Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 86

Sponsored Links

Page 86

“Ka gaji?,ka gaji dani kenan kake nufi?,saika dauki mataki ai k…….” Kafin ta qarasa ta daka mata tsawa,dukkan yadda yakeson ya taushi kansa haqurinsa ya gaza

“Kada ki gayamin maganar banza da wofi,kin dauka ina tsoronki ne da bazan iya daukan mataki a kanki ba?,to ki shiga hankalinki wallahi,saboda idan nace hukuntaki zanyi abun bazai miki da kyau ba” yana kaiwa nan yayi gaba abinda har yana yin ball da botikin daya ciko da tarkacen kaya masu tsada daya wulaqantar.

Da kallo ta bishi zuciyarta na suya,mamaki kuma ya cikata,wai yau ita abbas yakewa haka?,sai zuciyarta ta karye qafafunta sukayi sanyi,hawaye ya fara sauka daga idonta,ta koma ta zauna gefan gadonta tana share hawaye.

Zuciyarsa na zafafe sosai sanda ya baro mata sashen,ya isa sashensa kai tsaye ya wuce bedroom dinsa,wannan karon bazai qyaleta ba,ko yaya zaiyi magana da wani magabacinta ko za’a samu sassaucin wani abu,yana tsoron faruwar abubuwa da yawa a nan gaba daga gareshi,baisan me zamansu zai zama ba a gaba,ga yara mata da yake dasu da yasan dolen dole wataran gidan wani zasu je,uwa uba kuma yanayi na lafiya,ta yaya muhalli babu cikakkiyar tsafta za’a samu ingantacciyar lafiya?.

Saman sofa bed dinsa ya zauna yayi waya ta a qalla mintuna goma,koda ya gama wayar riqeta yayi a hannunsa yana jin banbarakwai babu dadi,yau ya aikata abinda bai taba aikatawa ba wato kai qarar hafsat din, tsahon zamansu tare na wasu shekaru.

Ta bangaren widad tuni ta gama tsaftace sassanta, hankalinta bai kwanta ba saida ko ina ya dauki qamshi,ta fiddawa mimi uniform dinta ta sake mata wanka,akwai ragowar kayanta a sassan tun wancan zuwan da tayi,ta saka mata su,saita tsaya tana kallonta.

Yarinyar kyakkyawace,kawai rashin tsafta da gyara ne yake dakushe duk wani kyau nata

“Anty ki kaini wajen daddy yaga kwalliyata,dama inata cewa mommy tayimin tana cewa bata da lokacin wannan” murmushi ta sake

“Wanka zanyi nima,ki bari idan nayi saina kaiki” marairaicewa tayi

“Don Allah anty,nidai yanzu” ba yadda zatayi,dole haka ta dora qaramin mayafinta ta kama hannun mimin suka fice tana cewa

“Duk chocolate din da daddyn ya baki kin yarda zamu raba?” Tana dariya ta gyada mata kai.

Babu shi a parlor din sanda suka shiga,saita cewa mimi

“Bari na duba shi a daki” ta gyada kai yarinyar ta zauna saman kujera cikin zaquwa.

A nutse ta tura qofar dakin,daidai lokacin da yake zaune cikin sofa bed din,ya kwantar da bayansa sosai a jikin sofa din,idanunsa da suka rusuna ya daga yana kallon fuskarta sanda ta tsaya daga bakin qofar tana riqe da handle din tana kallonsa kamar yadda shima.ya zuba mata ido,duk sai taga kamar ya sauya daga zuwansu bauchin.

Hannunsa ya daga yayi mata nuni da tazo,ta saki qofar ta soma takawa a hankali kamar mai tausayin qasa,ya zuba mata ido yana jin nutsuwa tun gabanin ta iso gareshi.

