Auren Shehu Book 2 Page 14
AUREN SHEHU 2
Bayan ta yi mai isar ta, ta tashi ta fara hade na ta ya na ta, tsoron abin da ke cikin takardar da Usman ya bata ya sa ta kasa budewa bare ta karanta, dan kuwa idan ta ga saki uku za ta iya zarewa. Kayan da Usman ya kawo mata ta sanya, kafarta sanye da silifas ruwan dorawa. Kallo daya za a mata a danganta ta da fulanin daji.
Idan aka dauke Raqeeba babu wanda jikin sa be yi sanyi ba ganin Zainab ta fito dauke da akwatin ta, tsakar gidan Shehu cike da jama’a manya da yara sun zo mata sallama, su Iyalle kuwa cikin su har da ma su kuka. Zainab ta karaci waige waigen ta ko za ta ga Shehu, hakan ya sa Bello fadin
“Tun dazu ya fice…..ya ce ba sai mun tsimaye shi ba”
Kai Zainab ta gyada kawai ba tare da ta iya furta komai ba. Ta na kuka su Iyalle na kuka tare da neman yafiyar juna, har su ka mata rakiya daidai mararraba da Usman ya taba aje Tanko sannan su ka juya cike da alhini.
Tafiya ce mikakkiya Muhamadu Bello da Zainab su ka yi, duk sanda ya nemi su zauna ko dan Zainab ta samu ta huta, sai ta ki, gaba daya a tafiyar ta ke sauke fushin ta, ganin haka duk sanda lokacin sallah yayi Muhamad Bello ya ke bata lokaci ko ya samu ta huta.
Ta ki ci, ta ki sha sai kuka. Sai yamma likis su ka Isa Mambila, dake sun saba sosai da Bello sun sami tarba na karamci, in da aka ware ma Zainab daki na musammam dake wasu daga cikin su ba su mance Zainab ba. Ita kuwa sam ba ta iya tuna komai bare ma ta gane su. Da adduar Allah ya sa Usman ya biyo sahun su ya ce ta dawo ya fasa mayar da ita ta kwana cikin ran ta. Ba ta yanke zato ba sai da washagari da sassafe Bello ya sanya ta cikin motan Taraba. Makudan kudin da Usman ya ce a bata, kulle cikin bakar leda Bello ya aje a kan kafarta bayan yayi yayi ta karba, ta ki.
Har zai juya ganin halin da Zainab ta ke ciki ya sa ya kasa tafiya ya bar ta kamar yanda Usman ya ce, tare su ka karasa Taraba. Wajan kwana ne ya gagara sai da Allah ya taimaka wani driver ya kai su wani dan karamin hotel wanda za a kira shi da ba yabo ba fallasa, Bello ya kama mata daki guda, tare da siya mata abinci. Ya sheda mata shi ya na daga can waje kila ya kwana wajan masu gadi dan kuwa shi be saba da rayuwa mai tsada haka ba.
Abincin na su babu laifi, Amma kasancewar ta na cikin bakin ciki da kewar Usman da kyar ta dan caccaka sannan ta yi sallah ta na mai rokan Allah mafita. Kasancewar Zainab ta kwana biyu ba ta kwana kan katifa ba, sai ta ji gadon ya mata wani irin, ta gwammaci ta yi kwanciyar ta bisa dadduma duk da ta san baccin ba zuwa zai yi ba.
