Noor Al Hayat 51
Khaleel na xaune waje idonsa a kan wayar hannunsa Khadijah ta nufosa, ya daga kai yana kallonta har ta iso inda yake, yace “Is he awake?” Tace “Yace yana son ya ga shureim wai” Khaleel yace “Yana sama” ta d’an bude ido tace “Wajen wa?” Bai ce komai ba, hakan yasa ta hade rai tace “But me yasa ka bar sa ya je can? Why did u allow him go to him?” Khaleel ya ci gaba da danna wayarsa yace “He followed him, sae in hanasa…” Juyawa tayi a fusace ta wuce office din Aliyu, Khaleel ya d’an yi murmushi ya tashi ya shiga clinic din shi ma, Aliyu na tare da Dr Mukhtar Khadijah ta shigo office din, duk suka juya suna kallonta, ta dinga kallon office din tana neman shureim can ta hango sa kwance kan gadon masu ciki a office din yana bacci, karasawa tayi xata tashe sa, taji Aliyu yace “Don’t wake him” ko kallonsa bata yi ba xata daga yaron taji jikinsa yyi xafi sosai, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, a firgice ya farka ta rikesa sosai tana kallonsa da damuwa tace “Shureim me ya faru, ur temperature is high” rungumeta yayi yyi lamo jikinta, ta sauke sa kan gadon ta nufi kofa, Aliyu ya bi ta da kallo, ba su kai ga kai wa kofar ba yaron ya shiga kwarara amai, ta dukar da shi da sauri ita ma ta duka hankalinta tashe tace “What’s wrong shureim, me ka ci?” Dr Mukhtar ya taho gun su ya dagosa yana masa sannu, dai dai nan wata nurse ta shigo tana kallon Aliyu tace “Dr, ur attention” daga haka ta fita, Khadijah ta bi nurse din da kallo, Aliyu ya fita office din Dr Mukhtar ya cire ma Shureim rigar jikinsa yana rike da hannunsa ya isa table din Aliyu, duba sa yyi, bayan wani lkci ya ajiye stethoscope din hannunsa ya nuna ma Khadijah bathroom yace “Ki gyara masa jiki sai ki kwantar da shi kan gado, let me get him drug? Ya ci abinci?” Ta girgixa masa kai yace “Ohk” daga haka ya fita xuwa gun nurses, Ganin duk basa wajen yayi tunanin ko an kawo emergency ne, ya kalli direction din Emergency ward, yaga Aliyu tsaye ya jingina da bango, Karasawa Mukhtar yyi gun sa, ganin yanayinsa yace “Me ya faru Dr?” Kallonsa kawai Aliyu yake ya kasa cewa komai, Dr Mukhtar ya shiga cikin emergency ward din, khaleel ne kusa da gadon da sudais yake ya hade kansa da karfen gadon, Dr Mukhtar ya dinga bin Doctors din da kallo, ganin yanda suke tsaye hopelessly, can ya kalli Sudais lkci daya jikinsa yyi mugun sanyi, gaba daya he became lost of words ya kasa karasawa cikin ward din, juyawa yyi da kyar ya fita office din yana kallon Aliyu dake jingine da bango har lkcn, ya dafa shoulder dinsa cikin sanyin murya yace “Hardluck Doctor, Allah ya masa rahama” Aliyu bai iya yace komai tunaninsa daya a lkcn Khadijah, Khaleel ma ya fito ward din yana kallon Aliyu amma ya rasa abinda xai ce, Aliyu yyi karfin halin ce masa “Plss take her home” Khaleel ya bar wajen a sanyaye ya fiddo wayarsa yyi dialing number sudais, yana dagawa a hankali yace “Barrister the boy is late” daga haka ya katse wayar, kujera Aliyu ya nema ya xauna jin ya kasa ci gaba da tsayuwa, sai a sannan ya ji hawaye na sakko masa ya rike kan sa, how will Iman take this?? Who is to break the news to her, Khaleel ma na tsaye ya jingina da bango yana tunanin yanda xai yaudareta ya mayar da ita gida, can ya nufi sama xuwa office din Aliyu ya ganta ta fito office din rike da shureim, khaleel na ganinta sai da gabansa yyi mugun faduwa ya nufeta da sauri sai dai bai bari taga idonsa ba trying hard to be okay yace “Where did u see him?” Da damuwa tace “Amai yake ta yi Dr, kuma jikinsa da xafi” Khaleel ya duka yana kallonsa yace “What happen shureim” yace “I want go to Sudais” Khaleel ya hadiye abu da kyar yace “Okay xan kai ka my boy” daga haka ya mike yace “Bani wayar