Noor Al Hayat 58
Aliyu bai ce komai ba ya tada motar a hankali ya bar premises din school din, har suka isa babu wanda yace komai, yana gama parking ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita tace “Nagode” yace “ki gaida min Shureim” ba tare da ta juyo ba tace “Ohkk” Da ido ya bi ta har ta shiga cikin gida, yayi wani murmushi ya ja motarsa ya bar wajen, tun da Khadijah ta shiga compound take ta kallon motar khaleel, lkci daya mood dinta ya canxa ta isa apartment dinta ta bude jaka ta fiddo makulli ta bude kofar ta shiga. Wanka tayi ta kwanta parlor ta fada duniyar tunani, murda kofar parlorn taji anyi ta mike xaune da sauri, Shureim ya shigo ya taho wajenta da gudu ya hau kanta yace “Anty we came back before you” ta rungumesa tace “How are you?” Yace “Am fyn” tace “Have you eaten?” Ya gyada mata kai yace “Uncle ya bani” tace “Toh mu je ka cire uniform” tashi tayi ta daga sa suka wuce bedroom, wanka tayi masa ta sa masa kaya da sweater ta bar sa dakin yayi assignment ta fito don daura girki. Tana kitchen tana fere Irish taji kamar mutum waje, a hankali ta leka window ta gansa xaune waya kare kunnensa, hada ido suka yi, ta dauke kai da sauri, ta ci gaba da abinda take cikin sanyi. Shidda da yan mintuna ta fito kitchen din bayan ta tsaftace ko ina, daki ta wuce taga Shureim kwance kan carpet yayi bacci, ta daukesa ta daura sa saman gado ta kwashe books dinsa ganin ya gama assignment din ta sa a jaka ta rufe, har xata fita wayarta dake kan gado yayi haske, ta karasa gadon ta dau wayar tana kallon screen din, alert ta gani na dubu dari da hamsin, a hankali ta ajiye wayar ta shiga bathroom, Karfe takwas saura Khadijah ta fito parlor da hijab har kasa, duk gaba daya ta rasa sukuni, a sanyaye ta wuce kitchen ta xuba abinci ta fito ta xauna, kasa cin abincin tayi ta tura plate din daga gabanta tana hadiye na bakinta da kyar, tashi tayi ta kara shiga kitchen ta dau warmer ta wanke ta xuba abinci a ciki ta rufe sannan ta fito, ta fi minti uku tsaye parlon kafin ta nufi kofa ta fita gabanta na faduwa, a hankali ta danna bell din khaleel, tana ta tsaye gun ga wani sanyi dake ta shigarta, ganin bai bude ba ta kara dannawa, lkci daya ya bude kofar tayi saurin sunkuyar da kanta kar su hada ido, barin bakin kofar yayi ya koma ciki ta bi bayansa kamar mai tausayin kasa ta rufe kofar sannan ta isa tsakiyar parlorn ta durkusa ta ajiye abincin hannunta ba tare da ta yarda sun hada ido ba tace “Good evening” Xaunawa yyi kan kujera yace “Evening ya kike?” A sanyaye tace “Lafiya lau” Yace “Ya lectures?” Shiru tayi bata ce komai ba, tana dai duke inda take yace “Baxa ki xauna ba” a hankali ta mike tace “Sai da safe” yace “Alryt, Allah tashe mu lafiya, todays cold isn’t gonna be funny ki sa ma Shureim sweater and lock all the windows” tace “Toh” daga haka ta nufi kofa xata fita yace “And….” Tsayawa tayi bakin kofar don jin abinda xai ce, yace “Thanks for the food” bata ce komai ba ta fita ta rufe masa kofar. Abincin da ta xuba ta kai kitchen ta fito ta kashe wutan parlorn ta wuce bedroom, warm water ta xuba a kettle ta daura alwala ta fito ta kashe wutan dakin ta hau gado ta kwanta kusa da Shureim ta rufa masu Duvet, har ta fara bacci vibration wayarta ya tasheta, ta bude ido a hankali ta jawo wayar, tasan Barrister ne xai kirata wannan lkcn, tayi picking call din ta kai kunne tayi sallama cikin sanyin murya, daga daya bangaren yace “Amira…” Tace “Uhm Ina yini?” Yace “Lafiya lau, Ya Boy dina?” Tace “Yayi bacci” yace “Maa Sha Allah, kema tashin ki nayi koh?” Tace “Uhn, na dai kwanta ne, ina little Amira fah?” Yace “Tana gun Mum dinta” Khadijah tace “Am sorry ban kira ka ba Barrister, daxun na ga sako thanks very much we are grateful” yace “Is there any need for that Amira?” Murmushi tayi bata ce komai ba, yace “I think nan da 3 days xan taho ba sai next week ba” Khadijah tace “Ayya Allah ya kawo ka lafiya” yace “Ameen, daxu ma naje gun Umma” Khadijah ta bude ido tace “Haba dai?” Yace “Sure, kafin in taho Uk xan je can katsina” shiru Khadijah tayi bata ce komai ba, yace “Are you there?” Tace “Uhm ina jin ka” yace “Me yasa kika yi shiru” a hankali tace “Isn’t it Early barrister” yace “It’s not Amira, I want everything to be done in not less than 2 months plss, ba ki jin tausayina koh” jikinta yayi sanyi tace “Amma barrister ni tsoron Ummu Amira nake, plss ka sanar da ita don ya xamo da amincewarta kake yin komai, Ni tsoro nake ji” D’an murmushi yayi yace “Ba ruwan ki da Jiddah, beside ta san komai, ke din dai ce bata sani ba, sannan ba gida daya xa ku xauna ba” Ita dai har