Da sassafe wajan karfe Shida ya sanya ta motar Kano, Zainab na masa magiyar kar ya barta shi kuma Bello ya na bata hakuri, har ta kusa tara masa jama’a ciki har da masu cewa
“Toh ana tafiya dole ne? Tun da ta ce ba ta yi a rabu da ita mana”
Wani kuma fadi ya ke
“Kai kuwa ka juya da ita mana”
Cike da rarrashi Bello ya furta
“Ki yi hakuri uwar gida, ban san takamamman dalilin da ya sa Shehu hakuri da ke ba, bayan jaddada soyayyar ki da yayi a gare ni, Shehu na kaunar ki matuka kusan sai na ce ke ce diya mace dal tilo da zan iya bugar kirji na ce Shehu ya so, so daya tal! Shehu ya zabi barin mu, barin Rugar Shehu da komai na shi domin ya dawo birni ya rayu da ke. Dan haka ni sai dai na ce ki yi hakuri, wannan al’amari na ku da daure kai ya ke, Allah ya saka hakan ya fi zama alkhairi, Allah ya sada mu da alkhairin sa, bissalam”
Ya juya ya na mai matse kwalla, in da ya bar Zainab cike da da na sani iri iri, musammam na kasa rokan Usman da ta yi, da ta sani da ta nemi yafiyar shi, da ta san zai ce su dawo birni da ba ta ji zugar Rahila ba, da kuma ba ta bari zugar Raqeeba ya rude ta ba, duk da a lokacin neman hanyar tafiya ta ke Ido rufe, yanzu gashi Allah ya yassare mata lokacin da sam ba ta bukatar komawar ta gidan. Gaba daya rayuwar ta ta sauya cikin watanni kalilan, shin ina ta dosa? Daga ina za ta fara? Tunanin da ta yi ta yi kenan a hanya.
Ba kamar da ba duk check point in aka tsaya sojoji sai sun tanka ta, wannan karan babu wanda ya lura da ita saboda shigar fulanin da Usman ya sanya ta tayi, da kuma wannan shekin da fatar ta take gaba daya ya tafi. Sanda su ka isa Kano Magarib ta yi, dan sahu ta tara ya kai ta gida. Amma ko da ta doshi kofar gate din gidan Malam, gaban ta na faduwa ta shiga bugawa, wani saban maigadi ne ya bude. Ganin mace tsaye bakin kofa ta yi dagaje dagaje da ita cikin kayan fulani ya dube ta ya ce
“Lafiya? Ku barar ku ba dare ba rana?”
Cike da bacin rai Zainab ta furta
“Na ma ka kama da yar bara? Kai wanene ma?”
“Kut! Kanin uban ki ne ni! Ja’ira! Sai ki ta zama a nan tunda ke abin na ki ma har da rashin kunya!”
Baki Zainab ta bude, duk tsiwar ta yau sai gashi ta rasa ta cewa, wai ita ake kira almajira a gidan uban ta. Katan dutse ta dauka ta shiga buga kofar da iya karfin ta. Isowar mota tare da fitowar Jauro da saban maigadi wanda bugun da Zainab ta ke yiwa gate din ya sanya su fitowa a fusace lokaci guda ne. Motar ce ta dalle Zainab wacce Jauro ya hau da fada da shi kan shi be gane ta ba, fadi ya ke
“Wallahi sai mu yi kasa kasa da ke a wajen nan! Kofar gidan uban ki ne za ki kama da bugu ko akwai wanda ki ke bi bashi? Kai muntari ko wani ya siyi nono gun ta ne be biya ta ba?”
Cike da takaici Zainab ta furta
“Kai din gidan uban ka ne ai! Ba nono ba Shanu ya sa siya! Wallahi duka sai kun ci uban ka ni Zainab sai na yi maganin ku!”
Jin Murya irin ta Zainab Jaura ya bude idanu ya na duban ta, gaba daya ya ma manta da motar da ta tsaya ta na shirin a bude kofa su shiga. Muntari da har lokacin be gano komai ba cewa yayi
“Wallahi ban taba siyan nono gun ta ba, kai ni yau ma na fara ganin ta….”
“Hayaniyar me ku ke mana ne da ba za ku zo ku bude mana kofa ba?”
Cewar Falmat wacce ta gaji da sakarcin su Jauro, ta sauke gilashi cikin neman ba’asi. Gefan ta Halitta ce zaune, da ke sa’ad da su ka je umara ta makale lalle sai da Sudais ya bari ta biyo su Nigeria, za ta yi wata guda ya zo ya dauke ta.
Tsayawa Zainab ta yi ta na duban motar cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, dukan su biyun ba su lura da ita ba, musammam Falmat wacce ta ke bambamin sun ki su bude mu su gate su shigar da mota.
