Auren Shehu Book 1 Page 15
15
Yanda Ammy ta fito afujajan da kuma sumbatun da ta ke ne ya sanya su Halitta rudewa, kamar yanda ta ke kuka, haka su ma din kukan su ke. Cikin kankanin lokaci su ka shirya, gaba daya sun manta da Zainab da ke can BQ, sai da su ka shiga mota, dukan su uku gidan baya su ka zauna, direba na shirin tayarwa sannan Halitta ta furta
“Yakura, Ammy ba a fadawa Yakura ba”
Ammy na share hawaye ta furta
“Ai kuwa dai, kai na yayi zafi wallahi! Halitta je ki sanar mata”
Halitta ba ta so Ammy ta aike ta wajan Zainab ba, haka babu yanda ta so ba ta fita ta same ta ta yi dai dai ta na bacci hankali kwance. Yanda Halitta ta tashe ta cikin gaggawa fada fada, da kuma sakon da ta fada mata na hatsarin Malam ya sanya ta tashi a gigice har ta na neman fadowa daga kan godo. Fadi ta ke
“Innalillahi na shiga uku! Ina Dadyn ya ke? Yaushe za mu tafi Maidugurin?”
“Idan har kin iya shiryawa da wuri za ki iya tafiya da mu, dan kuwa har mun shiga mota Allah ya sa aka tuna da ke…”
Halitta ta bata amsa tare da juyawa ta fice, ta na jiyo kukan Zainab wacce ke fadin
“Tsabagen wulakanci ni din ce za a mance fisabilillahi! Dady be da lafiya har ku shiga mota sannan za a tuna da ni? Wallahi kin yi da yar halak Halitta! Duk wannan munafuncin da ki ke kulla min za ki gani a kwaryar cin tuwan ki…..”
Sai da kusan minti goma sha biyar ya shude suna jiran Zainab, Ammy ta kule har ta ce da direba ya ja mota su tafi, sai ga ta nan har da yar jakar ta da ta tsaya shiryawa, idan aka dauke Zainab wacce ta shirya tsaf cikin bakar rigar abaya, daga Ammy har su Halitta hijabi ne jikin su. Kafar nan ya sha takalmi mai tsini kamar mai zuwa club. Taikaici ne ya sa Ammy kau da kai gefe yayinda ta karaso, boot ta bude ta aje jakar kayan ta, sannan ta dawo jikin mota daidai saitin Falmat, ta na mai nuna ta da dan yatsa ta ce
“Malama kin san dai ba za ki sani zama tare da Direba ba ko? Gwara ma ki fito ki bani waje!”
“Kun ji irin halin sakarcin na ta ko? Sai da na ce mu tafi mu barta ku ka ce ah ah! Dan uban ki idan ba za ki shiga mu tafi ba ki sha zaman ki! Kai Malam Habibu ja mota mu tafi!”
Cewar Ammy a fusace ta na mai watsa ma Zainab harara. Ganin direba ya tada mota ya sa ta bude gidan gaba ta zauna ta na zumbure zumburen baki da guna guni babu wanda ya tanka mata. Su Jauro na mu su Allah ya tsare hanya, tare da fatan Allah sa Malam be ji rauni sosai ba su ka dauki hanyar Maiduguri.
Gudu direba yayi sosai dan kuwa Ammy ji take kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ganta a Maiduguri. Tafiyar awa biyar sai gashi sun yi ta a awa hudu, dan kuwa baikwai daidai a Maiduguri ta mu su. Sun tarar gidan Malam da ke New GRA babu kowa sai mai gadi, gun shi su ka sami labarin mutuwar Direban da ke jan motar Malam, cewar Maigadin take Direban ya rasu be ko shura ba, haka kuma ya sheda mu su cewa Malam ma ya na can kwance rai a hannun Allah a nan UMTH (University of Maiduguri Teaching Hospital).
Asibitin Ammy ta ce a kai su ba tare da ta tsaya jin sauran bayanan tashin hankali da Maigadi ke fada mu su ba. Tun kafin su isa asibitin ta ke kiran number din Hajja Dudu amma ya ki shiga, da kyar bayan isar su asibitin sannan ta sami numbar Gana, shi ya sheda mu su suna Emergency and accident.
