Auren Shehu Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Auren Shehu Book 1 Page 12

Sponsored Links

12

 

 

Umarnin da Malam ya bawa Zainab na ta koma BQ ba karamin tashin hankali ya haddasa tsakanin Malam da Ammy ba, abin da bai taba shiga tsakanin Ammy da mijin ta ba ranar kuwa sun yi abin sam ba dadin gani bare ji. Shi kan shi Malam mamakin dama akwai ranar da Ammy za ta dubi tsabar idanunsa ta gasa masa maganganu haka ya ke. Ya na daga kwance ya ke kallonta, tun shigowar ta falon ta tsaya kan sa hannu rike da kugu in da ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, sai da ta dan tsagaita Malam ya furta

“Alesha kin gama?”

“Ban gama ba Malam, idan ka ga na gama to ka raba wannan bakin aure mai cike da cuta da ka kulla tsakanin diyarka ta cikinka da Mai gadi wanda be da asali Malam! Ai ko addini cewa yayi mu zaba ma ‘ya’yan mu mazaje na gari, haka kuma mu yi bincike akan mutum kafin mu ba su auren ‘ya’yan mu, ban ga dalilin da zai sa ka lalatawa yarinya rayuwa ka aura mata maigadi wanda ba mu san komai game da shi ba! Ni jinin shuwa sulallan gwal ka biya sadaki na, Amma ka dauki diya ta, jini na ka bayar da ita sadaka!”

Ammy ta bashi amsa cikin tsiwa. Shiru Malam ya mata tamkar ba da shi ta ke magana ba. A hasale Ammy ta furta

“Malam ka na ji na fa!”

Dagowa yayi yana duban ta, ainihin so da kauna na hakika ya ke yiwa baiwar Allah nan, dan kuwa yanda ya ke san ta be so uwargidan sa Hajja Kulu ba, badan komai ba sai dan Ammy ita ce zabin ran sa, uwargidan sa kuwa zabin iyaye ce.

“Alesha duk yanda ki ke tunanin kaunar ki ga Zainab ya kai, ba ki fi ni san ta ba, Ni ne mahaifin Zainab dan haka ba zan cutar da Zainab ba, aure kuma na daura, babu abin da zai kashe auren nan sai Allah…..”

“Karatun ta Malam? ka na nufin ka salwartar da karatun ta kenan? Yakura ta yi nisa a jami’a, wata daya ya rage su koma makaranta, aji uku Yakura ta ke, semester daya ya rage ta shiga aji hudu, yar jami’a ka daurawa ma Maigadi dan ruga Malam!”

Ammy ta katse shi ta na maganar ne kamar mai shirin fashewa da kuka. Cikin halin ko in kula Malam ya ba ta amsa da

“Wannan tsakanin ta da mijin ta ne, karatun na ta, idan ya ga zai iya barin ta ta karasa fabini’ima, idan ba zai bari ta karasa ba ma wannan zabin sa ne…”

“Toh kuwa sai ka zaba! Aure na da kai ko kuwa auren Zainab da Maigadi! Wannan zalinci ba zan iya jurar ganin shi ba!”

Gaban Malam ne yayi mummunar faduwa, da sauri ya tashi tsaye ya na mai duban Ammy ya ke fadin

“Alesha? Ni ki ke fadawa haka? Auren mu ko auren Zainab?”

“Kwarai Malam, ba zan iya zama gidan nan diya ta ta ciki na ta na auren Maigadi ta na kwana a BQ ba, ba zan iya zuba ido ina kallo ana tauye hakkin diya ta ba, ka zaba Malam”

Ta bashi amsa cikin dakiya, dan kuwa ta san yanda Malam ke kaunar ta ba zai taba zaban wani bayan ta ba duk da tsanar subda ta ke zargin ya yi. Ga mamakin ta sai ji ta yi Malam ya ce

“Na zabi auran Zainab da Usman, sai yaya? Me zai biyo baya?”

Zuciya tsinke dan kuwa sam ba ta yi zato ba Ammy ta ce

“Ka zabi ka sake ni kenan? Saki nawa ka min?”

