Gidan Aunty Book 1 Page 10
BOOK 1 đ
Free page 10 đŠ
Shigowar bintalo dakin kamar wacce aka jefo ta ko sallama babu, yasa dije kamewa, komai sai ya tsaya mata, kallan kanta da dungayi ganin duk ta ya mutsa jikinta, kallan ta bintalo tayi rai a bace tana toshe hanci âHaba Dije , kazantar taki har takai kiyi kashi a jikinki, gaskiya kina bada ni , ji beki katuwar kawai sai wari kike faman yi , ga kashin ki me shegen dâoyi, ta karasa da hararanta. Dije ce ta soma magana âHaba bintalo , Kema kinsan haka kawai bazanyi kashi a jiki ba , lalurace ta sameni , ni kaina bansan ya akai hakan ta faru baâ, ta kare zance da zunbula hijabi, gudun kar yan gidan su ganta, tayi sauri tashige bayi bayan dan ruwan da ta dauka a buta.
Su tahee ma ransu fess suka koma daki, bayan sun gama aikin su , haka suka yini a daki, lokaci zuwa lokacin tunanin dan iskan da akace za a aura mata yana fado mata arai.
*******
A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau watan su tahee 1 da âyan kwanaki a bunkure, abubuwa da dama ya faru ciki harda maganar Auran tahee da tanimu da tayi mugun tsana. A yan kwanakinan ba karamun wuya suke shaba wajan mutanan gidan, musamman kaka tabawa da dije datayi mugun tsanar su, kullum da kalar ukubar da zasuyi musu, abu daya ne ke kwatarsu , duk lokacin da kaka ta bawa ta wahalar da su ranar bata iya baccin arziki sai safiya , a lokacin su tahee ke samun damar hutawa . Taheer ma yanxu ya koyi faci, Inya futa tun safe bashi ke dawowa ba sai 6 na yamma, a gida kuwa daga oumma sai tahee, yanxu ma kwance take kan cinyar oumma tana taje mata uban tilin gashin kanta da ya zubo har gadan bayanta da cikon da yake dashi, âoummaâcewar tahee,ânaam aunty taheeâoumma ta amsa mata cikin zolaya , dariya tahee ta saka, âAllah oumma ni banasan wannan gashin kan nawa wani lokuta, kallifa ko tajeshi bana iyayi da kyau, âaikinsan hanyar iliya me aski, sai kije ya aske mikiâ, turo baki kawai tahee tayi dan tasan magana oumma ta fada mata.
Suna zaune sukaji an banko kofar dakin , duk kallan kofar sukai lokaci daya , bintalo dake tsaye se faman cika take ta kalli tahee ba ko sallama , âtoh matar mashayi sai kije angwan naki yazoâ, tana gama fadar hakan ta banko musu kofa. Tsaki tahee taja tana kokarin kontawa oumma ta dakatar da ita âtashi kijeâbata ce wa oumma komai ba ta zura hijabinta tare da ficewa waje.
A tsaye ta ganshi cikin wasu yan iskan Riga da wando, sai faman tashin warin giya yake, saurin toshe hanci tahee tayi jin zata yi amai, ga bakikkirin bakar fuskarsa sai faman naso nake , cikin Maye ya zuba wa tahee jajan idanuwansaâ ke dan uwarki , shine zan dunga kiranki kina kin zuwa, ke gaki yar iska koâ ya karasa yana tangal tangal kamar ze fado mata, matsala tahee tayi baya tana binsa n da kallan tsana âinka gama zan wuce dan banda lokacin dan iskaâ, wayo idanuwansa yayi cikin maye yana kifkifta kana nun inaduwansaâ ke, ni kike cewa dan iska dan uwarki, toh bari na nuna miki iskanci, kafun na bada sadaki zan dâanaki nasan zakiyi ruwaâ ya karasa tare da daga hannunsa zai tabata, saukar marin da yaji a fuskarsa ne yasa shi tangal tangal zai fadi, ganin yana ganin biyu biyu ne yasashi kara ware mummunar fuskarsa â kutumar ubancan , ya na fara ganin garin yana juyawa ko an fara hazo ne âbe kammala maganar tasaba tahee da idanuwanta suka juye ta kara tsinka masa mariâ saurin dafe fuskar tasa yayi har yanxu bakin nashi be mutu baâ auzubillahi, ko an fara tafiya lahira ne ban sani baâ saukar marin da yaki a fuskarsa ne ya sashi zabura da fita âshikenan a fara sha hada , an fara mutuwa â, sai da ya bace wa ganin ta sannan idanuwan ta suka dawo Daidai ganin ba kowa a wajan yasata dage kafada da komawa cikin gida . Koda ta kowa cikin gidan oumma bata ce mata komai ma , itama tahee batace komai ba sai hirarsu da suka cigaba .
