Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 17

Sponsored Links

*Khadija Sidi*
Auren Shehu

17

 

Da ya ke mijin Anty Sauda a barracks ya ke General, cikin gida kuwa sai yanda ta yi da shi, tuni ya dorar da bukatar ta, in da yayi waya Bokabo barracks ya ba da umarnin dauko masa Usman a daren ranar, ya bayar da adireshin gidan Malam, tare da fasalta kamannin Usman kamar yanda Zainab da matar shi su ka fasalta ma sa shi, ya ce a kawo shi Giwa barracks da ke Maiduguri. Dan haka wajan goman dare sojojin da aka tura su ka nufi gidan Malam.

Bakin gate su ka tadda shi tsaye da alama jira ya ke a zo a bude masa kofa, kamar yanda Zainab ta fasalta yanayin shigar shi, sanye ya ke da riga yar shara, wando wanda shi wanda shi ba gajere ba, shi kuma be kai masa har kasa ba ke kara nuna daudar da kafarsa ta yi, dan kuwa yayi futu futu da shi tsabagen tafiyar kasa da ya sha kafin ya isa gidan Malam. Haka kuma kan sa dauke da rawani da ya zaga har fuska.

Yanda su ka delle shi da hasken mota ya sanya shi saurin kai hannun ga fuskar shi ya na mai kare idanun sa. Su uku ne cikin motar dukan su sanye cikin shiga irin ta sojoji. Biyu da cikin su ne su ka diro daga cikin mota, su ka nufo shi gadan gadan hannayen su dauke da bindiga, dan kuwa yanayin shigar sa, tsayin sa da komai na sa ya tabbatar mu su da shi din ne wanda su ka zo tafiya da.

Sai da su ka karasawa dab da shi sannan ya ankara da yayayin shigar su, hakan nan gaban sa yayi mummunar faduwa musammam ganin bindiga tsirarara a hannun su, ya zabura zai gudu daya daga cikin sojojin ya sa kafa ya tade shi, sai gashi tim ya fadi kasa wanwar

“Gidan uban wa za ka je!”

Cewar Soja yayayinda ya dago shi, ya na mai tisa kyeyar sa ta hanyar hanakada shi da bakin bindiga, be gushe ba ya kara

“Dan uban ka ko tarin ka na ji sai na ci uban ka wallahi! Dan haka salin a lin ka wuce mu tafi!”

Be yi mu su musuba, haka su ka tasa shi gaba su ka sanya shi bayan mota, shigar shi ke da wuya su ka hade hannun sa biyu a baya su ka daure, sannan su ka fidda bakin kyella su ka rufe masa idanu kai ka ce sun dauko dan fashi da makami. Motar su ka tada, hakan yayi daidai da lokacin da Isa ya bude gidan Malam dan kuwa ya ji sanda ake bugawa bawali ya ke, kuma shi kadai ne kusa shi ya sa be bude da wuri ba.

Ganin tashin motar sai yayi tunanin ko na ciki ne ke bugawa su ka gaji su ka tafi, dan haka yayi kokarin tsayar da su, Amma ganin yanda su ka figi motar ya sanya shi fadin

“Toh ko lahira za ku ai sai haka! A sauka lafiya!”

Ya mayar da kofa ya rufe. Suna isa Bokabo barracks aka shedawa General isowar su. Yanda Anty Sauda ta matsa a kawo Usman ya sa General ba da umarnin a kawo shi Giwa barracks a daren. Cikin wani motar sojoji aka saka shi, wajan shabiyun dare su dauki hanyar Maiduguri. Tsabagen gudun da su ka yi, karfe uku a Giwa barracks ta mu su, har aka shiga barikin be san in da ya ke ba, illa bayan da aka sauko da shi, sun dan yi tafiyar kasa mai tsayi, sannan su ka tsaya, ya ji kamar ana bude kofa, ya na ji su ka caje shi tas, su ka cire duk wani abu da ke jikin sa, ciki har da takardar da yar tawadar sa da ya ke rubutu duk sanda bukatar haka ya taso, daga bisani aka hankada shi cikin wani waje da shi kan sa be san yanda wajen ya ke ba, ya ji an mayar da kofa an rufe. Sai a sannan wani sabon tsoro ya rufe shi, ya fashe da kuka cikin ran sa ya na mai ambaton ubangiji da ya kare shi daga sharri wannan mutanan da su ka dauko shi ba gaira babu dalili. Jiki da jini be jima ba baccin azaba ya dauke shi nan zaune.