Kai Malam ya girgiza yayinda ya koma ya zauna, fuskar sa dauke da murmushi ya kai hannun sa ga qur’anin da ke aje can gefe bisa dan teburi. Ya na kokarin budewa Ammy ta sake fadin

“Saki nawa ka min”

Ya na murmushi kaici ya ke girgiza kai, kana ya ce

“Alesha ashe dai har yanzu ba ki dena tunani irin na yara ba, saki? Ni Birma na saki mata ta? Ban taba sakin iyali na ba, ba zan fara akan ki ba Alesha, kin ce na zaba ko auren Zainab da Usman, ko aure na da ke, na zabi auren diya ta, ban yarda na mayar da diyata bazawara ba, haka kuma ban sake ki ba, ba zan kuma sake ki ba…!”

“Ni kuma ba zan zauna da azzalumin miji irin ka ba! Kai ne kullum cikin wa’azi Allah ya ce annabi ya ce! Amma ka kasa kare hakkin iyalin ka sai ma cutar da mu da ka ke kokarin yi! Allah ya saka mana! Ko ka sake ni ko ba ka sake ni ba zama na da kai ya kare!”

Baki bude Malam ke duban ta ya kasa magana tsabagen mamakin maganganun da Ammy ke fada masa. A fusace ta juya fuuuu ta fice ta na mai buga masa kofa ta wuce bangaran su.

Ganin yanda ta shigo a fusace ya sa Falmat bin bayan ta tana tambayar Ammy lafiya? Me ya faru? Ba ta bata amsa ba, sai ma hade kayan ta da ta shiga yi. Cikin kankanin lokaci ta hade kayan ta tsaf cikin yar akwati. Ganin haka Falmat ta kira Halitta da Zainab wanda duk abin nan da ake ko waccar su na dakin ta tana fama da kan ta.

A falo su ka tadda Ammy ta na jan akwatin ta niki niki za ta fita. Iya na tambayar lafiya Hajiya za ki yi bulaguro ne? da sauri Halitta ta karasa gaban ta, ta na mai taro akwatin ta ke fadin

“Innalillahi Ammy me zan gani? Ina za ki je haka da yamma likis Ammy?”

“Gidan uban ku zan bari, aure na da shi ya kare, ya zabi auren Zainab akan aure na da shi!”

“Ammy ki rufa min asiri idan ki ka tafi ina zan sa kai na?”

Cewar Zainab ta na mai riko hannun Ammy.

“Uban ki ya dafa ki ya cinye!”

Ammy ta bata amsa a hasale. Cike da tashin hankali Falmat ta ke kuka, Zainab kuwa dama ta nemi kuka ta rasa sai dai na zuci, wani tsanar Usman ta kara ji, ta kuma kullaci Malam da har ya zabi rabuwa da mahaifiyar ta akan auren ta da Usman, wato ya tabbata Malam ya tsane ta ya kuma tsani mahaifiyar ta. Halitta na mai girgiza kai cikin rashin gasgata maganar Ammy ta ce

“Ammy ba haka ba ne, Daddy ba zai taba zabar rashin zama da ke ba Ammy, wannan masifa har ina, Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ammy da kuruciya ba ki taba yin yaji ba, dan Allah kar ki yi da tsufan ku, Dan Allah Ammy…..”

“Ke rufa min baki! Kuruciya ko tsufa namiji namiji ne! Uban ku ma namiji ne! Ba uba na ba ne, ba gidan uba na ba ne, wallahi ba zan zauna bakin ciki ya kashe ni ba, matsa min daga hanya!”

Ta na mai hambare Halitta ta tare da buge hannun Zainab ta ja akwatin ta ta yi waje. Iya kuwa wacce duk abin da ya faru ba ta gidan cike da al’ajabi ta ke bawa Ammy hakuri, Ganin dai Ammy ta ki ji Iya ta ce da Falmat ta yi maza ta shedawa Malam halin da ake ciki. Falmat ta fita da sauri ta nufi bangaran Malam, ta tarar da shi zaune in da Ammy ta barshi ya na karatun al’qur’ani, ganin Falmat da kuma abin da take fada masa hankali tashe be sa ya motsa ba, bare ya nuna mata wani damuwa. Kallan ta yayi cikin nazari kafin daga bisani ya bata amsa da

“Ammyn ku ta zabi ta tafi, ku bar ta ta tafi za ta dawo ne da kafafun ta, ku kasance masu hakuri Falmat”

“Daddy ba za ka tsayar da ita ba? Ba za ka hana ta tafiya ba Daddy?”

