Matar Makaho 100
đ„ENDđ„
Page1âŁ0âŁ0âŁ
Wani irin magana ne haka nabila?toh nidai bazaâayi wannan haukar dani ba, kinji na fadâa miki taya yaro da matarsa koh sanin dadin aure basuyi ba, gani tsohowar banza nazo nasa bakina a shaâaninsu salon nayi bakin jini a wajen baiwar Allah, yarinya na ganin girmana najawa kaina raini wallahi da sakel ki barni na mutu da mutunci na.
Kuka nabila ta sake cikin maganar shagwaba tace, ni shikenan babu inda zanje naji dadi, dedena naje mata da zancen zagina tayi kema shine xaki mini haka?
Jin abinda tace yasa mahmah kashe wayar ta aje ta fita a dâakin.
Ammar yazo sun gaisa da khadija kuma ba laifi ta sake jiki dashi kadâan, kuma yana samun hankalinta, Amma ba karamin kunyar muhammad yake jiba duk lokacin da zaizo sai ya tambaye khadija a waya yayan ta na nan intace eh tofa ba zuwan zaiyi ba.
Bayan sati uku Ayau ne dubun Alâumma suka shaida dâaurin auren sarki yusuf mutallaf tare da Amaryar sa zainab Rabiâu ubangari sai kuma Abdulsalam AbdulâAziz shugaba da Amaryar sa Amina Ahmad Adara, dâauren auren da ya samu halaktan manyan mutane daga nijar har nigeriâa tabbas yan uwan zainab sun nuna mata gata a bikinta.
Bayan dâauren Auren ne mahafin Ammar ke wa yusuf zancen khadija, wanda yace sai dai aje nijar ayi batun Auren tunda canne mahaifarsu kar yan uwa suga ana musu wariya.
Su sumayya da muhammad harda khadija ayau sukabi gida gidan yan uwa domen musu sallama, washe gari taje abuja tama mahaifiyarta sallama zasu tafi nijar wajen dangin mijinta, kuma daga wajen zasu wuce America.
Ayau ne sumayyya dasu khadija da mahmah tare da tawagar sarki da Amaryar sa,suka nufi nijar, sun samu kyakkyawar tarba, saidai fa sumayya ta fuskanci sauyi a wajen nabila wanda hakan yasata shawa nabila mur, ganin duk lokacin da taga Alâameeen zatana wani kwarkwasa shikam baima nuna yasan tanayi ba, ga lawiza da kishi ke cinta, Amma dai ta kwantar da hankalinta ganin yanzun tana samun kulawa a wajen mijinta fiye da da.
Nabila tayita nacewa mahmah akan zancen ta da muhammad, wanda abin yasa mahmah tarar yusuf da zancen, kai tsaye yace mata, mahmah banki bin umurnin kiba amma mama inkin duba duk abubuwan da suka faru Nine na fata ballo ruwan, da ace nayi biyayya ga mahaifina da duk abinnan bai faruwa ba, duk da bawa baya wuce kaddararsa mama bazan iyyama muhammad wannan zancen ba,A tausayawa yaron nan yasha wahala A rayuwar sa yanzun lokacine daya kamata Ya huta, duba da irin halakcin da yarinyar nan ta masa bata cancanci haka ba, in shine ya taso da zancen aure bazan hanasa ba, Amma mama bazan iyya tikasta masa ba kiyi hakuri bawai don yana dâana ba, zaki iyya tuntubarsa duk Abinda ya yanke shikenan.
Jikin mahmah yayi sanyi kuma taji shawaran da dâanta ya bata don/a dalilin Auren dole yusuf yasha wahala, hakan yasa bata ma tinkare muhammad da zancen ba.
Gidado da badaru dayake ba boko sukayi ba, kuma yanzun sun wuce shiga makaranta, yasa sarki bada umurnin a sasu a islamiyya, da kuma yaki da jahilci koh karatun hausane da turanci su iyya,ya bude musu manyan shaguna a kasuwa,in sunje boko sun dawo sai kuma su tafi shago, asabar da lahadi suje islamiyya.
