Arubuce Ta Ke 71
Page 71
Har ta karbi kudin ta dawo da baya,tunda dama.ba karbar kudinne a zahiri ya shigo da ita ba
“Wai niko latifa,akace widad tazo ita kadai da tsakar ranar nan,kuma na shigo banganta ba,ko tana bandaki?” Kallonta latifa tayi,banda tana ganin girmanta cewa zatayi tana cikin masai ba bandaki ba,amma saita dauke kai tana ci gaba da aikace aikacenta
“Kinsan ni bana shiga hurumin wasu,iya matsayina nake tsayawa a gidan nan,inaga da kin koma wajen ummu da kika wuceta a falo,zakifi samun bayani” ta gane sarai magana takeson gaya mata,sai kawai tace mata
“Eh,kuma haka ne” ta juya ta fita tana tabe baki a ranta tana fadin
“Koma dai meye idan tayi wari maji,oh…..yau ga ‘yarso a gida,da alama ma dai auren ne ya balle,dama waye zai dauki wannan sakalcin nata,shafaffa da mai”.
Tun tana kukan har bacci yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba,bata farka ba sai wajen qarfe uku na rana,ta miqe ta zauna tana murza idanunta,ta manta shaf a dakin ummu take,komai ya dawo mata,tabi dakin da kallo,dai dai lokacin ummun ta buda qofar ta shigo,tazo ne dama fa dubata kota tashin.
Qin yarda tayi su hada ido,sai ta kauda kanta tana kallon qasa
“Ki tashi kiyi wanka kici abinci” kai ta gyada,sannan ta zuro qafafunta qasa ta miqe,har yanzu wajen tana jinsa wani dundurus,duk da zafin zuwa yanzu ya baje.
Ruwa me zafi ta hada sosai tayi wankan,wajen yin tsarki taji ruwan dumin ya mata dadi a wajen,ta dinga kwararashi har sai data ji wajen ya saki gaba daya sannan ta fito,ta samu ummu ta aje mata doguwar riga cikin ire iren kayanta da bata gama kwashewa ba daga gidan,ta sakata tayi sallar la’asar da aka soma kira sannan ta daure ta fito falon ummun.
Su biyu ta samu,ita da anty madina,madinan batasan da zuwanta ba,don bata gidan,yanzun ta dawo ta biyo kawowa ummu sallahu data bata,baki ta riqe cikin madaukakin mamaki da kuma farinciki
“Widad din ummu….. innalillahi,yaushe kika zo,babu sanarwa bare nayi miki kyakkyawar sauka?,saida kika bari ranar da bana nan fisabilillahi” murmushi ya qwace mata,karon farko kenan tunda tazo gidan.
Tabe baki ummu tayi tana duban anty madina
“Waye ma yasan da zuwan nata?,koshi mijin nata ai baisan zata zo ba,muma ganinta kawai mukayi” gaban anty madina ya fadi
“Kamar yaya?,widad me ya faru?” Tambayar dai dai take da sukar bulalai a jikinta,ta yaya zata iya ce musu ga abinda yayi mata?,sai kawai ta fara hawaye bayan ta zauna a wajen.
“Kici gaba da kukan,karki bude baki ki fadi abinda ya kawoki,mahmudu kawai nake jira ya dawo,ai jibi yacemin zai dawo,yana hanya” cewar ummu bayan tayi qwafa,da alama ranta ya baci wannan karon akan widad din,a tausashe anty madina tace
“A’ah,ai baza’ayi haka ba,ki bita a hankali ummu don Allah”
“Yo madina meye ban mata ba?,indai ba so take na tsugunna tahau gadon bayana kuma na goyata ba,shine kawai abinda ya rage”.
A nan suka sanyata gaba da tambaya harda latifa amma ta kasa cewa komai,har ummu ta qulu ta tashi ta barsu,daga baya suma hakanan kowa ya haqura ya qyaleta.
A ranar duk wanda ya shigo gaida ummun cikin yaranta maza kawunnan widad din sai ya kirata ya tambayeta,amma ta kasa cewa komai sai kuka,haka washegari akayita fama taqi magana,tace duka su qyaleta, mahmudu ne dai dai da ita,a goben kuma ko jibi zai dawo,abinda ya sake ruda cikin widad din,amma batajin zata iya ce musu ga dalili.