Hannunsa ya bata sanda ta iso kusa dashi,ta saka nata hannun a ciki,sai ya fincikota cikin jikinsa a tausashe,ya mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,yasa labbansa masu taushi yayi kissing goshinta,sai ta dan saki ajiyar zuciya

“Mimi na rako zata nuna maka kwalliyarta” ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba yi masa magana,birkitota kadan yayi yana kallon fuskarta

“Ina taki kwalliyar…..ita tafi muhimmanci” kunya ta kamata ta sauke fuskarta a qirjinsa tana shaqar daddadan qamshinsa

“Banfa yi wanka ba,aiki na gama yi,gurin duk yayi qura” girarsa ya dage sama duka biyun

“Iyyee,abun ‘yar haka ne?,shine kika share iya wajenki banda nawa ko?” Kai ta girgiza da sauri tana ‘yar dariya

“Ba haka bane uncle,nasan mummy hafsat ta gyara maka fa” kai kawai ya jinjina

“Yanzu yaushe ne za’a yimin kwalliyar,ta musamman nakeso,i will pay” dariya ta saki,tanajin dadin yadda yake yaba komai nata

“Za’a yi maka uncle” ta furta tana rufe fuskarta da hannunta

“That’s my baby doll” shima ya amsa mata yana jan dogon hancinta

“Muje naga mimi’ ya sake fada yana dagata a jikinsa,gaba daya sai ya rasa kaso hamsin na bacin ransa, shigowarta kawai ya tafi da komai,ta miqe ya sanya hannunsa cikin nata ya riqe gam suka fara takowa xuwa falon.

Babu irin abinda bata saqa a ranta ba sanda take tsaka da kukan,sai datayi me isarta sannan ta dauraye fuskarta,bata da wata mafita,komai ya tsaya mata cak,batasan me ya kamata tayi ba,saita dauki wayarta ta soma lalubar number anty ummee ko xata samu wasu shawarwari.

Abun takaicin tana kira taji suna sanar mata kudinta ya qare,dama already taci bashin mtn na kusan dubu uku,duk kuwa da cewa duk wata sai abbas din ya saka mata kudin credit ta account dinta bama credit din ba,taja tsaki ta sauka ta koma bank dinta ta sakawa layin bashin da suke binta,bonus din da suka bata tayi amfani dashi ta kira anty ummee din.

Shuru tayi har ta gama bayaninta sannan ta dora

“Ina tsoron kada yarinyar nan ta fara shiga rayuwarsa anty ummee,ni zuwan nan da sukayi ma sai naga kamar ta fara budewa ta zama mace,harda kai mata kayanta sashenta fa,duk da na sanshi bashi da girman kan wannan wa iyalinsa,amma yarinyar ai bata cancanci wannan kulawar ba” baki anty ummee ta tabe,tana jin kamar ta jawo hafsat din tayita jibga

“Nidai da farko saidai nayi miki addu’ar Allah ya yaye miki wannan baqar qazantar,bansan irin ribar da kike samu da ita ba” maganar ta bata ran hafsat,don duk yadda kake da ita kace mata qazama ce to sai an ganku a rana

“Meye haka anty ummee?,nifa ba akan wannan na nemi shawararki ba,tunda dai ni ina iya bakin qoqarina,abubuwane sukeyimin yawa,kuma nayi nayi ya daukon mai aiki yaqi,to bazan kashe kaina ba” kai anty ummeen ta jinjina,gwara ta bita a yadda suka soma,kada ta yiwa kanta rasa rasa

“Ke gaskiya ce baki so,na daina kuma gaya miki,amma indai kansa kike san shawowa dole kidan gyara inda idanunsa zasu ganki tsaf,tunda da tsafta aka jarabceshi ke kuma ea qazanta…..muddin kinason ganin dai dai dole ki sauko daga ra’ayinsa kibi nasa ko yaya ne,koni da kikaga ina yadda nakeso,wasu abubuwan ra’ayinsa nake bi kafin na murda idan naga ya biyu yadda nakeso na koma kan nawa ra’ayin” sun dan dauki lokaci suna fafatawa ma kafin hafsat ta fahimci abinda anty ummee take nufi,dole ta yarda tadanyi gyara a ranar ko zata cimma manufofinta ta ruwan sanyi.

Suna gama wayar ta miqe tana tunanin ta inda zata fara,sai ta yanke ta shiga da kanta ta kira widad din,can qasan ranta tana mamakin yadda ko motsinta bata sake ji ba bare ta shigo taga abinda ya kamata tayi mata.