sannan bata ji hankalin ta ya kwanta ba, banda faduwa babu abinda gabanta ke yi, cikin sanyin murya tace “Toh shikenan, Allah yayi jagora” yace “Ameen Amira, let me allow you sleep” tace “Toh nagode” a hankali yace “Do have a nyc nyt rest” Ta d’an yi murmushi tace “Thanks” daga haka ya katse wayar, komawa tayi ta kwanta ta rufe har kanta da duvet. Washegari bata da lectures da safe amma saboda Shureim dole ta tashi cikin sanyi don shirya sa, tausayin little boy din nata take don sanyin isn’t funny at all, haka dai ta shirya sa ta sa masa rigar sanyi babba da head warm, tea ta hada masa ta soya masa kwai sanin baya cin bread, tana xaune parlor tana jiran ya gama aka danna bell, kallon agogo tayi kafin ta mike ta isa kofar ta bude, khaleel ne tsaye ya shirya xai fita, shi ma kayan sanyin ne jikinsa yana kallonta a hankali yace “Good morning” ta kasa kallonsa ganin yanda ya tsare ta da ido, ji tayi yace “let me drop Shureim in school tunda baki da lectures yau” tace “Toh” daga haka ta dawo parlorn, yana ta tsaye har Shureim ya gama ta dauko masa lunch box dinsa ta mika masa, ya nufi kofa yana daga mata hannu har ya fita khaleel ya kama hannunsa xuwa gun motarsa, ta tsaya bakin kofa tana kallonsu har suka fita gidan. Washegari Thursday da yamma Khadijah na parlor tana goge ma Shureim kayansa da uniforms, shi kuma yana bedroom yana waya da su Umma, mikewa tayi bayan ta kashe iron din jin an danna bell, ta isa kofar ta bude, khaleel ta gani tsaye, ya shafa kansa ba tare da ya kalleta ba yace “I will be traveling to Nigeria today Khadijah” shiru tayi tana kallonsa, yace “You take care of the little boy” tace “Toh Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare” yace “Ameen” xai shiga apartment dinsa ta fito a hankali tace “Dr…” Tsayawa yayi ya juyo yana kallonta, Kasa magana tayi, murya can kasa yace “Am all ears Khadijah” Jin hawaye na neman taruwa idonta ta juya ta koma ciki kawai, da ya tashi tafiya kuma bai ma ce mata ya tafi ba yayi wucewar sa. Tun da Khadijah ta tashi sllhn asuba duk ta rasa me ke damunta, gaba daya ta ji bata jin dadi, komawa tayi ta kwanta kasancewar friday ne, tana ta kwance har kusan karfe takwas, can dai ta tashi tunawa da tayi anytime soon flight din su Barrister xai sauka kasar, Ruwan wanka ta hada ta fara tashin Shureim ta wanke masa baki tayi masa wanka ta sa yayi alwala sannan suka fito bayin, shirya sa tayi ta shimfida masa darduma yayi sllh sannan ta wuce bathroom don yin wanka, tana tsaye kitchen misalin karfe goma tana tunanin abinda xata girka ma Barrister, Shureim ya kawo mata wayarta dake ring, karba tayi ta kai kunne hade da sallama, yace “Kun tashi lafiya Amira?” Tace “Alhmdllh, har kun sauka kenan?” yace “Sure, tun karfe tara” Tace “Toh ina ka sauka?” Murmushi yayi yace “Baki san ina da apartment nan ba koh?” Ta langwabar da kai tace “I never knew” yace “You now know” murmushi kawai tayi, yace “Ina Shureim” kallon bakin kofar tayi taga ya wuce tace “Yana parlor, barrister sorry I asked… plss mai xan girka maka I don’t know what u like most” Yace “Noo you don’t worry dear, Ni nayi breakfast ma” shiru tayi jin abinda yace, Can tace “Toh lunch fah?” Yace “Just tea may be with cake” xaro ido tayi tace “Tea da cake kuma?” Yace “Uhm sure” tayi murmushi tace “Toh shikenan yaushe xaka taho?” Yace “After I am done with what I am doing, may be in the afternoon” tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ameen, bye dear” daga haka ya katse wayar, fita tayi daga kitchen din don dama sun yi breakfast da Shureim. Karfe Sha daya ta shirya tare da Shureim suka fita don yin shopping, sun fito daga shopping mall wayarta dake jakarta ya fara ring, ta ajiye kayan hannunta ta bude jakar ta ciro wayar, number Aliyu ta gani, ta d’an yi jim kafin ta daga, shi yayi mata sallama ta amsa tayi shiru, yace “Ya kike Iman” tace “Lafiya lau” yace “Ya Shureim?” Tace “He is fine” yace “Maa Sha Allah” shiru tayi bata ce komai ba, bayan few seconds yace “Xan tafi Nigeria later, you need anything?” Tace “As in?” Yace “I mean ko kina bukatar wani abu daga Nigeria?” Tace “Nothing” a hankali yace “Ohk can I go with Shureim plss” wani kallo ta shiga yi kamar yana gabanta tace “Beg your pardon?” D’an murmushi yayi kafin yace “Ranan litinin xa mu dawo Iman, daurin auren Neighbor din ki xan je, it’s tomorrow, so we will be back Monday morning” Shiru Khadijah tayi tana son apprehending abinda Aliyu ya ce mata, a hankali yace “Hello, are you there Iman?” Ta dake tace “Waye Neighbor dina?” Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace “Dr Ayman”