Arubuce Ta Ke 85
Page 85
Yau din tunda suka tashi daga kaduna basu tsaya ba,don bata jima ba bacci ya dauketa,don dama yawanci saboda ita yakan tsaya din,ya samar mata wani abun da zataci,to har suka je inda yakan tsaya din suyi sallah da sauransu tana baccinta,don haka ya wuce abinsa kai tsaye,lokaci lokaci yana waiwayawa ya kalleta,yana monitoring baccin nata.
Bata farka ba sai da suka shiga unguwarsu,tadan kalleshi,suka hada ido,yasan me takeson cewa,gidan hajiya takeson zuwa,to amma bayajin zai iya barinta,tunda duka duka kwana hudu zasuyi su juya,suya saki murmushi kawai ya shafi gefan fuskarta
“Ba kwana gidan hajiya wannan karon,i need you by my side” shuru tayi kawai,ta langabar da kanta gefe guda ba tare data ce komai ba,duk da ba haka taso ba cikin ranta.
Yana gama parking kusa da motar hafsat din data dauki qura mimi na shigowa ita dame daukota daga makaranta,ganin motar babanta ya sanyata tahowa da gudunta tana kiran sunansa,ya dagata ya rungumeta yayi kissing dinta,saita zame daga jikinsa ta koma wajen widad.
Ta yima widad din nauyi,amma saita riqe hannunta tana tsokanarta hadi dayi mata waqar ‘yar makaranta,tana ta dariya,dadi ya cika yarinyar,ko banza tana samun nishadi kulawa da kuma canjin rayuwa a duk sanda baban nata da antyn nata sukazo.
Kamar sama sama take jiyo muryar mimi din tana kiran sunan baban nata,sai taja tsaki ta share,a ranta tana jin haushin yadda yarinyar keda qulafucin ubanta,tana tsoron gaba kadan ma zaiyi wahala idan batafi sonta akan uban ba,saita ci gaba da lissafin kudinta,amma kuma jin shiru bata ji motsin mimin ba,saita ajjiye wayarta da take lissafin a ciki ta miqe tana gyara daurin zaninta,ta sako kai zuwa harabar gidan.
Dai dai sanda sale ke cire kayansu a booth din motar,abbas din yana gaya masa kada yayi nisa zai kaishi kasuwa.
Cikin wani mugun mutuwar jiki ta sauke hannuwanta data tokare bakin qofa dasu
“Kanbun bal bala’in bala’i!” Bakinta ya furta duk da batasan yaushe hakan ta faru ba,daga inda take tsaye tana iya hangen widad wadda ke riqe da hannun mimi,fuskarta kwance da murmushin daya qarawa fuskar tata kyau da kuma kwarjini
“Wanne irin girma ne haka cikin wata guda kacal?” Ta tambayi kanta da kanta,har yanzu idanunta na saman fuskar widad din,ko sau daya ma bata waiwayi inda abbas din yake ba.
Takawa ta soma yi zuwa inda suke tsaye a hankali tanason sake gasgata abinda idanunta ke nuna mata,saidai duk taku daya idan tayi bugun zuciyarta sai ya qaru,kyau da yadda girma ya fara nunawa a jikin widad din suka soma bata mamaki.
Qaramar jakarta abbas ya dora mata saman mota bayan ya kulle motar
“Keda mimin banga marabarku ba” yayi maganar yana kafeta da idanu hannayensa duka biyun cikin aljihun rigarsa.
Dariya ya bata,tadan juya ido cikin irin nuna mamakin nan,saidai hakan batasan mugun kyan da ya qara mata ba
“Uncle kace na girma fa?” Har tsakiyar zuciyarsa ta aike da saqo,bayason yayi saurin bada kai tun yanzun,tunda dai nan ba kaduna bace
“Yes…..amma ga jakarki nan,ki dauka sai mu gani” ya fada tsadajjen murmushin nan nasa yana fita daga fuskarsa.