Cikin inina ya na mai nuna Zainab da yatsa Jauro ya furta
“Ran-ran-ki ya da-de ina ga fa kamar dai Hajiya Yakura ce……”
Sai a sannan su ka lura da Zainab, Halitta ce ta fara fitowa da sauri inda Falmat ma ta bi bayan ta, gaban ta su ka karasa idanun su kan Zainab yayinda ita ma din su ta ke kallo, shigar su, yanayin su da kamai na su yayi daban, musammam Halitta wacce ta yi jajur kamar balarabiya cikin bakar abaya. Sai Zainab ta ke jin kan na ta tamkar almajira kamar yanda saban mai gadi ya yi zato, hawayen da su ka dade ba su zuba daga idanun ta ne su ka fara shirin zubowa, ta yi saurin kawar da kai gefe.
“Yakura……….”
Cewar Halitta yayinda ta rungumo ta da sauri, kamshin turaren ta ya maye warin ranar da Zainab ta kwaso, ta ma rasa yanda za ta yi, murnar ganin Yakura ko kuwa kuka za ta yi, Falmat kuwa rugawa ta yi ciki ta ihu fadi ta ke
“Yakura! Yakura ce! Wallahi Yakura ce! Ammy Allah ya karbi adduar mu!
Halitta ta janye Zainab ciki dan kuwa yan unguwa har sun fara tsayawa ganin ba’asi. Ammy ba ta gasgata maganar Falmat ba sai da ta ga Halitta ta shigo hannun ta rike da na Zainab, nan ta zube ta yi sujjada na godiya ga Allah sannan ta tashi ta rugume Zainab, dukan su hudu kuka su ke, aka rasa wanda zai rarrashi wani, musammam Zainab wacce ita na ta kukan biyu ne, har da na rashin Usman.
Sai da su ka dan nusta ne Falmat ta fita shigo da mota, Halitta zaune kusa da Zainab har lokacin ta kasa sakin ta, Ammy ce ki ta kiran yan uwa da abokan arziki ta na sheda mu su Allah ya dawo da Zainab, Yakura ta dawo. Anty Sauda kuwa cewa ta yi da Yakura ta huta Ammy ta fara tambayar ta in da za a samo tsinannen almajirin nan da kuma in da ya kai ta, idan Allah ya wayi gari ita za ta zo.
Duk yanda su ka so Zainab ta fada mu su daga in da ta ke, ko kuma yanda aka yi aka tafi da ita, da kuma wanda ya tafi da ita sai Zainab ta sa mu su kuka. Hakan ba karamin dada tayarwa Ammy da hankali yayi ba, dan haka ta ce kada wanda ya kara tambayar ta komai, a bari ta huta tukunna ko zuwa gobe ne.
Ruwan wanka aka hada mata, bayan Falmat da kan ta ta gyara mata daki. Sai ta ke ganin komai daban musammam da ta shiga bandaki, wai itace cikin tangaran maimakon zagayen kara da Usman ya sa aka mata, cikin kokarin tsayar da hawayen ta yi wanka ta fito. Cikin kayan ta da ta bari a gida ta sami wata doguwar riga mara hannu ta sanya. Gaba daya jin ta ke tamakar bakuwa, komai na gida ya zame mata tamkar sabon abu, gadon katako maimaikon gadon karar da ta saba, carpet maimakon tabarma ko ledar da ta saba, tiles maimakon kasa da tsakuwar da ta saba takawa.
Ta idar da sallah kenan sai ga Halitta dauke da farantin abinci, ta aje gaban ta tare da fadin
“Yakura ki daure ki ci abinci”
Zainab ta yi mata shiru kawai ta na duban ta. Ganin ba ta da niyar bude kolar ne Halitta ta bude ta fara zuba mata, shinkafa ce jellof ya sha bushesshen kifi, yanayin turirin da ke fitar da kamshin kifin ne ya daki hancin yakura, tun ta na iya jurewa har ta kai ga toshe hanci da hannu, cikin ta ne ki hautsinawa sanadiyar rashin abincin da ba ta ci ba tun safe, ba ta ankara ba sai ji ta yi amai ya taso mata, ta tashi a guje ta shiga bandaki. Nan ta yi ta amai kamar wacce za ta amayar da hanjin cikin ta. Hankali tashe Halitta ta kira Ammy.
