Noor Al Hayat 52
Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace “Toh kar ki masa butulci Iman, baki san xai baki shi ba ya baki, prayer is all what ur little boy wants from you, kiyi masa addu’a ba kuka ba Iman, if you continue like this what will be the fate of his twin, kin ga shi ma xai shiga damuwa sosai na rashin halve dinsa and this might affect him badly…. Or did you want anything bad to happen to him also, For his sake plss ki kwantar da hankalin ki so you won’t loose him too, am telling you damuwar da shi xai shiga sai ma ya fi naki” khadijah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace “Na shiga uku don girman Allah kar ya bar ni shi ma” yace “Then ki kwantar da hankalin ki and accept this fate” hawaye na xuba idonta tace “Toh” yace “Promise me baxa ki sake kuka ba Iman” k’in cewa komai tayi, ya kira sunanta a hankali ta daga kai tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, ta kuma rushewa da kuka tace “Yanxu Sudais ya tafi ya bar ni…. Shi fa yace min in je in kira masa Shureim he wants to tell him he is sorry, dama mutuwa xai yi baya son ya mutu a kusa da ni” Ta hade kai da gwiwa tana kuka kamar ranta xai fita maganar Sudais na karshe na dawo mata “Anty ki ce Shureim ya xo, I want to tell him am sorry” kuka ta ke kamar ana dada tunxurata, Aliyu ya kasa ce mata komai duk jikinsa yyi sanyi, Ta rikosa tana girgixa kai cikin tashin hankali tace “Yanxu shkkn baxan sake ganin sa ba, me yasa ya tafi ya bar ni da Shureim” Aliyu ya kasa cewa komai wani mugun tausayinta na shigarsa, cikin sanyayyen muryarsa yace “Pls ki daina kukan nan Iman, da duk biyun Allah ya raba ki da ya xa ki yi kenan, you neva knew why he took him so soon, be a good Muslimat plss” shiru khadijah tayi jin yace Dukka biyun, ta goge idonta gabanta na mugun faduwa cos she can’t just imagine that, Murya can kasa yace “You make the promise now, that baxa ki sake masa kuka ba sai dai addu’a….” Ta gyada kai da kyar trying not to cry tace “I promise” yace “Add in sha Allah to the promise” a hankali tace “In sha Allah” Ya d’an yi murmushi yace “Good” mikewa yyi ya dago ta ta mike ita ma tana goge idonta yace “Ki wuce ciki and remember the promise you make” tace “Toh” daga haka ta fara tafiya ya bi ta da kallo, da sauri ta juyo sai kuma ta dawo tace “Ina shureim plss” da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace “Yana nan tare da mu” ta hadiye abu da kyar tace “Ka dauko min shi plss” yace “They are people everywhere, later xa a kai maki shi” shiru tayi sai kuma ta juya a sanyaye ta fara tafiya, Juyowa tayi ta kara dawowa idonta har ya fara kawo kwalla tace “Toh me yake yi?” Yace “Kukan xa ki fara kuma” da sauri ta girgixa kai tana goge idonta, yace “He is just sitting down” bata ce komai ba ta fara tafiya kamar iska xai kadeta ta fadi har ta bar wajen, Aliyu ya koma a sanyaye ya xauna ya jinginar da kansa jikin bango yana jin mutuwar yaron har cikin ransa, Tun da khadijah ta dawo compound din khaleel ke bin ta da kallo har ta shiga parlor, sai a sannan barrister Sudais ma ya dauke idanuwansa daga kallonta, Bedroom ta wuce duk mutanen parlon suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Umma na xaune har lkcn duk jikinta yyi la”asar, da ido ta bi khadijah har ta dauko Hijab dinta ta sa ta xauna kan darduman dake shimfide ta jingina da bango, hawaye ya cika Idon Umma don bata yi xaton hakan ba, tashin hankalinta ta Inda xata fara lallashin Khadijah sai ga shi taga ta ma daina kukan, Wata frnd din umma ta dawo kusa da ita a sanyaye tace “Kiyi hakuri kinji Khadijah, Allah yayi masa rahama…” A hankali khadijah tace “Ameen” Umma taji hankalinta ya kwanta sosai, tashi tayi ta fita da kanta taje kitchen ta hado mata shayi ta dawo, kasa sha Khadijah tayi har lkcn ta kasa yarda Her lovely Sudais is gone forever, tana son kuka amma sai ta tuna promise din da tayi, hakan yasa xuciyarta ya dinga mata xafi sosai, kowa ya ganta sai yaji tausayinta, Umma har lkcn mamakin karfin halin nata ta dinga yi, a haka har aka yi la’asar, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh umma ta xubo mata abinci ta xauna kusa da ita cike da lallami tace “Don Allah ko kadan ne ki ci Khadijah, tun jiya fa baki ci komai ba” Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, can ta dago da kyar tana kallon Umma tace “Umma yanxu shikenan Sudais ya tafi” Rungume ta umma tayi tana kokarin ganin bata xubda hawayen dake baraxanar xubo mata ba, cikin sanyin murya tace “Pray for him daughter, Allah yasa can ya fi masa nan, Allah ya sa mai ceton mu ne” cikin rawar murya Khadijah tace “Ameen” umma tace “Toh ki ci abincin kadan don Allah” ta girgixa kai tace “Umma baxan iya ci ba” Umma tace “Ko cokali biyu ne ki yi” Nanny ce ta shigo dakin da kumburarrun idonta ta duka kusa da su tace “Umma akwai baki parlor sun xo mata gaisuwa ta daure ta fito” Umma tace “Kice su shigo nan” mikewa Nanny tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da su Mumy, Baby da su seeyama da wata daban, Mikewa Umma ta yi ganin su ta shimfida masu babban darduma tana masu sannu da xuwa, Khadijah ta dinga kallon Mumy har ta xauna, A hankali tace “Sannu da xuwa Mumy” mumy da kana ganin idanuwanta kasan ta yi kuka sosai tace “Sannu Khadijah, ya hakuri” Khadijah ta kasa amsawa ta dakar da kanta, Su siyama ma suka mata gaisuwar a sanyaye, sai a sannan khadijah ta kara dago kanta tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta suka xubo ba, Kallon warce ke xaune kusa da baby ta dinga yi, ita ma yarinyar kallonta take da mamaki, Khadijah tayi karfin halin cewa “Maryam sannu da xuwa” Maryam tace “Ashe yaron ki ne ya rasu Khadijah, Allah ya ji kansa” Khadijah tayi karfin halin cewa “Ameen” sai dai xuciyarta cike yake da mamaki, Maryam dama yar uwar su Aliyu ce kenan, makarantar su daya a UK amma Hi kadai ne mutuncin da ke tsakaninsu kawai ta rasa me yasa bata son yarinyar, kawarsu Vanessa ce dai. Mumy sun kusa minti sha biyar a dakin, duk tausayin khadijah ya cika don tasan rashin yaro da ciwo sosai ga uwarsa barin yaro mai shiga rai irin sudais, bata ma samu courage din tambayar ina Shureim ba, Karfe biyar da yan mintuna tace ma umma xa su tafi, Umma tace “Toh mun gode kwarai Hajiya, Allah ya bar xumunci” Mumy tace “Ameen, kuyi hakuri bamu xo tun safe ba kanwata ce ba lafiya tana asibiti sun yi hatsari tun shekaranjiya” Umma tace “Subhanallah, toh Allah ya bata lafiya, ya yaye mata” Mumy tace “Ameen mun gode” hakuri ta kara ba khadijah Umma ta rakasu suka fita parlor, Sai a sannan Mumy tace “Kanin Aliyun yana waje ya xo mata gaisuwa amma ko xuwa anjima sai ya dawo” Umma tace “A’a bari ta fito” mumy tayi convincing dinta kan ta bari sai anjima ya dawo daga haka suka wuce Umma ta koma ciki. A hankali khadijah ta tako har cikin parlor tana sanye da Hijab dinta har kasa ta xauna kujera a sanyaye tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yyi, ta sunkuyar da kai a raunane tunawa da lkcn da suka dinga dragging sunan da ta xabar ma sudais dinta da shi, A hankali yace “Amira…” Ta daga kai tana kallonsa lkci daya idanuwanta suka kada, cikin sanyi yace “Keep on praying for him, Allah ya sa mai ceton mu ne, life moves on plss, ai da baki san Allah xai baki shi ba, so kiyi hakuri ki cire sa ranki, tsakanin ki da shi yanxu addu’a, baxai ji dadi kiyi ta masa kuka ba” Tana gyada masa kai da kyar tace “Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna” Barrister sudais yace “Ameen, Allah ya kara maki hakuri” Murya can kasa tace “Ameen” yace “Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa” Ta mike tace “Toh” daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito, da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba. Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace “Allah ya ba mu hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai” shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace “Mama tana Ciki ne?” Umma tace “Ehh tana ciki bari in mata magana” Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace “Aliyu tayi bacci kuwa” yace “Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri” tace “Ameen, Allah bada lada” tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace “Aliyu ina shureim din fa?” Juyowa yyi yace “An tafi da shi mama” tace “Can gidan ku?” Ya girgixa mata kai, Umma tace “Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya” daga haka ya fita, umma ta san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace “Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki dakin ki” Umma tace “A’a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne” daga haka ta fita dakin.
Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace “Taso mu je an xo maki gaisuwa” ta d’an hade rai tace “Umma ba ga ku ba bacci fa nake” Umma tace “Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki” shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho ya rungume ta yana kallonta yace “Anty are you sick?” Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace “Sannu Khadijah, ya karin hakuri?” kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace “Alhmdlh Mumy, nagode” Ummu tace “Allah yayi masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne” Umma tace “Ameen thumma Ameen” don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace “Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn’t we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I promise I will never fight him again….” umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace “He will be back soon sweetheart, and I am sure he is missing you too” Shureim yace “Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him” Ummu dake ta kallon shureim tace “Shureim har ka gaji da wasa dasu fadeel, ain’t they ur frnds anymore” ya juya ya kalleta yace “Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also” Ummu tace “Toh taho mu wuce tunda ka gaida Anty” kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace “Anty, is sudais coming back soon? I want the both of us to be frnds with fadeel and Adeel” Ummu ta mike tace “Toh xo mu wuce Shureim, idan ya dawo xa a kawo sa wajen ka” da haka suka fita parlorn bayan shureim ya daga ma khadijah hannu, Umma ta rakasu har bakin mota, sai a sannan taga tare suke da Khaleel dake xaune motar, ganin umma ya sakko ya gaisheta da ladabi sannan ya mata gaisuwa ta amsa tana murmushi tace “Allah ya saka da alkhairi, ya bar xumunci” yace “Ameen” sai da suka shiga motar gaba daya sannan Umma ta koma cikin gida, bata tadda Khadijah a parlor ba hakan yasa ta wuce daki ta ganta kwance, mamaki ya cika umma ta xauna kusa da ita da damuwa, yanxu kuma rashin kukan nata ya fara damunta don wani lkcn gwara mutum yyi kukan da kukan xuci, Umma ta yi shiru na d’an lokaci kafin a hankali tace “Look daughter, cry… even if it’s a little so you will feel relieve, kiyi kuka don Allah bana son wannan rashin kukan naki kuma, kin dai san matsalar ki, kar kije ki tada ciwon ki, it will be worst gaskiya idan haka ya faru” Jin bata ce komai ba umma ta mike a sanyaye ta fita, ba a jima da tafiyar mahaifiyar khaleel ba su mumy suka xo gidan, yau kam sun d’an dade kafin su wuce kuma khadijah ta fito ta amshi gaisuwar saleem, da yamma shaheedah ta xo gidan da sadeeq, shaheedah tayi kuka don bata ba sudais mutuwa so early ba, duk taji tausayin khadijah sosai, su Vanessa duk suka kira khadijah yi mata gaisuwar sudais da har lkcn a xaton su kanninta ne yan biyun. Da daddare ta fito wanka Shaheedah ta mika mata wayarta da yake vibrate, karba tayi ganin Khaleel ne ta daga ta kai kunne, cikin sanyin murya yace “Khadijah…” A hankali tace “Na’am” yace “Xa ki iya fitowa yanxu?” Shiru ta d’an yi kafin tace “Toh gani nan xuwa” shiryawa tayi ta sa hijab ta fita xuwa dakin umma, ta durkusa kusa da ita tana kallonta tace “Umma ina xuwa khaleel na kirana” Umma tace “Toh sai kin dawo” daga haka ta mike ta fita, cikin sanyi take tafiyar kamar mai tausayin kasa har ta isa waje, yana tsaye ya jingina jikin motarsa, kanta a kasa ta isa gefensa ta tsaya, murya can kasa tace “Ina yini?” Kallonta kawai yake bai ce komai ba har ta dago a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa kasa daga kallonta da yake yi, cikin sanyayyan muryarsa yace “Ya hakuri khadijah” ta hadiye abu da kyar tace “Alhmdllh” yace “Ban san me xan ce maki ba shi yasa ban kira ki ba khadijah, I know it’s very sad, it’s a great lost, but don’t forget ba wayon ki yasa Allah ya baki shi ba, and there is always a reason for everything, and you knw God plans best, don haka ki sa ma xuciyar ki dangana, you have ur handsome shureim, he will act as both him and his twin to you, this is part of ur fate, and it’s already written, plss kin san condition din ki Khadijah kar ki kara sa mutuwar sudais a ran ki I know its very painful, but idan wani abu ya same ki i will be very sad, come to think of ur only son, for my sake and his don Allah kiyi hakuri, forget about Sudais, but don’t forget to pray for him always, Allah ya hada mu gaba daya a aljanna” cike da damuwa ya kare, Khadijah tayi murmushin karfin hali tana share hawayen da ya taru idonta, tun ranan da Aliyu yace kar ta sake kuka bata kara ba sai yanxu da take gaban khaleel, a hankali tace “In sha Allah Dr, baxan sa damuwa a raina ba, ae ban ma san Allah xai bani shi ba, so baxan butulce masa ba, na hakura Allah ya haskaka kabarinsa ya sa can ya fi masa nan, kuma ya raya min d’an uwan sa” cikin rawar murya ta kare maganar, khaleel ya lumshe ido yace “Ameen Khadijah, am happy with ur words” Bata ce komai ba ta dinga kallon motar da yayi parking bayan na Khaleel, Aliyu ne ya fito cikin motar, kallo daya khaleel yayi masa ya dauke kansa, Aliyu ya iso inda suke yana kallon khaleel ya basa hannu khaleel ya amsa amma fa da kyar, Aliyu na kallon cikin idanuwansa yace “Ya hakurin mu?” Khaleel yace “Mun gode Allah” Aliyu ya kalli khadijah suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, cikin gidan Aliyu ya shiga, khaleel na juya wristwatch din hannunsa yace “Wajen ki ya xo?” Ta girgixa kai tace “A’a” Khaleel bai sake cewa komai ba bayan