A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 32

Sponsored Links

Part 02

Page 32

“Hasbunallahu wani’imal wakil,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” itace ya samu kansa da maimaitawa,jujjuya kansa kawai yakeyi yanajin kamar zai zauce,kamar hankalinsa na shirin yin qaura daga gangar jikinsa ne,wasu irin muryoyi ne daga qasan zuciyarsa ke karanta masa abubuwa iri daban dabanya kama kansa da kyau ya riqe,sai yaji hawaye na shirin fita a idanunsa,kewar hajiya ta mamayeshi,ita daya ce yake iya jingina da ita a duk sand aya shiga matsanancin hali irin wanna,ita daya yake raba yaji snayi ya kuma samu mafita cikin sauqi,gaba daya kansa ya gama kwancewa,yanason yayi wani abu amma sai yaji kamar ana dannarsa,a wannan gabar abu daya ne kadai tunda ya darsu ya kasa barin zuciyarsa,yana son widad ta dawo,koma yaya ne yanason ta dawo,idan ta dawo koma meye sai yafi gabatar dashi a nutse,nesantarsa da tayi sainyakejin kamar bashi da sauran komai da ya rage masa a rayuwa,gaba daya maganin da likita ke bashi da sauran treatment da yake bashi ana bashine kawai badon suna wani amfani ba,a wannan rana da kansa ya kira yace ayi masa allurar bacci,saboda daina gane komai da yayi,kowanne sashe na zuciyarsa da abinda yake umartarsa da ya aikata.

Cikin kwana uku ya gaza samun sukuni,gaba daya a rikice yake,yanatabyaqi da zuciyar dake umartarsa da nisantar widad da dukkan wani abu da ya shafeshi,ya dinga naci wa su kawu hassan da basu haquri,ba yadda suka iya,shi din mai alkhairi ne da maida damuwarsu tashi,haka suma suka dinga ziryar zuwa kano neman bikon widad din,zukatansu suma duka babu dadi.

Tun abba yana saurarensu tare da jadda musu cewa,shifa takardar sakin widad yake jira bawai batun biko ba,har takai yama daina sauraron kowa a cikinsu,ba abbas da har yanzu yake kwance yana jinya ba,hatta dasu kawu hassan abun ya daure musu kai,don basu tsammaci samun hakan daga wajen abba ba.

A yanzun har takai ta kawo baya saurarensu,sai yasa a kaisu dakin baqi suyita zaman jiransa,har sai sun gaji sun tafi.

Yanayin da yake ciki na jinya a asibiti ne kawai ya hana su kawu zame hannunsu daga batun bikon widad din,duk yadda suke zaton al’amarin daga wajen abban ya wuce nan,dole suka yanke shawarar tuntubar tsoho mai ran qarfe alhaji salim,suna da yaqinin shi kadai ne zai iya masa magana yaji,shi daya ne zai iya sakashi yayi.

*******K’arfe takwas na safiya ne,tana zaune saman kujerar dining din ummu tana kurbar tea mai dumi sosai,a yanzun ta zama wata acici,ita da abinci bai wani dameta ba,amma yanzun tun farar safiya take fara neman abinci,ita kuwa latifa bata gajiya da bata duk kalar abincin da takeso.

Cikin kwanakin ta gama amincewa juna biyu ne da ita,bata buqatar zuwa asibiti su gaya mata,don dukkan wasu alamu sun nuna mata,a yanzun ba kamar lokacin cikin affan bane,babu quruciya sosai a kanta bare ta gaza fahimtar komai.

Hankalinta a tashe yake sosai da fahimtar hakan da tayi,duka duka watan affan nawa?,sai taji tana shakka da d’ar d’ar na gayawa wani,a wannan situation dinma da take ciki?, yanayin da take ciki na zargin zina daga mijinta,mutumin da ya kamata ace shine mutum na farko da ya fada bata yarda?,sai ya zama shine mutum na qarshe da zai gasgatata?,iya wannan tunanin ya sanyata taji ta qoshi da tea din,ta ajjiye cup din gefe tana ta kokawar yage tunaninsa ta ajjiye gefe kamar yadda ta daukarma ranta,cikin kwanakin ta dan samu nutsuwa albarkacin addu’a da kuma karbar qaddararta da tayi,ta jawo wayarta ta buda tana duba saqonnin customers dinta,don har harkar business dinta ta dawo kai yanzu sosai.

Sallamar abban nata ya sanyata daga kai da sauri,ta kuma miqe tana masa sannu da zuwa cike da mamkin fitowarsa da safe haka,saita samu kanta da faduwar gaba,amma ganin baice komai ba sun gaisa kamar ko yaushe yana tambayar abokinsa affan saita saki jiki,ummu ta fito ya tsugunna ya gaidata

“Alhajin ya tashi?”

“Eh kai yake jira ma,yace zaka kaishi dubiya”

“Na iso, za’a sanar mas ako za’a min iso”

“Bari na shaida masa” ummu ta fada tana komawa ciki.