Cike da tsoran abin da zuciyar ta ke ayya na mata Ammy ta furta
“Yakura ayya kuwa? Tun da na gan ki na san ba ki da cikakkiyar lafiya, tin kafin dare yayi mu tafi asibi…”
“Ammy gajiya ce kawai da yunwa, tun safe ban ci abinci ba hanji na ya kulle, da na sha ruwan zafi I will be fine”
“Duk da haka gobe sai mun je asibiti Yakura…..”
“Allah ya kai mu”
Cewar Zainab cikin kaguwar su tafi ko ta samu ta huta. Ammy ba ta barta ba sai da ta tabbatar ta sha ruwan bakin shayi kamar yanda ta bukata, bayan shi ba ta iya cin komai ba, dole haka su ka bar ta ta kwanta.
Tun da su ka fita take juyi kan gado, Baccin gaji ya ke diban ta amma hakan be sa ta dena ganin Usman da ke mata gizo cikin idanun ta ba. Filo ta ja ta rungume tamkar shi ne Usman cikin magagin bacci ta furta
“Ina san ka Usman, ba zan iya rayuwa da wanin ka ba, dan Allah ka rufa min asiri ka dauke ni daga nan…….”
Inda Zainab ke cikin radadin san Usman, shi ma a nashi bangaran gaba daya ya rikicewa su Iyalle tun bayan da ya dawo ya tadda Bello ya cika umarnin shi ya tafi da Zainab.
Ko zaman cikin Rugar baya iya yi bare ya yarda ya shiga bukkar sa ko wanda Zainab ta koma bayan ya farfado da ga ciwo. Kamar yanda ya ke mata gizo shi ma din gizo ta ke masa. Fatan shi Allah ya sa ta isa gida lafiya gashi be da hanyar da zai gane hakan.
***
Anty Sauda tare da Ammy da Halitta ne su kai Zainab asibitin premier washagari da azahar bayan isowar ta, tare ta ke da sojoji wanda a fadar ta su ne za su rubuta statement din da Zainab za ta ba su bayan sun dawo daga asibiti, ta sha alwashin kama Usman da duk wani da ya ke da sa hannun dauke Zainab. Babu gwajin da ba a yiwa Zainab ba, ciki har da na HIV, hepatitis da na juna biyu.
Bayan an gama gwaje gwajen suna zaune jiran fitowar sakamako Zainab ta yi zaman ta can gefe a reception, ba ta iya zama cikin su Halitta bare ta saki jiki da su.
Anty Sauda wacce ke zaune tare da Halitta da Ammy, ta girgiza kai bayan ta karewa Zainab kallo ta ce
“Wallahi wannan tsinannan almajirin ya cuce mu! Dan Allah ki ga yanda yayi breaking Zainab completely? Ji yanda Zainab ta koma, ji irin shigar da Zainab ta ke yi ta fita?”
Duka ukun kallan ta su ke yi, ita kuwa sam hankalin ta ba ya wajan su, tunanin sakamon gwajin da aka mata ta ke na game da juna biyu, duk da dai ita kan ta ba ta san wani irin sakamako ta ke fata ba, burin ta dai Allah ya tabbatar mata da abin da ya fi alkhairi.
Sanye ta ke cikin hijabi ruwan toka wanda ya sauka har kasa, sam babu wani alamar rawan kai da jin kai da aka san Zainab da shi. Hannu ta sa ta goge hawayen da ke gangarowa daga idanun ta, hakan ya sa Ammy dauke kai cike da jin zafin halin da diyar ta take ciki, ta na mai zargin kan ta da Malam da laifin sanya ta cikin duk wata masifa da ya afka mata.
Halitta da Anty Sauda ne su ka koma wajan ta, inda Halitta ta rungume ta cikin rarrashi, Anty Sauda kuwa fadi ta ke
“Ki dena kuka Yakura, wallahi sai an kwatar mi ki hakkin ki, na mi ki alkawarin kamo duk wanda ke da sa hunnu cikin wannan lamarin ko da kuwa wannan tsinannen almajirin ne! Ai ga irin ta nan! Na dage sai ya sake ki uwar ku ta ki goya mana baya, yanzu wa gari ya waya?”