Tun sassafe labarin dauko Usman ya sami Zainab, ba karamin nishadi da annashuwa ta tashi da shi ba, musammam idan ta tuna umarnin da ta bayar na a tabbatar Usman ya ji a jikin sa sannan a gaggauta tilas ta masa sakin ta, dan kowa ko zuwa in da ya ke ba za ta yi ba, ita dai kawai a karbo mata takardar saki. Babu wanda ya san wainar da ta ke tauyawa daga Anty Sauda sai Anty Hannah dan haka hankalin ta kwance ya ke.

Saukar ruwan sanyin da ya ji ya sanya shi tashi a gigice, be gama warewa ba ya ji saukar mari bisa kuncin sa, wanda hankan ya sa shi komawa ya zauna ya na mai ware idanu. Wanda ya watsa masa ruwan ya fara bi da kallo, Soja ne, daga gani sojan ma karamin wanda ake kira kurtu, sanye cikin kaki, ya tsare shi da jajayen idanun shi.

“Dan uban ka an ce ma ka nan gidan bacci ne?”

A tsorace ya shiga girgiza masa kai alamar “ah ah”

“Ba ka da baki ne? Open your mouth and talk to me friend!”

Maimakon ya bashi amsa, sai ya cigaba da girgiza masa kai, hakan ne ya kara tunzura kurtun, ledar abinci da ke aje bayan sa ya janyo, ya bude kosai ne da biuredi, da ke rabon sa da abinci tun jiya da rana tuni zuciyar shi ta kwadaitu da kosai da buredin. Ganin yanda ya ke kallan abincin ya sanya kurtun murmushin mugunta, ya ce

“Duk sanda ka budi baki ka yi magana a ba ka abinci! Giwa barracks ka ke dan uban ka, ma’ajiyar tsinannu irin ka! Wai dan ka mushe mu yar da kai ba wani abu ba ne!”

Ya na gama fadin haka ya ja bakin kyallen zai rufe masa fuska. Kai ya ke girgiza masa, kokarin rokan sa ya bar shi yayi sallar asuba ya ke amma babu dama dan kuwa yana ji ya na gani ya kara sanya bakin kyallen ya rufe masa fuska sannan ya ja kofar ya rufe ba tare da ya ba shi abinci ba.

Da yammacin ranar Zainab ta ci ado kai ka ce gidan biki za ta je jin Kori da Falmat na tsokanan Halitta akan za ta yi bako. Sanye ta ke cikin material baki mai duwatsu ruwan zuman, dinkin goguwar riga ne da ya amshi jikin ta sosai. Karamin mayafi ta saka dan ta burge Sudais ganin shi din ma da alama wayayye ne, haka kuma ta shafa tsadaddun turaren ta masu tafiya da hankalin jama’a.

Ta na zaune falo Madu ya shigo shedawa Halitta isowar Sudais, in da ya ce ta same shi falon da Malam ke saukar baki kafin Allah ya masa cikawa. Jin haka Zainab ta faki idon Halitta ta fice, sai ga ta falon baki ta tadda Sudais zaune ya na jiran Halitta.

Fuskar ta kunshe da fara’a ta masa sallama, ganin ita ce maimakon Halitta da ya ke tsammani be sa ya fasa mata fara’a ba, tare da amsa sallamar ta. Cike da kissa ta ce

“Ka ba ni izini na shigo? I’m welcome?”

Zuciyar shi daya ya murmusa, murmushin da ke kashe Zainab dan kuwa sai da bugun zuciyar ta ya karu. Jin ya furta

“Why not? You’re welcome babbar Yaya”

Zainab ta dan tsuke fuska,
‘wato har wani yaya ka ke ce min ko? Wai kai mijin kanwa ta! Ka yi ka gama ni ce matar ka! Da ni ka dace’

Abin da ta ke fada cikin ran ta kenan yayinda da ta karasa shiga falon, tana taku dai dai, ta sami kujera dab da shi ta zauna, wanda hakan ya sanya shi daga Ido ya kalle ta, ita kuwa ta sakar masa murmushin da ta san ba karamin jan hankali da rikita maza ta ke da shi ba. Sai a sannan ya lura da irin adon da ta yi, sai dai kuma sama Sudais ba abocin son ado irin na Zainab ba ne, sam ba ta burge shi ba. Ga mamakin ta sai gani ta yi ya dauke kai, yayinda ya kunna wayar hannun sa ya shiga dube dube. Cikin kulewa ta ce

“Ina wuni?”