pls ina son inyi call mine is out of airtime” mika masa wayar hannunta khadijah tayi ya kama hannun Shureim yace “Mu koma ciki in duba sa” tace “Ai wani Dr ya duba sa yanxu” yace “Ehh let me check him again sai a basa magani” tace “Toh ku tafi, let me go to sudais…” da sauri ya juyo yace “Noo ki xo mu je sai ku tafi tare da shureim he won’t be happy idan bai ga shureim ba” a hankali ta bi bayan Khaleel dake rike da shureim, office din Dr Aliyu ya shiga, ya xaunar da Shureim kan gadon office din, ya kalli khadijah yace “You stay with him ina xuwa” daga haka ya juya ya fita, Number Umma ya shiga dubawa a call logs dinta, Ummata… yaga tayi saving number da, nan ya gane number umma ce, yayi saurin kwashe number a tasa wayar, ya sauka kasa bayan yyi dialing, ba a dau lkci ba Umma ta dauka, ya gaisheta cikin sanyin murya yace “Umma khaleel ne, I called to inform you that Sudais is late umma, yanxu ya rasu” mikewa umma dake xaune tayi cikin tashin hankali tace “Innalillahi wa inna ilai raji’un ya rasu?” Jikin Khaleel yyi sanyi jin yanayin da umma ta shiga, a hankali yace “Ku yi hakuri Umma, but har yanxu Khadijah bata sani ba kuma ba a son ta sani a nan so plss, ban san ya xa ayi ko xaki kirata ki dai fada mata wani abu da xai sa ta wuce gida yanxu, cos we can never convince her taje gida ynxu” Kuka kawai Umma take ta kasa cewa komai ta katse wayar ta dinga salati wanda hakan ya ja hankalin Nanny ta shigo, cikin tashin hankali tace “Umma me ya faru?” Da kyar Umma ta iya ce mata “Sudais” tun umma bata fada ba Nanny ta san kwanan xancen ta fashe da kuka ta xube wajen tana salati ita ma, tausayin khadijah ya sa Umma ta kasa controlling kanta, kuka take kamar ranta xai fita, babu mai lallashin wani ita da Nanny, Khaleel ya kasa komawa sama gun khadijah duk iya kokarin sa na ganin ya dake ya ji ya kasa kuma, kujera ya nema shi ma ya xauna yana ganin abun kamar a mafarki yanxu shikenan yaron nan ya tafi, Nurses din ma gaba daya duk jikinsu a sanyaye yake, Aliyu yyi karfin halin fiddo wayarsa ya shiga kiran Mumy, bayan ta daga cikin sanyin murya yace “Mumy ya rasu yanxu” Yanda mumy ta rikice a lokacin sai ayi tunanin sun yi shekara shidda tare da yaron ne, ta dinga kuka kawai ya katse wayar sa,Sudais ne ya shigo reception din duk hankalinsa a tashe ya nufi khaleel cike da karfin hali yace “Dr plss kar ku ce min yaron nan ya rasu, tell me he is still alive” Khaleel ya kasa ce masa komai, Sudais ya tafi gun wata nurse yace “Take me to him plss” nurse din ta nuna masa emergency, da sauri ya shiga wajen, kallon gawar yaron ya dinga yi ganin kamar mai bacci da murmushin sa a fuska, sudais ya karasa gadon ya hade kai da karfe hawaye na sakko masa ya dinga nanata “Innalillahi wa inna ilai hi raji’un” Bai taba ba yaron mutuwa yanxu ba, ranan da aka haifesa tare da d’an uwansa ya tuno, da irin wahalar da khadijah ta sha kamar baxa ta yi ba, ya ji ya kasa controlling hawayen sa, memory din ya dinga dawo masa freah, tun daga san da yaran suka fara wayo, suka yi mugun sabawa da ahi har xuwa ranan da ya barsu suna kukan xa su bi sa amma har ya fita bai waiwayo su ba, cikin raunin murya sudais yace “Allahummaghfir li-fulanin Aliyu warfa’ darajatahu fil-mahdiyyina, wakhlufhu fi’aqibihi fil-ghaabirina, waghfir-lanaa wa lahu yaa Rabbal-‘aalamina, wafsah lahu fee qabrihi wa nawwir lahu feehi” daga haka ya karasa rufe masa idanuwansa amma ya kasa barin dakin hawaye na xuba idonsa, ya jima bai ji mutuwar da ta taba sa haka ba tun bayan rasuwar maminsa 3 years back, hakan yasa ya kasa daina hawaye, ya ki fita ward din don gani yake kamar yaron xai tashi. Da kyar Umma ta iya dialing number Khadijah, khaleel dake xaune ya jingina da