A kasuwa gidado ya hadu da indo kanwarsa na bara, cikin wani irin yanayi ya tisata har inda suke da zama, aiko suna zuwa saida yayi hawaye ganin wani kazamin waje kusa da bola innarsa ke rayuwa gata a kwance ba lafiya ga yarsa cikin datti ,sai abinda indo tayi bara ta sama musu, dâaukar su yayi wanda a lokacin inna koh sanin wake kanta batayi ba.
Sarki a washe garin ya tura su saudiya da inna,saboda ciwonta ya kazanta blood Cancer ne, yayinda indo ke zaune a gidan sarki tare da lantana karama.
Muhammad da sumayya sun wuce America tare da yaransu suna mai kewar kasarsu da yan uwansu.
Bayan tafiyar su akayi auren Gidado da nabila sai badaru da wata yarinya yar tsohowar unguwansu, sarkin shayi ma Yusuf ya hadâasa da wata bazawara an hadâasu aure.
Jikin inna yayi sauki inda sarki yasai musu gida ita da indo da yar gidado , dâaya shashin kuma gidado ne da nabila, dataga ba sarki sai Allah ta aure sa abinta.
Su sumayya basu dawo ba saida sukayi shekara dâaya, lokacin auren khadija da Ammar sukazo, khadija tayi weac dayake har lokacin tana Nigeria a abuja wajen hafsa, yayin da yaran sumayya suka cika shekara 1 da watanni a lokacin kowa yaga sumayya da muhammad sai sun basu shaâawa, gaskiya ne mahakurci mawadace, mai hakuri yana tare da riba, sannan duk mai biyayya ga iyaye zaiga Amfaninsa wata rana.
Ana bikin Ammar da khadija suka koma wajen aikin Ammar a maiduguri bayan aure ya maidata makaranta, don result nata yayi kyau sosai, su sumayya sun koma America bayan biki.
***************
Bayan wasu shekaruâŠâŠâŠ
Wani matashin magidanci ne tsaye a wani hadedden compound mai dâauke da shuke shuke mai ban shaâawa, sanye yake da kakin sojoji a jikinsa wandone da riga, kansa ba hula sai gashinsa dake kwance baki kirim yana sheki, yayi farine tas yayin da idanunsa ke dâauke da bakin glass, dukar da kansa yayi yana kallon agogon sa mai masifar tsada, dake hannunsa dâan yamutsa fuska yayi hade da dan sakin tsiririn tsaki,ganin 7:21pm Amma har yanzun gimbiyar tasa bata fitoh ba bare yaransa, jin karan bude kofar falonsu da akayi yasa sa saurin dâagowa.
Sanye take da siket baki mai kauri yana nan kamar pencil Amma baâa tsaga baya ba,sai takalmi mai tsini a kafarta dake dâauke da socks baki, shirt ne a jikinta white mai botur da dogon hannu, wanda tayi stokin dashi, Have sunnah ne a wuyanta baki, da agogo fari a dâaure a farin tsintsiyar hannunta, sai jakan office dake rataye a hannunta dâaya Tabar daya hannun na lilo, fuskar nan nata yayi fayau babu kwalliya alamu dai jin dadi ya samu waje, rike take da wani kyakkyawan yaro fari yana sanye da uniform na primary bazai wuce shekara 5 ba, ga wani yaron na binta a baya zaikai 7 shima yana sanye da uniform hannunsa dâauke da jaka dâaya hannun kuma lunch-box nasa.
Da sauri ta kara hanzartawa ganin fuskar mijin nata a hade, don tasan tabbas sun sasa jira don yau dai sun makara.
Yanzun ke kullum in zamu tafi aiki da safe sai kin sani lettin kike jin dadi, ki duba yanzun minutes 30 ina tsaye ina jiranku?
