talking about,” Ta langwabar da kai tace “Why” Sudais ya bude hannu alamar bai sani ba, tace “Where did you guys meet him” Sudais yace “Shuraim will make u understand Anty” dai dai nan Shuraim ya shigo tare da Nanny, ya taho da gudu ya hau kanta, yace “I missed you Anty” ta daura lips dinta a forehead dinsa tace “but I’ve warned you to stop talking to strangers times without number.. I mean that man u were greeting outside” Ya xaro ido yace “I never knew he was a stranger, sorry Anty” tayi murmushi tana shafa kansa tace “But you don’t knw him, so he is a stranger”
*Haske writers association*💡
✨ *Noor-Al-Hayat*✨