â°â°â°â°â°â°â°â°â°
LAGOS
Tun dâazu ta kasa zama sai faman zirga zirga take , Aunty kawai take jira ta shigo, ta dade a tsaye kafun hajiya Amina ta shigo falon duk rai a bace , kallanta amrah tayi kafun ta sauke a jiyar zuciya, âAnda ce aunty!?â Ta tanbayeta da sigar tanbaya , bata kulataba sai da ta samu waje ta zauna â amrah ban taba sanin matar nan makira bace sai yau, wai harni tsohuwar matar nan zata karya taâ, tass ta bawa amrah labarin abunda ya faru ta dora da cewaâ wai ni amrah kina shafa kwallin tayar masa da shaâawan da Malam ya baki â cikin kun burin fuska Amrah ta amsa mata â ina shafawa aunty, gasky ya kamata a koma wajan Malamin dan bazan taba yadda wata ta same shi in ba ni ba, ni ko baze aureni ba inaso mujiyar da juna dan inasan na dâadâandâana zumarsa kona kashe shaâawar dake tasomunâjin jina mata kai kawai hajiya Amina tayi, itama amrah bata kuma cewa komai ba ta shige daki, da kallo aunty Amina ta bita â ba ke ba ai amrah ko ninan da zan samu damar dâandâanasa so nake , musamman yadda yake da kakkarfar jikinta, ni kadai nasan dadâin da zansha â duk cikin zuciyarta take wannan saâke saâken kafun ta nufi haryan dakin ta itama .
***********
Ya dan Jima a hospital yau sabida wasu Mara lapiya a dake dake cikin wani mayuwacin hali, successfully kuwa akayi musu aiki, bayan ya dawo ne zaki ya kawo masa files din company, ba karamun barnan kudi akai ba, makudan millions sun âbata, batare da kwakkwaran daliliba,duk account din da kudin ke fita ta wajansu anne mesu anrasa, Wanda hakan ya bashi alamar tanbaya , tabbas ana fitar da kudi sannan dasa hannun wasu daga cikin companyn , amma tanbayar su wanene suke fitar dashi, daya daga cikin secret agent din companyn king yasa a nemo masa, tare da bashi Umarnin binciko masa komai daya danganci file din companyn,suna gama aikin da zasuyi sukai futar gaggawa shida zaki yau ko masu tsaro be fita dasu ba.
â°â°â°â°â°tunda ta tashi yau da fargaba ta tashi, ganin kullum mutanan gidan sai sunyi maganar aura mata dan iskan da suka ce, komai cikin sanyi take yinsa, âtaheeâoumma ta kira sunanta ânaam oummaâsosai oumma ke kallantaâmeke damunkine yauâmurmushin yaâke tahee ta saki âbabu komai oumma kawai yau da fargaba na tashiâ, murmushin manya oumma ta sakiâ in Auran nan kikesa wa aranki kicireshi, ki dunga yawaita addua in alkairi ne, in kuma sharrine Allah ya nisan taki dashiâjin jina mata kai tahee tayi âinsha Allahu oummaâ.
Bin bayan ta da kallo oumma tayi , abun na damunta sosai amma tana boye rauninta ne sabida kar tahee ta karaya, kullum adduar ta Allah ya zaba mata mafi alkairi.