wani lkci yace “Alryt then, xan koma Khadijah, Allah ba mu hakuri gaba daya, sleep without worries plss” ta gyada masa kai tana kallonsa, yana daga kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta, yyi murmushin sa mai kyau yace “Amma kin ci abinci kuwa? Tell me the truth plss” ta girgixa masa kai a sanyaye tace “I don’t have appetite” yace “Toh idan na siyo maki abu yanxu make me the promise xa ki daure ki ci” tace “Akwai abinci fa a gida” yace “Ai na sanin, just promise me xa ki ci plsss” murmushi tayi tana fidgeting fingers dinta a hankali tace “Toh nagode” yace “Yauwa, I will be back soon” tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ya xata xai shiga motarsa ita kuma ta shiga cikin gidan, xaune ta tadda Aliyu kan farar kujera a wajen compound din, kallo daya tayi masa ta dauke kai xata wuce ciki, taji a hankali yace “Iman” kasa ci gaba da tafiya tayi, maganganunsa na jiya da safe na mata yawo a kai, can ta juyo ta kallesa ta gan sa tsaye, yace “Plss just few minutes” tana ta tsayuwa idonta a kan yatsunta har ya iso gabanta yace “Few minutes pls” Ta dake da kyar tace “Toh” juyawa yayi ya nufi gun kujerun ta bi bayansa, ya xauna kan kujerar ta xauna ita ma. Kallonta kawai yake ta ki kallon sa ta hade rai, murya can kasa ta ji ya fara cewa “Iman ba dan ni ba don Allah ina son ki mance abinda ya faru tsakaninmu six years back…..” Da sauri ta dakatar da shi tace “Toh ni nace maka ban mance bane?” Ya girgixa kai a hankali yace “I mean ki yafe min ki cire a ranki da gangan na maki hakan wllh ba da gangan bane, it’s a set up, though ba lallai ki yarda da hakan ba, amma don Allah kiyi hakuri mu dinga xumunci” Ji tayi kamar ta fashe da kuka don ya fama mata ciwon da ya ki healing har yanxu a xuciyarta, A sanyaye yace “Kin ji Iman, ki raga min ko albarkacin daya yaron da ya rage a tsakaninmu even if I didn’t deserve it” Khadijah ta kasa cewa komai, Bayan wani lkci ta daga kai a hankali tana kallonsa ta ga kallonta yake, da sauri ta sauke idonta tace “Ni fa na mance, ya kuma wuce a gu na” yace “Toh nagode sosai, amma xaki bani yaron?” Da sauri ta daga kai tana kallonsa, cikin rawar murya tace “I can’t give you my son, kayi hakuri…” Yana gyada kai a hankali yace “No offense, amma xa ki bari ai mu dinga xumunci da shi, I mean in dinga xuwa ina ganinsa, once in a while kuma xa ki bari ya xo gun mumy koh” shiru tayi ta kasa cewa komai, murya can kasa yace “Kin yi shiru” a xuciyarta tace “Nasan maganin ka” a fili kuma tace “Toh” Wani murmushi yayi yace “Toh nagode sosai, Allah ya raya sa” tace “Ameen” kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d’an risina ta karba a hankali tace “Nagode” ya d’an yi murmushi yace “No thanks” daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace “Xan wuce ciki sai da safe” mikewa yayi yace “Toh ina yake, I mean the boy? Though ban san sunan sa ba” da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace “Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais” kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace “Barrister Aliyu… Sunan sa ya ci” daga haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace “Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba” tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace “Toh yana ina yanxu, I haven’t seen him since yesterday” tace “Yana gidansu Dr khaleel” shiru yyi bai ce komai ba, can a hankali yace “Ohk good nyt” daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa, tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace “Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am outside” tace “Toh” daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace “Waow ya sunanta?” Sudais ya jingina da motar yace “Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta, na kawo ta ne ta gaida Antyn ta” Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace “Naji dadi sosai” Yace “Sure?” Ta kallesa da sauri tace “Eh mana, ko xaka bar min ita” yar dariya yayi yace “In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita” Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace “Baxa ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace ” Ka ji na fada haka?” Yace “Uhmn dont forget who is standing before you” ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace “A barrister” ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace “Toh ya k’arin hakurin mu dear?” Tace “Mun gode Allah” yace “Har yanxu shureim din bai dawo gida ba?” Ta gyada masa kai tace “Bai dawo ba” yace “Ohk, ya su umma?” Tace “Suna ciki” kamar warce ta tuna da sauri tace “Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki” yayi murmushi yace “Aa bari in yi ta tsayuwa ta” ta turo baki