Tun bata qarasa ba taga sassan nata a kulle,ta juya cike da mamakin ina taje?,ko gidan hajiyan da aka rufe babinsa ta koma?,harta dawo da baya…..amma tana kallon sashen abbas din akalar tunaninta ya canza,saita nufi can,duk da zuciyarta na gaya mata bata ciki,to amma mafi rinjaye na tunaninta yana rinjayarta ga zuwa sashen nasa.

Tana buda qofar falon abbas dake riqe da hannun widad yana bude ta bedroom din,idanunsa na kallon gefansa yana magana da widad din,cak hafsat din ta tsaya kamar an dasata,qirjinta yana harbawa,ta zuba masa ido tana son ganin waye yake biye dashi.

Wani mugun ashar ne taji ya taso mata,saidai abinda yazo ya tsaya mata a wuya ya hana kowanne kalma fita daga bakinta,widad fa take gani,widad yau a dakin mijinta?,riqe da hannunsa?,baqar zuciya da kuma fushin dake cin zuciyarta ya sanyata cikin zafin nama ta harbo zuwa cikin falon.

Takunta yaja hankalinsa sanda yake tsokanar mimi tayi kyau,ya tashi daga durquson da yayi,ya zuba mata idanu,don kallo daya yayi mata zuciyarsa ta bashi akwai wani abu na daban.

Kafin ta qaraso idanunsu suka sarqe cikin na juna,wani irin baiwar idanu gareshi masu tsananin kwarjini,abinda yayi mata tasiri kenan,kallonsa ya ratsa zuciyarta ya karya duk wani zafi data debo da kima qissime qissime da zuciyarta keyi mata na irin abinda zata aiwatar,saurin data kwaso ya canza zuwa nawa.

Kallon kallo suka ci gaba da yiwa juna,sai taji zuciyarta kamar zata fashe idan bata ce komai ba,a sannan ta tuna ita din me laifi ce,ta kuma tuna gargadin da anty ummee tayi mata

“Kissa saida kwantar da kai”maganar data gaya mata ta qarshe kenan

“Nace me za’a dafa maka?” Ta maye gurbin dukka wani bala’i daje qasan zuciyarta da wannan tambayar,tambayar da yaji sam bata dace da yanayin da ya ganta a ciki ba,to amma koda ta tambaya dinne da gaske,yanajin ya zuwa yanzu ya kamata ya nuna mata fushinsa,saiya dauke idonsa daga kanta ya maida kan ‘yarsa

“Bana buqatar komai” ya amsa mata a dake yana duqawa yana gyarawa mimi kwalar rigarta.

Wasu irin hawaye ne masu dumi suka cika mata idanu,ta zubawa widad ido,wadda sam idanunta baya wajen,ta tattareshi akan tv,haka kawai takejin wani irin itama cikin ranta, yanayin gidan a yau ya sake mata rashin dadi,ta tabbatar a lokaci irin wannan a kaduna ita dashi din suna kitchen tare suna girki,ko suna backyard dinsu suna wankin undies,ko suna karatu ko kallo.

Qwafa taja can qasan ranta tana danne hawayen,batason ta zubdashi a gaban widad din,ta juya tana barin falon,kamar zatayi bindiga ta fashe haka takejin kanta,nadama da dana sanin ma tambayarsa me za’a girka din ya cika Zuciyarta,gashi ya yarfata a gaban qaramar yarinyar da a haife ta haifeta.

Hanyar data fita yabi da kallo,yaja dan qaramin tsaki sannan ya koma ya zauna kusa da mimi

“Hadamin coffee ko black tea” ya bata umarni yanason danne shima nasa fushin,tadan kalleshi da wani irin yanayi,cikin zuciyarta takejin akwai wani abu dake damunsa,don ba haka yake ba,kamar zatayi magana saita fasa,ta miqe tana nufar qofa.

Tana sanya qafarta a falonta taji an biyo bayanta,ta tsorata sosai,taja da baya tana dubanta,sai data gane hafsat dince saita saki ajiyar zuciya tana lumshe idanunta hadi da budesu tana kallonta.

