Gidan Aunty book 2 Page 18
BOOK 2
Page 18
WASHE GARI
Yau ma gabaki d’aya basu zaunaba suna kan aikace aikacen da za’ayi na tar’bar bakin da zasuzo, gabaki d’aya yagowar manyan part d’in gidan guda biyu an gyarasu, yau tun safe bata sanya shi a idanunta ba , bata d’aga hankalinta sosai ba itama dan Tasan hayaniyar ba’kin ce zata sakashi ‘kin fitowa . Sosai akayi wa baki abubu da yawa na har sai kowa ya ajje , ‘karfe 12:30am na safe aka je a aka d’auko Mahma da sha’a’ban a airport, mahma bata tsaya a ko ina ba sai cikin part d’inta ta da take sauka a ‘bangaran dada , sha’aban kuma daman yana building Dinsu haroon a nan d’akinsa yake Duk lokacin da yazo shima a cikin d’akin nasa yake sauka , ko wannansu part d’insa aka kai masa abinci sabida kar’a takura wa ko wannansu Sabida gajiya , karfe 2:20 itama samreen ake d’akko ta a airport , sai a lokacin tahee ta san ta , sosai kuma take mata kama da king d’inta dan dai ita macace sai fari da king ya fita sosai duk da cewar itama fararce, a ‘bangaran ummeynta ta sauka itama , a wannan karan mimi da tahee ne suka kai mata abincinta, sosai taji dad’in hakan kuma ta gode musu, dan gabaki d’aya ukti bata da wula’kanta d’an Adam tun lokacin da Akhiee ya rasu hakan ya ‘kara shiga cikin ranta . Tun safe su tahee suke abu d’aya dad’insu familyn ango da akace zasuzo sai 8 jirginsu zai shigo Lagos dan ko tasowa basuyi ba su, small mom ba jirgin ‘karge 10 ne zai shigo dasu cikin Garin lagos. Allah sarki duk yadda ummey tayi akan su huta haka tahee da Mimi su’kayi komai dasu akan dunga aikace aikace wannan karan har ita kanta ummey bata zauna ba , sai dasu tahee suka amsar mata aikinta, kamar wasu aljanu ko gajiyar jikinsu basaji sannan ko afuska babu basa nuna alamar kajiyawa da aikin da suke yi duk da tsananin gajiyar da sukayi, babu abunda yake tsayar dasu sai sallah , shima da sun gama zasu cigaba da aikinsu , ‘karfe 8:25pm na dare familyn ango suka shigo cikin Al-nahyan, babban part d’insu da aka gyara musu aka kai musu Kayansu , tahee da Mimi suna ta zuci zuci suga familyn d’in Amma basu samu sun gani ba suma Sabida ayyukan da suke yi, ‘karfe goma da rabi ma sai labarin zuwan small mom sukai tare da zoya da wani had’ad’d’an kamar balarabe da suka zo tare da zoya , kowa sai faman kud’i kyan da zoya tayi, duk rigimar nan babu yanxu ta zama ‘yan Mata , yadda suke tafiya cikin gidan lokaci zuwa lokaci zoya tana yiwa kyakkyawan guy d’in zakaga ba ‘karamin burgeka sukai ba . Itama ummey bata had’u da small mom ba , sai su momy ne suka tar’beta zuwa part d’inta itama , kowa yana mamakin yadda zoya ta koma budurwa abunta , ga mamakin inda small mom ta samo balarabe suke duk da duk cikinsu babu mu nana . Tunda aka soma hidimar nan a marya bata fito ba , itama kamar yadda akai wa tahee d’auke ta akai Sabida kar a dunga zuwa ganinta .basu tahee ne suka samu kansu ba sai wajan ‘karfe 11 na dare , ko wannansu makwanci yake bu’kata tun lokacin da Ammey ta saka su d’ibar abincin su dukda sun ce mata ba yunwa suke jiba Amma haka ummey ta zuba musu da kanta , musamman tahee da ta saka mata cikin tray , sai faman saka musu albarka take, Mimi da tahee basu wani tsaya hira ba kowa ya nufi makwancinsa , ita tahee d’auke da tray d’in da aka zubo