“Uncle itama wannan din da nauyi don Allah…..” Widad ta fada cikin shagwabar data saba yi masa
“Ya salam” ya fada yana miqa hannu hadi da dauke jakar,yayin da hafsat taji tana shirin faduwa,sai takai hannu tana neman abinda zata riqe gudun faduwa,hannunta ya sauka kan kyakkyawar luggage din widad guda daya da tayi saura sale bai dauke ba.
Hannunta ta janye,mamaki yana sake kasheta,gata kusa da wajen amma cikinsu ba wanda yama lura da wanzuwarta a wajen,wani tunani yazo mata,tayi qoqarin saita kanta ta hanyar yin gyaran murya kadan,abinda yasa duk suka waiwayo
“Sannu da zuwa,saukar yaushe?” Tayi maganar tana tsare gida hadi dayin kicin kicin da fuska,sannan ta miqa hannu tana son karbar jakar widad dake hannunsa a zuwan tasa ce
“Yanzu ne,ko kayanma ba’a gama daukewa ba”
“Fitar wuri kukayi kenan” ta sake fada tanason calling attention dinsa,sai ya dan gyada kai,abun nata nayau yana dan bashi mamaki
“Ina wuni” widad ta fada ba tare data dubi sashenta ba,haka kawai takejin wani abu mara dadi yana dan taba zuciyarta,taji kuma.ba zata iya gaidata yadda ta saba ba,sai hafsat din ta waiwaya tana kallonta,sai a lokacin ta sake ganinta sosai
“Oh….. amarya lafiya lau” can qasan ranta tana dan mamakin yanayin data gaisheta dashi,ba haka ta saba gaisheta ba dashi,ta saba ta gaisheta tana fara’a bayan ta rusuna mata,sa’an nan idan tayi kamar bata ji ba sai ta sake maimaitawa
“Ba jakata bace ta qanwarki ce” ya fada yana kulle motar sanda yaga tana nufar sashensa da jakar
“Oh, okay” ta fada tana dawowa baya inda widad ke tsaye da mimi,kai tsaye ta miqa mata jakar,don dama abinda takeso kenan ta karba kayarta.
Ba tare da nufin komai ba ta kalli abbas din a shagwabe
“Allah uncle da nauyi,kuma kace zaka kaimin fa”
“Bance na fasa ba ai” ya fada yana miqawa hafsat hannunsa,kamar sakarya ta sakar masa jakar,xallar mamaki yana cikata,ta bishi d kallo sanda yake cewa
“Muje na ajjiye miki”
Su ukun suka juya zuwa sassanta,mijinta….. diyarta ta bisu da kallo,me yake shirin faruwa ne wai?,ko kuma tace meye ne ya farun?.
Kamar wadda aka tsikara saita kasa tsaiwa,ta daga qafarta da hanzari tabi bayansu,ta cimmasu ya karba keys din ya saka yana bude mata qofar sassan nata,sai ya waiwayo yana duban hafsat din da tayi tsaye a bayansu,ta kasa ta tsare tana dubansu,ya dauke kai ya qarasa buda qofar ya matsa mata gefe ta sanya kai ta shige ita da mimi da suketa surutunsu ko a jikinsu.
Cikin falon ya ajjiye mata jakar,sannan ya juya ya fice daga falon yana tsokanar mimi,a sannan hafsat din tana qifar parlor din bata shigo ba,saidai tana jin zuciyarta na mata wani iri,ta kasa tuna komai bare tayi tunanin me ya kamata tayi,jikinta yayi mugun sanyi,zuciyarta kuma tana bata akwai wani abu.
Kallonta ya sakeyi sanda ya fito,tana tsaye qyam kamar wadda aka bawa gadin qofar falon,yadan kalleta sai kuma ya wuce,ta taka ta bishi a baya,zuciyarta kamar sata fito daga qirjinta,tanason masa qorafi to amma kuma tace masa meye?,haka taci gaba da binsa a baya har zuwa sashen nasa.