Kai ya gyada mata, sannan ya kara da

“Ki yi hakuri Falmat, babu yanda zan iya da hukuncin ubangiji dan kuwa auren Yakura ba mai rabuwa ba ne har illa mashaAllah”

Shiru ne ya biyu baya, jiki sanyaye Falmat ta juya ta fita. Malam ya bi bayan ta da kallo na wasu dan mintina kafin ya mayar da hankalin sa ga karatun da yake.

Duk kokarin su na dakatar da Ammy a iska ya tashi, karshe ma cewa ta yi duk wanda ya biyo ta wajan gate sai ta tsine masa, su na ji suna gani ta ja akwatin ta ta fice, ko da ta zo giftawa ta bangaran Malam can kasan zuciyar ta ta so Malam ya fito yayi kokarin hana ta tafiya kamar yanda ‘ya’yan ta su ka yi. Haka ta na share kwalla ta damkawa Jauro akwatin wanda ganin fitowar ta ya taso da sauri. Shi ya sanya mata cikin mota, ya na mata fatan Allah ya kiyaye hanya.

Ta na mai watsawa Usman harara ta shige mota. Shi kuwa gate ya bude, haka kuma be fasa mata a sauka lafiya ba yayinda mota ta fice daga cikin gidan.

*****

Kamar gidan makoki haka gidan Malam ya kasance. Duk yanda Iya ta yi kokarin sanin halin da ake ciki daga wajan su Falmat abin ya gagara. Sai da ta sami Jauro ya kwashe komai da karya da gaskiya ya fada mata. Ita kan ta sai da ta kullaci Malam da Usman.

Tsoran fushin Malam ya sa Zainab ta hade kayan ta tsaf kamar yanda ya umarce ta. Iya ta sa ta kai mata su BQ ta aje, Amma ta yi kwanciyar ta daki duk da dai ta na jiran tsammanin shigowar Malam matukar ya san ba ta bi umarnin shi na komawa BQ din ba. Malam shiru be shigo ba, haka kuma ba ta ji muryar shi sanda aka yi sallar Magariba da isha’i a masallaci ba kamar yanda su ka saba ji idan ya na jan sallah ba. Fushin da ta ke da shi be sa ta kasa shiga damuwa ba, Amma tashi ta je bangaran sa ta duba ko lafiya ne ba za ta iya ba gudun abin da hakan zai jawo mata.

Da wannan tunanin ta fito falo ta tarar da Halitta sanye da hijabi da alama shirin fita ta ke.

“Ina za ki je?”

Zainab ta tambaya a dake, maganar da ta fara shiga tsakanin ta da Halitta kenan tun faruwar masifar da Zainab ta jawo mu su.

“Daddy zan kai wa abinci”

Ta bata amsa a takaice kafin ta shige kitchen, jin batun abinci ya tunawa Zainab raban ta da abinci tun jiya da rana, dan haka ita ma kitchen din ta nufa.

Iya ta hade abincin Malam bisa wani dan kwando, Halitta ta dauka, ta na jiyo Zainab na tambayar Iya ko da kaza ta na so ta yi mata farfes Halitta ta fice, cikin ran ta tana fadin

‘dole ki ci ferfesu hankalin ki kwance ya ke Yakura bayan kin dagula na kowa kin hana mu farin ciki’

A bakin kofar da zai sada ta da bangaran Malam ta hangi Usman tsaye, tuni gaban ta ya shiga faduwa hannun ta na rawa tsabagen yanda zuciyar ta ke harbawa, ta na shirin juyawa ta koma ya gan ta, cikin hanzari ya nufo ta da sauri ya na mai fadin

“Alhamdulillah, kada ki juya ina bukatar taimakon ki”

Yanda zuciyar ta ke bugawa kamar mai shirin fitowa ya sanya ta runtse idanun ta, ta na mai saurin bude idanun ta juyo ta na kallan shi yayinda ya karaso kusa da ita. Tsayin Usman ya sanya sai ta dan daga kai kadan take iya duban fuskarsa, dan kuwa in dai tsayi ne da fadi ka sami Usman an shafa fatiha.

