Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 5

Sponsored Links

Idanu ya zuba mata yana kallonta,kullum sake canza masa takeyi,tana dada girma tana kuma sauyawa,yana kuma sake jinta a ransa,a haka ta qaraso wajen,amma ko sau daya taqi kallon sashen da yake zaune ma.

“Ina yini?” Ta gaidashi tana rusunawa kadan,saidai bashi take fuskanta ba,wani sashe na daban take fuskanta

“Lafiya lau widad,ya shirye shiryen sallah?”

“Lafiya” ta amsa masa a cunkushe tana duban ummu

“Ummu yunwa nakeji,me aka dafa?” Abinda ta tsana ummun ta fara yi wato miqewa,da alama zata basu waje kenan,gamin haka sai tayi wuf ta riga ummun miqewa,daga kai tayi ta kalleta

“Ki zauna, na’eema zata kawo miki abincin yanzu” yadda ummu tayi maganar babu wasa saman fuskarta ya sanya ta koma jiki a mace ta zauna tana tara hawaye a idanunta,tana kallonsu suka fice daga falon.

Ajiyar zuciya ummun ta sauke bayan barinta wajen,wanan wanne irin abune haka?,me yake faruwa ne?,har yanzu komai yaqi ya canza tsakaninta da mahfood din?’.

Cikinsu shi da ita ba wanda ya iya cewa komai,har na’eema ta kawo abincin ta ajjiye ta juya ta fice,a hankali yasa hannu ya jawo abincin gabansa sannan yace

“Kamar yunwa naji kince kina ji ko?,matso kici abincin kada ya huce” ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata cin,yayita fama amma qememe tayi biris,dole yaja ledar da yazo da ita zuwa gabansa

“Ga kayan sallah nan,da fatan za’ayi kwalliya me kyau” sosai ya sake quleta,don tana da son kwalliya da gayu sai ya maidata wata qwalamammiya?,bashi da aiki sai kawo mata kayayyaki,yadda taji haushinsa sosai a yau din har taji tana qwarin gwiwar gaya masa abinda bata taba gaya masan ba,daga fararen manyan idanuwanta tayi ta azasu a kansa

“Nifa bana so,banason komai naka,sannan ma ni ba wani auren dangi da zanyi,ni ba yanzu ma zanyi aure ba,don Allah ka rabu dani,ni…..bana sonka” dai dai lokacin da alhaji mahmud salim mahaifinta yayi sallama cikin falon ya kuma sanyo qafafuwansa.

Idanu yake bin widad din dashi,yaji kalamanta guda biyu na qarshe,zallar bacin rai ne kwance akan fuskarsa,ita kanta suna hada ido da abban nata ta sadda kanta qasa gabanta yana tsananta faduwa,mahfood kuwa miqewa yayi yana masa sannu da zuwa

“Zauna mahfood……me naji kina fada widad?” Tsoro da firgici suka hanata yin koda qwaqwqwaran motsi bare ta amsa shi,cikin tsawa ya sake maimaita mata tambayar,saita ida rikicewa gaba daya,ta kuma saki kuka a lokaci guda,saboda sam sam bata saba da irin wannan tsawar ba.

“Dan uwanki kike gayawa bakiso saboda baki da kunya?,wato kin fara girma kenan widad?” Ya fada cikin mugun fada da kuma daga murya,sautin muryar tasa da ya isarwa da ummu saqon akwai abinda ke faruwa a falon,taji kuma ta kasa nutsuwa saboda kama sunan shalelenta da taji anyi,saita yunqura ta miqe tana duban na’eema

“Ki qarasa hada muku kayan waje guda ki maida daya dakin kafin gobe gidan ya sake cika,ina zuwa” ta fada tana takawa a hankali saboda dan ciwon qasa da take fama dashi lokaci lokaci.

Isowarta wajen kadai tafahimci abinda ya faru,fada sosai abban yake zuba mata,da alama ransa ya baci sosai

“Mahfood dan uwanki ne,da kike cewa kuma bakya sonshi gwara ki koya tun wuri,don baki da miji sai shi,shi zaki aura ki jini da kyau” ya fada yana kama kunnensa da hannunsa guda daya

“Tashi ki bani waje” ya fada a tsawace,ta gudu ta miqe tayi hanyar dakinsu fuskarta jiqe da hawaye,saman gadonta ta fada wanda ba kasafai ma take kwana a dakin ba,koda yaushe tana maqale da ummu,a dakinta take kwana,koda tana wajen alhajin to itakam tana dakin nata,haka zata hada duka filallukan dake saman gadon ta qudundune a ciki saboda shegen tsoron da take dashi,bare ma ba kasafai ummun ke barinta ba,wani lokaci ma bata sanin bata dakin idan baccinta yayi nisa ko kuma nauyi.

