Kanwar Maza 3
Page3
‘yan matasan yaran maza sun girmi Rumaisa, kuma duk da haka ƙarfin namiji da na mace ba ɗaya bane ba.
Tana cikin tafiya ta ji ana ke!ke! Ta tsaya waiwaya ta ga da wa ake.
tawagar yara ta gani sun nufota gadan-gadan, tana ganinsu ta san masu dukanta ne, sam bata karaya ba, maimakon ta gudu sai ta durƙusa ta fara kwasar duwatsu, ta shirya duk wanda ya kawo kai, sai ta ƙwale masa kai da dutse.
Amma a haka sai da wasu daga cikin su suka cim mata.
Sani Yayan Habiba, ya na zuwa ya kwarfeta da ƙafarsa ta faɗi ƙasa, wani danƙo ya ɗauko a aljihunsa, ya fara dukanta da shi, duka take kai masa ko ta ina da allonta har ta samu ta tashi tsaye da ƙyar a kan ƙafafuwanta.
Ta yi kukan kura ta kafa masa haƙora a kafaɗarsa, tsananin azabar zafi ya sanya ya kurma wani uban ihu ya ja da baya, dan har ƙashinsa ya ji haƙoram Ruma, sai ka ce mayya.
Ganin ta gigita Sani, wasu daga abokan nasa kuma suna fama da raɗaɗin jifan da suka sha, ya sanya ta durƙusa ta ɗauki takalminta da hijjabinta a hannu, ta tsula da gudun tsiya.
Rufa mata baya yaran suka yi, suna a taro ta, amma kamar walƙiya haka take sheƙa da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta kai filin ball ɗin su Yaya Aliyu. Suna tsaka da ball, sai ratsa cikin ƙartin mazan nan take sai gata a tsakiyar filin da maza ke uban gudu suna ball, ta cinma Aliyu a tsakiyar filin ƙwallon ta rirriƙe shi.
Mamaki ne ya kama shi, ganin hijjabinta a hannu, kanta sai hula idanunta duk sun yo waje, tana ta haki tana waige-waige.
Riƙeta yayi yana tanbayarta lafiya? Wasu daga cikin abokansa suma suka tsaya suna tambayarta ko lafiya, amma taƙi magana sai ajiyar zuciya take yi.
Aliyu ya ja ta gefe, ya sanya mata hijjabinta, ya kalleta a tsanake ya ce ‘Menene?” Shiru ta yi bata yi magana ba sai sauke numfashi take.
Haushi ne ya fara kama shi ya ce “Dan ubanki menene, me aka yi miki kika biyoni nan cikin maza?” Yayi mata maganar a hasale.
Fara gaya masa abin da ya faru tayi, kuka ya ƙwace mata.
Ɗan shiru yayi sannan ya ce “Amma ina fatan baki yi kukan a gaban yaran ba?” Ta jinjina masa kai alamar eh.
“Kin taimaki kanki, dan da kin yi musu kuka wallahi sai na ƙara miki”.
Cikin shesheƙa ta ce “Ban yi ba”
Aliyu ya ce “Bari na canza kayana muje, ɗaya bayan ɗaya ki rakani gidajensu sai naci uban yaran nan, dani suke zancen”
Ya zaunar da ita a gefe, aka cigaba da tambayarsa meya sami Rumaisa ya ce musu babu komai, su cigaba da ball ɗin su, shi zai tafi.
Su Sani kuwa tun da Allah ya sanya Ruma ta ɓace musu, suka haƙura da binta, amma suka yi alwashin sai sun kuma saka ranar da zasu naɗa mata duka, dan tayi musu ɓarna sosai.
Suna tafe a hanya, Aliyu ya ce “Ke amma ba a banza zan je rama miki ba, sai idan ki yadda zaki wanke mini kayan ball ɗina da takalmina”.
Cikin hanzari ta ce “Eh na yadda, zan wanke maka”
ya ce “To shikenan”
Ya sakata a gaba har ƙofar gidan su Habiba, Aliyu ya aika yaro yace a kira masa Sani.