mata abinci ta nufi hanyar part d’in Ammey duk da batasan ta yadda zata shiga da tray d’in ciki ba , batare da Ammey ta kula Dashi ba . Mamakinta rashin ganin Ammey da tayi , inda da ne tana cikin masu yin ayyukan tar’bar baki amma ko ayanxu tana da tabbacin Ammey ta san duk abunda yake wakana na ba’kin da akai , fitowa ne Kawai batayi ba . Ta’be baki tahee tayi irin alamun don’t care d’innan itama , zata ta’ba handle d’in kofar taji anri’ko hannunta , saura kad’an ta saki tray d’in hannunta . Sanye yake cikin wasu ba’ka’ken kananan kaya da suka fito da hasken fatansa sosai, sai black p-cap d’in fuskarsa da ta ‘boye , tray d’in hannunta ya karba da Sauri ta zaro idanuwa ga idanuwanta dasuka fara lumshewa alamar gajiya , ganin tana ‘bata masa lokaci ne yasa ya ri’ke mata hannu ya nufi part d’insa da ita , Allah ya temaketa babu kowa da babu abunda zai hana wani ya gansu . Yana shiga part d’insa tray d’in abincin ya ajje kafun ya cire p-cap d’in kansa ,lallausan gashinn kansa ya fito fess dashi, kallan yadda take layi yayi kafun ya d’auketa gabaki d’ayanta ya nufi toilet da ita , da kansa yayi mata wanka ya shiryata , lokacin har ta fara bacci sabida yadda ta gaji, abinci ma da ‘kyar ta Samu taci sabida baccin da takeji. Sai daya lalla’ba kayarsa tukunna kafun ya kashe duka light ya d’auki babyn sa zuwa bedroom , ganin yadda take ta faman lumshe ido ne yasashi d’ora kanta akan chest d’inshi, ya ja musu blanket, yadda taji d’umin jininsa kuwa hakan ba ‘karamin dad’i yayi mata ba shiyasa ta ‘kara rungumeshi a jikinta daddad’an kamshinsa na ratsata, ko cikakken mintu biyu tahee batayi ba bacci ya d’auketa . Shima sabida ayyukan da ya tsaya yi be dad’e ba yayi bacci rungume da babynsa.
Kamar ko da Yaushe sallahr asuba ne yake ta yar dasu , wannan karan shi kad’ai ne ya farka tahee sai baccinta take. Kallan yadda take bacci hankali kwancane yasa ya ‘kyaleta ya nufi toilet ,har yayi wanka ya shirya cikin farar jallabiyar sa tahee bacci take , sau biyu yana tashinta tana koma wa, saida yayi da gaske tukunna tahee ta tashi, saida ya tabbatar da ta shiga toilet tukunna ya bar part d’in , tahee ma wanka tahee ta ta yar da sallar ta , tana idarwa bayan tayi azkar d’in safe ta ‘kara bin lafiyar gado yau ko tunanin ammey zata nemeta batayi ba tacigaba da sha’kar baccinta hankali kwance . Lokacin da ya dawo ya tarar da ita tana baccin ta be tasheta ba , shima kwanta wa yayi a gefanta, be jima ba bacci ya d’aukesa . Karfe 9:30am tahee ta farka , idanuwantane suka sauka kan agogon d’akin da Sauri ta tashi zaune tana zare idanu, ta tashi daniyar sauka daga kan gadon ya ri’ko hannunta tare da jawota jikinsa, zatayi magana yayi mata alamar tayi shiru, shirin kuwa tayi tana binsa da kallo a tunaninta zai saketane sai taga itama ya ja mata blanket ya rungumeta a jikinsa , cikin rad’a rad’a a kunnanta ya furta “ go back to sleep “, itama cikin rad’a ta futurta “ nasan Ammey zata nemeni fa “ shima amsa ya bata “ and so ? Akwai Wanda zai hanani kasancewa da matata? So keep silent ok and sleep”, ganin ba wasa yayi maganar shiyasa itama bata kuma cewa komai tayi hugging d’insa a jikinta , daman baccin ba isarta yayi ba , and ga d’umin jikinsa shiyasa bata jima ba bacci ya ‘kara d’aukar ta.