Wani irin kallo take bin widad dashi,tana jin kamar ta fincikota ta rufeta da duka,yarinya qarama amma tana neman dagula mata lissafi,tanaji a jiki da zuciyarta abbas ya sake canzawa ne sosai ta sanadin aurenta,a baya idan ya fiya cika masa ciki tattarawa yake ya koma inda ya fito,sanda suna gari guda kuma saidai ya tsiri zaman gidan hajiya,ko kadan bata damuwa,saboda tasam ba wani wajen yaje ba,kuma shi din ba mai kula kulen mata bane,asalima sam basa cikin tsarinsa,don haka ba kasafai ta fiya damuwa,idan ya qare fushinsa zai dawo yaci gaba daci abincinsa ko yaya ta dafa kuwa,idan yaji bai masa bama zai shiga kitchen ya dafa da kansa
(Hmmmm,duk a lokacin bata taba kawowa miskilanci bane irin na mijinta,ta aza hakan akan babu yadda zaiyi da itane,kamar dole yayi duka abinda yakeyi din).

“Uban me kika shiga yi dakin abban mimi” kamar daga sama furucin yazowa widad,mamaki ya kamata,for now dai ta fahimci matsayinta daya da hafsat din,ta kuma fahimci me kalmar aure take nufi,indai haka ne bataga muhallin wannan tambayar ba,duka wannan ba damuwarta bane,abinda yafi bata mata rai kalmar UBAN WA data fada,wanda dai dai yake da zagi a wajenta

“Dake nake!” Ta sake fada cikin tsawa kamar zata kai mata duka,amma ga mamakinta sai taga widad din ta tsireta da manyan idanunta

“Ai ba haramun bane tunda kema naga kina shiga” ta fada a sakalce abunta tana dubanta.

Zallar mamaki ya saukowa hafsat din,tayi sakato tana kallonta

“Ni kike gayawa wannan maganar?” Ta fadi tana jin wani zafi har cikin ranta

“Me nace mommy?” Ta tambayeta kanta tsaye,a karo.na biyu ta sake shiga mamaki,anya kuwa?,anya abinda take tunani bai faru ba?,yaushe yarinyar tabfara fahimtar abubuwa haka?.,da tayi wani qaramin tunani sai tabar wancan maganar tace

“Ki wuce kije kiyi aikinki,suna can suna jiranki”

“Tom,bari na dafawa uncle tea” tea?,har tea yake sakata dafa masa saboda zallar jawo mata raini?,wanne girki ta iya da zai buqaci tea daga wajenta

“Ni kike.maidawa magana widad?” Juyowa tayi tana kallon hafsat din,ita gana daya sai taji ta sire mata daga zuciyarta,tunda ta fahimci akwai qaryayyaki da yawa data taba gaya mata,a dabi’arta kaifi daya ce,ko meye za’a yi mata bata qarya haka ta taso tun quruciyar ta,dalilin da ya sanya ta sake shan wahala kenan sosai a wajen ‘yan uwanta da cousins dinta

“Me nayi mommy?,aikinsa shine gaba da kowanne aiki fa,ba kyau miji ya saka kaqi” zuwa lokacin gaba daya hafsat din ta gama sarewa,lallai qaryarta ta fara qarewa,tund har yarinyar ta fara sanin ma’anar kalmar miji,ta kuma fara tantance bin umarnin wata a gaba da nata umarnin,basu taba musayar magana da ita ba koda da sau daya,amma yau da ita suke musu?,tana ce mata ga yadda za’a yi itama kuma tana fadin nata,ah wannan babbar musifa da babbar guguwar canji ce ta tunkarota,wadda take buqatar zama na musamamn da shawarwari don sanin meyenmatakin dauka na gaba,daga wannan sai bata sake cewa komai ba,ta juya tana barin wajen tana jin kamar duniyarta tazo qarshe gaba daya.

Tsakin da batasan yazo bakinta ba shi ta fitar,tadan harari hanyar data wuce din

“Kawai kawai ni….”sai kuma tayi shuru tana quna quni,ita tunda taga yadda taketa wani tsare mata uncle dinta da kallo taji tana jin haushinta,bata taba ma kula da haka take zuba masa ido ba sai yau din,haka ta shiga kitchen din,ta fara duba kayan hada tea din da tasan yana matuqar so ta fara hada masa,lokaci lokaci tana dan jan tsaki.[3/19, 5:42 PM] +234 808 711 8630: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button