Hausa NovelsHausa NovelsNamijin Zuma Hausa Novel

Namijin Zuma 9

Sponsored Links

Free page9
Garin Kano.
Kimanin karfe goma na daren yau asabar. Alhaji Rabi’u tsaye yake a kayataccen falonsa, Wanda yaji kayan Alatu yagaji Kai dagani kasan mamallakin falon yaci ya tada da kudi. Dogo neshi yanada kiba sosai, kallo Daya na masa na fahimci yanada shekarun da Akalla baze wuce 50yrs ba, Amma a ido se kace yakai 70yrs. Zagaye kawai yakeyi a falon ba kakkautawa yayinda yake sanye da jallabiya nude color, idanuwansa sanye da farin glass, sun kad’a sunyi jajawur, ya rasa ina zesa rayuwarsa se zirya yakeyi a tangamemen falon, ko ganin girman falon da fadinsa bayayi. “ina baze yuba wlhi!” ya fadi da karfi tamkar zararre, yayinda yakaiwa bango naushi cikin kunar zuciya,,. “Wallahi sena kasheshi! Ni rabi’u nine ajalin wannan tsinannan yaron!” ya fadi yana meci gaba da zagaye a falon,. Wata farar mata ce ta turo kofar falon tashigo me matsakaicin kyau, ta tsura masa Ido, tana kula dashi a kwanakinnan dukya rikice yazama kamar mahaukaci,gashi ba fuskar daxata tambayesa meke damunsa, daman tini zaman hakuri takeyi dashi ba karamin Azzalumi bane Kawai darajar yara kesata zama dashi. Ajiyar zuciya hajiya Madina tasauke tana me kara kallon face dinsa a sace, kallo Daya ta masa tayi hanzari dauke kwayoyin idanuwanta a kansa sbda tsoronsa datakeji. Rissinawa tayi Hadi dacewa “Alhaji Aminu da Alhaji nuhu sun iso shine nace bari a maka magana, su karaso Nan n….” Ai be bari ta karasa ba ya hau matsifa daman a sama yake. “gidan bakonsu ne? Koke kikace su tsaya waje? Se kiyitamin Iko da gida kamar da kudin ubanki nasiya gidan, tinda bada kudin uwarki da ubanki aka ginamin gidana ba, kije kice su shigo…gida kmr gidan ubanki, ke kanki ba a bakin komi kike a gareni ba, duniyata tafimin ke sau dubu, ni sex dake ne kawai amfaninki a gidannan , kuma inada kudin dazan yi sex da mata goma a rana daya,dake da gindinki din Banza, jaka kawai dangin tsiya, Yar iska!..” Hajiya Madina tayi shiru tana mejin zafin kalamansa a cikin zuciyarta Amma ba yadda zatayi inda sabo ta saba dacin mutumcin Alhaji rabi’u. ” fitarmin a falo bansan ganinki!” ya fadi cikin tsawa,cikin hanzari ta juya ta bar falon, yabi Bayanta da tsuki shifa dabadan yaran data haifa masa guda biyu ba duk mata wlhi shima da baze zauna da ita ba, Allah yasa masa San yaran data haifa masa, ita dince beso, saboda daman tin asali ba auren soyayya sukayi ba ita dashi, irin Auren hadinnan ne, mahaifinsa ya hadasa da yar me masa noma, mahaifin Alhaji rafi’u nada rufin Asiri sosai mutum ne nagari, mahaifin Madina shike masa noma a wata gonarsa, rafi’u beso Auren madinaba kwata-kwata Amma ba awa mahaifinsa gaddama dole yasa ya auri madina, rafi’u irin Mutanennan ne, marasa wadatar zuciya yanada hangen na gaba dashi, Sam bashi da godiyar ubangiji, yanada San kudi, shide kudi kawai, kudi sunfi masa komi na rayuwarsa ta duniya dadih, rabi’u ma’aikacin soja ne, yayindaya jima a aikin soja, shine kasa da Aeezad Amma sam hakan be masa ba, kasancewar shi rabi’u mutum ne me sata da son zuciya, to zuwan Aeezad ya tsayar da komi, ko zasuyi magudi ba dama Dan haka duk yabi ya tsani Aeezad a duniyarnan ba wanda rabi’u da Aminansa guda biyu Aminu da nuhu suka tsana kamar Aeezad sunyi sunyi su kaudasa yana kaucewa kaidinsu, a kullum tunaninsu da kulle kullensa a kan Aeezad yake, su bakin cikinsu ya akayi yazo ya fisu komi ya fisu kudi ya fisu mukami, bayan kwanan Nan ya fara aikin soja ko rabi be Kai jimawarsu ba. Aminu da nuhu Suma duk ARMY ne Amma duk suna kasan Aeezad ne,. Karasowa sukayi cikin falon ko wannensu sanye da babbar riga a Ido dattawa ne Amma a ciki ba haka bane babban ciwo na dawainiya dasu wato (Hassada) ciwo me wuyar warkewa kenan. A Ido dukkaninsu bazasu girmewa Alhaji rabi’u ba. “lafiya Alhaji da Kiran meeting a darennan?” cewar Alhaji musa bayan sun iso falon sun zauna A kan kujerar 2ctr. “Ai da daddare mugu ke yawo…* cewar Alhaji rabi’u. “Wannan haka yake,, duk Wani mugu se dare ya tsala yake bayyana…” Cewar Alhaji nuhu. “Tinda mukaganka a haka munsan tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i. “Cewar Alhaji nuhu fuskarnan bakikirin shima se uban zane irin na gobirawa. “Tabbas…ai bazamu dena meeting dinnan ba harse mun bude Ido munga tsinannan nan baya duniya ..” cewar Alhaji musa. Alhaji rabi’u ya kwalkwale da dariyar mugunta a rayuwarsa babu Labarin dayafi masa dadih kamar ace wai ya bude Ido yaga yaronnan baya numfashi a doron duniya, Yana mutuwa shi zeyi cuku-cuku ya rike commander, shida abokansa susha shagali. Se yanzu ne Alhaji rabi’u yasamu ya zauna da murmushi a kan fuskarsa yace “tabbas wannan karon se munyi galaba a kan tsinanneN da bayajin mgnr kowa hatta na gaba dashi tsoronsa sukeji tomu bama tsoronsa ..”ya karashe Hadi da fashewa da dariya.””ah bade girin girinba a bari a gani in zatayi Mai…” cewar Alhaji nuhu. Alhaji musa ya amshe da “Gaskiya Kam, domin wannan yaron tsoro yake bani me tsanani, wannan yaron yaFi ifritu minaljinnu kaidi, komi muka shirya masa seya kauce..” ”wannan Karan be isa ya kauce ba ko ubansa wanene!” Cewar alhaji Rabi’u. “Yesss haka mukeso… Tabbas dase mun zuba ruwa a kasa munsha…Amma ya tsarin yake? Cewar musa. Alhaji rabi’u yace “Yan fashi nayi haya daga garuruwan arna, irin manyan Yan fashinnan domin su gama mana dashi,,dabadanma jirgi yabi zuwa katsina ba ai da tuni angama dashi, da sede kuji labari, na gama tsara komi kawai yabi jirgi zuwa katsina tsinannan yaronnan, yadda kukasan kamar an shaida ma shegen yaron gadar zaren dana shirya masa. ” Alhaji nuhu yayi Wani shu’umin murmushi kana yace “wannan yaronnan tsinanne ne na karshe shu’umin ne, ,..” Alhaji musa ya amshe da “Yaro ne Amma yanada brain tamkar yana Aiki da aljanu, dubafa kaga yadda mukasha d’ana masa tarko Amma sam baya kamasa…wannan in kakaga an turesa da kmr wuya, bango neshi na karfe turesa se Wanda ya shirya…” “Ni na shirya…” Cewar Alhaji rabi’u. A tare nuhu da Musa suka amsa da “Muna bayanka ranka shi Dade ..” Alhaji rabi’u ya ajiye hannu, Musa ya daura hannunsa kan na Alhaji rabi’u, nuhu ya daura nasa, suka kalli juna kana Alhaji rabi’u yace “tabbas a wannan karon se munga bayansa mune ajalinsa…” Alhaji musa ya amshe da “Tabbas, domin sarkin yawa yafi sarkin karfi, tako Wani hali semun kasheshi!” “Tabbas!!!” suka hada baki gun cewa tabbas. Haka suka dinga kulle-kulle iri-iri na yarda zasu kashe Aeezad ba tare da ansan su suka aikata ha, sune har karfe Biyun dare sunata shirya hatsabibanci kana kowanne ya nufo hanyar gidansa zuciya fal cike da rashin imani.

