Auren Shehu Book 2 Page 9
Khadija Sidi
Auren Shehu 2
9
Ya na mai duban ta ya ce
“Ba zan kashe ki ba Abu, ba kuma za ki kashe kan ki ba har sai kin haifa min yaro ko yarinya, bayan nan sai ki yi duk abin da ki ka so da rayuwar ki”
“Allah ya isa! Da hankali na ba zan haihu da bagidaje kamar ka ba! Da na san rana irin ta yau za ta zo, ranar da kazami irin ka zai min fyade da ban adana kai na ba!”
Cewar Zainab cikin tsananin tsanar Usman. Ba ta gushe ba ta kara da
“Ka cuce ni! Ka lalata min rayuwa! Na tsane ka! Na tsane ka!”
Cikin nuna halin ko in kula Usman ya tashi ya shirya tsaf duk da har cikin zuciyar sa ya ke jin zafin kukan Zainab. Ya na gama shiryawa ya sa mukulli ya bude daki ya fita, har zai fita sai kuma ya tsaya ya na kallan ta ta wutsiyar ido ya ce
“Na gane darajar ki be kai ki zauna cikin ahali na ba, dan haka daga yau wajan zaman ki kenan…..”
“Allah ya isa! Mugu azzalumi! Har wani ahali gare ka? Yanda ka min Allah ya ma ka!”
Cewar Zainab a fusace, ji ta ke kamar ta sheke Usman har sai ta ga ya dena numfashi. Ta na juyo sa ya sa kwado daga waje ya kullo daki. Duk yanda ta so ta sami makami a dakin rasawa ta yi, tabarmar ce dai nan tilo ciki. Ta na mai hade kai da gwiwa ta fashe da kuka tamkar ran ta zai fita.
Usman kuwa da fitar shi kogin da ya bi ta yankin gidan gonar ya nufa, da ke dama an killace wajan ne musammam saboda Shehu, Dake ruwan kogin ba tsayayye ba ne, mai tafiya ne, ciki yayi wankan shi har da na tsarki sannan ya koma cikin Rugar Shehu. Tun shigar sa Rahila ke zuba ido ko za ta ga Zainab dan kuwa matukar Usman ya mayar da ita ba tare da Tanko ya damke ta ba ba karamar asara za su yi ba. Sauran jama’ar gidan kuwa farin cikin ganin Usman shi kadai ya dawo su ka yi, a tunanin ya sallami Zainab sun huta.
Bukkar sa ya shiga ya hade kayan Zainab tsaf cikin akwaiti, sanan ya kira Iyalle ya ce da ita idan ta na da sabbin kayan saki na siyarwa ta ba shi zai siya. Cike da mamakin wacce za a siya Iyalle ta dauko kayan saki har biyu ta bashi, Nan ta ba shi labarin zagin da Zainab ta yi ma ta. Ya na mai bata hakuri tare da mata alkawarin hakan ba zai kara faruwa ba dan kuwa yayiwa tufkar hanci, can gidan gonar sa Zainab za ta zauna ita kadai. Iyalle ta amsa da
“toh hakan ma yayi”
Duk da har cikin ran ta ba haka ta so ba. Shi ya dauki akwatin Zainab da kan sa ba tare da ya bari an daukar masa ba, ya koma gidan gona. In da ya bar ta nan ya tadda ita zaune ba ta motsa ba, ganin shi da akwaiti ta ga kuma kayan saki hannun shi, ta zuba masa jajayen manyan idanun ta ba tare da ta tanka masa ba. Shi ma din tun da su ka hada idanu ya ya dauke kai tare da aje akwatin gefe guda, ya daura kayan bisa sannan ya fice.
Jim kadan ya dawo, ya na duban ta ya ce
“Tashi ki yi wanka”
Zainab ta masa banza. Hakan ya shi kara fadin
“Wankan tsarki na ke nufi, lokacin sallah na gabatowa…..”
Zainab ta ki kula sa sai ido kawai. Da ya ga haka sai yayi ficewar sa. Nan cikin gidan gonar ya ta kai kawo, ya rasa abin da ke masa dadi dan ko fada ya kasa komawa tunanin Zainab da halin da ta ke ciki ne ya addabi rayuwar sa, fata ya ke Allah ya sa be ji mata rauni ba dan be taba kallan Zainab a matsayin budurwa ba, ba dan komai ba sai dan dabiun ta da kuma yanda ta kaya tsakanin sa da tsohuwar matar shi Cangwai.