A cikin gida kuwa ko wanna part ankai musu breakfast d’insu , har part d’in family d’in ango duk sai da aka kai musu breakfast d’insu , duk da har yanxu family d’in basu had’u waje d’aya ba. Darana ma haka aka kaiwa kowa lunch d’insa kamar yadda akai da safe , lokacin ne Abeey ya bada umarnin kowa da kowa su had’u a babban falournsa anan za’a yi dinner gabaki d’aya family din. Duk wannan abun da yake faruwa babu Wanda ya saka Ammey a cikin idanuwansa , abun mamaki kuma babu Wanda ya tanbayi inda take . A ‘bangaran Ammey kuwa jin labarin dinner d’in da za’ai tsadaddiyar gezna d’inta tasaka a ka Fito mata da ita tare da had’ad’d’an gold d’in me shegen tsad’a dan tayi al’kawari babu Wanda zai fita had’uwa yau da daddare , yau ko neman Tahee batayi ba sabida gyara kanta da take sosai har da saka cream d’in fuska. Itama tahee gabaki d’aya yinin ranar a part d’in king tayi shi , yadda ya hanata fitan ba ‘karamin mamaki da d’aure mata kai yayi ba , bata gama shiga mamakin yanayinsa ba sai lokacin da ya bata wata rantsantsiyar abaya da duk yadda mutum ya motsa sai tayi walwalin stone d’in, ba ‘karamun kyau da tsaruwa abayar tayi ba red colour sai stone d’inta da suke shinning, hatta takalmi da jaka suma red colour aka kawo mata rantsatstsu masu shegen kyau . Duk yadda taso guda ya toshe wannan kafar har mamakin yadda ake kawo masu abincin da suke ci take , ganin bata da wani Za’bi ne yasa ta rungumi mijinta su kad’ai sai faman soyayyarsu suke me tsayawa arai.
???????
Karfe 8:30 aka fara harrala cikin babban falourn Abeey da ya gama tsaruwa da had’uwa , babban falour ne sosai me set d’in kujeru kusan biyar aciki, daga gefen dama Kuma wani step ne da za’a taka befi biyar ba zai kai ka babbar dinning table d’in da a kallah zai d’auki sama da mutane 30 sabida girmanshi, ga kalolon abinci da aka saka , ta ko ina ‘kamshi ne yake tashi, ga sanyin acn da yafi komai dad’ad’a zuciyar mutanan wajan. Su ummey ne suka fara zuwa part d’in abeey, daga ita sai samreen, bayan su kuma dada ce sai mahma da ya sha’aban da suka shigo ciki suma kowa kagani cikin shigar alfarma zaka samesa , bayan su kuma familyn uncle musaddiq da uncle saleem ne Suka shigo , yau hatta amarya da su firdausi har dasu aka hallara Dan abbey yace wannan dinner d’in ta gabaki d’aya family ce , kowa da kowa ya hallara , yanxu ma small mom ce ta shigo falourn bayanta zoya ce sai had’ad’d’an matashin saurayin da a shekaru bazai wuce shekara 22 to 23 ba shima kyakkyawa ne , kana kallansa shida zoya zaka ba ‘karamun sabuwa sukai ba . Daga su kum babu Wanda ya sake shigo wa palour kusan mintuna biyar kafun suma su ango su shigo palour shida zahra kawai, banda oumma , kana kallan fuskar khaleed zaka ga annashuwa kan fuskarsa sai faman satar kallon amaryar sa yake. A cikin falour su abbey kawai babu a ciki sai haroon da bai shigo cikin falourn ba dan tukuni kabeer yazo shima dan ya gaji da neman haroon shiyasa yayi tahowarsa. Tunda zahra ta shigo cikin falourn sha’aban yake binta da kallo duk motsin da zatayi akan idanunsa , tun bata kula da shi ba har ta gane kallanta yake , ganin yadda ya ‘kura mata ido ko kunyar aka masa bayayi Yasa zahra a fakaice ta murgud’a masa baki, murmushi ya sakar mata yadda baza’a gane ba sannan ya nuna kansa , ‘kara murguda masa bakin tayi ‘kasa ‘kasa ta furta “Kurwata dai kur sai wani bina kake da kallo sai kace kaga wata sabuwar halitta, daga ‘karshe ma zahra had’e ranta tayi wai dan karya ‘kara kallanta , Hakan da tayi ba ‘karamun kyau tayi masa ba , shiga ya d’auko phone d’insa yayi snapping yadda ta had’e rai ba tare da kowa ya ankare da shiba. Sai da aka gama gaggaisawa kafun uncle saleem da uncle musaddiq shigowa falourn bayan su kuma Abeey ne tare da dadyn su zahra da abeey ya je ya d’auko shi dakansa, ko wannansu cikin shigar dattako amma da ka kalli uncle saleem zaka ga kamar yayi rashin lapiya Sabida yadda ya fad’a, aunty ba duk yanda take yatsine yatsinen ta saka kaya masu tsad’a lokacin da ta shigo cikin falourn saida jikinta yayi sanyi dan babu me shigar banza a cikinsu. Falourn yayi Sauri daga su oumma sai su tahee ne basa cikin falourn , a wannan karan hatta Mimi itama bata cikin falourn gabaki d’aya tun safe . Lokacin da su abeey Suka shigo ‘kara gaggaisawa akai gabaki d’aya familyn , tunda dama ba gabaki d’ayan su ba , ba’kin juna bane , Dady ne ya d’an bada uzurin su hajiya akan cewa mu fara cin abincin tunda tun safe zahra ta fad’a masa ciwan kan da oumma ta kwana dashi, tunda suka shigo kalon kuma yake bin saurayin nan da kallo amma be ce komai ba , daman abeey yasan halin king ba Lalle ya shigo cikin mutane haka ba duk da ya bashi umarnin shima ya shigo cikin falourn kamar kowa , umarni abbey yayi da a nufi dinning, gabaki d’aya familyn kuwa can suka nufa har lokacin Ammey itama bata shigo cikin falourn ba , a wajan dinning ma yadda sha’aban yaga zahra tana faman kunbura baki duk lokacin da ya kalleta hakan ba karamun ‘kayatar dashi yayi ba , saida ya daidaiti kujerar da zata zauna kafun shima ya zauna a wacce take facing d’inta, su momy ne sukai serving d’in kowa na falourn , and tunda suka soma cin abinci babu Wanda ya yi magana, shi sha’aban tunda aka soma cin abincin ma tsakura kawai yake sabida yadda yake kallan zahra kamar zai had’iyeta, ganin yadda ta ta’be fuska kamar me shirin kuka kuma tana ‘ko’karin Tashi daga Wajanne yasa sha’aban kallanta, tare da girgiza mata kai alamar kar ta tashi, duk da yadda take jin Haushin kallan da yake mata sai ta kasa musa masa ta zauna d’in, khaleed ma ba’abarsu a bayaba , shima tunda suka zauna yake kallan ilham da har saida yasa ta jin kunga gabaki d’aya , duk abunda suke shi da sha’aban a idanun abeey da ummey, babu abunda suke sai sakin murmushi, a haka gabaki d’aya familyn suka gama cikin abinci kafun su koma falourn gabaki d’ayansu ana hira . Zoya ce ta mi’ke tsaya amarairaice takalli abbey “ shima murmushi yasaki “ auta har yanxu baki girma ba ko, Menene kike?, ganin ya ganota ne ysa ta saki dariya “ Abbey a kwai film d’in da zan kunna mana gabaki d’aya kaji?” Hararar ta ummey tayi “ baza ki iya kunnawa anan ba sai kinje wani wajan ?” Kamar zatayi kuka ta kara kallan abbey ta ‘ki yadda ta kalli ummey ba , “ ah ah far kusa mana auta kuka , maza auta jeki kunna mata muyi kallo abunmu”, cewar dady yana d’an kallan Abeg , shima abeey Alama yayi mata akan zata iya zuwa , har ta soma tafiya tayi saurin tsaya wa tana kallan wannan matashin da suke tare “ bro Dan Allah kazo ka rakani”, d’an harararta yayi kafun ya tashi ya biyo bayanta, kallan small mom abeey yayi “ wannan son d’in naki ya burgeni, ko zaki bar mana shi”, zai yi magana shima dady ya furta “ Nima dai abunda zan fad’a kenan ka rigani, amma bari muga wazata bawa, ita small mom dariya ma suka bata , wai wazata bawa , ai me rabata da son d’inta sai Allah, tana ‘ko’karin yin magana Ammey ta shigo cikin falourn taci ado na kece raini harda ‘yar ‘karamar makeup tayi wa fuskarta, gabaki d’aya mutanan