Tun daga nesa su ka hangi Hajja Dudu, Hajja Kilishi, Madu dan Malam na biyu sai kuma ‘yayan Hajja Kilishi mata guda biyu, Zinaru wacce ita ke bin Madu, sai kuma Kori wacce ita ce sa’ar Zainab. Kukan da su ka tarar Hajja Kilishi da sauran yaran na yi ba karamin daga mu su hankali ya yi ba, Gana da Madu ne kawai su ka iya daurewa duk da dai su ma din idanun su cike ya ke fal da kwalla, musammam Gana wanda gaba daya jinin Malam ya bata gaban farar rigar sa sanadiyar rungumosa da yayi sa’ad da aka dauko su daga wani dan karamin asibiti kusa da kauyen da su ka yi hatsarin.
“Menene wannan jikin ka Gana? Ina Malam? Kar ka ce min jinin Malam ne haka jikin ka!”
Cewar Ammy ta na mai ruko hannun Gana. Kai kawai ya girgiza mata dan kuwa tsoro da tashin hankali ya sa ya kasa magana, a kan idanun sa Direban Malam ya cika, haka kuma har lokacin salatin Malam ne ke masa yawo cikin kunne. Salati ya ke yi da karfi wanda duk wanda ya ji ya san Malam na cikin tsananin ciwo, Malam be dena salatin nan ba har sai da su ka iso Maiduguri, sai kuma tsit. Har Gana ya fasa kuka a tonanin shi Malam ma ya cika, shigar su asibitin aka sheda ma sa Malam na raye, sai dai yayi doguwar suma ne mai kama da mutuwa, wato ya shiga “Coma”
“Gana ku fada min mana, ku amsa min dan Allah wani hali Malam ke ciki!”
Ammy ta sake tambaya ta na mai fashewa da kukan da take ta kokarin dannewa.
“Malam ya na ciki, kusan awa hudu kenan da aka shige da shi, Amma har yanzu dai shiru, hana rantsuwa dazu wani likita ya ce da mu suna iyakan kokarin su, Bayan wannan ba mu kara ji daga gare su ba Hajiya”
Madu ne ya amsa mata ganin Gana be da niyar magana. Jin haka su Halitta su ma su ka kara saka na su kukan, waje ya kaure da koken iyalan Malam kai ka ce Malam ya cika, tun Madu na kokarin tsawatar mu su, har ya gaji ya sa mu su Ido, sai jama’ar wajan ne ke ba su baki.
Su Ammy ba su jima sosai da zuwa ba Likita ya fito, ganin sa gaba daya su ka yo kan sa kowa da tambayar da ya ke masa, hakan ya sa ya nemi ganin Hajja Kilishi da Gana a Office, Ammy ta ce ba ta san zance ba kafar ta kafar Likita, ita ma din matar Malam ce. Su uku su ka dunguna zuwa Office din Likita.
Bayan Likita ya yi kokarin kwantar mu su da hankali ne ya sheda mu su cewar sun yi iyakar kokarin su domin ganin Malam ya farfado daga doguwar suman da yayi Amma abin ya ci tira, dadin dadawa kuma ya sami “Spinal cord” injury, ya ji ciwo kashin bayan sa
“Innalillahi wainnailaihi rajiun!”
Cewar matan Malam suna mai fashewa da kuka. Cikin dakiya Gana ya furta
“Haba mana dan Allah! Ku shiru ko ma ji bayani daga bakin sa, yau ko mutuwa Malam yayi kukan nan na ku ba zai amfana masa sa komai ba sai ma azabtar da shi da zai yi!”
Jin haka duka su ka yi kokarin yin shiru, Gana na mai kallan Likita ya ce
“Yaya kenan? Menene shawara ko fitar da shi za mu yi zuwa karsar waje?”
Likita na duban Gana ya ce
“Zan ba ka shawara tsakani da Allah, kada ku wahalar da Malam, ku bar shi nan gida Nigeria, a kuma masa addua, sauki na Allah ne, Allah ya yassare masa”
Jin haka gwiwowin Gana sun yi sanyi kwarai, dan kuwa jiyayi tamkar likita na fadin Malam ba zai tashi ba. Da sanyin gwiwa su ka yi sallama da likita, in da ya ce a bar Malam ya kwana emergency ward suna monitoring din shi ko Allah ya sa a dace.