“Yi hakuri na tsayar da ke, Malam be fito sallar Magarib ba haka ma Isha’i, a zato na wani uzuri ne ya hana shi, sai yanzu da lokacin karatu yayi Jauro ke sheda mana duk sanda ya shigo ya karaci sallamar shi Malam be amsa ba, kin ga abun da damuwa, yanzu ma na yi sallama na ji shiru”

Tun da ya fara magana ta saki baki da hanci ta na kallan sa, yanda muryar sa ta ke da girma be hana sa magana mai cike da kwanciyar hankali ba, Iyakar gaskiyar shi ya ke mata bayani duk da dai hausar ta shi ba ta fita sosai.

“Ko yaya ki gani? Ki taimaka ki duba mana domin Allah”

Halitta na mai gyara murya ta ce

“Toh toh, bari na shiga”

Ta yi saurin wuce shi ta na mai tasbihi ga Allah akan wannan masifa da ke dankare cikin zuciyar ta, wato masifar son Usman da ya ke miji ga yar uwar ta. Ba ta sami nutsuwa ba sai da ta shiga falon Malam ta na mai doka sallama, shirun da ta ji ne ya sanya ta karasawa har tsakar falon, ganin Malam ba ya ciki ya sa ta aje kwandon abinci, ta nufi dakin sa ta fara sallama, Nan ma shiru, a tsorace ta fara bugawa da karfi ta na sallama, jin shiru ta bude kofar dakin da sauri ta shiga, nan ma Malam ba ya ciki.

Ta na shirin juyawa ta fita ta jiyo kamar gurnanin numfashi na fita daga bandaki, a guje ta karasa ta bude bandakin, idanun ta yayi tozali da tashin hankali, Malam kwance a kasan bandaki hannun sa bisa kirjin sa, yanda ya ke gurnanin wajan fitar da numfashi ya sanya Halitta fasa ihu ta na fadin

“Daddy! Na shiga uku! Daddy Innalillahi wainnailaihi rajiun!!”

Jan shi ta fara yi tana kokarin tada shi, sai da ta sa iya karfin ta, Amma ta kasa sannan ta tuna da Usman da ke tsaye ya na jiran ta. A guje ta fita ta na fadin

“Usman Daddy na! Usman zo ka taimaki Daddy na!”

Tun kafin ta karaso ya juyo ihun ta, da sauri ya kutsa kai ciki kafin ta kai ga fitowa in da ya ke, tambayar ta ya ke

“Me ya faru? Me ya sami Mallam?”

Nuni ta ke masa da hannu izuwa dakin Malam, ta kasa magana tsabagen kuka da ya ci karfin ta. Cikin zafin nama Usman ya karasa dakin Malam, in da ya tarar da Malam kwance cikin halin da Halitta ta barshi.

“Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifna minha! Innalillahi wainnailaihi rajiun”

Cewar Usman yayinda yake duba tufafin jikin Malam domin ya tabbatar da duka tsaraicin sa rufe ya ke. Ganin Malam na sanye da dogon wando kasan farar jallabiyar da ke jikin sa ya sanya Usman daukan Malam cak da ke Usman ba aboci karfi ne, cikin sassarfa ya yi waje da Malam Halitta na biye da shi. Kafin su kai ga farfajiyar gidan in da daliban Malam ke jira Usman ya dakatar da Halitta cikin bada umarni ya ce

“Ka da ki biyo mu, ki koma wajan yan uwan ki ku shedawa duk wanda ya kamata su sani, na mi ki alkawarin kula da shi, za mu tafi asibiti yanzu, wani asibiti ya ke zuwa?.”

Halitta na shirin ma sa musu, Amma yanda ya juyo ya kalli idanun ta cike da tabbacin alkawarin da ya dauka mata ya sanya ta gyada kai tare da fadin

“Premier, a court road ya ke, Dan Allah kada ya rasa ran shi….”

“In Sha Allah……”
Cewar Usman yayinda ya juya da sauri, Halitta na kallan sa har ya kure ganin ta. Yanda ya fito dauke da Malam ya sanya hankali kowa tashi. Tuni daliban Malam su ka to kan sa, kowa na tamabayar lafiya, me ya sami Malam, me ya faru.

 

Back to top button