falourn zuba mata idanu sukai har ta ‘karaso cikin falourn , suna had’a ido da abeey , abeey ya had’e rai lokaci guda ransa ya baci yana binta da wani irin mugun kallo , ita kanta dada mamakin ganin ammey tace cikin falourn Amma dai bata ce komai ba sabida bataso tsaran da aka had’a yau ya ‘baci sabida wata ,gabaki d’aya sai Ammey ta tsargu da kallan da suke binta dashi amma kasancewar ta shu’umar mace sai ta ‘boye hakan a fuskarta ta Samu waje itama ta zauna tana d’an sakin masu murmushi, haka kawai taji zuciyarta na tsanan ta bugawa , ko magana ta kasa yi, lokaci zuwa lokaci kuma a wayance tana d’an sosa jikinta ta ydda bazaa gane ba . Sallar su zoya ce ta katse mata tunanin da ta fad’a , da Sauri kuma Ammey ta d’ago da idanuwanta kansu , gabantane ya fad’i ya tsinke aranta take furta meke faruwa ? , saurayin dasuka shigo tare da zoya Ammeey ta soma bi da kallo har suka shigo cikin falourn gabaki d’aya , a mugun zabure da tsananin firgita Ammey ta mi’ke tsaye tana tunanan saurayin, kirjinta da yake neman fashewa ta dafe bakinta har rawa yake wajan furta “ TAHEER !?” A Daidai lokacin da oumma ta ke shigowa falourn ita da Mimi da suka had’u a hanyar shigowa , kallar taheer da aka ambata ne yasa ta kara saurin tafiyarta, gabaki d’aya falon sai aka zuba musu idanuwa kowa yana mamakin inda tasan sa , kalmar taheer kawai oumma take maimaitawa a cikin zuciyar ta bakinta har rawa yake ‘kafafuwanta gabaki d’aya sunyi sanyi kamar sata fad’i haka take jinta , da d’inta d’aya ma Mimi dake tare da ita , itama tana shigowa cikin sar’kewar murya me cike da rauni ta furta “ taheer “ tana tunasa, muryar wacce bata ta’ba tsammani bane Ammey taji da Sauri ta kalli ‘kofar, oumma da tagani ne yasa bata san lokacin da ta hantsula ba sabida shiga tashin hankali, gabaki d’aya kokarin fita take daga hayyacinta ga susar da take ya ‘kara yawa , jiki na rawa shima taheer ya soma nuna oumma , hawaye har ya fara ‘bata masa fuska, zahra ce ta kasa yin shiru ta furta “oumma kinsanshi?”, kanta kawai oumma ta gyad’a mata a hankali ta furta taheer d’ina , taheer d’inane , Aushe zan ‘kara ganin ka taheer ? “ shima taheer kuka kawai yake da Sauri ya nufi inda oumma take ya rungumeta , sai alokacin kowa ya fahimci wanene musamman su zahra da suka gane taheer d’in da oumma take basu labari ne , sosai zahra ta cika da farin ciki kuwa finally sun ga taheer d’in umma, bata gama zancan xucin nata ba sabida ‘karar da Ammey ta saki tare da tsige d’an kwalin kanta , hankali a tashe cikin fitar hayyaci ta soma magana “ bazai yuwa ba , me ya dawo daku? Baku mutuba ? Nace me yasa baku mutuba?” Gabaki d’aya falon babu Wanda beyi mamakin furucin Ammey ba sai ma binta da kallo da suke , zata nufi hanyar fita daga falon ta ji muryarta cikin babbar tvn falon kamar wata almara. Da Sauri ta ‘kame jikinta har rawa yake yake lokacin da taji muryarta , jikin abeey har rawa yake lokaci guda , gabaki d’aya familyn kuma hankali a tashe suke kallan tvn da basu san wanene ya kunna tava , Ammey ce zaune cikin lambun sha’katawarta tare da abokin sharholiyarta da ba a Ganin fuskarsa , labarin yadda zasu kashe king da abin cikin taheera suke tattauna , da irin tsarin muguntar da Suke shirin yi suke tattaunawa , cike da tashin hankali falon a ka d’auki salati, basu gama shiga cikin tashin hankali ba sai lokacin da next vidoen ta y shiga lokacin da take kamar a haukace ta shiga d’akin tsafinta gabaki d’aya batasan ana ganin tava lokacin da take waya tana zayyane