A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 3

Sponsored Links

PAGE 03

Sakin qofar tayi tayi gaba,abbas din yabi qofar da kallo sannan ya taka zuwa cikin gidan,ya cimmata sanda take juyawa abinta zuwa ciki,daure da zanin atamfa saman wata kodaddiyar rigar baccinta daya jima yana ganinta jikinta,jin takunsa ya sanyata dan dakatawa kadan ta waiwayo,suka hada ido.

Duk da dare ne da kuma qarancin haske,amma tana iyabhangen yadda taga yayi wani mugun fresh,qamshinsa ya cika wajen,ya mata kyau,amma data tuna a yanzun tare da wa yake sai taji komai ya gushe mata,kishinta ya motsa sosai,wanda tunda umar yazo ya dauki motar da zummar daukosu tahau kan zafinta,ita tunda suke tare dashi bata taba ganin yayi kyau da gogewa irin hakan ba,kuma ba wannan bane ai zuwansa aikin hajji na farko ba

“Me kikeyi mintuna kusan nawa muna tsaye muna bugu?” Ya fada ransa a dan bace

“Bacci ne fa ya daukeni” ta fada murya a cunkushe tana bata rai,sai ya janye idanunsa yana dan jan qaramin tsaki

“Ta yaya zaki kwanta kinsan muna hanya?, at least dai ai kya tsaya kiga shigowata” ya fada yana qoqarin buda gate din gidan da kansa yana yiwa umar maganar ya shigo da motar ciki dare yana qara yi.

Ranta ya sosu,ta tura kayan baki gaba tana jin kamar ta maida masa magana,ason ranta ta shige ciki,amma sai taji tana son tsaiwa taga yarinyar,ta sake tabbatarwa babu cikin da a kullum ta kwanta cikin mafarkinta take ganin kamar tana dashi.

Tana tsaye daga gefan har umar ya shigo da motar ya fakata a parking lot na gidan,ya kasheta sannan widad ta buda murfin motar ta fito tana jin ranta da zuciyarta duka babu dadi.

Rawa qafafun hafsat suka danyi,ta kadu sosai da yadda taga yarinyar ta sake canzawa,sanye take da wata lafiyayyar abaya baqa sidik mai sulbi, balarabiya sakkk!! Haka ta koma,hasken fatarta sai daukan ido yakeyi,ta sake cika sosai,ta zama cikakkiyar mace,kai bazakace widad din da aka mata aure da qananun shekaru bace,duka cikin watannin da basu wuce biyu da tafiyarsu ba irin wannan gagarumin sauyin na babu zato bare tsammani?.

Kasa amsa gaisuwar da take mata tayi,gaba daya a rude take har umar yayi musu sallama ya fice daga gidan bayan abbas ya masa izinin tafiya da motar ya kawo masa ita gobe.

Gajiya gami da tsanar data yiwa gidan ya sake kashe mata jiki,ta kallai abbas

“Uncle bacci nakeji fa” yadda tayi maganar a mugun shagwabe ya taba ran hafsat sosai,saidai a wajen widad din hakan ba komai bane,don kusan a haka yanzun ta saba magana dashi

“Muje sashena,nasan bangarenki akwai qura kam yanzu,dare kuma ya riga yayi bare ki gyara” ya amsa mata a tausashe yana mata wani irin sassanyan kallo da ya riga ya saba yi mata shi,har baisan yana fidda kansa da kansa daga idanunsa ba.

Turqashi!…..me abbas din yake nufi?,taje sashensa ta kwana?,aiko sama da qasa zata hadu ba zata bari hakan ta faru ba,wannan ba komai bane ba face zallar rainin hankali,ta gama fadi tashin gyaran sashen saboda shi sannan yace wata ce zata kwana?,uwa uba ma watansa nawa basa tare,hakan yana nufin zai karbe kwananta na yau ya bawa yarinyar?.

Taku biyu sukayi tasha gabansu,dubansu takeyi kai tsaye

“Ba inda zata ta kwana wallahi,bazan dauki wannan rainin wayon ba” ta fada tana fidda idanunta.

Ido yadan qanqance yana dubanta

“Me kikeyi ne haka?”