Da ya kasa hakuri sai ya komawa Iyalle, kunya da nauyin ta da ya ke ji ya aje gefe ya tambaye ta ya su kewa macen da ta kai budurcin ta dakin miji. Jin haka Iyalle ta san ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata, Kado dai zama ma yanzu ta fara kenan. Nan ta sheda masa cewar lalle ya kamata ta kama ruwa da ruwan dumi koda kuwa ba za ta yi wanka da shi ba, haka kuma za a bata abinci mai kyau da nama tare da kunu ta sha da zafin shi wannan tukwici ne na musammam.
Itace ya sa a aika masa gidan gona, ya na mai adduar Allah ya sa su wanye lafiya da Abu. Sai da ya tabbatar ya barwa Iyalle dukkanin abin da za a bukata domin a yiwa Zainab girkin tukwici sannan ya sake komawa gidan. Da kan sa ya hada murhu ya dora ruwan zafin, ya sami bokiti da kuma wani garwa mai fadi ya aje kewaye wanda be da maraba da na gidan Shehu, dan shi ma din babu masai. Sai da ya jira ruwan yayi zafi, ya zuba cikin bokitin da garwan ya sirka yanda Zainab za ta ji dadin sannan ya koma bukkar ya tadda ta zaune in da ya bar ta. Ganin ya nufota be sa ta motsawa ba, sai da ta ga ya sunkume ta ta rufe shi da zagi da tsinuwa ta na mai kai masa duka. Sam be kula ba haka ya kai ta har kewaye, da kayan jikin ta da komai ya aje ta cikin garwan ruwan na mai fantsalo masa gaba daya ya jika gaban rigar sa.
“Ba dan ina gudun kar na kai ki kogi wani ya gane min ke ba wallahi da can zan kai ki na ga karshen taurin kunne!”
Cewar Usaman ya na mai kara mayar da Zainab cikin garwar wacce har lokacin yunkurin tashi ta ke, hannyen sa biyu ya sa a kafadar ta yayinda ya ke dada zaunar da ita cikin ruwan.
“Allah ya isa! Mugu azzalumi! Ba zan yi wankar ba jikin ka ko nawa!”
“Jiki na! Ke makalla ki na ce haka Allah ya tsara shi ya sa ma duk lalacewar ki ba ki ba da budurcin ki ga wani ba….”
Tas ta dauke shi da mari, maimakon ta tunzura shi sai ma ya sakar mata murmushi, yayinda ya saki kafadar ta ya ce
“Ko Iya ta bata taba kai hannu fuskata ba Abu, Amma na mi ki uziri domin yau kin bani abin da ban taba tsammani zan samu daga gare ki ba duk da ta karfi na karba amma hakan ma na gode Allah ya yi albarka….”
“Allah ya isa!”
Zainab ta katse shi cikin kuka da ihu. Hakan ya sa Usman ficewa ya na mata dariyar mugunta. Bayan fitar Usman Zainab ta dan sami nutsuwa har ta fara jin dadin ruwan. Da burin kwatarwa kan ta yanci ta hakura ta cire kayan ta yi wanka ta na kuka, sosai ta wanke jikin ta ta na mai fatan wanke daudar hada jikin ta da na Usman.
Zanin da ya aje mata ta daga waje ta janyo ta daura bayan ta gama dauraye jikin ta ta yi wankan tsarki. Ko da ta fito ba ta gan shi ba sai ta yi maza ta shige ciki. Kayan ta mai dauda ta saka ta na mai watsi da kayan sakin da Usman ya aje mata. Wajan karfe uku aka aiko yara da kwararen abinci. Zainab na kalla ga bakin yunwa ta na ji amma bakin ciki ya sa ta kasa bude kwararen bare ma ta san abinda de ciki. Haka ta wuni ita kadai, tun tana firgita duk sanda shanu su ka yi kuka, har ta saba da jin koken su.
Da la’asar sakaliya ya dawo ya tadda ta zaune baci ba sha, ya na mai duban kwararen da daga gani ko bude su ba a yi ba ya furta
“Halan azumi ki ke?”
Ta masa banza. Ya na mai gyara tsayuwa ya kara da
“Toh ai ko azumin ne ai na karya shi dazu Abu, ki saki ran ki ki ci abinci”
“Ba zan ci abincin ba! Ina ruwan ka da cin abinci na?”