âDon Allah kayi hakuri dear wallahi neman socks in naâima nake wai bataga dâaya baâ
Toh surutun ma ai ya cinye lokacin daya saura manan, yace yana kamo yaron dake hannunta ya bude seat back ya ajesa, kallon mai shekara bakwan yayi, Au kaima salim(takwaran salim marigayi, muhammad ya hana a masa inkiya yace a barsa da sunan sa)so kake na dâaga kane koh me? kana tsaye.
Washe fararen hakoransa yayi cikin dariya ganin yau ran baban nasu a bace, yace, sorry Dady.
Shiga gaba sumayya tayi ta aje jakanta akan cinyarta da mamaki Alâameen yake kallonta, wai sumayya ina sauran yaran ne?
âAu wai basu shiga bane tare fa muke futowa dasuâ
Kinsan Allah sumayya yau in kikayi tsiya sai kija mota da kanki tunda dai naga kowa nada shi, ya fadâa a hankali yanda yaran bazasu ji ba.
âKayi hakuri tohâ kawai tace tana fita a motar daidai lokacin wasu yaran mata da zasukai shekara 10 masu tsananin kama da juna, gasu kyawawa sanye suke da uniform suna gudu da school back a hannu dâaya nabin dâayar da gudu.
Da sauri sumayya ta kalli wance ake binta da gudun, tazo ta makale a bayan Dadynsu,âNaâima mekika mataâ?
Momy wallahi babu abinda na mata.
Kallon naâifa dake hawaye a gefenta tayi, tana tsaye batabi naâima bayan dadyn sun baâ meta miki kika biyo taâ?
Wallahi momy colour nata dâauka guda hudu, kum drewing zanyi dashi fa.
Ke naâima ina naki colour da zaki dâauka mata nata?
Dady toh banga nawan bane bafa.
Da sauri sumayya ta karbi maganan jin Amsar data bawa muhammadâDaman ke haka kike kome naki baâa gani, kina ganin da safen nan harkin batar da socks naki daker na gane inda kika aje, kome naki baya lastic wannan biro in aka saima yar uwarki sai yayi 1 month tana amfani dashi, amma ke koh kwana bayayi sai kice ba pen ah ah pen ya bata, don haka oya bata colourn ta koh na saba mikiâ?
Ba musu ta bude jakanta ta mikawa naâifa abinta, sai kuma ta fashe da kuka.
Muhammad dake tsaye ne ya dubeta, toh wai kukan na menene?
Dady kuma fa bangama drewing ba gashi uncle yace duk wanda baida colour waje zai korasa bazai masa makin ba.
Ina dai akan colour ne?muhammad ya tambaye ta.
Dâaga masa kai tayi alamun eh.
Toh muje a hanya saina sai miki sabo koh?yanzun ku shiga mu wuce mun kusa makara.
Dady nimafa bani da calculator?
âDa sauri sumayya ta dubi yaron ta, kaji tsoron Allah khaleefa(yusuf) ba jiya naga calculator a jakan ka baâ
Momy Abokina kullun sai uncle ya bugesa wai bayida calculator, shine na tambayesa mai yasa baâa saya masa ba, wai Auntin sa(step mother)in dadynsa ya basa kudin saita kwace, shine na basa kyautan nawa jiya.
âMasha Allah yaron kirki haka nakeso Allah ya muku Albarkaâ
Gabaki dâayansu suka Amsa da Ameeen .
Jan motan muhammad yayi mai gadi ya walgale musu makeken get nasu suka fice.
Sai da suka bi ta bookshop ya sai musu abinda suke bukata, yaran ya fara saukewa a school, kafun ya kama hanyar bank da sumayya, tun a hanya ta makala ID card nata a wuya, suna isa bank ta sabi jakanta sukayi sallama ya wuce wajen aikin sa.