Madu da Gana aka bari za su kwana wajan Malam. Duk yanda Ammy ta so ganin Malam ba a bari ta gan shi ba saboda gudun abin da ganin na shi zai haifar mata ta, haka duka su ka koma gidan Malam. Kamar yanda aka saba duk sanda su ka zo hutu Maiduguri, bangaran da aka ware na musammam domin saukar baki su Ammy su ka sauka. Manyan dakuna uku ne kowannan su da bandaki ciki, sai kuma madaidaicin Parlour mai dauke da kanan kujeru ruwan kasa. Halitta da Falmat dama tare su ke zama duk sanda su ka zo, Ammy da na ta dakin da ta saba sauka, sai kuma karamin ciki Zainab ke kwana ita kadai.
Idan aka dauke Zainab babu wanda ya iya runtsawa daren ranar, Musammam su Hajja Kilish da su Zinaru, mutuwar Direban nan ya tsaya mu su rai dan sun saba sosai. Mutum ne mai kirki da haba haba da mutane. Daren ranar sarkin Musulmai ya sanar da ganin watan Ramadan, aka kwanta da niyar tashi sahur domin daukar azumi.
Washagari da sassafe su ka koma asibiti, ba a mayar da Malam patient ward ba, Amma an bar su sun ga Malam. Ganin yanda aka daure kirjin Malam, ga robar samar da numfashi baki, hannun sa makale da robar ruwa, ga kuma na fitsari nan wanda yar robar ta fito ta cikin jallabiyar da su Gana su ka sanya masa daren jiya. Gashi fuskar Malam kumbure sosai goshin sa an daure da bandaje saboda tsayar da jinin da ke zuba da gan kan shi da ya fashe, babu wanda be zubda hawaye ba, lalle mutum ba a bakin komai ya ke ba.
Matan sa duka biyun hannun shi su ka ruke, Ammy ke furta
“Malam dan Allah ka warke ko na nemi yafiyar ka, na yi nadama, dan Allah ka yafe min”
Zainab kuwa kallo daya ta yi masa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Wai Dadyn ta ne kwance haka kamar mutum mutumi! Yanda su ka mayar da dakin tamakar gidan makoki, ya sanya Gana tsawatar mu su, tare da fadin
“Duk wanda ya san zai zo mana asibiti ya mana kuka dan Allah yayi zaman sa gida, ba ma bukatan zuwan sa!”
Hakan ya sa duk wanda kuka ya zowa sai ya fita yayi kayan sa waje gudun fadan Gana. Yan uwa da abokan arziki, ciki har da daliban Malam, Wanda ke sauraran tafsirin sa duk sanda aka fara azumin Ramadan, sun yi cincirindon zuwa duba Malam, Amma babu damar ganin shi likitoci sun hana. Asibitin nan babu wanda be san da kwanciyar Malam Birma ba, haka lungu da sakon Maiduguri haka labari ya zaga ko ina.
Sai da Malam ya kwana uku Emergency Ward aka mayar da shi Aminity 4. Jikin sa dai ba canji, ya na kwance sai an tayar sai an kwantar, su Gana kullum suna cikin wanke kayan jinyar sa, da yi masa wanka idan ya kama. Satin Malam uku a asibiti aka fara shirye shiryen fita da shi India. Ammy da ‘ya’yan kuwa hado nasu ya na su su ka yi su ka tare a Maiduguri karo na farko da kan iyalan Malam ya hadu sosai, kowa ya dukufa wajan ibada da rokawa Malam sauki alfarmar wata Mai girma.
Ranar da aka akai azumi ishirin da biyar, Ammy ce a wajan Malam, ita ta karbi Gana da Madu ta ce su dan je gida su huta.
Zaune ta ke kan kujera, ta kurawa fuskar Malam Ido ta na mai kukan zuci. Sam ba ta lura da motsin da hannun Malam ke yi ba tsabagen nisan da zuciyar ta ta yi na tunani da begen Malam. Ganin murfin idon Malam ya motsa ya sanya ta kara matsawa kusa da shi da sauri yayinda bugun zuciyar ta ya karu. Kamar gizo haka ta kara ganin murfin idanun Malam sun motsa, haka ma yatsun hannun sa. Cikin ihu ta ke kwallawa su Zainab wanda ke zauna daga waje kira.
