Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 12

Sponsored Links

Page 12

*Widad*

Dole qanwar naqi ta fara sakin jikinta,duk da cewa gaba daya hankalinta yana kan gida,abu daya ke mata burki ya sanya mata ko kwanto da kuma qaunar komawa idan ta tuna case din data bari a gidan.

Satinta guda uncle muhsin ya maidata makarantar dasu nujood ke zuwa,baiyi shawara da kowa ba,hakanan bai gayawa kowa ba,yayi dai karambani ne,yana fatan karambanin nasa ya samu nasara.

Makarantar boko ce hade da islamiyya,qarfe hudu ake tashi zuwa biyar yawanci duka yara suna gida,sosai widad tayi murna,don ita dinma akwai son karatu,cikin sati guda ta sake sosai abinta,zaka dauka tsohuwar daliba ce.

**********

K’arfe takwas da rabi na dare ne,bayan su widad sun gama cin abincinsu su wuce daki,daga hajjaa sai uncle muhsin kawai a falo din,ta qaraso tana ajjiye masa zobon data dafa masa,ya dauka yana mata sannu ya fara kurba,sai ta gyara zamanta

“Abba na cike foam din nan fa” ba tare da ya dubeta ba yana ci gaba da aikinsa bayan ya tura glass dinsa baya kadan yace

“Ma sha Allah,to Allah yasa a fara a sa’a” fuska tadan bata kadan

“Amma fa abba akwai matsala” sai a sannan ya waiwayo ya kalleta

“Matsala wacce iri?”

“Yara abba,bansan ya zanyi dasu ba,babu kowa a gida bare nace driver ya kawosu nan su zauna tare,kuma daga qarfe hudu zamu dinga farawa zuwa shida” ajjiye cup din hannunsa yayi yana dubanta

“To yanzu ya za’a yi kenan?” Shuru ta danyi tana juya hannunta,sannan daga bisani tace

“Eh to,da wai cewa nayi ko gidan hajiyan gida dubun zansa driver ya dinga ajjiyesu,tunda babu nisa wajen namu daga nan,idan yaso in mun tashi qarfe shidan sai na shiga na daukosu mu zarto gida?kaga kwana biyar kawai an gama” Kai ya jinjina

“Qwarai kuwa,hakan ma yayi”

“To abba ko zaka gaya mata kada suga yara kawai?” Dan dubanta yayi

“Ke hajiya,ai fada zatayi tace don zasu zo sai an gaya mata?,ta wuce duk yadda kike zato,kamar uwa take a wajenmu,ba damuwa idan kinje kyayi mata bayani”

“to shikenan ba matsala,godiya nake oga”

“Baki da damuwa” ya fada yana murmushi tare daci gaba da aikinsa,ita kuma ta soma tattara kayan abincin da ya gama dasu ta wuce dasu kitchen,sannan ta biya ta dakinsu nujood din ta gaya musu gobe kowa ya dauki kayan gida cikin jakarsa zata saukesu ne gidan hajiyan.

***********
Yau din tun safe da ya tashi dukka wayoyinsa na akashe,bashi da niyyar fita sam sam sam kamar yadda ya qudurta tun jiya,zaunawa yaso yayi a gida ya huta,saidai ra’ayin hutun ya kau daga ranshi daga sanda gari ya waye,sai kawai ya hau sanitation na gidan da kanshi,yana yi su mimi na biye dashi yana tayashi da aikin surutu,surutunsu bai dameshi ba,duk da kasancewarsa mutum marason hayaniya,sai surutunsun ya zame masa tamkar abokin hira.

Sanda ta tashi ta taddashi yana aikin sai tayi kamar bata ankara da me yakeyi ba,ta qaraso inda yake tsaye saman wata stool yana cire yana,rungume take da hannayenta,tadan rusuna kadan tana fadin

“Ina kwana” kansa yadan sauke kan,ya dubeta da manyan idanunsan nan masu kwarjini,a dai dai wannan lokacin kamata yayi ace ta kammala gyaran gidan gaba daya,ta kuma shiryawa iyalinta abun buda baki,shike kwance yana hutun da takeyi amma reshe ya juye da mujiya

“Lafiya lau” ya amsa mata yana maida kansa ga aikin da yakeyi,sai taji sam sam ba dadi,tunda ya dawo babu wannan tarairaya da soyayyar tasa mai tsaya mata a zuciya,gaba daya fushin ma data tanada zatayi kamar ma ya fita yin fushin

“Dame zan taimaka maka?” Tayi qarfin halin fada,batason ya soma nuna mata halin ko in kula din nan nasa dake mata ciwo,bai iya miskilanci ba ko kadan,idan ya fara sai kinji babu dadi

“Inajin yunwa yara sukeji,ki sama musu abinda zasuci” ya amsa mata,sai ta sauke hannunta dake wuyanta,ta wuce kitchen dinta,tunda tuni ya gama da sassansa ya dawo nata.

Tea ta hada musu da bread ta soma basu,amma da yake sun gaji da cima daya sai suka watsar suka kama gabansu

“Ubanku ya bataku da cima,bazan iya wannan bautar ba,idan na gama kwaci gaba daya” ta fada tana nazarin abinda zaga dafa.