Kan mahfood a qasa sanda abba ke bashi haquri

“Nasan harda quruciya abba,har yanzu shekararta sha hudu”

“Da kuma sakarci ba”

“Ayi haquri” ya sake fada kansa a qasa,sannan ya miqe yayi musu sallama ya fice daga sassan ummun yace zai shiga cikin gidan su gaisa da sauran mutane.

“Ka dinga bin al’amarin nan a hankali mahmudu,wannan fadan duka ba shine ba” ummu ta fada bayan dukkaninsu sun zauna

“Ummu abunne yake dauren kai,anata cewa quruciya ce,to amma tana sake girma tana sake qinsa?” Kai ummun ta jinjina,ita kanta bataga na meye abba din sai ya matsa har haka ba,shi zumuncin da yakeson a qarfafa a kuma sake qullawar ai ba dole sai ta hanyar hada aure ba,inda akwai wata diyar gareshi wadda tadan tasa kamae widad din ma ita zaifi mata sauqi ya maida alqawarin kanta,bata qaunar wannan rikicin da aketa yi da widad din

“Kasan haduwar jini ne,idan kuma Allah bai sanyata tsakanin bayinsa ba babu yadda za’ayi”

“Haka ne,Allah yayi mana mafita”

“Ameen ya hayyu ya qayyumu” ummun ta amsa masa,sai ya miqa mata babbar jakar da yasa aka shigo da ita,wadda ke shaqe da kayan sallah na mutanen da ya saba yiwa duk shekara,wanda yaran gidanne ‘ya’yan qannensa da suke sa’annin widad,wasu kuma qasanta a shekaru,ga kuma nata na musamman ita da widad din da alhaji

“Alhajin baya gida ne?”

“Kasan yau daren sallah,suna can fadar mai martaba,har sai an sanar da ganin wata sannan” kai ya jinjina,don kusan al’adar sa ce duk shekara

“To Allah ya dafa mana” ya amsawa ummun.

Kuka take sosai da hawayen daya fara jiqa pillow din da take kwnace akai,juyin duniya na’eema tayi ta tashi tayi haquri ta dauki abincinta taci amma ko kulata batayi ba,sosai take jin qin mahfood din cikin ranta,ko sau daya bata taba jin tana sonshi ko yana burgeta ba,yana da kirki ta sani,amma ita ba wani magana datayi kama data aure a tsakaninsu da take jin zata yiwu.

Har abbanta ya tafi tana kwance tana kuka,ummu na falon bata motsa ba,duk da na’eema ta gaya mata,bataso taje taga yanayin da take ciki zuciyarta ta karye ta gaza bata qwarin gwiwar yiwa mahaifinta biyayya,wannan yasa tayi zamanta a falo,duk da zuciyar da hankalinta na kanta.

Duk wanda ya shigo nemanta sai tace masa kawai tayi bacci,wasu su zauna suyi hirarrakinsu wasu kuma su wuce,tana nan zaune har qarfe goma na dare,zuwa sannan juriyarta ta qare,sai ta miqe ta shiga dakin da kanta.

Tana kwance rub da ciki har yanzu,saidai ba zaka iya tantance bacci take ko idanuwanta biyu ba,ta qarasa a hankali tasa hannu tana taba kanta gami da kiran sunanta,sheshsheqar data sauke hadi da ajiyar zuciya ya tabbatar mata idanuwanta biyu

“Meye haka wai widad?,tashi mana” ta fadi tana qoqarin dagota ta zaunar da ita,sanda ta kalli fuskarta sai zuciyar ummun tayi rauni,kallon marainiya takewa widad shine dadin abinda yasa batason komai ya sameta mara dadi,yarinyar da batasan dumin uwarta ba?,gaba daya fuskar tata ta tashi ta kuma yi jazur da ita abinka da farar fata

“Kukan kike har yanzu kamar wadda akace mata zata mutu?,tashi ki wanke fuskarki kici abincin naki”

“Ni banaci” ta fada muryarta na rawa hawaye yana sake barke mata,sai kawai ta fada jikin ummun tana sakin sabon kuka,har cikin ranta ummu takejin kukan,sai ta fara lallashinta,da qyar ta ciyo kanta taje ta wanke fuskar ta sanyata a gaba taci abincin,da qyar tayi cokali biyar tace ta qoshi,ummun taso sanyata a gaba su wuce dakinta ta kwana kamar yadda ta saba amma tace anan zata kwana,tunda ga na’eema,sannan Aafiya ma yau a nan zata kwana,dole ta rabu da ita tabar musu dakin bayan ta ja mata kunnen kada ta sake irin wannan kukan,ta kwantar da hankalinta kuma.