“Lafiya lau Alhamdulillah”

Ya amsa ba tare da ta daga Ido ya kalle ta ba. Zainab na mai cije lebe, ta kara da

“Ya ku ka je gida rannan?”

“Lafiya lau”

Ya ba ta amsa a taikaice, har lokacin hankalin sa kan wayar sa ta ke. Ran Zainab ya fara baci, ta saba maza ke bin ta kamar jela, Amma ga wannan ita da kan ta ta zo wajan shi, ya share ta kamar ma be san da zaman ta a wajen ba. Jikin ta be yi sanyi ba sai da ta ga yanda fuskar Sudais ta sauya cikin kankanin lokaci yayinda ya ji sallamar Halitta, da kuma yanda ya bi ta da kallo tamkar zai cinye ta.

Ta ga dai hijabi ne jikin Halitta, har kasa ma kuwa, haka kuma fuskar ta sam ba kwalliya kai ka ce ita ce ma mai takaba ba su Ammy ba, Amma hakan be sa Sudais fasa kallan ta da tarerayan ta ba har ta zauna kujera can nesa da shi. Yanda ya ke kokarin yiwa Halitta hira bayan sun gaisa, ya tambaye ta ko ta na cin abinci da kyau kuwa, tare da rokonta da ta rage damuwa cike da kulawa ne ya sanya Zainab ta shi ta fita ba tare da ta yi masa sallama ba.

Dakin ta ta koma dan bacin rai ji take kamar za ta yi hauka. Gaba daya fushin ta ya fi karkata kan Usman, gani ta ke duk auran sa ne ya ja mata, dan ba dan Malam ya daura mata aure da Usman ba, da Sudais ne mijin ta, babu yanda za a yi ya kalli Halitta, har ma ya kulata bayan ga mace kamar ta gaban shi, idan har ta na son jan hankalin Sudais dole sai Usman ya sauwake mata auren masifar da aka daura mata. Ta na kuka ta kira Anty Sauda, fadi ta ke

“Anty Sauda na gaji da nauyin auren almajirin nan kai na! Dan Allah ku karba min takarda ta ko na huta!”

Jiki sanyaye Anty Sauda ke rarrashin ta, cewar ta

“Ki yi hakuri Yakura, tun da ya shigo hannu zai sake ki ne ai, ba dan taurin kai irin na shi ba ai da tuni an wuce wajan, kin san kuwa yanzu na ke shirin kiran ki, yaran General sun ce mutumin nan tun da aka kawo shi ya ki yayi magana, babu irin horan da ba a masa ba, Amma sam ya ki nunawa ya san abin da ake magana a kai, bare ma ya furta komai, ya zama beben karfi da ya ji, an ya kuwa ba a yi kuskure ba wajan dauko shi?”

“Zai ci uban shi kuwa! Wallahi sai ya sake ni! Babu kuskuren da aka yi tsabagen taurin kai ne irin na almajiri!”

Cewar Zainab a fusace. Daga dayan bangaran Anty Sauda girgiza kai ta yi ta ce

“Ah ah dai Yakura, gwara dai mu je mu gan shi da idanun mu, dan kuwa hotan da General ya nuna min na ga kamar ya dan canza akan ran da na gan shi a fili, ke kuma ba wayar arziki ba bare na ce zan turo mi ki ki gani, ko Halitta zan turowa…..”

“Halitta fa!”

Zainab ta katse ta da saura, ba ta gushe ba ta kara da

“Ai Anty Sauda Halitta ba za ta rufa min asiri ba, na dade da ganewa ba ta kauna ta, gwara dai mu je din kawai, da ban yi niyar kara ganin wannan kazamin mutumin ba wallahi, amma ya zan yi!”

“Da dai ya fi din, gwara dai mu je. Ni ina ganin Halitta mai hankali me ya faru haka?”