tace “Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki” daga haka ta nufi gate rike da Little Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda wai sai gobe, tace “Toh bari in kai mata Little Amira ta gani” yace “Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na” dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace “Maa sha Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki” khadijah tace “Naga kamar bata magana” Umma tace “A’a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta isa tayi magana” fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace “Umma ina xuwa” Umma tace “Toh sai kin dawo” Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace “Ya aiki?” Ya langwabar da kai yace “Ba dadi, Amira har yanxu you didn’t answer my questions…” Ya lumshe ido ya bude yace “Ohk let me leave it this way, you don’t want to answer my question” shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace “A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana… saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja, daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it’s not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar ki sai gashi na koma mata cos I don’t have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu’a every blessed day, ba tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin tsarin rayuwata, I need you plss Amira” Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata.
Shiru Umma tayi tana kallon khadijah, a hankali tace “Ko saboda me?” Khadijah ta langwabar da kai cikin sanyi tace “Umma I will be lonely all alone, I want him to be by my side” Umma tace “Life with him there won’t be esay Khadijah, karatun ki na bukatar natsuwa sosai kin sani, shureim will ba a distraction, baxai yiwu ba Khadijah” da damuwa Khadijah tace “Umma ai shi ma makarantar fa xai dinga xuwa, plss ummata” Umma tayi shiru alamar bata san me xata ce ba kuma, can tana ci gaba da linke kayan da take tace “Rabani da shi dai kike son yi koh?” Murmushi Khadijah tayi kunya ya kamata tace “A’a wllh ummata” Umma tace “Gaskiya ne mana, ke gashi baki kusa da ni, grandson din ma kina son daukesa” Khadijah ta xaro ido, da damuwa tace “Allah sarki Ummata ba haka bane ba fa” Murmushi Umma tayi tace “Toh shkkn tunda kina son tafiya da shi sai ku je, Allah ya tsare” Sosai Khadijah taji dadi, Umma ta xauna gefen gadon tace “Yanxu ya xa mu yi da maganar sudais Khadijah, kin ga samu na yayi ya min magana….” khadijah tace “Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne” Umma tace “Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?” Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace “Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun” Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace “Sun gode Ummu” Ummu tace “Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce” ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace “Ina ji Ummu” sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace “Abuu kasan fa saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi” Khaleel ya shafa kansa yace “Ina sane Ummu” tace “Toh Alhmdllh tun da kana sane, amma ba wani shiri da xa ku yi ne?” Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace “Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron nan na aura….ina da interest a kanta” Ummu ta dinga masa wani kallo tace “Kana da hankali ma kuwa khaleel???” hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa Arabiya… toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d’an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d’an yi murmushi a hankali tace “Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi” Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace “Khadijah jiran ki fa suke” a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace “I missed you Anty” ta shafa kansa tace “I missed you same” Umma tace “Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota” Khadijah tace “Yanxu Shureim din ya shigo?” Umma tace “Yanxu ya shigo” Khadijah ta karasa gun umma ta rungume ta tace “Ummata sai mun dawo” Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace “Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss” murya can kasa Khadijah tace “Nagode Umma” Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar, Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace “Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim” Umma tace “Lah kin ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport” Khadijah ta gyada mata kai ta fita parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara’a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace “Good morning” yace “Morning