Likita ce ta fito ta bukaci ganin Zainab ita kadai domin bata sakamakon gwaje gwajen da aka mata, Anty Sauda ta ki yarda lelle sai dai a fadi sakamakon a gaban su, ai su ne su ka kawo ta, da abin na sirrin Zainab ne da ba za su kawo ta ba sai su ce ta yi tafiyar ta ita kadai.
Sai da Zainab ta ba da izini sannan likitar ta yarda su ma din su ka bi Zainab zuwa ofishin likitan, Halitta ce kadai ta zauna waje.
Zainab da Anty Sauda zaune kujerar da ke fuskantar teburin likita, in da Ammy ta sami kujera can gefe ta zauna. Da Ammy har Anty Sauda likita su zubawa ido cikin jaran tsammani. Cike da nutsuwa likita ta musu bayanin cewa duka kwaje kwajen Zainab negative results aka samu ma’ana ba ta dauke da wani cuta da ake tsoro, likita ta kare jawabin ta ta hanyar fadin
” Sai dai kuma sakamakon gwajin juna biyun da aka mata ne mabambamci, dan kuwa ya nuna ta na dauke da juna biyu….”
Wani irin shauki ne ya ziyarci zuciyar Zainab ta tsinci kan ta tana mai runtse idanu, yayinda ta ke jiyo maganganun Anty Sauda tamkar ruwan zafi, fadi ta ke
“Ko juna dari ne zubar da shi za a yi wallahi! A yi polishing tsinannen……”
Ammy kuwa kuka ta saka ta salati, cewa ta ke
“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Innalillahi wainnailaihi rajiun!”
Anty Sauda ta kara da
“Sai yanzu ki ke da bakin salati? Ai dama aka ce wanda be ji bari ba ya ji hoho, mu ka yi mu ka yi ki dakile auren nan ki ka min kunne uwar shegu! Ai ga irin ta nan! Kai idan har ba a kama min yaran nan ba ban isa Sauda ba! Likita mu na so a cire cikin nan da gaggawa….!”
“Babu wanda zai cire min ciki!”
Cewar Zainab a fusace. Hakan ya sa su Anty Sauda sakin baki su na kallan ta. Ba ta gushe ba ta kara da
“Cikin shege ake zubarwa ba na halas ba, dana dan halas ne kada wanda ya kara aibata min ciki bare ya tsinantar min da shi! Idan har wahalar hanya be zubar min da ciki ba, ban ga dalilin da zai sa wani mahaluki ya taba min shi ba!”
Ta na gama fadin haka ta tashi fuuuu ta fice ta bar Anty Sauda da salati da sallallami ta na tafa hannu. Fadi ta ke
“La’ilahaillahu muhammada rasulillahi! Hajja Aleesha wannan yarinya ba cikin hayyacin ta take ba! An riga an juyar da kan ta sai mun dage da addua!”
Ammy kuwa rasa ta cewa ta yi, dama dai in tsiwa ne kadan daga aikin Zainab, mamaki daya shi ne ikirarin da ta ke akan cikin ta,
“Allah dai ya sa ba cikin hayyacin na ta take ba….”
Ammy ta fada a sanyaye.
“There is no two ways about it! Ki ma dena raba dayan biyu ba cikin hayyacin ta take ba, sai an yi rokan Allah!”
Cewar Anty Sauda. Da haka su ka yiwa Likita sallama su ka tafi. Cikin mota su ka tadda Zainab zaune ta hada girar sama da na kasa. Babu wanda ya tanka ta sai bayan da su ka isa gida sannan Anty Sauda ta saka ta a gaba da tambaya. Zaune su ke a falo, sun zagaye Zainab kamar suna gudun za a iya sake sace ta
“Za ki gane wanda ya dauke ki? Wannan tsinannan almajirin ne ko?”
