Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 3

Sponsored Links

3…..

Muryar mace taji tace “Sorry for intruding Madam….” Jigum tayi na d’an lkci kafin ta bude kofar tana kallonta, baturiyar matar tace “Good evening….” Ta gyada mata kai tace “Same…” baturiyar tace “I am Clara Edward” a takaice ita ma tace “Khadijah Muhammad” Clara ta mika mata textbooks din hannunta tace “Can you please help keep this for you Neighbor? I mean Dr Ayman…” D’an buda ido Khadijah tayi ta girgixa kai da sauri tace “Of course noo, you just wait for him, I think that will be better” Clara tayi murmushi tace “But he said I can hand it over to you, I just gave him a call now…” kallon litattafen na tsaya yi gabana na faduwa, Clara tace “Yeah, i am travelling today, and i can’t go with his material” Khadijah dai ba don ranta ya so ba ta karba, Clara ta mata godiya ta juya ta wuce, Khadijah ta rufe kofarta, nan kan kujera ta ajiye books din a parlor. Ta fito daga wanka misalin karfe takwas da wani abu aka danna bell, tsaye tayi da mamaki tana tunanin to waye kuma wannan, jin an sake dannawa ta xura Hijab ta fito parlor tace “Who?” Ba a ce komai ba hakan yasa taki karasawa, ga xuciyarta da ya fara bugawa, aka kuma danna bell din, dakewa tayi tace “Who’s there?” A takaice taji muryarsa yace “Somebody, open right away” mamaki ya cika ta sosai har lkcn kuma xuciyarta bai daina bugawa ba, tayi karfin halin cewa “So? What did you want from me?” Yace “Open now” A fusace tace “Did you miss ur road!” Yace “Did you knw I can open the door my self?” hankalinta yyi mugun tashi, kamar xata yi kuka tace “And did you know I can also report you to the police right away” cikin tsigar rainin hankali yace “Ohh really? ohk then, let me get the door open for u so you can have ur way to d police” baya ta koma da sauri cikin rawar murya tace “Plss stay away from me, I don’t knw you” hawaye cike idonta ta kare maganan, shiru bai ce komai ba, har ta fara tunanin ya wuce ne tana nan tsaye dai kamar an dasa ta don ta dade bata shiga tashin hankali irin na lkcn ba, can cikin husky voice taji yace “Then…. I want to get my reading materials from you” da sauri ta kalli textbooks dinsa da ta ajiye daxu, gaba daya ta mance da su, ta hade rai kamar yana ganinta tace “Sorry, i can’t open my door now, you’ll get it tomorrow at ur door step” yace “You must be joking, wil u get that door open and hand over my property to me” mamaki ya cikata tace “Sorry I can’t” yace “This is serious” juyawa tayi ta koma kan kujera ta xauna, sai dai fa gabanta faduwa yake, bayan kusan second talatin yace “Look I am having exams, and I need those books” banxa tayi masa, a hankali taji yace “Alryt… Plss” shiru ta yi tana naxari d’an ita gaskiya tsoro take, can tayi tsaki ta kwashi books din ta nufi kofa, gabanta sae faduwa yake ta bude a hankali tana karanto addu’o’i a xuciyarta, tana bude kofar taji ya cafko ta, ta yi wani ihu ta saki books din hannunta jikinta na rawa, ya rungumota firmly har tana iya juyo numfashinsa, turasa ta shiga yi hankali tashe ta dinga cewa “Let go of me….” ya ki saketa yana kallon kwayar idonta fuskarsa daure yace “Isn’t this what you’re afraid of?” Yatsine fuska yyi ya turata yace “I am waiting for the police” daga haka ya duka ya kwashe books dinsa, tuni ta shige ciki dai dai lkcn da ya mike tayi banging kofarta ta sa lock, ya ja baya da sauri yace “Damn it….. What a f**k… I will get you” Da gudu ta koma daki kamar ya biyota din nan, ita kadai tasan irin tsoratan da tayi. Gaba daya ta kasa bacci har kusan karfe daya gashi ko wanka bata yi ba balle ta sauya kaya xuwa na bacci, duk kamshin turarensa ya cika ta tun rikon da ya mata, ko ta ya ta juya kamshin kawai take ji, a hankali ta tashi kamar mara laka ta cire kayan jikinta ta shiga toilet, wanka tayi ta fito ta xura rigar bacci ta kwanta bayan ta feshe jikinta da turarrukan ta, sai a sannan bacci ya dauketa. Sai kusan karfe bakwai ta tashi washegari ta mike da sauri ta shiga toilet tana salati ganin ynda ta makara, karfe takwas da rabi ta fito shirye cikin doguwar rigar kanti kamar ko da yaushe, blue ne rigar mai stones baki, sai white veil da ta daura kanta, takalminta ma fari ne haka karamar jakar hannunta sai handouts dake hannun, kana ganinta kasan a tsorace take, ta rufe kofarta da sauri ta nufi gate dai dai nan suka kusa cin karo xai shigo, sosai gabanta ya fadi ta juya kamar kiftawar ido har ta bar bakin gate din, can