how was ur nyt?” Ta sauke idonta tace “Alhmdlh” Wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace “Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan suka yi waya tana yawan tambayar ta shi….” Khaleel yace “Ohk then” daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace “Ku shiga toh” tace “Kai baxa ka shiga ba” da sauri yace “A’a, am waiting for you two a nan” a hankali khadijah tace “Ohk,” daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace “Come down” daga mata hannu yyi yace “Anty ki dauke ni” ta hade rai tace “Sakko my friend” khaleel yace “Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?” murmushi kawai tayi ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga, babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi Shureim yake yana kallonsa yace “Uncle good morning” Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace “Morning how are you sweetheart” yace “Am fine” Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace “Good morning Iman” kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa “Ina kwana, wajen mumy muka xo” yace “Ohk tana Bedroom” taki yarda ta sake kallonsa tace “Toh kayi mata magana muna sauri ne” yace “mu je up stairs” daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace “Mama good morning” lkci daya bakin cikin dake tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace “Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka” Yace “Ni da Anty na” Aliyu ya juya yana kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace “Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah” kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace “Ina kwana mumy” da fara’a mumy tace “Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?” A hankali khadijah tace “Suna lafiya Mumy” gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace “Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in kawo sa yayi ma ki sallama” Mumy tace “Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema” kallonta Kawai Aliyu yake jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace “Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan” daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta tace “Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai” Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace “In sha Allah Mum na gode” Bayan kusan minti goma Mumy ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace “Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh” khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara’a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci daya mood din mumy ya canxa a hankali tace “Mu shiga ki gaida iklima” Khadijah tace “Toh” daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace “Sannu iklima Allah ya sauwake” kallonta kawai Iklima take ita ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace “Mu je” Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace “Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping” murmushi kawai khadijah tayi tace “Ba komai mumy na gode” Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace “Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah” Khadijah tace “Ameen mumy” daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace “Baxa mu yi sallama ba?” Still ba tare da ta kallesa ba tace “Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba” yayi murmushi yace “Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow” Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace “Me ya samu iklima haka?” Da kamar Aliyu baxai ce komai ba sai kuma yace “She is suffering from Hiv” Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace “Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da ita…” Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace “Toh Anty khadijah fa?” Yace “Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?” Khadijah ta girgixa kai tana kallonsa, yace “She had accident 2 weeks back” da damuwa tace “Toh ya jikin nata?” Yace “Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don’t knw” Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa tace “Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci” ya d’an yi murmushi yace “No problem” tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace “Barka da asuba” sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace “Good morning” Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace “Allah ya tsare” Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “Ameen” ya rufe masu motar, driver ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace “Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a aljihuna, I told him no but he didn’t even listen to me” Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace “Uncle ma ya bani wannan” Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce.
Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi, khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai taxin yace “Bridge street” har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude idanuwanta yace “Ae da mai cab din ya wuce da ke” ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace “Hope baki mance makulli ba” karamar jakar hanunta ta bude ta dubo makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace “Hey, ai ba gudu xan yi da shi ba hajiya” Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace “Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci” mikewa xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace “Have you eaten?” Yace “Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor” Shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace “Kayi wanka?” Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace “Bari in yi alwala” Ko da ta fito daga bayin bata ga Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace “Kun sauka lafiya?” Tace “Alhmdllh Umma” Umma tace “Ina Shureim din?” A hankali Khadija tace “Yana can wajen khaleel” Umma tace “Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?” Khadija ta gyada mata kai tace “In Sha Allah Umma” Umma tace “Toh Allah maku Albarka” Khadija ta amsa da “Ameen” daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace “Ina kika shiga Amira?” Ta langwabar da kai tace “Bacci nayi” yace “Ohk, ya hanya?” Tace “Alhmdllh ya takwarata?” Yace “She’s good, where is my son?” D’an murmushi tayi tace “Yana waje” yace “Waje kuma, babu sanyi ne?” Tace “Akwai amma it’s not much” yace “Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won’t be funny from next week I guess” tace “Haka ne” yace “Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one’s, kema ki siya” murmushi tayi bata ce komai ba, yace “Alryt then, sleep tight dear” tace “Toh nagode ka gaida min Amira” yace “Xata ji” daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d’an tabe baki ta rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace “Xa ki fara koh?” Ta hararesa tace “Xan fara me?” Yace “Kin fi ni sani ai” Bata tanka sa ba ta bar wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace “Yes?” Muryar khaleel taji yace “Hmm koh?” Bude kofar tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace “Alryt good nyt” tace “Allah ya tashe mu lafiya” juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace “Me yasa baka yi bacci can ba” yace “I said I want to come to you” bata ce komai ba ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace “Good morning” ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace “Ina kwana?” Yace “Hamdan, Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?” Ta d’an bude ido tace “Gadi na kake yi kuma?” D’an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun windown yana kallonta yace “Ina kika je?” Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace “Market” yace “What did you get?” Ta hade rai tace “Ina ruwanka” yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace “Ohk then” daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida masa darduma tace “Idan ka gama sllhn meet me at the parlor” daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace “Anty na gama, good morning” tace “Morning dear” kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace “Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan” yace “Toh” ta bude masa kofa ya fita, ta danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace “Good morning handsome” Shureim yace “Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka” karba yyi yana kallon flask din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace “Uncle tace it’s remaining one” rufe kofar yayi yace “Kyaleta xata kawo da kanta” Khadija tayi ta jiran dawowan Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace “Uncle Anty is calling me” xaunar da shi yyi yace “Don’t worry she will come in now” Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace “Good morning” dauke kai Khadija tayi kamar ana tilastata tace “Morning” xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace “Good morning Dr Ayman….” Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace “Morning Lydia, hw did u knw I am back?” Tace “I just met with Dr Ahmad, he told me you are back” shafa kai khaleel yayi a hankali yace “Ohk, we will meet later in the day, I am about going out now” tace “Ohk do you mind dropped me?” Ya girgixa kai yace “You get a taxi” daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.