Zainab ta mu su banza. Anty Sauda ta kara da
“Yakura mun san abin da ciwo, matukar ba ki budi baki kin yi magana ba ta yaya za mu iya kwato mi ki hakkin ki daga zalincin da aka aikata mi ki? Ki fada mana ya aka yi ya sace ki, Kuma ina ya kai ki, ya sunan garin…?”
Zainab ta ki amsa ta. Cikin nuna gajiyawa Anty Sauda ta furta
“Ina ga sai dai sojojin nan su tambaye ta kila su ta fada mu su, in ba haka ba Hajja Aleesha sai mun tsaya tsayin daka akan Yakura! Wannan almajirin ya asirce ta ya kuma breaking din ta….”
“Ba zan yi magana da kowa ba!”
Zainab ya katse ta a fusace. Ba ta gushe ba ta kara da
“Kada ki kara kiran miji na da tsinannen almajirin! Usman miji na ne! Eh shi ya dauke ni saboda shi aka daura min! Da zai kai ni ya gusar min da hankali, Amma da ya tashi sallama ta da hankali na ya sallame ni, na roke shi ya sake gusar min da hankali na ko zuciya ta za ta dena min radadin barin sa, ya ki! Yanzu ya sa na dawo gida amma zuciya ta na can tare da shi, Kuma ku bar tunanin addua, cikin hankali na na ke, kuma Anty Sauda zan so ki sarara min dan kuwa maganganun ki kan miji na suna neman yin tsauri dayawa!”
Shiru ne ya biyo baya tamkar wanda ruwa ya cinye, inda kunyar yanda Zainab ta watsawa Anty Sauda kasa a Ido ya rufe Ammy, Anty Sauda kuwa ji ta yi tamkar kasa ta tsage ta shiga. Tashi Zainab ta yi ta shige ciki, bayan tafiyar ta Ammy ta nisa ta ce
“Tabbas Yakura ba ta cikin hayyacin ta, ya asirce ta yayi…”
“Hmmmm kin ga Hajja Aleesha matukar ba Yakura ce da kan ta ta zo ta same ni ta ce min ba cikin hayyacin ta take ba na yi hakuri, wallahi na cire hannuna a kan maganar ta, ke hatta General ma zan fada masa babu ruwan sa…..”
“A yi haka Hajja Sauda? Ai hannun ka ba ya rube ka yanke ba ko?”
Anty Sauda na girgiza kai ta furta
“Ah ah Hajja, a dai yi mata addua, matukar ba ta canza ba toh tabbas ki cire rai akan ta kema, ki sa a ran ki babu Yakura. shikenan ya tsafe ta har abada”
“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”
Cewar Ammy ta na mai sharar kwalla. Nan Anty Sauda ta barta, cike da bacin rai ta shige ciki tare da kiran mijin ta ta sheda masa halin da ake ciki.
*****
Bangaran Rugar Shehu kuwa, Muhamadu Bello ya tadda Usman tamkar mai makoki, cikin kankanin lokaci ya canza gaba daya. Zaune su ke karkashin bishiya in da Bello ya zo ya tadda shi bayan dawowar sa.
“Idan har ka na kaunar ta haka da ba ka bari ta tafi ba Shehu, domin kuwa Uwargida na kaunar ka ita ma, wallahi halin da ta ke ciki ya sanya na kasa barin ta har sai da na kai ta har Taraba, na bar ta a cikin wani hali”
Maimakon ya bashi amsa daidai da maganar sa, sai cewa yayi
“Ina nan a kan baka na na barin Rugar Shehu sati mai zuwa in Sha Allah, zan shiga uwa duniya kamar yanda na taba shiga a baya, Amma wannan karan hanyar neman cigaban Rugar nan ce zai fitar da ni”
Ya dan dakata kamar mai nazari. Muhamadu Bello ya nisa, kana ya ce
“Duk da ba haka aka so ba, Amma ka riga ka yanke hukunci ba tun yau ba. Ka ga Kado ba su da amana akan dukiya ko neman ta, akwai wani bafulatani dan uwan mu, Ibrahim Yerima Balla, dama mun saba cinikanyar shanu da shi, mutumin birne ne kwarai amma sai amana, ya kuma san darajar dan Adam. Nan Yola ya fiya zama duk da ya ce min ya na da gidaje a Kano da birnin tarayya, me zai hana idan ka tashi tafiya na hada ku?”