Sanda ya bude waiwayowa yayi yana kallonta,qura fal sashen,wannan abu yana masa ciwo,baisan sai yaushe zai fara dawowa yana samun sassan nasa a tsaftace ba,suna hada ido ta kauda kai,tasan qorafi yakeson yi,amma ba zata bashi dama ba,zata gyara tunda ga widad tazo,wasu ayyukan zasu ragan mata ai,sai ta karba jakarsa ta wuce bedroom dinsa da ita.
*_BAYAN AWA BIYU_*
Yana zaune saman kujera take gyaran falon,tana aikin tana gyara daurin zaninta dake kwancewa,fuskarta sam babu walwala,tunani ne cunkushe fal a ranta.
Nawwara na zaune saman doguwar kujerar da yake kai,yanata bare mata chocolate tana sha tana masa surutu,lokaci bayan lokaci yakan daga kai ya dubeta,tun daga tsefaffen gashinta da yayi cibiri cibiri har zuwa qafafunta dake cike da kaushi,babu digo lalle ko kadan bare su samu arziqin suturta kaushin qafartata,brassiere dinta ta saki sosai,don kana iya hangota ta gadon bayanta.
Ya lumshe idon takaici yana cikashi,duk wani abu da diya mace zaga gyara a jikinta ya bada sha’awa hafsat din ta kauda shi da kanta da mugun qazanta da rashin sanin ciwon kanta,tattausan qshin widad ya tuna,babu sanda zata giftashi bakaji tashinsa ba daga jikinta,sabanin hafsat din da saidai yaji wani na daban bawai qamshi ba.
Ta gama gyaran tana jin tayi wani gagarumin aikin azo a gani,gaba daya qugunta har ya riqe,saita taka zuwa qofar fita,tanason kiran widad din tazo ta gyara mata kitchen hade da kayan miya zata dora girki,sannan ta kama sauran gyaran falonta zuwa sassan part din nata
“Zo mana” ya kira hafsat din yana sauke lallausar qafarsa a qasa tsigar jikinsa nadan xubawa,haka kawai yake ji gyaran data yiwa sassan nasa bai gamsar dashi ba,saboda ya riga ya saba…..muddin widad din tayi gyara to sai ka rantse da Allah wani engine akasa aka kauda qazantar waje.
Dan jim tayi don ta qagu ta kira yarinyar,tanason jin abubuwa da yawa daga bakinta ko zata samu haske kan zarginta,amma ganin ya kafeta da idanu yasa ta kasa bashi uzurin cewa tana zuwa din,ta juyo ta dawo ta samu waje ta zauna
“Meye da meye a kayan amfaninki ya qare?” Ya tambayeta yana hada hankalinsa sosai a kanta with seriousness,don shikam Allah ya sani,bayason ya zalunceta,amma muddin za’a ci gaba da tafiya a haka komai zai iya faruwa,zuciyarsa zata gaza daurewa hada waje da ita.
Sosai ta kalleshi,saita girgiza kai
“Babu komai” shuru yadanyi yana jinjina amsarta,sai ya miqe ya kama hannun nawwara
“Ban yarda ba,muje na gani”, kamar zata fasa kuka haka ta miqe,shigarsa sassanta tasan ba abinda zai dadeta dashi wani bacin rai,bata da damar musu,haka ta miqe tabi bayansa.
Suna fitowa daga sashen sukaci karo da wata iska mai qamshi dake kadawa dukka ilahirin harabar gidan,yaja iskar sosai cikin hunhunsa ya fesar,a wajen mutum daya yakejin wannan qamshin,kuma ko yanzun ya tabbatar yana fitowa ne daga sassanta,kewarta yaji ta saukar masa,tamkar sun dauki wani lokaci mai tsaho ne basu tare,yayin da hafsat ta dinga shaqar qamshin itama,tana tunanin daga ina yake haka?,da bata gane ba saita watsar,ta raya a ranta qilan daga maqota ne.