Ba jimawa ta dawo ta gaya masa yace ya jirashi,minti goma basu cika ba tsohon ya fito a shirye tsaf yana qamshi cikin farin kaya da farin rawani,shigar da yafiyi,ko gaisawa bai tsaya sunyi ba yace suje sa gaisa a mota,ummu da widad sukayi musu fatan dawowa lafiya suka fice yana takewa tsohon baya.

Sai da suka dauki hanya sosai sannan tsoho yayi magana

“Mamuda an kawo min qararka,surukanka sunce kaqi haquri ka basu bikon diyarka ko?” Nauyi yadan kama abba kadan,mutanen sun masa shigar sauri sunyi kuma mugun shammatarsa,sam hankalinsa baikai zasu nema alhajin ba,da tuni ya musu kandagarki ko ya yiwa tufkar hanci,so yake ya hukunta hafsatun harma da abbas din gaba daya,ta yadda a gaba koda wasa abu makamancin wannan bazasu bari ya sake faruwa ba.

Ya muskuta ya dan gyara zamansa zai bada uzuri tsohon ya tari numfashinsa

“Kanaso ayi amfani dakai a ruguza auren widad kamar yadda akeso ta faru ko?,wannan abun da kake shirin yi ba komai bane face hanyar cikawa maqiya burinsu,koma waye ya shirya wanna,ya shirya hakanne na tabbatar don yaga bayan auren yarinyar,to inason ka bawa mara d’a kunya,ka turawa koma waye aniyarsa ka maida widad dakinta,sannan ina me baka shawarar ka barwa Allah,duk yadda zaka hukunta wanda yayi mata wannan qazafin baikai hukuncin da Allah zaiyi masa ba,qarshenta kasa a daure maka shi ko?,to daurin da Allah zaiyi masa har yakai wanda zakayi masa?” tunda alhaji ya fara magana gyada kai abba yakeyi cike da gamsuwa

“Hakane,in sha Allah za’a yi yadda kace alhaji”

“To alhamdulillah,Allah ya tsare gaba,ya basu zaman lafiya dawwamamme,ya kauda sharrin maqiya da mahassada”

“Ameeen ya hayyu ya qayyumu” abban ya amsa masa.

Sai bayan sun gama harkokinsu da alhaji ya maidoshi gida sannan yasa aka kira masa widad,a sannan bata jima da gama sallar la’asar ba,tana saman abun sallah tana cin popcorn,wai yunwa takeji bayan duka abincin da taci,tana jira latifa ta gama gasa mata kifin da take sha’awar ci,ta ajjiye popcorn din ta miqe tsam ta fita a dakin.

A falon baqi na gidan ta sameshi shi daya zaune

“Shigo mana widad din ummu” ya kirata da sunan da ake yawan kiranta,wanda bata taba ji ya kirata dashi ba sai yanzu,ta qaraso kanta a qasa ta zauna gefe.

“Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka,ya sake tsaremin ke”

“Ameeen ya hayyu ya qayyumu abba,na gode”

“Kinsan dalilin da yasa na kiraki?” Saita girgiza kai alamun a’ah

“Inason ki gayamin gaskiyar abinda yake ranki,banaso ki boyemin komai”

“To abba” ta sake fada tana bashi dukka hankalinta

“Kinason ki koma gidan mijinki?” A wani mugun ba zata maganar tazo mata,har sai data daga kai ta kalli abban nata sannan ta saukar da kanta qasa,tun randa taji labarin zaryar da su kawu hassan keyi wajen abban nata,bata sake bari anyi zance makamancin hakan a gabanta ba,don zuwa yanzun ita din bata jin akwai sauran gurbin abbas a zuciyarta,ta soma sabuleshi daga rayuwarta.

Har sau uku abba yana sake maimaita tambayar amma ta gaza amsa masa da komai,sai ana ukunne wasu hawaye masu zafi suka zubo mata,yadda abban yake nanata tambayar kamar yana alamta mata ya bada kai bori ya hau,su kawu hassan sun rinjayeshi

“Ni bana buqatar komawa gidansa abba,bana so,amma indai kai kana da buqatar hakan,zan maka biyayya abba zan koma” ta qarasa fada kuka yana qwace mata.

Sake saka mata albarka yayi sosai tausayinsa yana ratsata,ya dora da cewa

“Ni bazan cuceki har abada,bazanso kuma ki shiga takura da damuwa ba,burina dukkanku ku rayu rayuwa ingantacciya me kyau,inaso ki koma gidanki,zan kuma maidaki ne saboda maqiya susan cewa basu isa su raba aurenku ba,kiyi haquri idan hukuncina baiyi miki dadi ba”

“Kafi qarfin haka abba a wajena,ka isa dani ta kowavce fuska” tayi maganar siririn kuka yana qwace mata,don tuni ta fara shiryawa kanta yadda zatayi rayuwa ba tare abbas din ba.

Maganganu masu dadi da kwantar da rai yayi mata gami da nasiha da jan hankali,har sai da kukan nata ya ragu sosai sannan ya sallameta,bayan ta fita kuma ya kira kawu hassan ya basu bikonta a bisa sharadan da idan ya amince dasu widad zata koma dakinta,idan kuma bai amince ba a shirye yake da karbar takardar sakinta.