Yaran gidan nata shigowa murnar zuwanta amma ta kasa sakewa,haka su Aafiya,saidai suyita hirarsu tana kallonsu,don ita a cikin damuwa take,tana tsoron gamuwarta da babanta,amma kuma tayaya zatace musu ga abinda yayi mata daya sanyata guduwa?.
Abbas kuwa umnu ce tasa muhsin ya gaya masa basai yazo ba,yayi zamansa,abinda ya bashi mamaki yadda yakejin damuwa sosai a ransa,har ya taba kuzarinsa,ya kira number dinta kuma sau babu adadi amma kullum wayartata a kashe take,inda don ta tashi ce da tuni ya tsufa a kano,kwana ukun kacal amma yana jin kamar wasu kwanaki ne masu dimbin yawa,hafsat ta lura da hakan,duk da kusan ba wani sabgar juna suke shiga ba,ta kuma ji qishi qishin zancan tafiyar widad din kano,duk da bata da tabbacin meye ya kaita,amma ko babu komai taji dadin hakan har qasan ranta,tunda dai tasan ba lafiya bace ta kawo hakan,fatanta ma ta tafi kenan,kada ta sake dawowa har abada.
Abu daya ne ya tsaye mata a rai,damuwar data fuskanci abbas din kamar ya shiga,ta rasa gane ma’anar hakan,ya fara son yarinyar kenan?, tambayar data yiwa kanta kenan,sai kuma ta qaryata kanta da kanta,ta yaya abbas din zai fara son diyar cikinsa?,banda kyau babu wani abu data ga yarinyar tana dashi,samun kanta tayi da duqufa addu’ar kada Allah ya bata ikon dawowa.
**********Dukkaninsu suna falon ummu,mahaifinta da ya kasance babba da kuma qannensa gaba daya,ummu da widad na gefe,yayin da widad din tayi kamar ta shige cikin ummun
“Tunda taqi cewa komai yaaya,me zai hana a sake kiran abbas din aji” girgiza kai alhaji mahmud mahaifin widad yayi cikin takaici
“Ya riga yace min babu komai,kuma tunda yace din babu,ita dai tana kwaso wadan nan siraran qafafuwan nata tazo,ita zata bude baki tayi mana bayani ko na tashi na babballata a wajen nan na zubar” ya fada cikin tsananin fushin da tun dazu idanun ummu yasa yake cinyewa.
Duka kallo sai ya koma kanta,cikin hargagi kamar zai kai mata duka yace
“Zaki bude baki kiyi magana ko saikin daku?” Kamar an rufto mata duniya haka taji,ga wani mugun tsoron yadda abban nata ya juye da yake ratsata,tayi qas da kanta tana hawaye, abinda ya tunzura alhj mahmud,ba wanda ya ankara sai gani sukayi ya isa kanta da wayar tv daya ciro ya fara sauke mata ita.
Kuka ta saki sosai,don zata iya cewa wannan shine karon farko da aka taba mata irin wannan dukan kaf rayuwarta,kafin a samu a qwaceta kuwa ta daku yadda ya kamata,latifa ta karbota tana boyeta cikin hijabinta ta fice da ita daga sassan ummun cikin jimami da alhini.
Kai tsaye sassan anty madina tayi da ita,tana kwance a falo ta miqe tana salati
“Dukanta dama yaaya yakeyi dana jiyo muryarta daga nan?” Anty madina ta fada kamar zatayi kuka
“Wallahi,taqi ta fadi komai ne,shi kuma ransa ya baci” rungumeta anty madina tayi tana lallashinta
“Inda kin fada widad ai magani za’a yi miki na koma meye da yake damunki” a nan hannunta latifa ta barta
“Kada kice musu tana wajena please” anty madina tace da latifa ta juya ta fice,ita kuma ta jata zuwa bedroom dinta.
Shuru ne ya ratsa falon bayan fita da widad din,zuciyar ummu duka ba dadi,dukan da mahmud yayi mata saita dinga jin kamar ita aka daka,amma kuma babu wani sauran abinda za’a yiwa widad din
“Inajin ruqiyya zan sanya azo gida ayi mata” ummu ta fada cikin karyewar murya,kai kawu maisara ya gyada
“Eh to,ya kamata a bincika ta wannan fannin ma,saboda suna iya sakata yin hakan,kuma ba kasafai hankali yake kaiwa can din ba,sai abu ya ta’azzara sannan ba fata ake ba”
Miqewa abban yayi
“Ai magana ta qare,gobe in sha Allah zanzo na dauketa da kaina muje,idanma sune sayi bayani”
“Da kanka yaaya,ka bari wasu cikinmu su kaita”
“Gwara ayi komai a gabana sa’idu don qaniyarta” har dariya taso subucewa ummu,mahmud din badai zafi ba,duk cikin yaranta ya fisu zafi,musamman al’amarin aure,baya wasa dashi.