Sani ya zata a cikin abokansa ne wani yake nemansa, yana ta fama da kafaɗarsa saboda cizon da Rumaisa tayi masa, sai ka ce an sare shi da manjagara a wurin ba haƙorin ɗan Adam ba, ga Habiba ita ma sai kuka take, leɓe yayi suntum ya kusa haɗewa da hancinta, bakin yaƙi rufuwa saboda dukan da ta sha da allo a fuska, sai da bakin ya fashe, banda dukan da ta yi mata a ka da allon, da take jin tamkar an mata rawani da tukunyar ƙarfe saboda nauyin da kanta zuwa fuskarta yayi mata, ba ta iya banbance a wani sashi na fuskarta hancinta da bakinta suke.
Sani ne ya fito yana waige-waige, yana neman wanda ya aiko a kirashi, Aliyu yayi caraf ya danƙe shi.
Zazzare ido Sani ya hau yi, Aliyu ya ce “Kai, kaine ka tattaro abokan ka ka daki Ruma ko?”
Cikin fitsara Sani ya ce “Nima ƙanwata ta daka, kuma ta ɓatar mini da tayata”.
“Kuma saboda kai mahaukaci ne, sai ka tattaro abokan ka maza su daketa, saboda baka da tarbiyya ko? Meyasa ba ka bari ƙanwarta ka ta rama da kanta ba?”.
Fizge-fizge Sani ya fara, yana yiwa Aliyu rashin kunya, aikuwa Aliyu ya dinga kifa masa mari, har sai da bakin Sani ya mutu, fuskarsa duk tayi ja. Ya saka shi a gaba zuwa gidan abokansa da suka yi yinƙurin dukan Rumaisa.
Duk da irin ɓarnar da Ruman ta musu da duwatsu, hakan bai hana Aliyu kama yaran ɗaya bayan ɗaya ya zane musu jikinsu ba, sannan ya saka Ruma a gaba yana rarrashinta suka tafi gida.
Ko da suka je gida, yanayin Ruman Mama ta kalla ta ga kamar ba ta da gaskiya, amma ta share ba ta kula ta ba, dan idan ta biye wa halin Rumaisa kullum sai ta daketa.
Da daddare bayan sallar isha’i duk suna zaune a tsakar gida, Rumaisa na ta tunanin me zata ci yau, dan yau ma maƙiyin na ta Mama tayi, wato tuwo, Allah ya sani yau ba ta jin za ta iya cin wannan tuwon, gashi haryanzu ranta a ɓace yake a kan abin da ya faru, dan marin da Yaya Aliyu ya yiwa Sani bai gamsar da ita ba, ji take ba zata huce ba sai ta fasa masa kai, ko ta hankaɗa shi kwata, ga kuma tuwon nan da Mama tayi ya sake ƙara mata ɓacin rai.
Yasir ne yayi sallama, hannunsa riƙe da leda, duk suka amsa masa, banda Rumaisa da ta yi zurfi a tunani.
In da Rumaisa take ya ƙarasa, ya jijjiga kanta ya ce “Ke tunanin me kike?”
Haɗe rai ta yi ta ce “Meye kuma na dakar mini kai?”
Yasir ya ce “To kwalba uwar sharri, ni ban dakar miki kai ba”
Tsaki ta yi ta ce “Ai na saba in dai ƙarya ce”
Dire mata baƙar ledar yayi a cinyarta, ya wuce ɗakinsu.
Buɗe ledar tayi ta kwance, gurasa ce fal ta masu tsire a ciki.
Murmushi ta yi ta ɗaga murya ta ce “Na gode rabin ran”
Daga ɗaki ya ce “Ko ba rabin rai ba, tun da na baki abin duniya ba, uwar son zuciya”
Rumaisa ta ce “kai dai Allah yayi maka albarka, kamar ka san ba son wannan tuwon nake ba, tunani kawai nake me zan ci? Wannan tuwon ne yake toshe mini kai bana gane karatu sosai, Allah dai ya biyaka rabin raina ”
Murmushi Yasir yayi ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Ya gama abin da yake ya fito tsakar gida, zamansa yayi dai-dai da shigowar dodonsu, wato Yaya Umar.
Cikin muryarsa ta ƙasaita yayi sallama.