Da gudun su su ka shigo ciki, Ammy na goge kwalla ta ke fadin
“Ku duba ku ga yau Malam ya motsa, Alhamdulillah Malam ya motsa! Maza ki kira likita ku fada masa Malam ya motsa”
Ganin hannun Malam na motsawa Halitta ta fita da sauri sauri gudu gudu kiran likita, Zainab da Zinaru kuwa hannun Malam su ka ruko, daga mai fadin
“Alhamdulillah Daddy dama na san za ka tashi”
Sai mai fadin
“Malam ya tashi, Alhamdulillah Malam ya tashi”
Likitoci uku ne da Nurses biyu su ka biyo Hilitta jin motsawar Malam, a zahirin gaskiya sun ma fitar da rai da tashin sa. Cike da mamaki iko na Allah su ka umarci su Ammy su ba su waje. Nan su ka bar su ciki suna duba Malam, su Ammy kuwa sai kiran yan uwa da abokan arziki su ke suna sheda mu su Malam ya motsa. Sai da su ka dau kusan awa daya sannan su ka sami damar ganin Malam, su Gana da Hajja Kilish tuni su ka karaso jin labarin farin ciki.
Rashin baki be hana Malam aika ma iyalan sa da murmushi ba ganin yanda su ka zagaye shi. An cire masa rubar taimakon numfashi, sai na fitsari da na ruwa ne kadai ya rage jikin sa. Kowa burin sa ya ruke Malam, ko kuwa Malam ya kai kallan sa gare shi. Hajja Kilish kadai farfadowar Malam da kuma ganin sa ya dan kashe mata gwiwa musammam rashin maganar sa, duk da likitoci sun tabbatar mu su cewar a hankali Malam zai fara maganar.
Sai da la’asar su ka yiwa Gana da Madu Sallama domin su koma gida a yi girkin bude baki.
Ana gobe Sallah da sassafe Usman da Isa su ka dauki hanyar Maiduguri, Dan tun da Malam yayi hatsari ba zo sun duba shi ba. Shadaya da rabi su ka isa Maiduguri kai tsaye asibiti su ka wuce. Likitoci sun hana yan dubiya ganin Malam sai dai iyalan sa kadai, Amma Gana yayi magana su ka shiga. Duk da Malam ba ya iya magana, ganin su Usman sai gashi ya na fara’a sosai.
Shi kuwa Usman ganin yanda Malam yayi fari sosai ya kara tsayi ya sanya shi zubda hawaye, cike da mamakin hawayen Usman Gana ya ce
“Ai Malam Usman jikin Malam Alhamdulillah, yayi kyau fa sosai Malam ya sami sauki, ji fa yanda yayi fari sol da shi, kashin bayan sa ne ya sami matsala shi ya sanya ba ya iya zama ko tashi, ba ya iya motsa kafafun sa, Amma ka ga ai yana dan motsa hannun sa, da kuwa ko hannun ma ba ya motsawa wallahi!”
“Allahu akbar, Allah ya bawa Malam lafiya”
“Allahumma amen, in Sha Allah sauki ya fara samuwa, bayan sallah da sati daya ma za a fitar da shi India, mun sami wani asibiti na kwararrun likitoci a can”
Madu ya amsa mu su, ya na duban Usman ya kara da
“Na gane Malam Isa sosai, shi dai Malam Usman ne ban waya ba, ko shi ne sirikin namu ne? Mijin Yakura?”
Dab! Gaban Usman ya fadi jin an ambato auren da ya ke kwana da shi ya ke tashi da shi a kulli yaumin. Gana na mai murmusawa
” Ya ce eh fa shi ne, Malam Usman wannan shi ne Madu, shi ne ke bi na”
Nan Usman da Madu su ka kara gaisawa, in da Madu ya masa nasiha akan hakuri, a cewar sa zama da mace irin Yakura sai hakuri, dan kuwa mace ce mai taurin kunne. Sai da Gana ya dan zungure shi sannan yayi shiru, Usman kuwa cikin ran sa fadi ya ke be da buri da ya wuce a sauwake masa wannan karfen kafan da aka daura masa, wato auren Zainab.