Bayan Usman yayi dan tuntuntuni ya furta
“Ka na gani zai iya saka ni hanya Bello? Ni fa yanzu tsoran bil’adama na ke”
” Mutum abin tsoro ne, Amma kada ka damu na shedi Ibrahim, ba ya cutarwa”
“Toh Alhamdulillah, zan shedawa su Kawu Iliya, sati mai zuwa sai mu tasarwa Yola, zan fara tafiya da shanu dari biyu mu gani, idan da bukata wasu nan gaba sai na yo aike”
Da wannan shawarar Usman ya bar Bello ya tinkari su Kawu Iliya. Dan kuwa shi ma ba zai iya jure zaman Rugar Shehu ba bayan tafiyar Zainab, komai na Rugar tuna masa da ita ya ke, sai ya zama tamkar zuciyar ta na ma zuciyar shi fatalwa. Ji ya ke kamar ya bi ta Kanon ko ya sami sauki, Amma taurin kai ya hana, shi ya sa ya yanke hukunci shiga duniya ko ya sami sauki.
******
Babu irin adduar da Ammy ba ta sa an yiwa Zainab ba, islamiyoyi da makarantur allo ta saka aka kai sadaka in da aka sa yara sauka da zikiri. Amma Zainab ko gizau, ta tsaya tsayin daka babu mai zubar mata da ciki.
Bayan sati guda da dawowar Zainab, da la’asar Zainab zaune bakin gadon ta dake tashin ta daga bacci kenan, kamar yanda ta saba ta yi mafarki da Usman, takaicin farkawar da ta yi ne ya sanya ta zaman bakin gado tare da doka uban tagumi.
A hankali aka kwankwasa mata kofa, sanin ba za ta amsa ba ya sa suka bude kofar su ka shigo, Ammy ce a gaba, biye da ita Anty Sauda ce da Halitta. Halitta ta zauna kusa da ita, in da Ammy da Anty Sauda ke tsaye suna duban ta. Cike da damuwa Ammy ta furta
“Yakura wannan tunanin da bakin cikin da ki ke ciki zai iya lahanta ki da dan cikin na ki, me zai hana ki bi Antyn ki ku koma Maiduguri, can zai fi mi ki kwanciyar hankali kafin ki samu ki koma makaranta…..”
“Babu in da zani, ba kuma zan sake komawa makarantar ba, Nan zan zauna abu na har sai na haihu, idan kuma zaman nawa na damun ki Ammy sai na sami ko da gidan haya ne…..”
“Ah ah Yakura”
Ammy ta yi saurin katse ta. Ta kara da
“Nan din ai gidan uban ku ne, ku ne magada dan ko da aka raba gadon Malam gidan a naku ya fado ina kuma batun neman haya? Kuma ina ki ka taba Jin zaman diya a gida ya dami uwar ta, dama farin cikin ki shi ne fatan mu….”
“Usman shi ne farin ciki na Ammy, rashin shi shi ne sanadin bakin ciki na, idan har kuna so ku sake ganin walwala ta a duniya ku barmin ciki na na haife shi, ban da makiyin da ya wuce wanda zai yi yunkurin raba ni da ciki na, wannan cikin shi ne rayuwa ta…..”
Dan takaici Anty Sauda kasa magana ta yi ta juya ta fice fuuu tamkar za ta tashi sama. Ammy na mai dafa kafadar Zainab ta furta
“Na mi ki alkawari Yakura babu wanda zai sake cewa ki zubda cikin nan, Allah ya raba lafiya”
Ta fice jiki a sanyaye. Ya rage da Halitta sai Zainab cikin dakin. Shiru su ka yi kowannan su na sakar zuci, daga bisani Halitta ta furta
“Yakura?”