Na farko abbas din bazai sake hadasu zama gida daya ba tsakanin hafsat da widad,kowacce ta zauna gidanta daban,yace sam zamansu bazai yiwu ba,baya ga banbancin shekaru,irin wadan nan abubuwan da suka fara bullowa a tsakaninsu ba’a san gaba me ta dauki aniyar aikatawa ba,saboda bazai iya dauka da jurar abinda zata bullo dashi a gaba ba idan wannan sun barta da Allah sun qyaleta,na biyu ta kiyayeshi,koda wasa ya sake jin labarin ta aikata abu makamancin wannan to fa duk duniya babu mai tanqwarashi akan matakin da zai dauka dangane da ita,dukkansu sun aminta da wannan sharadin,sun kuma gode masa da har ya nuna dattako ya haqura yayi kawaici akan shariar da yace zasuyi,sun zaunar da hafsat kuma sun gaya mata komai,wadda tuni cikinta yayi bala’in durar ruwa sanda taji batun kai qara kotu,tana tsoron kada ballinta ya tashi,ta tabbatar idan asirinta ya tonu ta ba makawa wannan karon ba asiri ba,ko meye tayi abbas din bazai qyaleta ba,tanason taji cewar kotun za’a je ko an fasa?,amma ta rasa amsa daga wajensu,saboda batason ta matsa da tambayar da zata alamta musu bata da gaskiya,ta wajen abbas kuwa ta kasa jin komai,don ko wayarsa ta kira bashi yake dagawa ba, samuel ne ko wani cikin yaransa,kuma duk sanda zasu daga din zasu gaya mata ne cewa bacci yakeyi,sai suka barta cikin duhu,duhun da ya tafi da dukka nutsuwarta,dare da rana tana zulumin da tsoron ta ina ballin zai tashi?,abu daya yadan kwantar mata da hankali,kudaden data aikawa habiba tace ta koma wajen malamin nasu,ya kuma shaida mata magana ta mutu,har abada abbas bazai sake iya tada zancan ba,kai hatta da komen widad ma,yadda tabar gidan ta barshi kenan yadda yaro ke fita daga cikin mahaifiyarsa,wannan yasa ta saki jikinta taci gaba da sabgoginta.

Tana kuka tana komai haka ummu ta gyara mata komai nata ita da anty deena,daban anty deena suka kebe da ita ita da anty madeena suka sake mata lecture kan wasu abubuwan masu amfani,wuni guda,itadai jinsu kawai takeyi tana binsu da idanu,gani take a yanzun tsakaninta da abbas ai sai kallo.

A washegari lafiyayyar motar security tazo ta dauki widad tare da affan zuwa garin katsina,sabon muhallin da gurin aiki ya bawa abbas,tanata kuka ganin alhaji ya hana kowa yi mata rakiya

“Ku barta ta tafi ita daya,hakan zai bata damar sasantawa da mijinta da wuri,tunda na fuskanci kamar har yanzu akan fushi take”.

Tafiyar awa biyu da rabi ta sadasu da qofad kyakkyawan madaidaicin gidan,driver ya tsaya yayi hon aka buda qaramin gate din gidan ya saka motar a ciki,ya wuce qaramin parking lot na gidan da bai wuce yaci mota biyu ba ya tsaida motar

“Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzilin” ta fada tana lumshe idanunta sannan ta budesu,bata taba zaton qaddara zata sake hadasu zama da abbas ba,hakanan a yanzu batasan wanne irin zama zasuyi dashi ba.

Tana rungume da affan ta nufi qofar da ta tabbatar ta parlor ce,a hankali take takawa,sanye da wata irin doguwar riga ‘yar morocco mai sulbi da tayi masifar dacewa da fatarta data fara sheqi tun yanzu saboda qaramin cikin dake jikinta.

Yaji shigowarsu sarai amma ya gaza motsawa,yana zaune cikin doguwar kujera hannunsa daya maqale da carbi counter,wanda a yanzun zama tare da shi ne kadai yake bashi sanyi da nutsuwar zuciya,daya hannun nasa kuma wayarsa ce yake duba news akan abubuwan da suka shafi katsina da kewayenta kafin ya gama warkewa ya fara fita aiki.

Idanunsa qyar akan qofar sanda yaji an tabata,tana bude qofar idanunsu suka gauraya da juna,kowannensu sai yayi qoqarin janye idonsa daga kan dan uwanta,tayi sallama da siririyar muryarta daga can qasan maqoshinta,wanda banda Allah yasa ya saka kunne da kyau babu ta yadda za’a yi yaji abinda take fada.

Amsa mata yayi yana qoqarin fita daga page din da yake karatun,ya aje wayar hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe ya nufota.

Batasan ya taho din ba,don tunda suka hada ido dashi bata sake marmarin kallonsa ba,ya rame sosai har hakan ya bayyana a fuska da jikinsa,to amma sai taji sam bata damu ba yadda ta saba ji a baya idan bashi da lafiya, taci gaba da takawa zuwa cikin falon,sai ganin mutum tayi yasha gabanta.

[22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button