Misalin karfe 4:30 na yamma muhammad ne zaune a office yana aiki, yaji ring na wayan sa kamar bazai dâauka ba don aiki yake mai muhimmanci,dâauka yayi yana kallon mai kiran nasa da sauri yayi picking yasa a kunne,Assalamu Alaikum
Ta dâaya bangaren Ammar ya Amsa waâalaikumu salam, Captain muna fa Airport azo ya dâauke mu.
Da sauri muhammad ya mike cikin mamaki yace What? kana nufin kun shigo Lagos koh noteâs babu?
Surprise muke son muku.
Amma gaskiya ka kyauta gamunan zuwa, suna yanke wayar neman wayar sumayya yayi ya kirata
sumayya dake zauce akan kantan customer care tana aiki taji wayanta na ringing dâagawa tayi tasa a kunne ganin sunan maikiran nata, âHello Rabin Rainaâ
Hello sweetheart kin koma gidane?
âNo Rabin Rai yanzun nake kokarin fita, musa driver na haraban bank yana jiranaâ
Ok kice masa ya wuce dasu salim, ke ki jirani ina zuwa?
âLafiya dai naga kace mini yau sai 6 zaka dawo kana da aikiâ?
Lafiya yanzun Ammar yake sanar dani sun shigo lagos suna Airport.
Ok saika zo tace tana yanke wayar, number musa driver ta kira ta shaida masa ya wuce kawai gida, sannan yacewa bahbah(tsohowar mai Aikinsu)ta kara wasu abubuwan cin zasuyi baki.
Baâa jima ba da wucewar musa saiga muhammad jakanta kawai ta dâauka ta shiga motarsa suka wuce Airport, suna isa Jakanta sumayya ta bude ta zaro Abayan ta sakawa tayi daman akwai have sunnah a jikinta dukansu suka sauka a motar waya Alâameen ya dâaga ya kira Ammar.
Tsaye suke suna duduba masu fitowa, daga nesa sumayya ta hango Khadija da katon cikinta a gaba tayi kyau kamar ba khadin goggo ba hutu dajin dadi sun ratsa ta, sai Ammar dake rike da hannun yaran su biyu mace da namiji,macen baka kamar babanta sabanin na mijin dayake fari, da sauri sumayya ta dagawa Khadija hannu da sauri suka karaso garesu da gudu, yaran suka rungumi muhammad suna masa oyoyo uncle da murna suka tattaru sai gida.
Suna isa gida suka samu yaransu a tsakar gida, bahbah ta musu wanka, suna zazzaune a gaban malamin su dake can gefen flowern tsakar gidan, ai lokacin da suka gu momynsu ta sauko a mota da Ummi(khadija)gasu Amira(Aisha) da mukaddas yasasu rugawa da gudu suka nufesu da gudu, duk irin kwala musu kira da ustax keyi, ina sunyi gunsu da gudu da sauri suka rungume yaran suna murna.
Koran su sumayya tayi hardasu Ameer suka wuce wajen karatu, tace sai ustax ya tadasu sai su shigo duka.
Suna shiga cikin part daban sumayya ta sauke su khadija da mijinta, ta basu waje su kimtsa itama dâaki ta shiga ita da muhammad.
Bayan mangariba zaune suke akan daining dukansu suna cin Abinci, Ga yaransu a zazzaune Suma ana ci dasu, hira ake na yaushe gamo, kallon sumayya khadija tayi.
Aunty Gaskiya shagunan ki sun habbaka last months munje jalingo, nida maimuna mukaje shagon gaskiya nasha mamaki ganin harda saloon ga gyaran jiki duka?
âWallahi kuwa khadija kinsan yanzun shago hudu nake running Na make-up saloon gyaran jiki, lalle kuma gaskiya Alhamdulilh matar shagari na iyya kokarinta yarinyar ta burgeni akwai Amanaâ
Gaskiya ne Aunty nima na yaba da nutsuwar Rufaida.
âAi shiyasa na bar mata kula da shagunan a hannunta sannan ita ke iban maâaikata da masu trainingâ.
