Arubuce Ta Ke 48
Page 48
Tana cikin wannan mitar aka buga qofar falon
“Waye na?” Ta fada cikin fada fada,ranta fal quncin mimin ta karya mata budget
“Nine,sale ne”
“Shigo” ta fada kanta tsaye bayan taja tsaki,duk da tasan abbas baison haka,don baya bari a shigo masa har inda iyalinsa suke kai tsaye.
Da sallama yaron ya shigo yana sunkui da kai,don bai saba shigowar ba,ga hafsat din da daurin qirji,sauqinta akwai t-shirt a jikinta,a samanta taja zanin ta daura
“Ina kwana hajiya”
“Lafiya lau ya akayi?”
“Eh dama me yiwa engine service ne yazo,za’a bada kudin a siya kayan aikin,sai mechanic din da zai dauki motar oga ya kaita garage za’a mata service itama” tsuke fuska tayi,don tasan kudaden daya wara ya bata saboda a duba motar da engine din suna da yawa
“Bakaniken ya dauki motar,amma shi me yiwa engine service kace ya barshi kawai,sai mai gidan ya dawo”
“To….amma engine din yana bada matsala fa,jiya ma…..”
“Abinda nace kayi zakayi ko raayinka zanbi?”
“Sorry madam” ya fada yana juyawa yabar falon,cikin ransa yana Ala wadai da dabi’arta,sarai yasan an bata kudaden,fitar dasu ne ba zata iya ba.
Tsaki taja tana duban yaran
“Ku wuce muje na dafa muku abinci” jin xancan abinci sai mimi ta ware,sukabi bayanta zuwa kitchen din,saidai tana ganin ta buda kwalin indomie yarinyar ta bata rai,ta gaji da ita,don jiya da daddare ma ita ta dafa musu
“Indomie mommy?,bana ci nidai” cikin takaici ta kalla yarinyar,ubansu ya batasu da kala kalar abinci,ita kuwa ba zata iya dorama kanta wannan wahalar ba
“Ba zakici ba ubanme zakici?”
“Irin abincin gidan hajiya”
“Meye abincin gidan hajiyan?”
“Tuwo ko dambu”
“Nabi tuwon da gudu,zakici ubanki wallahi,idan bakici ki zauna haka,yunwar cikinki” saita bare kwalin ta dauko guda biyu ta zuba a tukunyar.
Kusan dai a gantale suka tsakuri taliyar,bata tsaya ta mata ma dahuwar arziqi ba bare darajar hakan ya sanya suci da yawa,daga qarshe ma.idan ta debo ta baiwa nawwara sai ta tankwabe hannunta,da yake ita din tafi mimi fada,sai ta tattarasu ta barsu ta shiga sabgarta,dole da yunwa ta ishesu suka dawo suka ci a haka bayan tayi sanyi.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢ Hirar da suka sha da ummu da abbanta na kusan awa biyu ya sanya tajita tadan sake,sai kuma dan motsin da take jiyowa lokaci lokaci cikin gidan ya sanya bata matsu da yawa ba,ta dan saki jiki ta soma kade dakin da gyarashi kamar yadda latifa ta koya mata,sannu a hankali sai gashi ta gyara dakin fes,sadai fa tadan dauki lokaci,ta shiga toilet ta wanke fes,ta kama qugu tana dariyar farinciki na ganin yadda ta gyara dakin kamar ba ita ba,ta kama baki tana murna
“Ashe dai na iya,amma ummu ke hanani,bari na kira umma latifa na bata labari” ta koma gefan gadon tana kaffa kaffa kada ta bata zanin gadon data d’ameshi da kyau,ta fara duba number latifa wadda basu jima da gama waya da ita ba itama,Latifa na daga wayar ta fara bata labari
“Iyeee shalelen ummu,girma yazo,haka akeso,kiyita tsafta kamar ummunki,saura girki” dariya tayi tana sake bata labarin wahalar data sha,latifa na biye mata,ummu ja gefansu tana murmushi,duk da rabin hankalinta nakan shalelen tata.
Wunin ranar bata wani ji yunwa ba,koda taji yunwa dinma tea ta hada tasha ta kwanta abinta.
Kafin magariba tayi wanka,ta shafe jikinta da turarukan da latifa ta hado mata a kayanta,kusan sai data shafa kowanne turare,har ya soma yawa ya fara hawa ka,kowanne mai sanyi da dadin qamshi ne,amma yawan da yayi yasa ya jirkita,amma ita ko a jikinta,wata dubai abaya ta saka,ta dawo falo ta maqale jikin window tana leqen harabar gidan,gabanta yana dan faduwa kadan kadan,saboda ganin magariba ta gabato babu shi ba alamarsa.
Ana qwala kiran sallar magariba motarsa tana shigowa cikin gidan,samuel ne ya kawoshi,shi ya koma shi kuma ya shigo ciki.
“sannu da zuwa” ta furta tana jan dankwalinta daya zame saboda santsinsa daya hadu da sulbin gashinta,ta miqe tsoron nan nata yana bayyana,tanason karbar masa ledar daya shigo da ita kamar yadda ta saba duk sanda taga kaya hannun babba,amma tana shakka matsawa inda yake,a haka har ya qaraso ya ajjiye,ya zauna yana tube takalman qafarsa
“Lafiya kika wuni?” Kai ta gyada masa,sai yadan lumshe idanu yana gyada kai,qamshin jikinta gaba daya ya cika falon,kamar anyi barin turare
“Samomin ruwa nasha” hanyar kitchen din ta kalla,baiyi duhu sosai ba,don haka da sauri tayi hanyar,a nufinta tayi sauri ta dawo kada wajen yafi haka duhu.
Binta yayi da kallo,ko yaushe ya kalletan sai ya dinga jin mamaki na shigarsa,wai matarsa ce wannan,ta dawo da ruwan ta russuna ta miqa masa kamar yadda ta saba yi tun a gida.
Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu.
Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta
“Subhanallah” sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa
“Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki” kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?.
A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi
“Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje” yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan.
Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara’a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata.
“Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?” Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a’ah
“Ko amaryar ce da kanta?” Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha’awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita
“Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya” bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi
“To ina zuwa” ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito.
A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu
“Gashi” ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito.
Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki
“Zonan” yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa
“Dauke abinki ki tafi dasu”
“Banaso” ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta
“Bake ta bawa ba?”
“Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu” dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi
“Zauna” yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi.
“kinsan amfanin wadan nan kayan?” Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba
“Oya….open your mouth,ban jiki ba”
“Ban sani ba,kayan ‘yan iska ne fa” tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka.
Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba.
“Kwashesu ki tafi” ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta.
Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe
“Lallai matar nan ma ‘yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?” Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba.
°°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama ‘yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida.
To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin.
Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon.
Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi.
Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai.
_wannan kenan_
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)