Halitta ta kira sunan ta a hankali. Zainab ta daga ido ta kalle ta. Karo na farko da su ka zauna tare cikin aminci ba tare da Zainab na neman ta da bakar magana ba. Halitta ta murmusa ta ce
“Kada ki damu, ina goyan bayan ki dari bisa dari”
“Na gode Halitta, Su Ammy sun kasa ganewa, ina son miji na, ina son Usman fiye da tunanin ku, akan wani dalili zan zubda cikin Usman?”
Duban ta Halitta ta ke cike da mamakin yanda te ke ikirarin kaunar da ta ke yiwa Usman wanda ada bubu wanda ta tsana kamar shi, lalle shi ya sa ba a so a fiya zurfafa kiyayya ko soyayya ga mutum. Halitta ta ruko hannun ta, cikin rarrashi ta furta
“Amma me zai sa ki dawo gida? Idan har ki na kaunar Usman me ya sa ki ka yarda ki taho ke kadai? Menene dalilin shi na barin ki ki taho?”
“Abubuwa sun faru dayawa Halitta, kin fi kowa sannin yanda na tsani Usman ada, ina zaman zama na Daddy ya daura min auren dole da shi, bayan rasuwar Daddy ni kuma na yi kuskuran sawa a kamo shi domin ya sake ni, shi ne aka kamo kanin sa……”
Nan takwashe komai ta fada ma Halitta, ta kare da
“Bayan ya warke shi ne ya gaba daya ya guje ni, dan Allah ina laifi na Halitta? Wallahi ban san kashe shi za su yi ba, I just wanted to go home then not knowing that Usman is the only home I’ve, yanzu gashi ya ba ni takarda, Allah kadai ya san saki nawa ya min….”
Ta kare maganar cikin kuka.
“Ina takardar ta ke?”
Kai ta girgiza mata ta ce
“Ah ah wallahi ba zan ba ki ba, ba za a bude ba, ba na so ma na san yawan sakin da ya min, ban shirya ba Halitta, haka ko da wasa kada ki bari su Ammy su san babu igiyar auren Usman a kai na”
“Kai amma be kyauta ba, Usman be ruke amanar Daddy ba…..”
“Ya yi iyakar kokarin sa Halitta, Ni na hada baki da ma su neman ran sa, kada ki ga laifin sa Halitta”
“Haka ke ma ba ki da laifi Zainab, kin yi komai dan neman mafita ne, kin yi ne domin ke samu ki tsira, kuma duk wanda yayi judging din ki base on that ba adali ba ne, you did what you thought was right for you”
Shiru su ka yi na wasu mintina kafin Halitta ta nisa, kana ta ce
“Nan da sati biyu zan koma Saudia Yakura, Amma kafin na tafi zan so a ce kin yarda an je makarantar ku a san ya makomar karatun ki ya ke, mate din ki fa sun yi graduating”
Murmushi Zainab ta yi, yayinda ta ja filo yanda za ta dan kishingida, sannan ta furta
“Shin ki na tunanin zan iya komawa makaranta a wannan hali da na ke ciki? Ku yi hakuri ba zan iya ba Halitta, waccar Yakurar da ku ka sani is gone…har abada..”
Tausayin Zainab ya dada rufe Yakura, gashi hawaye ya na son zubo mata, Amma sai kokarin ruke shi ta ke dan kar Zainab ta gani ta kara karaya. Tashi ta yi da sauri za ta fita, har ta kai kofa ta tsaya, ta dan juyo kadan yanda Zainab ba za ta lura da hawayen da ke zuba daga idanun ta ba ta ce
“Falmat ta ce wayar ki ba za ta gyaru ba, wacce iri ki ke so a siyo mi ki?”
“Waya? I don’t need it for now, ku bar ta kawai…..”
“Yakura! Wani irin rayuwa ce wannan? Hatta waya ma ba za ki ruke ba?”
Zainab na murmushi ta ba ta amsa da
“Sanda ina slaying kun ce na fiya fitina, yanzu kuma I’m managing myself kuna ta kokawa! Dan Adam kenan, ba na bukata dole ne?”
“Ah ah ba dole fa”
Cewar Halitta yayinda ta fice abin ta tana zubda hawaye.