Duk suka amsa masa, ba tare da ya kula kowa ba, ya ajiyewa Rumaisa leda da indomie ya ce “Tashi ki dafa mini” tabbas ba dan Mai sunan Baba ne ba ba zata yi ba, ita a rayuwarta tana son ko aiki zaka sanyata, ka lallaɓata shi kuwa mai sunan Baba bai san wannan ba, ya bada umarni a bi kawai ya sani mutum ya ƙi kuma jikinsa ya gaya masa.
Haka ta tashi ta je ta kunna wuta ta ɗora masa.
Rumaisa na tsaka da aiki, suka ji sallama, kai da jin yadda aka yi sallamar, ka san babu alheri a tare da mai sallamar.
Mama ta amsa tana faɗin maraba.
Jin yanayin yadda aka yi sallamar ne ya sanya Rumaisa faɗuwar gaba, ta tsaya cak tana sauraron abin da zai biyo baya, dan ta san babu wanda zai aikata abin da za a zo ana musu wannan sallamar a daren nan idan ba ita ba.
Mama tayi wa matar nuni da tabarma dan ta zauna, amma matar ta ce “A’a ba ma sai ma zauna ba, ai abin bana zama bane na”
Ɗan zuro kai Ruma tayi daga Kitchen, domin taga wacece, tozali tayi da Habiba da ƙaninta Sani.
Ita ba zuwansu ne ya ɗaga mata hankali ba, babu tantama ta san ƙararta aka kawo, amma tashin hankalin ta, Mai sunan Baba yana nan.
“Ban sani ba ko ke ce ki ka sanya ‘yar ki ta dinga abin da ta ga dama a cikin unguwar nan, saboda tsabar rashin mutunci da rashin ta ido, ta kama mini ‘ya ta daka, kalli fuskar Habiba, kuma duk da haka bai isheta ba, ta ɗauko yayanta suka biyo Sani gida shima suka daka, haka ake yi fisabilillahi wallahi sai da na biya na kai ta chemist aka yi mata allura.
Dawowata gida kenan bana nan kawai na tarar da yarinya baki ya haye, ya fashe ta riƙe kai sai kuka take, shima Sani kalli fuskarsa duk shatin mari tsakani da Allah Wannan adalci ne?” Ta ƙarasa maganar tana haska fuskar Habiba. Fuska ta kumbura suntum, bakin ko rufuwa baya yi, leɓen sama ya ɗage ya kusa danganawa da hancinta, duk dadashi a waje.
Duk da halin da Rumaisa take ciki na fargaba, amma sai da ta ƙunshe baki tayi dariya ƙasa-ƙasa, saboda yadda fuskar Habiba ta koma kamar an naushi fura.
Jiki a sanyaye Mama ta ce “Dan Allah dan annabi kiyi haƙuri, yaran yanzu ne sai addu’a kawai, kin ga ni ban ma san tayi ba, daga ita har yayan nata babu wanda ya zo ya gaya mini, ban ma san waye ba a cikin yayyan nata ba, amma kiyi haƙuri”.
Haidar yayi gyaran murya ya ce “Mama nine, su meyasa yaran ba a tambayesu me suka yi mata ba, hijjabi a hannu suka biyota da bulalai zasu daka…..
“Rufe mini baki ban tambayeka ba” Mama ta dakatar da haidar cikin tsawa.
Mama tayi ta bawa Babar su Habiba haƙuri, amma ba kunya babarsu Habiba ta ce “An bar yara babu tarbiyya su yi ta abin da suka ga dama, saboda tana taƙamar ita ƙanwar maza ce, sai tayi ta isakancin da ta ga dama, sai ta kashewa yarinyar fuska ta cuceni, wallahi ban da ana maƙota da sai na kai maganar wurin hukuma, dan ba zan yadda ba, ita ta dakar mini ‘ya, shi kuma ya zo ya zage ƙwanji a kan ɗana”.
Cikin muryarsa mai ban tsoro da babu alamar wasa a cikinta ya ce “Ke ya isheki haka malama, ke kamar ba uwa ba, kawai ki zo gaban mace kina cewa ‘ya’yanta basu da tarbiyya, tana baki haƙuri kina cigaba da ƙanan maganganu, kar Allah ya sanya ki haƙura ɗin, ki kai duk in da zaki kai ki je ki faɗa, kuma ko yau wani ya kuma yinƙurin taɓa Rumaisa a unguwar nan, sai mun nuna wa duniya ƙanwar maza ce, fice ki bawa mutane wuri”
Mama zata yi magana, amma mai sunan Baba ya haɗe rai, ya girgiza mata kai, tare da nunawa Babarsu Habiba hanyar fita.