Suna ratsa falon yana qare masa kallo,yadda dukka yabi ya haukace,harda kayan wanki zube saman kujera,ko meye ya kawo.kayan wanki falo oho,suna isa bedroom dinta ta qarasa tsinkewa da al’amarinta,anya hafsat bata da ciwon qazanta?,wani lafiyayyen zani da bashi bashi ne yake fitowa daga bandakinta yana baiwa dakin wani irin yanayi mara dadi,katifarta gayanta ce kawai,babu zancan bedsheet akai,dukka qofofin wardrobe din nata a bude suke hanhai,ga kaya wasu a qasa wasu a ciki.
Iska ya shaqa ya fesar yana lissafa yadda zai kutsa kai bandakin,yaja iska sosai cikin hunhunsa sannan ya saka kai tana biye dashi,ranta dukka a bace,inda ya bari widad ta gama gyarawa ai kome zai shigo yayi sai yayi.
Da daya da daya yake bude kowacce locker dake bandakin,dukka kayan da yake siya da sunanta na gyara kama daga shaving cream,shower gel, mouth fresh,relaxers,hair mist hand and foot cream dukka gasu nan jibge,wasu har ya manta daya siyesu ma saboda tsabar dadewa da sukayi,da ya saka hannu ya dauko da yawansu ma sun gaji da zama sun bushe a ciki,wasu sunyi expire,haka ya dinga tarkatosu gaba daya ya zuba a wani qaramin bucket ya fito dasu daga bandakin.
A bedroom din ya tsaya,ya sake wangale qofofin wardrobe din nata yana duba kayanta daya bayan daya,yanaso yaga ta inda ya gaza,yanason yaga ko daga shine,saidai dukka sutturunta suna nan danqare,ya buda bangaren kayan baccinta dake jibge masu uban yawa,kasancewarsa ma’abocin son nighties baya rabo da siyansu komai tsadarsu,su dinma suna nan kar kar dasu,wasu ma a cikin ledarsu bata bude ba,sai ya juyo yana dubanta,idanunsa fal bacin rai da kuma soma gajiya da halayenta
“Ta ina ne na gaza hafsat?,me kikeso nayi miki ne?,wanne hakki naki ne ban sauke ba?” Yaune kadai ta danji nauyi,amma girman kai da qi fadi yasa taqi hari hakan ya fito,sai ta bata ranta kadan tana cewa
“Nifa bance ka gaza ba,sannan kuma nima ya kamata ana dubawa anamin uzuri,aidai kasan ba haka ka auroni ba,kuma ba haka nakeyi ba tun farko ba,yanxun yarane da hidimar gida ta yimin yawa” ransa ya baci sosai,a qalla tunda taga laifinta quru quru ko accepting ai ya kamata tayi ko?.
“Ina yaran suke?,ni ban gansu ba,yara qwaya biyu kacal?” Ido ta fidda
“Aikai raina hidimarsu kekeyi?”
“Eh na raina,tunda koni ija iya hidimarsu,meye bana iya musu?” Baki ta tabe tana riqe qugunta,shikam ya fiya jidali da daga hankali,batasan meye damuwarsa ba da rayuwarta,yanzun nan ta gama gyaran sashensa ko hutawa batayi daga wahalar aikin ba ya tasota a gaba yana son tozartata.
Wani bacin rai dake taso masa ya hadiye,cikin danne fushinsa yace
“Am tired…..na gaji da wannan halayen naki hafsat,anzo gabar da dole ki gyara,bazan ci gaba da lamuntar haka ba” maganarsa ta farki zuciyarta ta kawo mata fassararta,zuciyarta na sake qarfafa mata gwiwa ba shakka akwai wata a qasa,bai taba gaya mata wannan kalmar ba sai yanzu,anya yarinyar can kuwa bata fara zamewa rayuwarta barazana ba
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*