Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 74

Sponsored Links

Page 74

Tana zaune saman kujerar dake fuskarta qofa yana kada qafartaranta cunkushe da tunani kala daban daban,warmer dinta da abbas ya bayar yafi komai bata mata rai a yanzun,don bata dauki widad din a wata matsala da zata kasa saitata ba,wannan kuma sai yazo ya hadu da rashin shigowar widad din ya qara tunzurata.

Widad din nayin sallama ta watsa mata wani irin kallo mai hade da harara

“Sai yanzu kikaga damar zuwa?” Ido widad din ta dauke yana qarasowa cikin falon

“Gefen uncle na fara gyarawa tukunna” miqewa zumbur tayi,har batasan ashar ta subuce mata ba

“Kina nufin dakinsa kika shiga kika gyara?,waye ya baki wannan izinin?” Kallonta take danyi da mamaki,sai kuma ta janye idanunta,saboda bata saba kallon babba haka kai tsaye idan yana mata fada ba

“Shi yace nazo na gyara” maganar ta sake tunzurata,ba bata lokaci ta nufi qofa ranta na suya,wannan wanne irin zubda mata da mutunci yayi shirin yi?,me ya hanashi kiranta ita tazo ta gyara masan,kawai sai ya kama ya kira yarinya taga makwancinsu?.

Har takai qofa kuma ta dakata,saboda tunawa da tayi ita din me laifi ce,sai tayi qwafa ta dawo ta zauna,koma meye akan widad din yau zata saukeshi

“Me kika tsaya kina kalla da baki wuce kin kama aikinki ba?,ki fara da kitchen idan kin gama ki wanke bandakina,akwai kayan nawwara data bata a toilet dina,saura kiyimin ha’inci” idonta ta bude a hankali daga rufesun datayi tun sanda tayi mata tsawar farko,bata ce mata komai ba ta doshi kitchen,tana jin wani abu me kama da bacin ran da bata taba ji ba yana son fara tana zuciyarta,me tayi mata da zata dinga binta da irin wannan tsawar?.

Tana ta cika tana batsewa ita daya a falon tayi baquwa,baquwar kaman customer a wajenta,tana siyan pieces na laces da hafsat din ke kawowa daga Lagos tana siyarwa,dadewarsu tare ya haifar da qawance a tsakaninsu,ta jima batazo gidan hafsat din ba,saboda dama ba kowa bane yakejin dadin ziyartar gidanta ba,saidai idan cikinka a cike yake da abinci,hakanan baka da qishirwa.

Already ta gaya mata idan ta shigo bauchin zata qaraso taga wasu lace,tasan kudi zata samu a jikinta,wannan yasa ta karbeta da fara’arta,ta kuma ajjiye duk wani bacin rai dake damunta.

Suna tsaka da gaisawa talatu ta dawo dasu mimi ta koma

“Ma sha Allah,mimi ta fara girma” baquwar me suna hajiya habiba ta fada

“Wallahi,aikin kwana biyu baki shigo ba,saidai aike”

“Bari kawai,abubuwa ne suka cushemin” daidai lokacin da mimi ta matso kusa da hafsat din tana gaya mata zatayi toilet

“Sarakan saka mutane aiki,baiwar taku ai ta dawo” sai ta sanya baki ta qwala kiran sunan widad din har sau uku.

A lokacin tayi nisa cikin tunanin dabi’un hafsat din,me yake damunta da take tara wanke wanke haka ba zata iya kintsawa ba?,ko ina na gidanta bashi da dadin shaqar qamshi har sai sanda tazo?,muguntar zatayi mata ne?,ko haka dabi’arta take?,itadai tunda ta taso a rayuwarta bata tana ganin kalar qazanta irin wannan ba.

Yadda take kiran sunan nata ya fargar da ita,ta ajjiye plate din hannunta da sauri,garin saurin wuqar dake ajiye a wajen tadan yanketa a dan yatsa,ta runtse ido tana jin zafin yankan yana ratsata,ta yarfe hannun tana bude idon nata sanda muryar hafsat ta sake iskarta cikin wani amo na gigitar kira.

Dukkansu su biyun suka zuba mata idanu,hafsat din ta jifanta da wata muguwar harara,yayin da hajiya habiba ke mamakin ganin widad a gidan,tunda bata santa ba

“Me kikeyi kina jina ina kiranki?” Ta fada cikin nuna isa taqama da gadara,tanaso ta yarfata sosai gaban hajiya habiba

“Banji ba sai daga baya”

“Kin fara canza hali ko?,indai kuwa hakane zakisha mamakina,zaki kuma sha wahala ne kawai,ki dauki mimi ki dorata a poo tayi toilet,kafin sannan ki kawowa baquwa ruwa” batace mata komai ba sai kama hannun mimin da tayi,tuni dama yarinyar ta iso wajenta tana mata sannu da zuwa,ita kanta yarinyar cikin walwala take,saboda me basu kulawar da mahaifiyar data haifesu ma bata iya basu ta dawo,surutan mimi ya rage bacin ran da a yau taji tana jinsa har cikin zuciyarta.