Da yake tasan ita din mai laifi ce,duk da batajin tayi laifin har cikin ranta,saita zage ta bata lokaci ta shirya breakfast mai kyau,gasashen kifi tayi da chips,ta dafa masa ruwan tea din da yafiso,sanann ta dama masa kunun gyada still.

Sanda ta gama bata gansu falon ba,sha biyu saura,sai ta jere komai a dining sannan ta wuce dakinta.

Wanka tayi ta shirya kanta da kyau cikin wata atamfa,ta feshe jikinta da turarukan da tasan yafiso,wadanda takan jima batayi amfani dasu ba,duk da ya siyo su din amma sun zama kamar decoration saman mudubinta,takan ce bata da time na wannan qaqale qaqale din,bata shafawa fuskarta komai ba illa mai,ta taje kanta tana bata fuska saboda yadda yadan dunqule waje guda,ta manta when last data tajeshi,tunda yasa qafa yayi tafiya ta sauke ‘yan gyaran da takeyi saboda matsawarsa da kuma qoqarin ganin ta hanashi qorafi a kanta. Daurinta ta kawo gaban goshi saita zari wayarta ta fito.

Har yanzu babu kowa a falon,don haka ta zarce sassansa,tana tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen.

Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba.

A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata

“Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan” ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa.

A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata.

Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya

“Fushi kake tayi dani abba?” Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo

“Me kika gani?”

“Abun ya motsa” ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam

“Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce” ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta.

Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana

“Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?” Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da sauri,saboda tsabar qi fadi dake damunta.

Idanun nata ta zare tana kauda kanta gefe guda sannan ta soma magana

“Amma dai tsakani da Allah,a wadatar da Allah yayi maka meye a ciki?,ka zabi ka kunyatani cikin qawaye na akan fiddani kunya kenan?,idan yaso duk fadan da zakamin ma kayimin shi daga baya” kai ya girgiza,mai hali baya taba fasa halinsa

“Bazan karba abinda bani nace kiyi ba,bayan nasan ban gazawa gidana da iyalina da komai ba,suturar da zasu sanya ko mai matsayin mijin mace iyaka kenan,bazan yarda ki dinga daukomin basukan da basu da tushe bare makama ba,har yanzu wuyana baiyi wannan kaurin ba” ya fada muryarsa na qara nuba bacin ransa,dole tadan sassauta muryarta

“Yanzu dai tunda na mayar kuma baka siya din ba ba shikenan ba?”

“Eh shikenan,amma kada ki qara,ko meye kike da buqata ki gayamin,idan naga akwai sarari nayi miki,idan babu ki jira sai zuwa sanda ya samu”

“To ai shikenan” ta fada tana kauda kanta gefe,ranta yana suya tana qoqarin dannewa,shuru ya ratsa dakin,yana ci gaba da shiryawa,yasan abu ne me wahala ta buda baki ta bada haquri,ba yau ya fara ganin hakan ba,yanason mata magana kan yadda take watsar da kula da gidan dama jikinta amma kuma yasan koda yayi dinma kamar busa ce a iska,babu lallai ta dauka,don haka yayi mata zance mafi muhimmanci yanzu a wajensa

“Banga kina shirin komai ba,ko babu abinda zaki tafi dashi?”

“Zuwa ina?” Ta fada tana waiwayowa da sauri,kafeta yayi da ido kafin ya dauke ganinsa,ya soma gajiya da wannan kayan takaicin,saboda tsabar rashin damuwa tana nufin har ta mance da maganar su dashi kafin ya tafi?,ko tsabar rainin wayo ne?.

Bai amsa mata ba saboda baya jin akwai buqatar yi mata tuni,sai yaci gaba da shirinsa kawai,ita dinma ta tuna,duk da ba mancewa tayi din ba,amma tayi zaton zai bar maganar ne,tunda ta gaya masa ita babu inda zata bishi,ba zata iya barin bauchi ba.

Tana zaune ya gama shirinsa tsaf cikin qananun kaya,binsa ta dinga yi da kallo,ba banza ba take tsakanin kishinsa,tasan ko kusa ko alama babu marching ko kadan tsakaninta da abbas,tako ina ya zarta mata,sau tari qawaye da ‘yan uwa kan furta kamar ba mijinta ba,kalmar data tsana kenan,wadda duk wanda ya fadeta sai sun haura dashi,idan kuma tana ganin mutuncinka ta bika da harara ko baqar magana.

Tsayawa yayi yana jifanta da wani kallo hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya lura da yadda take binsa da wani mayen kallo

“Zan samu abincin ko na zauna kiyita kallo na?” Ya fada da dan tsokana kadan cikin muryarsa,duk da fuskarsa bata nuna hakan ba,dama kuma yawanci ita daya ke ganewa wasan tsokanarsa, mmurmushi ya subuce mata,ta miqe tana cewa

“Kaci abincin tukunna sai na zauna nayita kallon naka”.

Har yanzu dai still taste na girkinta bai kai masa yadda yakeso ba,amma hakanan ya kama yaci,yana mai bata uzurin wataran zata qware,tunda a yanxun abincin yana ciyuwa alhamdulillah.

*RUMBUN K’AYA*🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank.

Shaidar biya tanan👇🏻
09033181070

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button