Ana yin azahar su Usman su ka yiwa Gana da Madu sallama, ga mamakin su sai ga Malam ya na ta motsa hannu kamar ya na son yiwa Usman magana, hakan ya sa Gana fadin
“Tun da Malam ya kwanta ban taba ganin yayiwa wani mahaluki yanda ya ke ma ka ba Usman, ka ga fa kamar so ya ke ya ma ka magana”
Cike da tausayawa Usman ya matsa gare shi, yana mai duban Malam ya sanya hannun shi cikin na sa, ganin har lokacin Malam be dena motsa hannun ba Usman ya ce
“Malam Gana shin ko za a sami takarda da biro? Ina ga kamar akwai abin da Malam ya ke son ya fada min”
Gana be ki ta Usman ba ya nemi yar takarda da biro, ya bawa Usman. Hannu na rawa Usman ya sanya biro cikin yatsun Malam, sannan ya dura hannun Malam bisa takardar. Ga mamakin kowa sai ga Malam na kokarin rubutu, amma ina rubutun ba ya fita tamkar na yaro dan koyo. Sai da Usman ya taya shi ruke biro, da ikon Allah sai ga Malam yayi dan rubutu da ajami sanin Usman be iya boko ba. Kalma biyu ya rubuta
“Zainab…. Amana….. ”
Ya na rubuta haka ya saki birun, Usman ya daga rubutun da ya fi kama da jagwalgwalon yara, da kyar ya iya karantwa, hanun sa cikin na Malam ya furta
“Na ma ka alkawarin Malam, Ni da Zainab mutu ka raba”
Cikin nuna jin dadi Malam ya murmusa. Jiki sanyaye Usman ya tura takardar da Malam yayi rubutu cikin aljihun sa, su ka yi sallama su ka tafi. Tafiyar su ba da dadewa ba Ammy da Falmat su ka ta zo. Ganin yanda Malam yayi fari sai murna ya kamata, fadi ta ke
“Kai Alhamdulillah ji yanda jikin Malam yayi fari, yayi kyau wallahi”
Madu ya ce
“Wallahi fa Hajiya, Amma tunda ya kwanta ba mu taba ganin fara’arsa ba kamar na yau da wannan bawan Allah Usman ya zo”
“Allah sarki ashe ya zo”
Cewar Ammy cikin faduwar gaba, dan kuwa ji ta yi ba za ta iya jiran Malam ya warke ba, gwara ta nemi yafiyar sa ko ta sami sauki cikin ran ta. Kamar yanda ta kudiri niya, sai da ta nemi gafarar Malam kafin ta tafi, ta na magana ta na zubda hawaye hakan ya sa Malam girgiza mata kai, sai da ta ga ya na murmushi sannan ta gamsu. Duk sanda ta dan gifta ta wajan gadon sa sai ta ga ya ruko hannun ta, hakan ba karamin dadi ya ke mata ba, ta san ta isa matar so, tunda ciwo be hana Malam nuna mata so da kauna ba. Cikin so da kewar Malam ta yi masa sallama, har ta juya za ta tafi ya kara ruko hannun ta. Ammy na mai darawa ta furta
“Ka yi hakuri Malam, da sassafe zan dawo na kawo maka tuwan sallah in Sha Allah”
Malam na darawa yayinda kwalla ya dan gangaro daga idanun sa ya dan motsa kan sa. Ita ma Ammy kwallan ce ta fara cikowa idanun ta, ta yi saurin zame hannun ta ta fita, idanun Malam na kan ta har ta fice.
Daren ranar da ke daren duba watan sallah ne gari sai hidima ake. Gana da Madu ma zaman hira su ka yi bayan sun sha ruwa, hiran Usman da auren shi da Zainab su ke. In da Madu ke nuna jin dadin shi akan hukuncin da Malam ya yanke na auren Zainab, cewar shi
“Ka san Allah Gana da ka san yanda yarinyar nan Yakura ta lalace a Instagram da sai ka koka, ai na nuna maka wani hotan ta ka musa min ka ce ba ita ba ce, har da kwaba ta kar da na bari Malam ya ji, ai ga irin ta nan, yanzu da komai ya fito zahiri wa gari ya waya? Bari ma ka ga na nuna maka wasu da ga ciki”
Ya shiga Instagram ya na neman shafin Zainab, Amma ga mamakin sa babu shi babu alamar shi. Cikin cije ya yatsa ya ce
“Kash yar banza ashe ta yi deleting, Shi ya sa Hajiyar mu ta birgeni da ta hana su Zinaru kowani Social Media! Wallahi ba karamin jan hankali yara mata ya ke ba, musammam masu rawan kai irin Yakura!”