Sai data dorata a poo din sannan ta shirya ruwan da lemo a tray ta dora cup a kai ta fito Parlor din.

Sai da widad ta bace hajiya habiba ta dauke kallonta daga kanta sukaci gaba da cinikinsu,amma kuma maganar dake ranta tana ta cinta,har ta kasa Shuru

“Wai nace ba…..me aiki kikayi ne?” Ta jefawa hafsa tambayar,dai dai sanda widad ke fitowa dauke da tray din.

Duban widad din hafsat tayi,bata kuma tashi bada amsar ba sai data iso tsakiyarsu tana ajjiye tray din

“Tayi kama dame aiki ko?” Ta fada a wulaqance tana tabe baki,amsar hajiya habiba shine ko daya babu kama da ‘yar aiki a tare da ita,amma data fuskanci akwai magana a bakin hafsat din sai bata amsa mata ba,har zuwa sanda tace

“Wai nan haka kishiyace aka yimin”

“Kishiya?!” Ta amsa da amo mai qarfi tana sake bin widad data juya zuwa kitchen da kallo

“Wallahi hajiya”

“Kan ubancan….ah banga laifinki ba,amma ke kuma kina meye har aka miki kishiya?” Wannan shine iya abinda widad din ta iya ji.

Ko data koma dakin hafsat din,tsaye tayi a gaban mudubi kalmar ‘yar aiki tana dukan ranta,meye tayi da tayi kama da ‘yar aiki?,tasan meye ‘yar aiki,amma har yanzu bata fuskanci ainihin ma’anar kishiya ba,a cikinsu wanne yafi zafi?,ta samu kanta da tambayar kanta da kanta,kunnuwanta na iya jiye mata yadda hajiya habiba ta maimaita kalmar kishiya da wani irin nauyi da girma,me yasa kalmar kawai tayi girma haka?.

Kallon hafsat hajiya habiba taci gaba dayi tana sauraren bayanin da take mata,da irin qoqarin da tayi take bautar da widad din

“Kinyi qoqari qwarai,amma kuma ina jiye miki ranar da maigidan zai fuskanci bautar da ita kikeyi,ina mai tabbatar miki yana son kayarsa,saidai wala’alla yana ganin tayi qanqanta ne kawai shi yasa.mautara bata fito fili a kanta ba,ke…..baya ga haka ma mijinki me kamewa ne,idan wani ne ko jaririya ce yadda take da wannan mugun kyau wallahi tuni aikin gama ya gama,waima kina kallon fuskar yarinyar nan da kyau kuwa?”tayi tambayar tana kama haba,idanunta akan fuskar hafsat data bawa hajiya habiba dukka hankalinta

“Girma ya fara zuwa mata fa,duk da dai ban santa a sanda aka kawota ba,kuma ke kin sani,ko makaho idan ya shafa ki ya shafata yasan ta fiku kyua nesa ba kusa ba,ta fiki diri,ke koni bazan yarda mijina ya dinga kallon wannan surar ba wallahi tallahi…..”

“Yanzu me kikeso kice?” Hafsat ta katseta daga yadda take kuranta kyan widad,saboda a yanzun a duniya babu abinda ta tsana irin taji an fada ko an yabi kyanta,ko tunawa ta fita kyau bataso tayi tsakanin ita da zuciyarta bare har a furta mata

“Yauwa,idan kana da kyau ka qara da wanka,kudi zaki saka ki shiga malamai su sake kauda idonsa da zuciyarsa daga kanta,sannan a sake kama miki ita sai abinda kika ce” shuru hafsat tayi tana nazari,nan fa daya,an kuma zo wajen,ita indai zancan ta fidda kudi ne to babu ita a wajen,sannan ma kuma me take da buqata wai,komai da anty ummee ke tsara mata yana tafiya yadda ya kamata,ko canzawar da widad din ta fara yi hakan baya rasa nasaba da raga matan da takeyi kwana biyu qila shi yasa ta fara sakewa,kuma ko yadda anty umnee ke gudanar da gidanta ya isheta ishara,babu boka ba malam,amma ko meye ta fada ya zauna,kowa juyashi take a cikin gidan ta ruwan sanyi.

“Gaskiya banajin a yanzu ina da buqatar wani malamin tsubbu hajiya,saidai ban sani ba ko nan gaba bana ma fata” jinjina kai kawai hahiya habiba tayi,tana ganin ta gaya mata iya abinda zata gaya mata,sauran dabara ta rage game shiga rijiya

“Yanzun nawa ne balance dina a hannunki?” Hafsat din ta dawo dasu kan maganar kudi,abinda tafi qauna kenan.

Gaba daya ta dinga jin sassan kamar a kanta yake,sai taji batason qara koda minti biyar a cikinsa,akwai tambayoyin da take da buqatar amsoshinsu,saboda haka sauri sauri ta gama mata duk abinda zatayin ta fito,sai mimi ta maqale zata bita,dama neman kai hafsat din take dasu tace su bita,amma sai nawwara taqi bin nata

“Sai kiyita zama ai”ta fadi tana jifan yarinyar da harara,so take tadan samu ta dafa ma abbas wani abun,kafin yazo yahau kanta da qorafi.