*katsina State*
Yau satinsa biyu, a garin katsina, kullum cikin ziryar zuwa gidan Aunty hafsat yakeyi, in beje ba hankalinsa baya kwanciya,kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa duk yabi yayi zuru-zuru kullum a gigice yake, for now de ya fara tunanin Anya ba Aljanu ne dashi ba, Anty hafsa Kam kullum cikin tunanin meke kawosa gidan kullum take, haka kawai se zuciyarta ta bata saboda yaranta ne, a fari kenan, daga baya ta fahimci gaskiya saboda Aunty nabeelah yake zuwa gidan, sbda inyazo be ganta a falon ba se ya kasa zama, harse ya bita inda take, ba Aunty hafsat ba har mijinta baban Noor na Ankare da hakan, kawai de sun zubawa sarautar Allah Ido ne, aunty hafsa Kam abubuwa da dama na Aeezad sun fara bata tsoro, ta fahimci in har bega Aunty nabeelah ba inyazo setaga kamar ze haukace. gabaki daya ma ya chanza rayuwarsa, ada seyayi watanni besamu yazo gidanta ba, inko yazo befi ma yazo sau daya ba a daddafe kuma yake zuwa,Amma yanzu inyazo seya wuni cir a gidan tin daga safe har dare, se wuraren 10:pm yake iya barin gidan da kyar. Na’eema Kam Sam Aeezad be nemeta ba, Dan haka itama kwata-kwata batabi ta kansa ba, tanata hidimar gabanta, kawai jira takeyi ya bar garin tayi tafiyarta Egypt , dabadanma mommy tace dole seya tafi ba,ita danta ita ai da tuni tabar garinma,Amma fa a kullum cikin tunani takeyi a kan meya samu Aeezad wannan Karan be dameta da jarabar Nan tasa ba, tabbas tasan gaskiya da walakin goro a miya, sede ita bame kulawa bace, itafa dadih ma taji, tinda yadawo sau daya taje bangarensa shima seda ta gayawa hajiya rafi’ah komi na cewar tinda yadawo be kusance taba kuma bezo part dinta ba, shine yasata taje ta gaidasa, sama-sama ya amsa saboda ya fara gajiya da rainin na’eema ta bata masa Rai sosai ranar daya ganta da kawarta dande kawai baya ta ita ne amma ta kona masa Rai sosai.