kujera jin wayar na vibrate ya kalla da sauri ganin Umma ke kiranta ya mike ya ba wata nurse yace “Plss ma ki dan taimaka ki kai ma warce ke office din Dr Aliyu wayar nan” ta amsa ta wuce ta kai ma khadijah, a stairs suka kusa cin karo xata sakko, nurse din ta mika mata khadijah ta karba ganin umma ke kiranta ta daga wayar, Umma tayi gathering courage bayan ta saita muryarta tace “Khadijah ki dawo gida yanxu ina son ganin ki” hankalin khadijah ya tashi sosai jin yanayin muryar umma a tsorace tace “Umma baki da lafiya ne?” Hawaye na sakko ma Umma cikin sanyin tace “Ehh bana jin dadi ki dawo yanxu kin ji daughter” tashin hankali ne sosai tare da Khadijah ta dinga kallon wayar sannan ta sauka kasa da sauri, khaleel na ganinta ya mike da sauri, ta nufe sa da damuwa tace “Dr Umma ce ta kira wai bata da lafiya yanxu” ya dake yace “Subhanallah, bata da lafiya kuma?” Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, yace “Toh bari inyi dropping din ki gidan yanxu…” Tace “Toh, Shureim din yana ta aman har yanxu amma wani Dr na gun sa” Khaleel yace “Toh shkkn mu je” juyawa tayi ta nufi ward da little sudais yake kafin a kai sa emergency tace “Let me check sudais kafin in tafi pls” Khaleel bai san lkcn da ya fixgota ba ta kusa fadawa kansa da mamaki take kallonsa, ya wara ido yace “Mu je, idan mun dawo sai ki duba sa, bacci yake daga can na fito yanxu” kasa cewa komai tayi Khaleel na rike da hannunta ya nufi kofar fita ta dinga bin sa, Aliyu dake xaune one side of the clinic duk yana kallonsu ya lumshe ido to prevent more tears, he still can’t believe that cute boy, his blood is gone forever, kiran Abbansa ne ya shigo wayarsa, ya san mumy ta kira sa ta fada masa kenan, don tun bayan da Mumy ta gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da khadijah da batun yan biyun ya dauke masa wuta duk da a ranan ma ya bar kasar, a hankali ya mike ya daga kiran Abban nasa. Har suka isa gida khaleel bai ce ma khadijah komai ba, sai dai ya lura duk a sanyaye take, yaji wani mugun tausayinta na dawainiya da shi, jiki ba kwari ta fita daga motar bayan yyi parking ta wuce ciki tana tsoron yanda xata je ta samu Umma, Xaune umma take har lokacin a daki tayi kukan har taji ba dadi, nanny ma duk ta fita hayyacinta da ta tuna sudais ya mutu sai ya rushe da kuka don tun suna jarirai take tare da su. suna ganin khadijah duk suka shanye kukan Khadijah ta karasa da sauri ta xube gaban umma gabanta na mugun faduwa tace “Ummata mai ya faru, why are you crying plss” rungume ta umma tayi ta sake fashewa da wani kukan, Khadijah duk ta rikice ita ma ta fashe da kuka tace “Umma don Allah ki gaya min me ya faru, waye ya mutu?” Nanny ta mike ta bar dakin wani sabon kukan ya xo mata. A sanyaye khaleel yyi reverse ya koma clinic din, dai dai lkcn da Sudais ya fito daga emergency ward, Dr Mukhtar kuma ya sakko kasa rike da shureim, shureim na ganin Khaleel ya nufe sa da sauri, Aliyu ya bi yaron da kallo a sanyaye, khaleel ya duka yana kallonsa murmushin karfin hali dauke fuskarsa yace “How are you feeling now?” A hankali yaron yace “Uncle I want to see my brother plss” Khaleel ya dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ya kirkiri wani murmushin yace “He is sleeping now” ya fashe da kuka yace “Nooo, I want to sleep with him too” daga haka ya juya xai tafi inda dan uwansa yake, khaleel ya jawo sa da sauri yace “He is sick, baka son ya samu lafiya, idan kana damunsa baxai samu lafiya ba ai” cikin rawar murya yaron yace “Toh uncle kar ya tafi ya bar ni” Khaleel dake kallonsa ko kiftawa babu a hankali yace “Ina xai je?” Shureim yace “Gida” tashi Khaleel yyi ya kama hannunsa ya fita duk jikinsa a sanyaye. Aliyu dake xaune ya dinga