A hankali anty madeena ta turo qofar dakin
“Kinyi bacci ne widad?” Widad dake zaune qasan carfet tana duba wasu litattafai data gani a dakin anty madinan ta amsa
“Ban kwanta ba maman walidi”
“Au na dauka mai gidan ya koya miki baccin wuri” ta fada tana duban fuskarta
“Uhmmm” kawai ta fada tana maida kallonta ga littafin,maganar da anty madinan tayi saita tuna da abbas din,yana da kirki matuqa,yana da tausayi,tanajin dadin hira dashi amma duka ya bata wannan ta sanadin abinda yayi mata.
Kaya ta zuba cikin cupboard sannan ta dawo gefen widad din ta zauna tana kallonta
“Ki shirya gobe inji yaaya abba(haka matan gidan suke kiran babanta),gobe da safe zaku gidan mai ruqiyyar cire aljanu” a tsorace ta kalli anty madina idanunta a waje
“Aljanu kuma?” Kai ta gyada cikin nuna halin ko in kula
“Eh,haka abbansu walid ya gaya min” tuni hawaye suka cika idanun widad,ta narke sosai tana kallon antyn
“Don Allah anty kice kada su kaini wallahi ni ba aljanu bane dani”
“To menene widad?,tundi kinqi gayawa kowa aka sani ko sune?,ai gwara aje can din,qila su zasuyi magana” yadda taga ta rude tana roqonta taji a ranta zasu samu bakin,sai ta gyara zamanta tana dubanta
“Kinga daga ni sai ke,ki gayamin me yasa kika taho kinji”
“Ni bana sonshi anty madina” baki anty madinan ta riqe tana kallonta cikin mamaki,lallai wani halin sai widad din,amma a yadda ta fadi maganar ta fuskanci akwai wani abu,don haka ta hadiye mamakinta tace da ita
“Bakya sonshi?,to me yasa bakya sonshi?”
“Dan iska ne” ta amsa mata kai tsaye hawaye na sauka a idonta.
Dariya ce taso qwacewa anty madeena,to amma tanaso su qarqare qarshen zancan
“Dan iska kamar yaya weedad?,me yayi miki na iskancin?” Kallon anty madeena tayi,idanunta kamar zasu fado,kunya da nauyinta takeji,amma.indai bataso a kaita wajen mai aljannu dole tayi bayani
“Tattabani yakeyi” ta qarasa fada muryarta tana rawa.
Zuwa wannan gabar dole dariya ta kufcewa anty madina,yayin da sautin dariyar ya sanya widad cikin rudu,ta dauka zataga ta saki salati tana tafa hannaye,kota rufeta da fada ko da duka ma akan ta bari ana tabata din,sai kawai taga tana dariya.
Kusan minti biyu sannan anty madeena tayi shuru tana nazari,ba shakka kuskure nasu ne,duk yadda akayi ummu bata zaunar da widad ta gaya mata meye gundarin aure ba,suma kuma bata jin wata a cikinsu tayi hakan,duk da kusan abun ma qurarren lokaci yazo,amma duk da haka alhmdlh da aka gano bakin matsalar.
A ranar dukka wata kunya anty madeena ta cire ta dinga gayawa widad komai gatso gatso,jikin widad har rawa ya dinga yi saboda mamaki,ta dinga kallon anty madeena tana mamakin haka take?
“Eh kalleni da kyau,wannan abun da kika gudowa,kowa yana yi indai mata da miji ne an daura musu aure,harni kaina da kike gani” kunya ta sanyata cusa kanta a cinyoyinta ganin anty madeena din ta danganta abun da kanta,ta kasa daga kanta,sai kuma kwanyarta ta shiga mata research,me yasa mommy hafsa ta dinga jaddada mata kada ta yarda ya taba ko yatsarta yadda ummu take gaya mata sanda tana gida,meye dalili?,tambayar data rasa gano amsarta,sai kawai ta daga kai ta fuskanci anty madeena taga gwara ta tambayeta…….
[3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*