Jiki na rawa ta saka su Sani a gaba suka fice, duk girma da ƙanƙantar mutum, babu wanda Umar baya yi masa kwarjini.
Sai da ya tabattar sun tafi, sannan ya dubi ƙofar Kitchen ɗin ya ce “Ke kuma fito nan munafuka” aikuwa kamar munafukar ta fito tana sunkuyar da kai ƙasa.
Ya ƙare mata kallo sannan ya ce “Muna zaman zamanmu lafiya aka haifeki, shegiya kamar rainon iblis, duk gidan nan babu mai fita ya ɗauko magana sai ke, tana zaman zamanta kin saka an zo har cikin gida ana gaya mata maganganun banza saboda ke, kai ma saboda hauka dan me zaka biye mata ku je kuna dukan ‘ya’yan mutane? Waye ya aiketa ta tsokane su?”.
Ran Aliyu ya ɓaci, ya harzuƙa ya ce “Bafa maganar hauka a nan, yarinyar nan hijjabi a hannu suka biyota, ba dan filin ball ɗin mu na hanya ba, haka zasu haɗu su yi mata duka, yara maza ba mata ba, har sun fara dukanta baiwarsu ce ita, ko kuma ce musu aka yi ba ta da gata?.
“Shut up! Ita ka san me tayi musu, wannan Yarinyar da rashin jin tsiya, ai gara su zane ta gobe ba ta kuma ba, ki cigaba da zuwa ki na janyo mata magana, wallahi ba zaki ɗora mata hawan jini a banza ba, da ki cigaba da ɗauko mata magana ana zuwa ana gaya mata maganar banza, gara na takeki na murɗe miki wuya ki mutu kowa ma ya huta”.
Tun da Mai sunan Baba ya fara sababi, Sentence ɗinsa na ƙarshe ne ya baƙanta mata rai, wai ya murɗe mata wuya ta mutu su huta. Ta yi shiru ya gama bala’insa ya ce ta wuce ta cigaba da yi masa aikinsa, ya fice.
Rumaisa tana aikin tana kuka, wato ma ba’a sonta, wai da suna zaman zamansu aka haifeta, ta hana mahaifiyarsu kwanciyar hankali.
Usman ne yayi tsaki ya ce “Wallahi Mama ɗan nan naki yana da matsala, na yi shiru ne kar na tanka masa yayi mini tijara, amma ba damar yarinya ta motsa sai faɗa, ke Ruma” ya kirata.
Ta goge hawayenta, ta fito daga Kitchen ɗin.
Ya kalleta ya ce “Duk shegen da ya takaleki kar ki raga masa, ki ci uabnsa idan yafi ƙarfin ki muna nan, yaran unguwar nan marasa mutunci, ki ka zama nusara raina ki zasu yi, duk ɗan da ya miki ki ci ubansa ko mace ko namiji mun tsaya miki”.
Mama ta ce “Zinnuraini, kai ne kake zigata ta ɗauko magana?”.
“A’a Mama bance ta ɗauko magana ba, amma duk wanda yayi mata, ta rama babu nusari a cikinmu, ƙanwarmu ba zata zama nusara ba, mu ci uban mutum ya zo kawo ƙara mu ƙara masa”
Martanin Yaya Usman ne ya ɗan sanya hankalin Rumaisa ya kwanta, ta kammala yiwa Yaya Umar aikinsa ta je ta nemi wuri ta kwanta, ko gurasar da Yasir ya bata ba ta ci ba.
Tana kwance lamo a kan katifarta, ta ji muryar Huzaifa a kanta yana cewa ki cigaba da ɗauko magana, ai gara ya murɗe miki wuyan ki mutu kowa ma ya huta da tijararki da rashin hankali.
Banza ta yi masa, kamar ba da ita yake ba, dan idan ta ce zata biyewa Huzaifa faɗa za suyi, kuma a kowane lokaci mai sunan Baba na iya shigowa, yadda yake a ƙule da ita ta san sai jikinta ya gaya mata, idan ya dawo ya tarar suna faɗa da Huzaifa.