Zainab na mai girgiza kai ta ce

“Kishi, envy, bakin ciki! tun da take kishi ta ke dani, na fita komai shi ya sa”

“Kai amma ko kuna ciki daya? ba ta kyauta ba, toh sai ki shirya zan zo na dauke ki karfe goma. Zan kira Hajja Aleesha na sheda mata za ki raka ni”

Cewar Anty Sauda cikin ran ta tana mai Allah wadar da halin Halitta. Da haka su ka yi sallama. Zainab ba ta kara bari sun hadu da Halitta ba tsabagen kishi da bakin cikin yanda Sudais ya mata.

Washagari da safe wajen goma Anty Sauda da Direban ta su ka zo daukan Zainab, duk yanda Falmat ta so bin su, kiri kiri Anty Sauda ta hana. Haka su ka tafi, Zainab da Anty Sauda zaune a gidan baya, direba da sojan da ke kula da Anty Sauda zaune gidan gaba, ba su zame koina ba sai Giwa barracks.

Ganin wacce ke tafe ba su sami damuwa wajan shiga barikin ba, kai tsaye aka wuce da su in da Usman ke kulle. Ana bude kofar wani warin datti ne ya buge su har sai da Zainab ta ja baya ta na mai rufe hanci da gefen mayafin ta, haka ma Anty Sauda wacce ta furta

“Huum! Hammatar mijin Yakura ke wari haka?”

“Ayya mana Anty Sauda!”

Cewar Zainab yayinda ta danna kanta cikin dan karamin dakin, ita dai burin ta Usman ya sake ta su bar wajan. Gaban ta ne yayi mummunar faduwar ganin wanda ke kwance hajaran majaran sai nishi ya ke da alama ya sha duka, idan aka dauke shekaru, tsayin sa, fadin sa, yanayin tufar sa da fuskar yayi kama da Usman sak, dan duk wanda aka fasaltawa Usman ya ga wannan zai ce Usman din ne, Amma ban da Zainab wacce ta san Usman sosai kamar yunwar cikin ta. Ta na mai duban shi ta ce

“Na shiga uku! Wannan ba Usman ba ne Anty Sauda! Wannan ba Usman ba ne! Wallahi ba shi ba ne!”

“Toh matsala! Ai nima na yi tunanin haka wallahi, kila tsabagen kama ne, bari na kira General din na sheda masa”

Cewar Anty Sauda cikin damuwa. Nan da nan ta kira General ta sheda masa halin da ake ciki. Waje su ka fito Zainab sai safa da marwa ta ke dan ta kasa nutsuwa. Suna cikin wannan yanayin ne wasu sojoji su ka zo su ka shige in da bawan Allah nan ya ke kwance, bayan wani yan mintini daya daga cikim sojojin ya fito dauke da takarda ya mikawa Anty Sauda, ka na ya ce

“We are very sorry Madam, an sami matsalar ne daga wanda su ka dauko shi, kamar yanda mu ka yiwa General bayani wannan ko magana be yi ba, sai yanzu da ku ka tabbatar mana ba shi ne wanda ake bukata ba, sannan mu ka gane da gaske ba ya maganar ba wai pretence ba ne, sanda mu ka caje shi mun ga takarda da tawada, hakan ke nuna mana hanyar maganar shi kenan, Ashe tun da alamar mu bashi ta kardar ya ke mana mu kuma ba mu gane na sai yanzu, gashi yayi rubutu jiki amma kuma rubutun da larabci yayi ban sani ba ko za ku iya karantawa”

Ya karasa maganar ya na mai mikawa Anty Sauda takardar. Zainab ce ta yi saurin karba ganin abin da ke rubuce jiki ji ta yi kamar ta kurma ihu yayinda ta mikawa Anty Sauda takardar.

“Muhamad Bello daga rugar Shehu, Dan Allah kar ku kashe ni, na zo kiran dan uwana ne jikin Iyar mu yayi tsanani, ku taimaka ku sake ni ban san me ku ke magana akai ba…”

Anty Sauda ta karanta a fili. Ta kara da

“Yakura wanene Muhammad Bello kuma? Ina ne Rugar Shehu”

“Ni ina zan san wanene shi! Na dai san Rugar Shehu sunan rugar su Usman ne, ya ma za su aikata wannan kuskuren dan Allah!!!”

*Khadija Sidi*Auren Shehu

Back to top button