kallon colleagues dinsa dake tambayarsa inda xa a kai gawar sudais ko a nan xai kwana, mikewa yyi da kyar yace “Xan tafi da gawar gida yanxu” a kunnen Barrister sudais da sai lkcn ya fito daga dakin da gawar sudais yake, ya karaso inda Aliyu yake fuska daure yana masa wani kallo yace “Gidan mahaifiyar sa xa a kai gawar yanxu….” kallonsa kawai Aliyu ke yi, Sudais yace “You will be the one to go break the news to her” Aliyu ya d’an bude ido yace “Why me?” Sudais bai sake saurarensa ba ya koma ya dauko gawar ya fita xuwa gun motarsa Aliyu ya bi sa da wani irin kallo. Kusan a tare duk su ukun suka isa gidan, khaleel ya fara fitowa sannan ya sakko da Shureim yana kallon Sudais da ya fito shi ma amma gawar na motarsa, dauke kai khaleel yyi ya shiga ciki yana rike da shureim, Aliyu ya fito daga tasa motar da Doctors biyu suka bi bayan Khaleel, Sudais ya kasa shiga ciki ya jingina da motarsa yana tunanin yanda Khadijah xata dau xan cen rasuwar d’an ta, lumshe ido yyi wasu hawayen na sakko masa, Nanny ce ta bude masu kofa khaleel yasa ta shimfida tabarma a nan balcony, duk gabansa faduwa yake damuwar sa daya khadijah, xuwa yanxu dai umma ta daina kuka bayan ta ce ma khadijah rasuwa aka mata, Khadijah sai kallonta take a sanyaye bayan ta gama kukan ita ma don bata san waye ya rasu ba kuma umma bata gaya mata ba, Umma ta sa Hijab ta fito a sanyaye ba tare da tace ma khadijah komai ba, khaleel ya dinga kallon umma da wasu hawayen ke xubo mata ganin su, Aliyu ya kasa kallonta a sanyaye yace “Allah ya yi masa rahama, ya sa mai ceto ne” Khadijah ta fito daga daki da sauri jin muryar Aliyu, kallonsu ta dinga yi daga inda take tsaye can ta karaso da sauri tana kallon khaleel gabanta na faduwa tace “Dr ina sudais din?” Khaleel ya kasa kallonta kuma ya rasa abinda xai ce, dai dai nan Barrister sudais ya shigo parlorn shi ma bayan ya ajiye gawar sudais kan tabarmar da ya gani balcony baya son ya shiga ciki da shi tukun, suna hada ido da khadijah yyi saurin sunkuyar da kansa, A hankali khadijah ta juya tana kallon umma dake share sabbin hawayen dake xubo mata, ta juya ya kalli Nanny da ta jingina da bango tana hawayen ita ma, a rikice ta nufi Aliyu ta durkusa gabansa cikin rudewa tace “Aliyu ka gaya min wani abu ya sami sudais dina ne, don girman Allah ka gaya min” kasa ce mata komai yayi ya kasa kallonta, lkci daya hawaye ya cika idonsa, mikewa khaleel yyi ya nufi kofa xai fita cos he can’t stand it any more, ta mike kamar mahaukaciya ta bi bayansa da sauri, tsaye khaleel yyi balcony ganin gawar yaron a wajen don bai san Barrister ya shigo da shi ba, ya juya a hankali yana kallon khadijah dake kallon gawar kan tabarma an rufe, lkci daya jikinta ya dau rawa ta kamo hannun khaleel cikin rawar murya tace “Dr meye wannan, what is it….” Jawota khaleel yayi jikinsa ya rungume ta gam, cikin sanyin murya hawaye na taruwa idonsa yace “Don’t forget Khadijah, Allahn da ya baki shi ya fi ki son sa…. Ba wayon ki ba ba dubarar ki ba ya sa ya baki, to yanxu ya amshe kayan sa, sudais addu’arki kawai yake bukata gare sa yanxu, pray to meet with ur son once again in
Jannah….” Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace “Anty me ya ke faruwa?” Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace “Ya jikin khadijah” shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace “Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah” kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace “Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni” Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace “Iman kin san Allah xai baki shi?” Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace “A’a”
*Sorry if I disappoint anybody*