Toh Allah ya kara budi.
âAmeen khadija waini ina labarin kamila neâ?
wallahi aunty tadaiji sauki yanzun ba kadangarun sai daifa Abin ya taba kwakwalwanta.
âToh Allah ya sauwaka,Yajikan momy(safina)da rahamaâ
Ameen suka amsa dukan su,bayan sun gama cin abinci Yaran suka wuce ciki yayinda su sumayya ke hira falo, sallan ishaâi sukayi sukaci gaba da zaman falo ana hira.
Da gudu Naâifa take saukowa daga upstair hannunta dâauke da system in sumayya tana kwala mata kira ga sauran yaran na binsu baya.
Da mamaki sumayya ta kalleta ganin vedio call suke da mutanen nijar, karban system in tayi ta aje musu akan center table dake falon, duk suna zazzauna akan kujeran da take gaisawa suke da su nabila indo Aunty zainab da nana(Aisha takwaran mamansu muhammad)sai muwaddat dake rike da sabuwar jaririya a hannunta, gaggaisawa suke tare da mata barkar haihuwa akan basu samu zuwa ba cikin khadija wata 8 amma insha Allah zasu zo auren muhibbat.
Bawa su muhammad da Ammar system in sukayi suma suka gaisa da yusuf dake cikin iyalansa cikin farin ciki don yara biyu zainab ta haifa masa Aisha da muhin, sosai akayita hira harda mahmah data kara tsufa sosai ga lawiza duka don yau akayi sunan muwaddat duk suna hade.
Sai kusan 9 sukayi sallama khadija da mijinta sukayi part da suke sauka in sunzo, dayake yaransu dasu Naâima zasu kwana, hadâa kansu sumayya tayi har bedroom na maza wanka ta musu dukansu tasa musu kayan bacci ta kwantar dasu, tufa masu Adduâa tayi taja musu kofa, dâakinsu naâima ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu Amira dayake duk zasu iyya ma kansu, Adduâa tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta.
Dâakin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani dâan iskan kayan bacci riga da wando jikinta sai kamshi yake ta wuce dâakin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga.
Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa.
Da sauri sumayya ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje dâaya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Rabin Raina menene sirrin ne kullum dadâa kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki.
Murmushi sumayya tayi sai kuma ta tuno wani abu cikin dariya tace,kai menene haka?
Dariya ya sake tuna masa da ranan su na farko, shima Amsa ya bata, yi hakuri gado nake nema zan kwanta ne?
Itama ta sake basa Amsa, wallahi bazan kwanta dakai gado dâaya ba gadai kujera acan jeka kwanta.
Gabaki dâayansu dariya suka sake a tare cike da farin ciki suke romancing na juna, hannu muhammad yasa ya kamo blanket in ya lulubesu.
*Alhamdulil!!!!!Alhamdulilah!!!!!!!! Alhamdulilh!!!!! nagode Allah daya nuna mini wannan rana cikin koshin lafiya, harna kawo karshen labarin matar makaho, duk wanda nama ba daidai ba ina neman afuwarsa*
*MATAR MAKAHO FANâS INA MATUKAR ALFAHARI DAKU, DON DA KARFAFAWARKU NA TAKA WANNAN STEPS DANAKE KAI AYAU, WAâINDA NAGA COMMENTS NAKU DA WAâINDA BANGANI BA WAâINDA NAMA REPLY DA WAâINDA BANMA WA BA, ALLAH YABAR KAUNA INA GODIYA*đ
*SANNAN INA MAI MUKU ALBISHIR HADE DA SANAR DAKU SABON LABARI NA DAKE TAFE MAI SUNA*
đ” *ALKAWARIN MASOYA* đ”
*WANDA NAKE DA TABBACI HADE DA YAKININ ZAI MATUKAR KAYATAR DAKU INSHA ALLAH*đ
âšRuqeenjalal ke muku sallamaâš