“Ni kuwa na ke da ruwa! Idan har ba ki ci kin koshi ba ina za ki sami damar bani hakki na?”
Usman ya bata amsa ya na mata murmushin mugunta. Hakan ba karamin tunzurata yayi ba, a fusace ta ce
“Ka sake ka kara zuwa kusa da ni sai na lahanta ka Usman!”
“Zuwa kusa da ke yanzu na fara, hakki na sai kin bani! Kuma ni ba na son raguwar mace! Na fi son mace mai kuzari, Dole ki ci abinci ko kuwa na dura ma ki ta karfi da yaji!”
“Hakan nan dai! Abin da ka iya kenan! Sai ka yi mu gani ai”
“Na baki minti talatin kacal matukar na dawo ba ki ci abinci ba ki kuka da kan ki”
Cewar Usman yayinda ya fice ya bar Zainab ta na bambami. Ko da ya koma bayan minti talatin din da ya ce, ba ta ci abincin ba. Kamar yanda ya ce zai mata dure, haka ya cafko ta cikin kokuwa ya matse kafafun ta cikin na sa, yayinda ya daure hannayen ta biyu ta bayan ta da wani dan kyelle, kunun da Iyalle ta aiko mata da shi ya shiga dura mata ta karfi da yaji Zainab ta datse bakin ta ki budewa bare ma ya samu ya shiga bakin ta.
Ganin haka Usman ya sa hannu ya ruke hancin ta yanda ba za ta iya nufashi ba matukar ba baki ta bude ba, da wuya ta yi wuya sai gashi ta bude bakin, yayi saurin dura mata, cikin kokarin numfashi kunun ya shige makoshin ta har ta kusa kwarewa amma Usman be sarara mata ba, haka sai da ta kusa shan rabin kunun sannan Allah ya bata iko ta sanya duka karfin ta ta kwabar da kwaryar da kirjin ta, nan bisa tabarma kunun ya malale.
Bin kunun yayi da kallo kafin ya dawo da kallan sa bisa fuskar ta wanda yayi shabe shabe da hawaye, ya bi bakin ta da yayi dumu dumu da kunun da ta tuzur ya ganganra har wuyar ta. Ba ta ankara ba sai gashi ya fara lashe kunun tun daga bakin ta yana kokarin sauka har wuya. Zainab ta saka ihu fadi ta ke
“Allah ya isa! Allah ya isa ban yafe ba! Allah ya isa wallahi sai Allah ya saka min! Maye! Maye kawai!”
Sai da ya lashe kunun nan tsaf sannan ya sake ta ba tare da ya kunce mata hannu ba, cikin akwaitin ta ya bude ya dauko doguwar rigar ta da bumshort, ganin ya sunkuya ya na goge kunun da ya zube bisa tabarmar cikin haki Zainab ta furta
“Wai kai wani irin azzalumi ne! Tufa ta ka mayar tsumma! Wallahi sai na saka an daure ka! Bari na samu na fita daga dajin nan! Ka kuka da kan ka Usman!”
Sai da ya gama gyara wajan tsaf, Zainab ta na ji ta na gani ya watsa kayan waje sannan ya kunce ta. A hankali ya furta
“Tun da wannan rayuwar ki ka zaba, Ni ma ita na fi so Abu, ki cigaba da taurin kunne ni ma kuma ba zan fasa aikata san rai na akan ki ba, ki sani daga ni sai ke a nan, ihun ki banza gwara ma kin sadudu….”
“Akwai Allah! Allah ne zai min maganin ka!”
Cewar Zainab cikin mayar da martani. Usman na murmushi ya furta
“Ashe kin san akwai Allah Abu?”
Shiru ta masa yayinda ta ke duban sa cike da tsana, cikin ran ta kuwa alwashin ramuwar gayya ta dauka kan Usman ko da kuwa za ta rasa ran ta ta sanadiyar haka.
Rahila kuwa ba ta yi kasa a gwiwa ba ta saci hanyar zuwa neman mijin ta Tanko, har ta fara fitar da rai sai gashi zaune in da Usman ya masa mararraba da Rugar Shehu. Sam be yi mamakin ganin ta ba dama tun kafin su iso sun shiryawa Usman, sun san zai iya hana Tanko zaman Rugar, dan haka su ka yi Rahila ta mu su leken asiri, haka kuma da ta sami wani hanyar tunkube Usman ta fito ta nemi Tanko.