Shigowar tahee dakin ne yasa taheer sakin murmushi dan duk yaji zancensu,kara sakin wani murmushin yayi yana kamo hannun tahee din, be bari tayi magana ba ya dora da ânayi mafarki, nayi mafarki kinyi aure ,kin auri babban mutum da kowa yake san mallakarsa ba wancan dan iskanba, zakiyi rayuwa dasu sosai wasu zasu soki, wasu kuma zaki nuna miki kiâbinsa da kallo kawai tayi duk da bata yadda da magan ganun saba amma hakan ya sanyaya mata zuciya .
Karfe biyu na rana wasu manyan motocine suka shigo garin, kowa sai bin motar yake da kallo ana dâaga musu hannu, Daidai kofar gidansu tahee motocin nan sukai parking yara da manya kowa ya cika wajan , cikin gida kuwa har an kawo musu labari, da sauri kaka ta bawa ta shige daki tare da dakko wata farar Leda data cukurkude, bude ledar tayi tare da dakko tsinken turaran wuta, bayan ta kunna turaren wutarne ta koma ta dauko sabuwar tabarmarta ta shinfida a tsakar gidan , komai cikin sauri take yinsa .
A hankali ta fito daga cikin bayan wata tinted prado,bayan uban damin kudin data bawa security su rabawa mutane , ba kowa bace face hajiya kilishi, a hankali cikin takun manyan mutane ta nufi cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, yayinda biyu daga cikin security din suka fara fito da kayan motar suna shigar dasu cikin gidan . Tun daga kan matasan gidan har manya kowa tsugunnawa yake yana gaisheta, cikin sakin fuska take amsawa kowa harta karasa zama akan tabarmar da aka shinfida mata batare da âkyan âkyanin komai ba. Sosai sukai hirar Yaushe gamo ta bawa kowa tsarabarsa , duk wannan abun da ake su tahee basu sai me ke faruwa ba , sai hayaniyar da suke ji tana tashi sama sama,anan ne suke mata gulmar dawowar oumma da Sanar da tahee, sosai hajiya kilishi ranta ya baci akan rashin sanar da ita da basuyi ba , da Auran da suke san yiwa tahee, ranta ba karamun baci yayi har suka fara dana sanin fada mata , bata nuna musu komai ba sai fadan da tayi musu da Nasiha me ratsa jiki , sun dade suna tattaunawa kafin ta mike ta nufi dakin su tahee, kwankwasa kofa tayi , TAHEE dake tsaye rike da tsintsiya ta bude kofar , cikin waro ido da tsananin farin ciki ta furta âAUNTYâ itama aunty tata murmushi ne kwance a fuskarta, budewa tahee hannuwa tayi da sauri kuwa tahee ta nufe ta , ta rungumeta sosai tayi farin ciki da ganin auntyn Tata har hakan ya kasa boyuwa, kallanta hajiya kilishi tayi ganin yadda ta kara ramewa ga bakin da tayi, batace mata komai ba sai girgiza kai kawai da tayi bayan tahee ta bata hanyar wucewa, sallar da hajiya kilishi tayi ne yasa ko wannansu kallan kofa, take ko wannansu ya saki murmushi, TAHEER ne ya tashi daga inda yake ya bawa aunty ta su waje , bayan sun gaisa sun dade suna hira kafun hajiya kilishi tayi wa oumma jajan abin da ya faru , kallan tahee hajiya kilishi tayi kafin ta kira sunantaâ taheera â tagowa tahee tayi tana amsa mata ânaâam auntyâ cikin dan hade rai hajiya kilishi ta soma maganaâ naji labarin kince kinaso kiyi aure har ankawo kudin ki , hakane â, fashewa da kuka tahee tayi tana girgiza kanta ni bana san shi auntyâganin yadda take kuka ne yasa aunty tausaya mata itama tayi mata hakan ne sabida ta san asalin gaskiyar âshikenan share hawayen toâ kamar yadda ta satan kuwa share hawayen tayiâ yanxu zan baki zaâbi zaki bini ko zaki auri tanimuâ saurin dago da idanuwan ta tayi da zubawa auntyn tata, murmushi hajiya kilishi tayi tana mikewa â kuyi shawara toh â, ganin yadda ta mike din zata basu waje oumma ta dakatar da ita âitama yar kice ai wata shawara zatayi , duk yadda kikayi ai Daidai neâ,Murmushin farin ciki hajiya kilishi tayi ânagode sosai yaya, Allah ya bar zumunci, nan da munti 30 zamu tafi â tana gama fadar hakan ta bar dakin.