Ruwa me zafi ta hada tayi wanka,ta yiwa mimi ma,take walwalar yarinyar ta qaru,don har gashin kanta ta wanke mata.

Cikin abaya ta shirya kamar yadda take zabinta,zataso shiga kitchen ta dafama yarinyar wani abu,to amma a gajiye take jinta,sai ta fidda snacks din da tayi ta zubo a jaka,ta zuba mata ta hada mata da lemo,sai gashi tana ci hannu baka hannu qwarya,don yafi mata indomie din da ta zame musu ‘yar kullum safe rana dare,sai randa Allah ya cishesu suka fita unguwa ko taso ta dafa wani abun.

Snacks kuwa irin haka ba samunsa sukeyi ba,muddin ba daddyn nasu bane yazo bauchin ya fita dasu wasu gureren ba.

Tana saman kujera a zaune tana sauraren hirar da mimi ke mata,gaba daya kuzarin jikinta babushi,sunayen da hajiya habiba ta kirata dasu su suketa mata yawo akai

“Kishiya/’yar aiki”,so take yamma ta qarayi ta kira anty deena ko anty madeena ko hajjaa tayi musu tambaya.

Tare da sallama ya tura qofar falon nata ya shigo,ya canza shiga zuwa wasu qananun kaya da sukayi masifar karbarsa,suka kuma fidda zatinsa sosai.

Idanunsa a kanta sanda mimi ta kamo hannunsa tana cewa

“Daddy zo muci,anty ce ta bani,yayi dadi sosai daddy,kace mommy ta dinga yi mana irinsa” biyewa yarinyar yayi,yaje ya tsugunna gaban plate din ya dauka ya gutsura yana yaba dadinsa,wasa wasa sai gashi yana ta ci,ya daga kai ya kalli widad dake zaune gefe tana kallonsu

“Ya akayi?,yau babu sakalcinne?” Ya tambayeta da sigar tsokana, murmushi ya kubce mata,itadai batasan me yasa yake mata kallon quruciya sosai da sosai ba,itakam tana gani zuwa yanzun ma ai ta isa mace

“Ga wayarki da kika manta” ya.miqa mata wayar yana kallonta,hannu biyu tasa ta karba,tama manta da ita

“Adan qara mana snacks din mana baby doll” sunan da ya fara kiranta dashi kenan,tun last week da akayi wani taro na matan police,rose ta kawo me kwalliya har gida tayi mata,ya dinga tsokanarta wai ta zama kamar ‘yar tsana,da wayo da wayo ma ya hanata zuwa taron,yace tayi kyau da yawa,bazai barta taje ba,data saka masa kukan shagwabarta sai yace

“Wa yace kiyi kyau haka?,bazan iya barinki ba kije,but i promised you zan fita dake anjima kiga gari” da wannan ya fanshi kansa.

Koda ta zuba musu snack din ta dawo zama tayi shuru,baice mata komai ba amma yaci gaba da karantar ta cikin qwarewa ta gefan idanu,ya fahimci kamar damuwa ce da ita,sannan tana yawan taba yatsarta

“Me ya samu hannun?” Ya tambayeta a tausashe bayan ya miqe yana kallonta,kai ta girgiza da sauri

“Ba komai” ta amsa masa tana dunqule hannun nata,baice komai,ya taka a hankali ya isa gabanta,ya kama yatsan yana dubawa,yanka ne,ga wajen yayi ja abinka da farar fata,sai ya daga kai ya kalleta

“A ina kikaji wannan?” Shuru ta danyi sannan a hankali tace

“Kitchen”

“Me ya kaiki kitchen daga dawowarki?” Rasa amsar da zata bashi tayi,saita zabi tayi shuru

“But na shigo sau biyu ban sameki ba kina wajen maman mimi”

“Eh na dan shiga ne” shuru yayi yana tattara maganganunta guri guda,ya fahimci tana yawan zama a wajen hafsat din,to amma a idanunsa na zahiri baiga wani hali ko wani abu da take mata da zai sanya ya hana ko ya tuhumi zuwanta ba,sannan yafi ta’allaqa zuwan nata can akan su mimi,yasan halinta sarai nason yara,saidai sauyawar yanayin nata a yau yasa yaji bai gamsu da yadda ya ganta ba

“Zanje na dawo indai da qarfe kika yanke sai an miki anti tetanus” narai narai tayi da.idanunta jin batun allura,yayi murmushin gefan baki,idan ya biyewa wannan sakalcin nata tabbas yasan ba za’a yi ba.

Har yakai qofa ya waiwayo yana kallonta,idanunsa qasa qasa,kasa jurewa kallonsa tayi tadan kauda kallonta gefe

“Ko zaki rakani,gidan suraj zanje na dubashi” kai.ta girgiza alamun a’ah,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,bugu da qari ma kuma tana son yin waya.

Kai ya mirgina hagu da dama sannan yace

“Alright,take care” yayi maganar yana aza mata nauyin kallon nan nasa,saita jinjina masa kai,ya juya ya fita.
[3/17, 1:28 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Leave a Reply

Back to top button