Cikin rawar jiki ta kwashe komai ta fada ma Tanko. Cike da jin dadi Tanko ya ce
“Biri yayi kama da mutum! Ni na ga soyayyar kwadon nan cikin idanun Usman, ko shakka babu Usman ya kasance mai rauni a kan ta. Haka kuma daga gani diyar masu daula da daukaka ce, lalle kuwa za mu jefi tsuntsu biyu da dutse daya Rahila, kin yi aiki mai kyau ina alfahari da ke”
Jin yabo daga bakin mijin ta dadi ya cika Rahila, ba su sallama ba sai da ta masa alkawarin cika masa burin sa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Usman da Zainab suna zaman doya da manja har tsahon kwana uku, haka kuma be mayar da ita cikin ahalin sa ba ba sai ma kwaso na sa kayan yayi, nan su ka zauna da ga shi sai ita a gidan gona. A iya kwanakin da su ka yi tare, Zainab ta gano wasu dabiu na Usman da ya sanya sam ba ta taba jin wari ko makamanci shi ba a tattare da Usman. Na farko dai Usman mai yawan aswaki ne, yayi koyi da wannan hadisin da Manzo (SAW) ya ce ba dan kar na takurawa al’umata ba da na ce su dinga aswaki duk sanda za su yi alwala, haka Usman ya ke shi ya sa ko da yaushe bakin sa ya ke wasai haka kuma ya ke da fararen hakora. Bayan wannan duk da ba a raba hammatar Usman da gashi, sam ba ta taba ji ya na bugawa ba, ta sha ganin yana shafa farin abu kamar gari a hammatar shi duk sanda yar tsokanar ta tashi ya zabi ya sanya kaya gaban ta, sai daga baya ta gano ashe alimun ya ke shafawa, har ita ma ta fara fakar idanun shi ta na dan shafawa. Batun kamanin Usman kuwa bugun zuciyar ta na karuwa duk sanda ta ga Usman ba rawani, har ta kai ta na gujewa kallan sa musammam idan be da riga jikin sa.
Ran da ta cika kwana hudu ne ta tashi da zazzabi, hankalin Usman ba karamin tashi yayi ba musammam yanda ya ga ta na rawar dari. Duk taurin kan Zainab sai da ta yi laushi, cutar ta mata mugun cafka dan har da rashin cin abinci da ta ke yi. Hatta wanka shi yayi mata a ranar, rigar nan ta saki ya sanya mata tare da rufa mata zani, kafin ya shiga daji neman magani.
Cikin kankanin lokaci ya samo maganin da su ka saba sha duk sanda su ke mashasshara, Iyalle ya bawa ta dafa masa shi tare da jan kanwa, aka hada da abinci aka kai gidan gona in da Usman ke ta kai kawo dan zama ma kasawa yayi.
Kamar yanda ta saba masa gardama, yau din ma da kyar ya samu ta ci abincin da aka aiko musu, shinkafa ne da mai da yaji. Sai da ya ga ta danci sannan ya fara kokarin bata magani, nan ma sai yayi da gaske ta sha, aje kwaryar maganin yayi yayinda da ya jawo ta kirjin sa ya rungume. Yanda ya ji ta yi lamo ba tare da ta yi yunkurin kwatar kan ta ba Usman ya tabbatar Zainab na jin jiki. Cikin rada ya furta
“Ya zan yi da ke Abu? Duk yanda ki ka bata min! Duk yanda na so na gana mi ki azaba Abu na kasa, Abu kin cutar da ni amma gashi kin shiga rai na, ya zan yi da ke Abu?”
“Ka rabu da ni na mutu ko kuwa ka mayar da ni in da ka dauko ni”
Cewar Zainab daga can kasan makogaro. Usman ya dada rungume ta kamar wanda zai mayar da ita jikin sa ya furta
“Ba zan iya ko wani daya daga cikin su ba Abu, ba zan iya rabuwa da ke ba…”
Jin haka Zainab ta fara kokarin cire jikin ta daga na shi, hakan ya sa shi kara ruko ta sosai. Ya na shafa bayan ta ya ce
“Shhhhh! Ni da ke ba mu taba samun kusanci mai cike da nutsuwa irin na wannan yanayin ba, ki kwanta kawai Abu, ki yi shiru abin ki idan kin sami sauki za mu tattauna, Allah ya baki lafiya”
Karo na farko da Zainab ta bi umarnin sa cikin kwanciyar hankali, ta na mai runtse idanu ta yi kwanciyar ta jikin sa har bacci ya sace ta.