Dan kallan oumma tahee tayi cikin damuwa tace âoumma kin yadda na tafi ya barkuâ yar harara oumma tayi mata kafun ta mike â idan ba kyaso ki bita sai kitsaya ayi miki auren inyaso sai ki tareâ tana gama fadar hakan ta shige dakin. Kallanta TAHEER yayi â shawarar da oumma tayi miki shine alkairi a gareki dan mutanan nan bazasu kyaleki ba sai sun aura miki shegen mutumin can , me kama da biri âjinjina masa kai tayi cikin damuwar dake fuskar nan, ganin yadda ta damu yasashi fara janta da hira har ta sake. Suna zaune oumma tafi to tare da kallansu, sosai tayi wa tahee fada da nasiha akan ta rike mutuncin ta, ta zama me hakuri da kawaici a duk yadda ta sameta, sosai oumma tayi mata nasiha da nuna mata illar rashin yin azkar, har kuka tahee tayi ganin yadda oumma take Mata nasihan me ratsa jiki, ko wannansu dauriya yake, shima taheer ji yake kamar ya saki kuka amma ya dake tare da sakin murmushi, suna zaune a hakan hajiya kilishi ta dawo , kasan cewar tahee tayi wanka hijabinta kawai tasa tana sharar kwalla, TAHEER ya dauki jakar kayanta tare da fita dasu, oumma bata biyota rakiya ba gudun abinda ze je ya dawo . Cikin sanyin jiki tahee ta fito waje , tsatstsaye ta same mutanan yan gidan kowa sai faman harare Harare suke ba bakin magana , musamman Dije da har kwallar bakin ciki se datayi, bintalo ba sai faman zaginta take ganin ba a tafi da ita . Saida hajiya kilishi ta gama sallamarsu kafun ta kama hannun tahee ta shigar da ita mota, a haka motocin suka fara tafiya, tunda aka fara tafiya tahee tunani take , har aka karaso airport din bata sani ba sai da hajiya kilishi tayi mata magana , wata Hanya sukabi a cikin airport din da ya kaisu wani babban fili, wasu manyan jiragene awajan kusan guda uku, ko wanne da tanbarin AL_NAHYAN a jiki , daya daga cikin jiragen suka nufa jikin tahee sai faman rawa yake,Daidai bakin step din jirgin ta tsaya ta fara rarraba idanu, ruko hannunta hajiya kilishi tayi âkarki damu ba abunda zai mikiâ saurin gyada mata kai tahee tayi zuciyarta sai faman bugawa take , ga hannun hajiya kilishi da ta rike gagam a haka suka shiga cikin jirgin, duk sauran bodyguard din Sara mata sukai tare da tsayawa a wajan jirginâŠ.
Comment and share âïž.
đTHE TALENT TROUPE WRITERS đ
đLITTAFAN SUNE KAMAR HAKA đ
đđđđđ
đDUK KARFIN IZZATA( star lady)đ
đGIDAN AUNTY (mss Lee )đ
đSARKI SAMEER (xeenat love )đ
đYA FITA ZAKKA (maman sayyid)đ
đJINI DAYA (mrs bbk)đ
Comment and share âïž.
Mss Lee đ
âOpen this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
đđGIDAN AUNTYđđ
(A heart touching love story )
Story & written
By
Mss Lee đ
đTHE TALENT TROUPE WRITERS đ
PAID BOOK
MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581