Da safe bayan gaisuwa ba abin da ya haɗata da mutan gidan, tana kwamce a ɗaki, ‘yan mazan suka gyara komai na gidan, suka ɗora abin kari. Ko ta kan abincin safen ba ta bi ba, ta saye gurasarta a hijjabi, ta ɗau allonta ta tafi makarantar allo.
Sai dai ashe tuni labari ya iske shugaban makarantar su, a kan faɗan da suka yi jiya, malam babba ya tara su ya ce sai ya zane su.
Idon Rumaisa yayi tsilli-tsilli, dan kusa bulalar malam Babba akwai ɗan karen zafi.
Kan Malam Babba ya kai ga zuwa ya yanke musu hukunci, ta zari allonta ta kwasa da gudu, ya tsaya yana ƙwala mata kira, amma tayi burus ta bar makarantar ta kama hanyar komawa gida, dan a rayuwar Rumaisa ba ta ƙaunar duka ko kaɗan.
A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce “Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?”
Ta tura baki ta ce “Kashi nake ji shine na dawo gida”
Tsaki yayi ya ce “Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya” banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa masa baki, ba tare da ya sani ba.
Ta shiga cikin gidan tana ciccin magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin fuskar Yaya Umar.
Babu tunanin komai, ta faɗa jikinsa tana murmushi.
Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce “Autar Mama, tun ɗazu zaman jiran dawowarki nake yi”.
“Babban Yaya, yaushe ka dawo?”
“Tun ɗazu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo”.
“Wayyo daɗi, yaushe rabon da na ganka, gaba ɗaya gidan babu daɗi, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murɗe mini kai su huta”.
Waro ido yayi ya ce “Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin a gidan nan?” Ta waiwaya sannan a hankali cikin raɗa ta ce “Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi”.
Yayi murmushi ya ce “Ai ba wanda ya isa ya taɓa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo”.
Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faɗin “Iya rigima, ya halinki?”
Sake waro ido ta yi ta ce “Yaya Abdallah”.
Ya amsa da “Na’am uwar rikici”.
“Haɗa baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?”
Abdallah ya ce “Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci”
Ta taɓe baki ta ce “Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi” Gaba ɗaya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira.
Sai da aka jima sannan ta shiga ɗaki ta ajiye allonta.
Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci.
Aikuwa faɗa ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.
Zuwa Azahar gida ya ɗinke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.
Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana tuna baya.
Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta haɗu da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa ɗan garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haɗu suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.
Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune ‘ya’yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana kaɗan Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba ‘yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba.
Mama gaba ɗaya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al’ada, sai ga cikin Rumaisa.
Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya ɗauki soyayya ya ɗora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata.
Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaɗai ‘yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faɗa, Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya.
Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su.
Haka tayi ta ɗawainiya, ‘yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya
Tasowar Rumaisa a cikin ‘yan mazan nan, wannan ya ɗauka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da ɗan karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba.
Mutum ɗaya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara’a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi.
Yanzu Rumaisa tana aji huɗu na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu, babu wanda yake da cikakken ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar gidan gaba ɗaya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da ƙanwarsu kawai suke tunani.
“Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo a cikinmu”.
Mama tayi murmushi ta ce “Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa mini kanku”
Suka amsa da “Amin”
Yasir ya ce “Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya”
Huzaifa ya ce “Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan yarinyar mai kama da Akushin”
Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce “Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa”
“Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya” Yasir yayi maganar yana dariya.
Haushi ne ya kamata ta buɗe baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haɗa maganar da zata yi, da lomar abincin ta haɗiye.
Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.
Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce “Fita ki bar mini ɗaki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.
Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
“Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?” Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.
Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka “Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni”.
Girgiza kai ya yi ya ce “Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar”
Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuɗin kitso.
Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.
Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba.
Ya fito da allon a hannunsa ya ce “Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?” Ta haɗe rai ta ce “To ban iya ba, sai na iya zan wanke”.
“Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke”
Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe”.
“Astagfrillah, ni ‘ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faɗa wani tarkon, ya zan yi da raina?.
Ayshercool
08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina na Cool hausa tv
[18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724
MIKIYA WRITER’S ASSOCIATION