Gana na mai mikewa bisa carpet din da su ka shimfida tsakiyar daki ya ce
“Toh sai dai Allah ya dada kare mana su, ba dai an aurar da ita kowa ya huta ba, Madu bari na dan mike kadan, dan Allah ka sheda min idan an ga wata, Allah ya sa ba talatin za a yi ba, azumin asibiti babu dadi”
Madu ya amsa da “toh” yayinda ya cigaba da danne dannen wayar sa. Cikin yardar Allah aka sanar da ganin wata, gobe sallah. Madu ne ya kira su Hajja Kilish ya fada mu su, tare da jaddada mu su lalle a kawo mu su karin kumallo da wuri.
Ranar Sallah rana ce da iyalan Malam ba su taba manatawa da ita ba. Motsin Malam ne ya tada Gana da asubar fari, ganin halin da Malam ke ciki, jiki sankare idunun sa sun kafe ya sanya shi ihu ya na salati ya ke fadin
“Madu Malam! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Madu Malam, Madu kira likita!”
Hakan ya sa Madu fita a guje. Hannun Malam Gana ya ruko, ya na hawaye ya ke fadin
“Innalillahi wainnailaihi rajiun! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi!”
Malam na mai damke hannun Gana ya tsinci kan sa ya na mai amsawa da karfi ya furta
“Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu……”
Sai tsit, Gana ya na ji ya na gani an zare ran Malam, kullu nafsin zaikatul maut
*Khadija Sidi*
*Khadija Sidi*Auren Shehu
(15 continuation)
Kafin likita ya karaso har Gana ya sa tafin hannun sa bisa fuskar Malam, ya na mai karanto adduar neman rahama ya rufe idanun Malam, tare da jan zani ya rufe fuskar sa, sannan ya zauna a kasa dirshen ya na kuka kamar kankanin yaro.
Ko da Madu da likita su ka shigo, Madu ya ga Malam rufe sai ya rufe Gana da fada, akan wani dalili Gana zai rufe Malam! Yaushe ya zama likita! Shikenan ya kashe mu su Malam!
Gana ya cigaba da kukan sa ba tare da ya kula Madu ba, wanda sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba. Likita be fasa yaye zanin da Gana ya rufawa Malam ba, ya sanya safar hannu na roba, ya dan kara duba gawar ya tabbatar ya cika da gaske, sannan ya zare robar ruwan da ke hannun Malam, ya fara kokarin zare na fitsari wanda ba a yi cikakeken awa daya da saka shi ba, Amma azarbar fitar rai ya sa shi cika har ya na komawa sama.
Ganin likita ya kara mayar da zani ya rufe Malam nan Madu rungume gawar Malam, ya na fadin
“Hasbinallahu wani’imal wakilu! Allah ya yafe maka kurakuran ka Malam! Allah ya ji kan ka! Allah ya sa annabi ya san da zuwan ka!”
Cikan kankanin lokaci aka hade komai na Malam. Gana ne ya kira Hajja Kilish ya ce kada su kawo mu su abinci, ga su nan ma an sallami su, Malam ya sami sauki, gida za su taho. Ita dai ta amsa da toh, azahiri kuma jikin ta ne ya dau rawa yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan kuwa jikin ta ya bata akwai abin da ya faru, hakan nan ba za a sallame su ba, in ba dai saukin mutuwa ya samu ba. Aikuwa zatan ta ya tabbata sai ga su Gana da gawar Malam, sun shimfide mata tsakar falo.
Hajja Kilish neman kuka ta yi ta rasa, ta na zaune daidai kan Malam ta ke tsawatar su Ammy da yara, wanda su ne su ka fi kowa ihu da kuka, fadi ta ke
“Kul kada ku kara mana ihu a nan! Sakayyar da za ku masa kenan? Ku dena mana kuka na ce!! Yanzu Aleesha har da ke? Malam fa ya na jin ku!”
Zinaru kuwa aljanu ta ringa tayarwa. Hajja Kilish tare da Gana da Madu ne su ka wanki gawar Malam, su ka masa sutura. Ko da aka dauki Malam za a fita da shi Hajja Kilish ta tashi da sauri za ta ruko makarar amma ina tuni ta yanki jiki ta fadi sumammiya, ba ita ta farfado ba sai bayan da aka sallaci Malam aka kuma kai shi gidan gaskiya. MashaAllahu Malam yayi mutane matuka. Su Usman da daliban Malam ba su sami janaiza ba, dan kuwa sai da aka yi awanni da birne Malam su ka iso. Sun zubda hawayen rashin Malam kwarai sanda aka kai su kabarin Malam su ka masa addua.
