Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 81

Sponsored Links

Page 81

Kamar ko yaushe a harabar gidan ya cimma yaran,sunata wasan qasa sunyi futu futu dasu,qasa har saman kansu,amma hakan bai hanasu murnar ganin juna ba,ya tsugunna ya kwashe abinsa sunata masa surutu yana kerbewa.

Dab da zai shiga sashen nata ta fito,sanye da atamfa dinkin doguwar riga,tayi daurin ture kaga tsiya,duka gashinta da ba kasafai ta fiya son kitso ba ya fito abinsa ta qasan daurin,hannun brassiere dinta daya fito ta kafadarta ya sake muzanta shigar tata,atamfar anko ce da sukayi biki tun shekaran jiya,kuma tun shekaran jiyan take jikinta bata cire ba,sam batayi tsammanin zuwansa a yau din ba,shi yasa ta saki jiki ya sheqi baccinta,bata jima da tashi ba ta biyo sahun su mimi jin shuru ba motsinsu tun dazun.

Tare hanya tayi tana masa sannu da zuwa hadi da karbar jakar hannunsa,bata son ya shiga sashen nata,saboda ita kadai tasan irin badaqalar daya kwasa ba,don hatta da uniform din mimi yana zube a falon da school bag harma da tsadajjen lunch box dinta daya siya mata

“Mu qarasa sashen naka,dama fitowar da nayi gyarawa zanje nayi” ta fada tana sake kankane hanyar.

Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa.

Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa

“Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din” manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta

“No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana”.

Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace

“Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye…..”

“Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s……” Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe

“Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?” cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai

“A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba”.

Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad.

Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace.

Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru.

Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera.

Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za’a mayar ‘yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma.

Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa.

*_W A S H E G A R I_*

Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki.

Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa.

Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra’ayin sunyi hannun riga da ta’ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa’a ranar tana da ra’ayinsa.

“Fita zakayi kenan” ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta

“Eh,akwai wani abu?” Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa.

“Aah,inason zuwa gidan hajiya ne” dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta.

A ka’idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita

“Saikin dawo” ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu.

Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare.
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button