Kamar kullum se 10:pm ki after ma yake barin gidan, haka yauma ya bar gidan, zuwa gidansa, Yana shiga gidan tin kafin ya zauna kan kujera yaji gidan dukya ishesa. “Inasan inga mommy again! I want to see her againt!…” Ya fadi a bayyane, yayin dayakeji kmr ze haukace,haka yakeji in baya kusa da ita se yaji kamar zeyi hauka. har Wani ciwo yakeji kansa na masa yau, kwata-kwata baya iya Wani baccin Arziki a rayuwarsa bacci ai sede barawo, idanuwannan nasa sun kuma bulu-bulu, duk yabi ya rude ya rikice ya fita a hayyacinsa,. Bathroom ya fada yayi wanka ko zesamu sassaucin abinda yakeji a zuciyarsa da gangar jikinsa. Be taba jimawa a bathroom irin na yau ba, seda ya kwashi 20mnt Yana watsawa kansa ruwa saboda yaji saukin abinda ke cikin kan nasa, da gangar jikinsa,Amma ina beji saukin komi ba,harya gaji ya fito yagoge jikinsa, ya shirya cikin kayan bacci light ash color, riga da wando abinda da kalar hutu, ba karamin amsarshi kayan baccin sukayi ba, yayi Matsifar kyau,. Kwantawa yayi a kan tamfatsetsen gadonsa, ya zubawa gefe Daya ba dakin Ido, Nan ta fara masa gizo ya tashi zumbur Yana fadin “mommy!”’ yaga ta bace masa, lumshe idanuwansa yayi ya tura hannayensa cikin sumar kansa, kawai se yaji hawaye na zirya bisa kuncinsa ya rike sumar kansa da karfi, abinda yakeji a zuciyarsa zuwa kansa bana lafiya bane. “Haukacewa zanyi!” ya fadi Yana kuka kamar karamin yaro,kukansa me fidda sounds, se juyi yakeyi a kan bed din, yafi karfin 1H a wannan yanayin, yayi kuka har seda idanuwansa sukayi jajawur, shifa Ya fara tunanin mashi mahaukaciya ne ynzu. Kamar an tsungulesa ya tashi ya dauki Daya daga car key din motocinsa, ko waya be dauka ba, ya ziraro takalma abai-bai ba tare ma dayasan ba dai-dai yasako takalman ba, ya fito harabar gidan, yashiga motarsa yafigeta tini aka bude masa get din gidan, ya fice daga gidan a guje, ma’aikatan gidan nata mamakin ina zeje cikin darennan ko tunanin kansa bayayi kuma cikin dare har haka, lokacin Ana neman After 12:am ne, Addu’ur’in kariya daga sharri kawai ma’aikatan suka bishi dashi.