Kamar yanda Malam ya ke yawan fada idan ya mutu kar a masa zaman makoki, su Gana sun yi kokarin hanawa amma ina hakan ya ki yiyuwa, kullum gidan cike ya ke fal da jama’a, yan unguwa, yan uwa da abokan arziki abin takaici shi ne yanda gidan mutuwar ya so ya zama gidan biki, iyalan Malam da su aka yiwa rashi ne kadai ke cikin bakin ciki da kuka, in da ake bikin sallah su kuma su ke fama da bakin ciki da alhinin rashin Malam. Ranar da Malam ya cika kwana uku su Usman su ka nemi yiwa su Ammy gaisuwa, duka iyalan Malam sun fito an gaisa, ban da Zainab wacce a cewar ta zafin mutuwar Malam daya ya ke da zafin ganin fuskar Usman. Ganin ba ta fito ba Usman be tambayi ina ta ke ba, yayiwa su Ammy gaisuwa su ka juyo Kano ya na mai tunanin yanda rayuwa za ta kasance akan alkawarin da ya daukarwa Malam.
Ranar da Malam ya yi bakwai Ammy ta so komawa Kano, yan uwan Malam ne su ka ruke ta da ta zauna nan gidan Malam ta gama takaba tare da yar uwar ta Hajja Kilishi, tunda ko ta je Kano ma gun wa za ta koma? Duk yan uwa suna nan Maiduguri. Da wannan ta hakura ta zauna.
Sai da Malam ya yi sati biyu da rasuwa, jama’a ka dan dauke kafa. Gidan ya fara shiru, gashi babu wanda ya ke cikin walwala musammam mutum hudu, kusan za a ce mutuwar Malam ta fi duka, wato Hajja Kilish, Madu da Gana, sai kuma Halitta. Gaba daya ta rame ta lalace, sai ta kara fari da manyan idanu.
Zainab kuwa bayan mutuwar Malam, babban burin ta shi ne a gama alhinin mutuwa a zo a raba auren ta da Usman, dan kuwa ko sama da kasa za ta hade ba za ta yarda da auren ba, musammam yanzu da aka wayi gari babu Malam a doran kasa.
Da la’asar sakaliya Madu da Gana su ka karbi bakwancin Shiek tare dan shi Sudais da kanan sa mata biyu, Zara da Ummi, kasancewar sanda aka yi rasuwar ba sa nan suna Saudiya. Bayan sun yiwa su Ghana gaisuwa ne Madu ya shigar da matan cikin gidan wajan su Hajja Kilishi, tare da sheda mu su cewar Shiek da Sudais na Falon waje, idan sun shirya za su shigo su yi mu su ta’aziya.
Ya ko ci sa’a Hajji Kilishin zaune ta ke tare da Ammy. Kanan Sudais su ka mu gaisuwa, tare da neman su Zinaru wanda dama su su ka sani, duk da dai suna kwadayin ganin amaryar yayan su da aka ce diyar amaryar Malam ce da ke zaune birnin Dabo. Zinaru da Kori ne su ka fito jin zuwan su Zara. Suna cikin gaisawa ne Madu ya dawo biye da shi Sudais da Shiek ne.
Bayan sun yiwa su Hajja Kilish gaisuwa, Shiek ke tambayar Ammy ina su Halitta su ke, da fatan ba su koma Kano ba ko. Ammy ta ce
“Eh suna nan tare da ita, Kano ai ta yi mana nisa in ba dai Zainab wacce ke da miji a can ba, bari a kira su, Kori kira yan uwan ki”
Kori ta tashi ta shiga kiran su. Tun tashin ta gaban Sudais ke faduwa, ya zubawa kofar da Kori ta fita idanu, da ke shi ne ke zaune kurar da ke kallan kofar, Shirin ganin matar da Shiek ya zaba masa ya ke cikin zulumi.
Jim kadan Kori ta dawo biye da ita Falmat ce sanye da hijabi har kasa, kallo daya Sudais ya mata ya tabbatar ba ita ba ce amaryar ta sa tsabagen kuruciya da fuskar Falmat ta nuna karara duk da kiban da ta ke da shi. Cike da ladabi ta durkusa har kasa ta gaishe da Shiek da Sudais. Su ka amsa tare da mata gaisuwa. Ammy ta gabatar da Falmat a matsayin autar ta.