abubuwan da sukai , tun daga kashe baban tahee har da kashe yah moh da sukai , da ‘kokarin kashe king da abunda ke cikin tahee duk saida ta lissafa su ita kanta bata san lokacin da take zayyano gabaki d’aya bad’alar da sukai, next da ya shiga ba su abbey ba hatta su taheer jikinsu rawa yake lokacin da Suka ga Ammey na shan Jini, dariyar da ta ‘kyalkyalene ysa suka mayar da kallansu gabaki d’aya Kanta daske dariyar take da ta kalli d’aya daga cikinsu zata kara saka wani dariyar tana nuna su , da ‘karfi ta furta “ na kashe su , eh na kashe su, bokanya ta cika mun aikina , saura kad’an aikina ya cika kuka ‘batamun, gabaki d’ayanku sai na kashe ku, saina kashe ku da kuka ‘bata mun shiri , lokaci d’aya kuma sai ta cigaba da susar jikinta da takejin kurajan da suke jikinta suna mata ‘kai’kayi, kallo d’aya tayi Musu sai kuma ta saka gudu daniyar barin falon , tun kafun abbey ya bada umarnin a tare sukai karo da tahee da tashigo cikin falourn sanye da abayar da king ya bata , ga baki d’aya falon mi’kewa tsaye sukai su dada har yar rigan furta “ tahee suke “ Sabida tsananin mamaki, yadda Ammey taga tahee ne Yasa ta fara dukan kanta tana ja da baya cike da rud’ani , itama tahee kallon ummey da taheer kawai take hawaye na sakko mata akan fuskarta, yadda idanuwanta sukai Jane saka gane ranta ba ‘karamin ‘baci yayi ba , a zuciye takalli Ammey , “ me mukai miki? Me muka tsare miki? Me mahaifina yayi miki da zaki kashe shi? “ sai kawai tahee ta saki wata irin kara da ta razana kowa nacikin falon , kafin kace me ta sha’ko wuyan Ammey da mugun ‘karfi, taheer ma da idanuwansa ya juye zuwa ja inda Ammey mn take ya nufa amai makon ya cire hannun taheera daga sha’karda tayiwa Ammey shima ai yasaka duka karfinsa ya dam’ki gashin Ammey , damka ba irin na wasa ba , har har fatar kanta sai da ta nuna haka sabida yadda ya dam’ki gashin kanta , a d’aya bankaran tahee kuma ta sha’ke mata wuya , cikin wata murya kamar ta namiji tahee ta soma magana “ me mukai miki zaki kashe mu? Me mukai miki? Me Nona tayi miki zaki rabamu da ita? Me mukai miki da zaki rabani da lulu?nace me mukai miki?” Ammey sabida yadda Tasha azaba gudawace ta kwace mata , gabaki d’aya nunfashinta neman d’ajjesa yake a cikin falon babu Wanda yyi ‘ko’karin da katar dasu dan gabaki d’aya jikin kowa yayi sanyi a falon , cikin wani irin ‘karfi tahee ta wulwula Ammey ta buga ta da ‘kasa, bakinta da ya kasance babu hakwara biyu kawai tahee take bugu gabaki d’aya bata cikin hayyaacinta, taheer ma da idanuwansa suka sauya hannun sa ya saka da mugun ‘kafi ya daki hanci Ammey take a wajan hancinta ya fashe da Jini gabaki d’aya Ammey bata iya kwakkwaran motsi Sabida ydda ta jigata a hannunsu tahee , ganin sunan’ko’karin yin kisa ne yasa su khaleed suka nufi taheer da niyar ‘ban’bare hannun da ya kama gashinta,abun mamaki duk yadda suke da wannan girman gabaki d’aya yayi jira dasu , su mahma ma da sukayi niyar zuwa wajan ta kallo d’aya tayi musu suka sha jinin jikinsu , kafun tahee ta mayar da kallanta kan Ammey da ta gama jigata , cikin muryar kuka ta furta “ me mukai miki? Me yasa kika cutar damu haka ? “ nan ma shiru tayi ta kasa magna sai faman zare idanu da take , hannayenta biyu taheee ta had’a ta bawa Ammeey wani gigitaccen mari a fuskarta da ysa Ammey suma take a Wajan , wani marin ta bata take a Wajan Ammey ta farka, ganin abun zai wuce hankali ne yasa mahma kiran layin king Amma gabaki d’aya bata shiga number tasa .
????GIDAN AUNTY????
07041879581
MSS LEE