Direct gidan Aunty hafsat ya nufa, su kansa ma’aikatan gidan sunyi mamakin ganinsa da darennan sbda be saba zuwa ba. Aka bude masa get ko packing din Arziki beyi ba ya fito daga motar , mukullin motarma cikin motar ya barsa,. Yaci sa’ah falon gidan a bude ya danna Kai yaga babu kowa a falon, tini aunty hafsat da yaranta suna sama sunkayi bacci kasancewar gobe monday. Direct bedroom din Aunty nabeelah ya nufa a kasa dakinta yake,. Tsayuwarsa a kofar dakin nata yaji Wani irin kamshi ya ratsashi me shiga Brain, seda ya sauke ajiyar zuciya, ba tare Daya ankare ba kawai sede ya tsinci bakinsa a kan kofar bedroom din nata ya manna masa kisses uku at one time, seyaji Wani irin mugun dadih da niimah sun ratsashi Nan take yaji sasssucin matsifar da yake ciki. A hankali Ya tura kofar dakin ya shigo, idanuwansa da nata suka sarke cikin na juna,tsaye take ta gama shirinta cikin kayan baccinta kenan yashigo hamdala tayiwa ubangiji da yanzu tsirara ze ganta da ace batasa kayan baccinba,domin ita inta fito daga wanka, bata tsayawa daura Wani towel data goge jikinta shikenan, tsirara take fitowa ta nufa Waldrop din kayanta tasakan. Kallon mamakin ganinsa tashiga binsa dashi, kmr ance ta kalli kafafuwansa taga takalman kafafuwan nasa abaibai yasasu ta zubo masa Ido ta fara tunanin bashi da lafiya gaskiya komi nasa ba nutsuwa yanzu.. shikam gogan daga lallausar kafafuwanta ya fara kallonta har zuwa fuskarta, rigar baccin jikinta tasauka kasa sosai , ta matsifar yi mata kyau peach color ce me flower dark Blue, kanta sanye da hula dark blue se kamshi take bulbulawa, tako ina ta cika taf, nonuwannan ta kamesu cikin bra batasa bra Amma haka kawai yau tasa bra kamar tasan zezo da yanzu yananan Yana kalle mata nonuwa a hakama tana kallonsa se kallon nonuwan yakeyi da cikakkun duwaiwuka ta. “Takalman kafafuwanka abai-bai kasasu? Anya kana lafiya kuwa Aeezad?” Ta fadi tana kallon kafafuwan nasa. Kallon kafafuwan nasa yayi shi se yanzuma datai magana yasani,cire takalman yayi daga kafafuwansa ba tare dayace komi ba,se yanzu ya kara yadda da dagaske ya haukace. ” tukunnama… Lafiya kazo cikin darennan?” aunty nabeelah ta fadi se Kara kallonsa takeyi duk yabi yayi zuru-zuru, 2 days Sam baya Wani cin abinci sosai ta kula da hakan. Ba tare Daya bata amsa ba ya karasa kan bed dinta ya kwanta ya juyo ya zubo mata Ido tanajin sadda taji yayi kutt wato hadiyar yawu. Kallon mamaki Aunty nabeelah tadinga binsa dashi yayin da mamakinsa ya ninku A ranta,ta kalli agogon dake manne a bedside taga shabiyu da rabi ma ta gota. “Bakaje gida bane? Dare fa yayi” ta sake fadi cikin mamaki, be bata amsaba, , se kallonta yakeyi kamar yau yasaba ganinta. “Kanaji ina maka magana ka Wani zubomin idanuwa kamar kaga sabuwar halitta…” Nabeelah ta fadi a hasale, nanma be tanka taba se kallonta kawai yakeyi bako kyaftawa, ba karamin nutsuwa yake samu a kallon nata ba, ya fahimci in Yana kallonta yana samun saukin komi dake damunsa. “tashi ka tafi ni bacci zanyi dare nayi wallahi..” Cewar Aunty nabeelah dataga yanama gyara kwanciya ne a kan gadon nata. Kamar daga sama taji yace “Wallahi Ai a Nan zan kwana ni…..”

 

Littafinnan na kudi ne, gameson Namijin zuma da Namijin duniya ze biya nera dubu daya da dari biyar kacal 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank. 08101626484.

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦250
2GB = ₦700. 1GB ₦500
3GB = ₦1050. 2GB ₦1000
4GB = ₦1400. 3GB ₦1500
5GB = ₦1750. 4GB ₦2000

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

 

🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
*NAMIJIN ZUMA*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥
(Love And Romantic Story)

https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
Free page group

SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)
Last free page.

game bukatar wannan book din ya tuntumi wannan lambar ze biya nera dubu daya domin karatun wannan littafin 08101626484.

Back to top button