Zainab wacce har cikin ran ta ba ta yi niyar ganin baki yau ba, da kyar ta tashi daga kan gado, bakar abaya ta ja ta dora bisa yar karamar rigar da ke jikin ta, ta ja mayafin abayar ta rufe kan ta. Za ta wuce ta hango Halitta cikin dakin su, bisa sallaya. Tun da ta ji sakon isowar Sudais ta ji wani bakin ciki ya kara ziyartar zuciyar ta, ta ma kasa tashi bare ta fito su gai sa.
“Malama wanda aka bawa ke ya zo,, you better bring your ass to the parlour, aha bari na je na ga wani local champion Daddy ya bawa”
Cewar Zainab cikin tsoka na, ta wuce ta na yiwa Halitta yar dariyar mugunta. Tun kafin ta karasa falon ta fara jin wani irin ni’mantaccan kamshi, zuciyar ta daya ta sanya kafar ta hakan yayi daidai da hada idanu da shi, gaban ta yayi mummunar faduwa har ta tsinci kanta ta na mai fadin
“Hasbinallahu wani’imal wakilu!”
Ta sha ganin maza wanda su ka amsa sunan su maza ma su kyau, Amma ba ta taba ganin wanda ya tafi da imanin ta kamar Sudais. Sudais wankar tarwada ne mai duguwar fuska da ke dauke saje da gemu baki wuluk har sheki ya ke, ba wani dogo ko siririn hanci gare shi ba, girma da tsayin hancin sa yayi dadai da fasalin fuskars sa, haka kuma idanun sa da ke manya dan ko ita Zainab ba za ta nuna masa kyawun idanu ba. Kasancewar zaune ya ke kan kujera be boye tsayi da fadin da ya ke da shi ba, sai ma kwarjini da ya mata. Idan ko gayu da wayewa ne kallo daya za a yiwa Sudais a san gidan shi aka zo, murmushin da ya sakar mata, gefan kumatun sa biyu su ka lutsa wato alamun dimpol ne ya dada rikita Zainab wacce ta tsinci kanta ta na mai shigowa Falon da sauri gudun kar sauran yan falon su lura da halin da ta tsinci kan ta ciki. Cikin ran ta fadi ta ke
“Innalillahi kar dai wannan shi ne mijin da Dady ya so aura min? Ya ilahi Allah wallahi da ni ya fi dacewa! Wayyo ya hadu! He should be mine! Da ni ya dace!”
Da kyar ta iya daurewa da gaishe da Shiek ya amsa tare da mata gaisuwa, sannan ta kashe da Sudais, wanda ya amsa ya na mai duban ta da kyau. Tun shigowar ta ya so kare mata kallo, Amma yanda ta ke kallan sa ya sa shi kasa tsayawa ya kalle ta da kyau har sai bayan da ta shigo ta zauna kusa da Falmat. Ko shakka babu ya amince da abu daya, Zainab ta amsa sunan kyakkyawar mace ta ajin karshe, kuma ga dukkannin alamu wayayyiya ce kuma yar gayu, sai kuma akwai abinda ya ke so da be gani a tattare da ita ba, shi kan sa ya kasa gane menene abun, haka kuma ya tsinci kan sa ya na mai fatan Allah ya sa ba ita ba ce matar da Shiek ya zaba masa ba.
Gaisuwa ya mata, ta na cikin amsawa yaji sassanyar muryar Halitta ya ziyarci kunan sa ta sigar sallama wanda shigowar ta yayi daidai ta furucin Ammy na
“Wannan ita ce Zainab, wanda mu ke kira Yakura ita ce babbar su”
“Allah sarki ita ce Malam ya sheda min maganar auren ta ranar da na masa ganin karshe, Allahu akbar duniya kenan”
In da Zainab ta ji kamar ta kurma ihu jin furucin Shiek akan auren ta, Sudais kuwa wani dadi ne ya ziyarci zuciyar sa yayinda ya zubawa Halitta idanu, sanye ta ke cikin hijabi fari kal har kasa, kan ta sunkuye har ta shigo falon ba ta kalli Sudais ba bare ta lura da kallon da ya ke mata
“Alhamdulillah for you, Alhamdulillah, she so MashaAllah! Na gode Abba da wannan zabi na ka”
Cewar Sudais cikin zuciyar sa, wanda ya fadada fara’ar sa dan kuwa ya kasa boye farin cikin sa na ganin Halitta, ta yi masa har cikin zuciyar sa.