Arubuce Ta Ke 23
Page 23
Duka dai yanata juya yadda abubuwan zasu kasance har ya gama abinda yakeyi yazo kwanciya,sai ya kauda wanann tunanin ya sake maimaita kiran hafsat amma kamar dai ko yaushe,sai abun ya shiga daure masa kai da kuma bashi tsoro,don haka ya sauya akalar kiran zuwa ga wani constable dake area din nasu,ya aikashi yaje gidansa ya duba masa lafiyarsu,cike da girmamawa ya amsa masa ya kashe wayar ya zauna yana jiran feedback.
Bai haura minti biyar ba yayi kiransa
“They’re fine sir”
“Are you sure?”
“Yes sir” ya sake tabbatar masa,sai yaji ransa ya baci,ya kashe wayar ya ajjiye yana gyara kwanciyarsa gami da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa
“Dole ya dauki mataki akan hafsat din,abun nata qara gaba yake,wannan zallar raini ne” ya fada a ransa.
Washegari daga strolling ya wuce gidan hajiya a qasa,duk da ‘yar tazarar dake tsakaninsu sai gashi yaje,saidai ya hada gumi sharkaf kafin ya isa din,hajiya nata masa sannu da fadan bai ganin nisa yayo wannan tafiyar a qafa?, qaramin murmushi ya saki
“Hajiya kin manta aikina ne?,tafiya tsaiwa wahala da yunwa duka an koyamana juriyarsu”kai ta jinjina kawai
“To Allah ya bamu dacewa” muneera ce ta hado masa breakfast kamar ko yaushe,yau din hajiya bata iya bari ya gama cin abincin ba ta jeho masa tambayar
“ya ake ciki?,kaje kuwa?” Kai ya jinjina
“Naje hajiya”
“Ina fatan komai yayi?” Me zai iya cewa hajiya,bashi da wata amsa data wuce cewa
“Alhamdulillahi” ya amsata yana kurbar tea dinsa,sai ta saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,ta sauke ajiyar zuciya
“Inaso ayin auren nan a nan kurkusa abbas indai zai yiwu” da qyar ya hadiye bread din dake bakinsa,sannan ya daga idanunsa yana duban hajiyan
“Kamar nan da yaushe kike so hajiya?”
“Zuwa yaushe zaka shirya dai?” Shuru ya danyi,tunda ta magantu lallai da gaske tanaso ayi a kusa din,koda yaushe babban burinsa shine ya cika umarninta
“Kada ka damu,kayi tunani a hankali,ko bayan ka koma ne sai ka fadi zuwa lokacin da kake ganin ka gama shiryawa”
“To hajiya” ya fada cikin girmamawa,saidai tuni kwanyarsa tayi nisa wajen tunanin yadda abubuwa suke ta sauyawa suna zuwa masa a bazata.
~~~~~~~~
Sai la’asar ya koma gida,kai tsaye ya shiga bandaki yayi wanka,bayan ya fito ya fito zuwa sassanta don ya samu Black tea,cikin mintuna ya hada ya dawo falon da zummar zama,amma sai ya dinga jin kamar hayaniya hayaniya daga qofar gidan,sai ya miqe ya yaye laluben window din da ya bulla har harabar gidan,harabar gidan fes babu kowa hakanan babu komai,amma qoramar qofar gate din gidan a bude take,ya kuma tabbatar hayaniyar a qofar gidan sosai take tashi,don haka ya ajjiye cup din ya zura slipper dinsa da ya cire ya doshi qofar fita.
Tun kafin ya qarasa ya dinga ji kamar muryar hafsa,amma sai ya qaryata kunnuwansa,tunda yasan bata nan,saidai yana dosar waje kunnuwansa na sake ji masa muryar tata.
A hankali ya buda qofar ya fita,take idanuwansa suka gasgata masa abinda kunnuwansa suka ji,zallar mamaki ya kusa kasheshi a wajen
“Hafsa a bauchi?” Ya yiwa kansa tambayar da bai san amsarta ba,yana sake zubawa hafsa din idanu,wadda bata ma fahimci ya fito ba,ta taqarqare sunata sa’insa ita da wani,nawwara na hannunta,mimi na tsaye gefanta tana riqe da hannunta,maqotansa biyu keta bada baki,yayin da wasu matasa dake sana’ar business center a wani dan container irin na mtn gaban gidan kadan suma suka iso wajen.
Yana fitowa daya daga cikin maqotan nasa ya ganshi,da sauri yace
“Yauwa alhmdlh,ga mai gidanta nan ma ya fito,mun dauka ai baka nan shi yasa tun dazu bamu yimaka magana ba” dukka idanu suka waiwayo suka zuba masa,take yaji ya muzanta,ya aro jarumta da juriya ya qaraso wajen yana riqe da hannun mimi,wadda tunda ta ganshi ta sheqo da gudu ta maqale ubanta.
Qarawa yayi ya miqa hafsa din ita yana cewa
“Wuce gida” saboda ganinta cikin mazan ba qaramin quntata masa rai yayi ba,ga kuma baqincikin tahowar da tayi babu izini ko shawara dashi.
“Alhaji kayi haquri,amma babu inda zata saita cikamin kudina,zata gane ni din matsiyaci ne na ainihi” fuska a daure abbas ya juya yana dubansa
“Kaga,barta ta tafi,za’a biyaka koma nawa ne”
“To shikenan alhaji” sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin
“Me ya faru?” Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa
“Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba” cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa
“nawa ne cikon kudin naka?”
“Dubu biyar ne ranka ya dade” mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa
“Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta” maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta.
Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv
“Ku kalli cartoon ina zuwa” ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki.
Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi.
Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la’asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka
“Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?” Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa
“Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za’a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?” Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?.
“Kinsan abinda kikeyi kuwa?” Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta
“Na sani mana” ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora
“Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar” sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa
“Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din” daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba.
Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he’s serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa
“Mu bawa juna mamaki dai” ta sanya hijabinta ta tayar da sallar.
Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa
“Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya” saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart.
Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta.
Bayan sun gaisa take ce mata
“Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa” take ranta ya baci fara’arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi
“Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi” takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa
“Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci” murya a cunkushe tace
“Nawa ne kudin?”
“Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata”
“Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu” bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili.*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks:Huguma*