Arubuce Ta Ke 47
Page 47
Komai nasa ya tattare a falon,abinda yasa widad ta fahimci ya gama zamansa a nan kenan
“Muje na rakaki daki,zan kwanta” jiki a sabule ta miqe din,yana gaba tana binsa a baya har zuwa dakin,tana zaune a gefan gado ya zuzzuge dukka glasses na window din sosai,ya kunna ac ya daidaita mata temperature dinta,duk abinda yake tana binsa da kallo,duka jikinta babu dadi,dan wankan da takeyi ma data yiwa anty deena alqawari bata samu yi ba,ta kuma riga ta saba da yinsa zuwa yanzu,ya tako a hankali yana ajjiye remote din acn sannan yace
“Kin iya addu’ar kwanciya bacci?” Kai ta gyada masa
“Da kyau,kiyi kafin ki kwanta” ta sake gyada masa kai,ba wannan bane a gabanta,tana qiyasta yadda abubuwan tsoro zasu kawo mata farmaki cikin dakin idan ta kwana ita kadai,babu abinda ranta da zuciyarta basu kawo mata ba,batasan sanda tayi wuf tabi bayansa ba sanda taga ya nufi qofa.
Tsaiwa yayi yana kallon ta,hawayen nan da basu da wahala a fuskarta suna fita
“Mene kuma?”
“Tsoro nakeji”
“A’ah….wai meye abun tsoron ne?” Kasa amsa masa tayi,illa d’ari d’ar da taketa yi,shuru yayi ya zuba mata idanu,yanason tuna abinda ya dace yayi
“Yanzu me kike so?” Saita kalleshi da dara daran idanunta masu haske sosai,bakinta yana dan rawa,ta kasa cewa komai,ganin haka sai yace da ita
“Muje dakina ki kwana” da sauri ta girgiza kai tana fidda ido waje
“To ki koma dakinki ki kwana” ya sake bata second option,nan ma ta girgiza kanta da sauri.
Ranshi ne ya baci,har yaja tsaki a fili,wacce irin yarinya ce ita?,duk option din da aka bata bai mata ba?
“Ba zaki dakina ba,bazaki dakinki ba,to zaman gadinki zanyi?” Ya tambayeta emotion din fuskarsa yana sauyawa zuwa bacin rai.
Maimakon amsa saita sakar masa kuka sosai,abind ya hasalashi ya sakar mata tsawa,tsawar data sanyata durqusawa a wajen tana kuma sakin wani kukan tare da kiran sunan ummu.
A take jikinsa yayi sanyi,yaga kuma rashin kyautawarsa muraran
“Sai ka dinga haquri da ita,kana kwatanta mata abubuwa,bata zama cikakkiyar budurwa ba,da quruciya har yanzu a tattare da ita,to zaka yita ganin yarinta,sai kayita haquri kana gyara mata,amma data gane abinda kakeso da wanda baka so,zakaji dadinta fiye da kowa” maganar da sukayi da hajiyansa ta qarshe ta dawo masa,wannan yasa temper dinsa ta sauka,ya tako a hankali ya tsaya a gabanta
“Get up….tashi” ya fada a tausashe,saita miqe din tana sanya gefan dankwalinta tana goge fuskarta,duk da hawayen sunqi tsaiwa
“Yanzu ya kikeso ayi?” Ya tambayeta yana narkar da idanunsa cikin nata,itama kallonsa takeyi,ya fuskanci ko a jikinta bata jin nauyin kallon qwayar idanunsa,ta gaza bashi amsa sahihiya,ya kuma gane tsoron hada daki takeyi kawai dashi,kamar kuma yadda take tsoron kwana ita kadai,tsahon wasu sakanni da shuru ya biyo baya sai ya gyada kai
“Shikenan,ki kwanta a daki,zan zauna a falo har kiyi bacci” a hankali ta gyada kanta,hakan yayi mata,yafi ace ya koma dakinsa ya kulle ba kowa a kusa,duk da dakunan kusa da juna suke.
A gaba ya sanyata har dakin nasa,ya dauki duk.abubuwan da zai dauka ya ajjiye a falon,ya maidata dakin ya tsaya harta kwanta sannan ya ja mata qofar ya dawo falon ya zauna saman kujera hadi da jingina filo bayansa da gefansa don yafi jin dadin zama,sannan ya buda wani qaramin littafi ya soma dubawa.
Fakare tayi cikin bargon data lulluba har kanta tana rarraba ido,lokaci lokaci tana dan jiyo motsinsa daga falo,wannan ne ya sanya mata nutsuwa,har sannu a hankali bacci ya saceta ba tare data sauya koda kayan jikinta ba.