*_W A S H E G A R I_*

Kamar yadda suka saba kusan kowa da kowa ake tafiya sallar idi a gidan,akwai wadatar ababen hawa,kowa zai diba iya mutanen da motarsa zata iya dauka,tun sassafe kowanne sashe suke tashi yaran suyita shiri,iyayen kuma suna qoqarin qarasa abincin sallah wanda idan an dawo saga udi za’a dira akai a fara ci da kuma rabo,to hakanma wannan karon ta kasance,har sassan ummun hayaniya ce ke tashi,saidai banda widad dake nannade a bargo,ko motsawa batayi ba bare ta shirya,sunyi sunyi ta tashin amma taqi kula kowa,ummu kuma tunda ta fito da asuba ta tadasu sallah bata kuma fitowa ba,sai alhaji ya gama shirin idinsa.

Karo na biyu latifa fa dawo,wadda itama ta shirya fes da ita cikin dinkin sallarta,duk sallah sai an mata dinki kamar kowanne yaro ko jika dake gidan,dinkinta masu kyau da tsada har kala hudu ko uku

“Widad din ummu,kiyi haquri ki tashi ki shirya,kinga kowa ya gama shiryawa,yanzun nan zakiji an fara tafiya”ta fada cikin lallabawa,bakam tayi kamar bata a wajen,duk iya dabara da hila ta latifa haka tayi ta haqura,daga qarshe dai haka suka tattara suka tafi sallar suka barta.

Bayan ficewarsu ummu ta fito

“Ja’irai,tunda naji shuru nasan sun tafi,kafin su dawo su hana mutun sakat” tayi maganar tana tura qofar dakin,sai idanunta ya sauka kan tudun bargon dake kan gado,cikin ranta zuciyarta ta bata mutum ne,sai ta qarasa tana yaye bargon.

Salati ta saka ganin widad din kwance tana sharbar kuka

“Na shiga uku ni laila?,wai dama baki haqura ba widad?” Hankalin ummun ya tashi sosai,haka ta sanyata a gaba sai data tashi tayi wanka ta kuma zuba mata abincin safe taci,tana gama cin ta koma ta kwanta

“Falo zaki fito ki kwanta,bazan barki ki sake kwanciya ba”

“Ki qyaleni kawai ummu,tunda abba baya sona” ta fada da yanayi na quruciya tana kuma sake sakin kuka,baki ummun ta saki,tana magana kamar wata babba?,duk yadda taso ta fiddota amma taqi sai kwanciya.

Koda aka fara dawowa daga idi tuni gidan ya fara cika da jama’a kamar yadda aka saba duk shekara,jikoki sun fara hallara,kowa fuskarsa da zuciyarsa cike da walwala da kuma farinciki,lokacin sallah lokacine na farinciki,amma wannan shekarar banda widad din,don kuwa duk budurin da akeyi tana kwance a qule a daki,da yake tana da kirki qwarai da son yara qananu,kowa yazo sai yace ina widad,saidai ummun tace bata da lafiya tana daki tana bacci.

Duk yadda jikokinta ke karakaina a falon amma rashin walwala da fitowar widad din sai taji komai ma baya tafiya dai dai,maganar mahfood din taji itama ta soma fita mata a kai,gwara abar zancan,idan yaso a gwada bata wani,duk da abban nata ya gaya mata ita din bata son auren zumunci,to amma maiyuwuwa ta haqura idan aka gwada mata wani indai jininsu yazo daya,da wannan maganar a ranta tayita dakon shigowar alhaji don suyi maganar ita dashi.

Bai samu shigowa gidan ba sai yamma liqis,zuwa lokacin manyan yayyensu maza dake sa mota sun debi yaran gidan da yawa zuwa guraren wasannin sallah da shaqatawa,gidan sai yayi shuru,sai dai daikun yara dake shigowa su fita,har sannan widad din tana daki a kwance,duk da tulin kayan sallar da take dashi bata sanya ko guda daya ba bare ta fito.

Sai data gabatar masa da abinci yaci ya qoshi sannan ta fara magana dashi,yayi shuru yana sauraren ta har ta gama bayananta gaba daya,sannan yayi gyaran murya yana dubanta…….

*_TOFA,TAFIYAR BA’A FARA BA,KO SHIMFIDA BAMU GAMA BA_*

*_INA SAKE TUNA MUKU,IDAN KIN KARANTA HANGEN DALA,TO TABBAS SHAFAR MAI NE,WANNAN TAFIYAR TA FISHI ZAFI AMFANI DA KUMA DARUSSA_*

*_LABARI NE DAYA QUNSHI TSANTSAR KISHI,KAIDI MUGUNTA DA KUMA SIHIRI_*

*_MUGUN TAKU IRIN NA BAQAR KISHIYA_*

*ZALLAR RAYUWAR GIDAJENMU TA GASKE*

*MADARAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUCIYA BURGEWA DA BARWA RAYUWA DARASI*

*GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*

0022419171
Maryam sani
ACCESS bank

*Saiku tura shaidar biya ta nan*

+234 903 318 1070

*Masu tura katin waya kuma zasu tuntubi wannan number*

09166221261

*Yan nijer zaku tuntubi wannan number*🇳🇪🇳🇪

+227 90 16 59 91

*Thanks for choosing us**H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button