gun da aka tanada domin parking space a gefen apartment dinta ta nufa sannan ta juyo tayi iya kkrin ganin ta boye tsoron fuskarta tana kallonsa tayi kicin kicin da fuska, lkci daya ta karasa kofarta ta ga ya nufo wajen, tsabar rikicewa ta kasa bude jaka ta ciro makulli sae rawa hannunta yake, ta fashe da kuka ganin ya kusa wajenta tace “Am begging you stay away from me plss, I don’t know you…. Stay outta my way” har ya karaso gun bata iya ta motsa ba, kawai ta durkushe kasa ta rufe ido, jin ya bude kofar sa ta dago da sauri, suka hada ido yace “I only have ur time at night” daga haka ya shiga ciki ya rufe kofarsa ta mike a sanyaye tana kallon kofar, da sauri ta fice compound din gabanta na faduwa. Suna gama lectures ranan tace da Vanessa a gidanta xata yi spending night din, don haka tare suka wuce gidan Vanessa dake Round church street, Vanessa tayi masu girki suka ci bayan Khadijah tayi sallah, karfe shidda saurayin Vanessa ya xo gidan Khadijah ta shiga bedroom ta bar masu parlorn, har ta fara bacci Vanessa ta tada ta wai Richard xae kai su shopping, duk yanda Khadijah taki amincewa aje da ita sai da Vanessa tayi convincing dinta suka fita tare, turarurruka kawai ta deba a mall din, sun yi kusan minti sha biyar kafin Vanessa ta gama siyayyar da xata yi suka bar mall din, gun siyar da ice cream suka tafi daga nan, Suna tsaye cikin Aromi ba a kai ga siyar masu cold stone ice cream din da xa su siya ba kamar ance ta juya suka yi ido hudu da neighbor dinta, xaune yake da wata kyakkyawar baturiya da baxata wuce ashirin ba ga kayan ciye ciye a gabansu yarinyar na rike da hannunsa cikin nata, tun daga sama har kasa yake kallon khadijah, ta hade rai tayi saurin dauke kai ta amshi ledan ice cream din da Vanessa ke mika mata, Richard ya siya masu har da pizza ya biya bills din, tuni ta yi hanyar fita Vanessa na biye da ita, ta d’an saci kallonsa taga kallonta yake yana wani murmushi ta jefa masa harara suka fita wajen, motar Richard suka shiga ya mayar da su gida. A gidan Vanessa tayi weekend din gaba daya, ranan lahadi ta shirya ta koma gida ba don ranta ya so ba, duk da a xuciyarta dama niyyar dawowa ta kwaso kadan daga kayanta ta dawo gidan Vanessa tayi, tunda taxi ya ajiye ta gabanta ke faduwa kamar mai tausayin kasa ta dinga tafiya tana waige waige duk da bata ga motarsa ba hankalinta ya ki kwanciya, tana kkrin bude kofa taji an bude nasa kofar a gigice ta sakko kasa dai dai lkcn da yarinyar da ta gani a eatry ranan ta fito daga parlornsa, yarinyar tace “Hello, seems I frightened you” banxa Khadijah tayi mata da farko can kuma tace “Never mind” daga haka ta shige apartment dinta bayan ta bude, bin parlorn ta dinga yi da kallo ganin ya d’an yi k’ura, kawai tayi deciding ta gyara ko ina kafin ta bar gidan, ta tsaftace ko ina ta goge, sannan tayi wanka ta canxa kaya ta fito parlor, kitchen ta shiga jin tana jin yunwa, cikin mintuna kalilan ta hada ruwan jollof din cous cous da yaji nama ta dawo parlor ta kwanta, har bacci ya dauketa ta farka da sauri don ko cous cous din bata xuba ba, ta dawo parlor bayan tayi hakan bacci ya sake saceta, cikin bacci ta dinga jin k’auri, ta shi da sauri ta nufi kitchen din, turus tayi komai nata ya tsaya ganin wanda ke tsaye bakin gas, wani ihu tayi ta juya cikin rikicewa xata fita ya fixgota, ya matse ta jikinsa ya rufe bakinta, kasa kwakkwaran motsi tayi ta kuma kasa freeing kanta, hawaye ya cika idonta taji kafafuwarta sun kasa daukarta, yana mata wani kallo cikin husky voice nasa yace “Kin gama gudun kin dawo?” Xaro ido tayi tana kallonsa da mugun mamaki, bai damu da hakan ba yace “All this while kina gidan boy Friend din ki right?” Takaici ya rufe ta dake tace “Yess” yyi wani murmushi yace “Kina me?” Tace “Abinda kke kawo yan mata suke yi a flat din ka….” Ko rufe baki bata yi ba ya hade bakinsa da nata, ta rude ta dinga kokuwa da shi amma ko gezau, don kansa ya saketa yana kallonta da lumsassun idonsa yana murmushin rainin hankali yace “Haka kenan” ta fashe da kukan takaici ta durkushe a wajen xuciyarta na tafarfasa, yace “Next time ba sai kinje gidan saurayin ki ba, you need it… Ki sameni a flat dina kawai” daga haka ya nufi kofa, sai kuma ya juyo yace “Mind you, I hate smell of burnt foods” yana kai wa nan ya fita gidan gaba daya cike da kasaita, ta mike da sauri ta na kallon kofar don a tunaninta ta rufe da ta shigo.

*Haske Writers association*💡

 

*Haske Writers Association*💡

Back to top button