Awa guda y bayar sannan y shigo dakin,ganin qarar qofar dakin bai sanyata ta motsa ba ya fahimci tayi bacci,sai ya koma da baya yana sake rufe mata dakin,ya koma falon ya kwashe kayayyakinsa ya wuce nasa dakin
“Case closed” ya fada a ransa,amma yana tunanun haka zasu maimaita da ita gobe?,kenan wani sabon duty dinne ya sameshi
“Ya rabb” ya furta yana furzar da iska daga bakinsa,ya ajjiye komai a muhallinsa y wuce bandaki don yayi wankan da rigimarta ta hanashi yi.
Tunda gari ya waye ta dawo falon ta zauna,bayan ta dafa ruwan zafi kamar yadda latifa ta koya mata,ta hada da cup da tea flask din ta dora saman table,tun daxu take jiyo motsinsa cikin dakin,amma bata yi qoqarin shiga ba,saidai ta zubawa qofar dakin idanu tana qiyasta sanda zai fito.
Yana taba handle din ta sake zubawa qofar idanu,ya fito a hankali cikin police uniform,sun masa wani irin kyau kai bakace uniform na ya sanya ba,haiba da kwajininsa sun fita sosai,tsayayyen namiji da siffar qarfi ke bayyana a halittarsa,qafafunsa saye cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba.
Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace
“Ina kwana?” Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace
“Lafiya lau….” Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta
“Kinci abinci ne?” Kai ta girgiza
“Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za’a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?” Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora
“Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga” ya fidda kudi ya ajiiye mata
“Sai na dawo” ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi
“Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya” ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta
“In sha Allah” yace mata sannan ya fita.
Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri.
A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga
“Hello…..ina abban mimi?” Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba
“Mommy ina kwana?,inasu mimi?” Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba
“Lafiya lau….ina abban mimi?”
“Ya fita mommy”
“Jiya a ina kika kwana?”
“A dakina”
“Shi kuma abban nasu fa?”
“Ban sani ba,na rigashi yin bacci” gaban hafsat ya fadi
“Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?” Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din ‘yar iska ce
“Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office”
“Karkimin qarya fa widad?” Kai ta langabe muryarta nayin sanyi
“Allah ki tambayeshi ma” ta furta zuciyarta na addu’ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari.
Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya
“Shikenan,ina fata baki manta komai ba?”
“Eh momy”
“Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula”
“To mommy…..mommy amma ki bani mimi ko….” Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska
“Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba” sai kuma murmushi ya subuce mata
“Anty ummee kinyi a rayuwa” ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi a rufe,sai taji kamar ta tafi kenan.
Tana cikin maida kudin kira ya sake shigowa mata,ganin sunan mai kiran saita hade ranta,taja tsaki ta dauke kai,anty shafa ce yayarta,tasan kiranta baya rasa nasaba da zancan kudi,kullum zancanta na ta kawo wani abunne,ita kuwa kudinta bana tabawa bane,don haka ta maida wayar silent ta miqe tana kallon agogo.
Sha biyu saura na rana,ko brush batayi ba bare ayi zancan breakfast shara ko gyaran gida,tana son abbas tana son ta kasance ko yaushe dashi,to amma idan suna tare irin wannan sakewar ce bata samu,shi yasa ba kasafai take damuwa da nisantar juna a tsakaninsu ba.
Tunawa tayi tabar yara a falo,har tayi hanyar toilet saita sauya akalarta zuwa falon,tana addu’ar Allah yasa basuyi mata barna ba.
Tun daga nesa ta hangi mimi tayi dafa’an a tsakar falon,ta fasa kwalin cornflakes ta cika madara kwano ta dama da ruwa tana ta durawa nawwara,tsawa ta kwaza mata,sannan ta fidda danu tana duban kwanon
“Innalillahi” ta fada da qarfi,sannan ta nufi mimi da sauri, batayi wata wata ba ta gabza mata mari,gaba daya yarinyar ta jawo mata asara,kudin da ya bayar a siya wadan nan kayayyakin ta lankafesu,ta fitar da tsohuwar madarar daya taba siyawa yaran tasu tashan tea,ta ajjiye a dining tace suyi amfani da ita kafin ya dawo,yanzu ta daga madarar dukanta ta zazzage musu.
“Uban wa yace ki taba?” Ta fada tana kama kunnen yarinyar,cikin kuka tace
“Mommy,nawwara ce takejin yunwa” sai lokacin ta tuna bata basu komai ba ashe,ta saki kunnen nata tana huci
“Ba sai kizo ki gayamin ba,kin tashi kin cuci mutane kin musu barna,matsa ki bani waje” haka ta sanya tsintsiya da ta gyara gurin,tana yi tana mita,yaran na rabe a gefe,mimi na hawayen murde mata kunnen da tayi.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)