“Abinda idonka ya gane maka” kafin abbas din ya sake cewa komai widad ta zame hannunta a hankali ta fara takawa zuwa shiyyar sashenta,shi da hafsat din dukansu suka bita da kallo,sai ya motsa da sauri yabi bayanta,yayin da hafsat ta rakasu da ido qirjinta kamar zai qone saboda zafi da tsananin kishi.

A qofar sassanta tana gwada keys din hannunta ya cimmata

“Me zakiyi a ciki?” Murmushi ta sake masa a nutse

“Zan shiga na kwanta ne uncle dare yana sake yi” ta fada a narke

“Amma ai ba’a gyare yake ba,nace muje part dina ki kwanta a can kafin safiya” a nutse ta girgiza masa kai,fuskarta still da murmushi

“Zan kwanta a nan din uncle,awa nawa ne gari ya waye?,kada ka damu,kana buqatar hutu,kaje ka huta” gaba daya saita gama kwance masa kai,abinda ya kamata ace hafsta dince tayi ita ta gaza sai ‘yar cikinta,wani irin qauna da kimar yarinyar ya sake qaruwa a idanunsa,ya santa gwanar tsoro ce,kawai dai tayi hakanne don ta samar masa da kwanciyar hankali da nutsuwa,ya fuskanci wannan din kusan a dabi’arta yake,batason hayaniya sam,sai ya rasa me zaice mata,ya matsa ya karba keys din ya gwada na qofar ya bude sannan ya tura yayi gaba tana biye dashi.

Sosai wajen yayi qura,da kansa ya dinga saka tsintsiya yana kade mata hanya har zuwa bedroom dinta,sai daya tabbatar ta gama komai ta kwanta sannan ya baro sashen.

Runtse idanunta tayi zuciyarta na matsanancin bugu da tsoron dake shigarta kamar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito,tana ji har cikin Zuciyarta kamar ana tunkudata ta fice,amma can qasan zuciyarta tana kiran sunan Allah kadan kadan,abinda ya kawo sauqin yanayin da takeji din wanda keta azalzalarta kamar ana gaya mata cikin kunnuwanta.

Bai samu Hafsat din a wajen ba,sai bai wani damu ba,har yanzu Zuciyarsa tana cike da mamakin halayenta, kullum babu sauyi?, sai sake ta’azzara al’amuranta sukeyi?,da wanann tunanin ya isa sassansa.

Ba laifi babu datti hakanan babu qura,yaci gaba da takawa har dakin gadonsa,yana tura kansa,sautin sheshsheqar kukanta yana masa maraba.

Dauke kansa yayi kamar bai ganta ba,baqinciki yana cika masa zuciya,baiga me akayi mata ba da zata zauna a daren daya dawo yana buqatar ya huta ta tusashi da koke koke ba,idan ita bai rufeta da fada ba bazata sashi gaba tana masa kuka ba,sai kawai ya fara rage kayan jikinsa ba tare da yabi ta kanta ba,rabin hankalinsa yana ga widad da yadda yaga taqi sakewa,lallai tsoronta ya dawo,irin tsoron daya ninka na baya,sai wani bangare na zuciyarsa ya bashi ko juna biyun da take dashi ne,qaramin murmushi ya kubce masa sanda ya tuna da ajiyarsa dake jikinta,dai dai sanda muryarta ta ratsa kunnensa cikin sautin kuka

“Da wannan wulaqancin da kakeyimin gwara kacemin ka gaji da zama dani na tafi gid…….”

“Hey….. stop it dallah!” Ya katseta da mugun sauri cikin bacin rai yana dubanta,bacin ran data gani a idanunsa sun ninka nata don haka dole tayi shuru tana binsa da kallo

“Banason rainin wayo da wulaqanci cikin daren nan,hutu nake da buqata,idan qorafi ya shigo dake ki tashi ki fita ki bani waje,idan kin fita idan kinga dama ki wuce gidan ban riqe miki qafa ba” sosai.maganar ta daga mata hankali sannan ta bata mata rai,ta sake fashewa da kuka ta miqe tana daukan yusra ta fice a dakin,yaja tsaki yabi bayanta ya kulle qofarsa ya dawo ya wuce bandaki,gaba daya ta gama fita a kansa,fushinta ko kukanta ya daina damunsa sam.

Wannan abun daya faru a daren ya sake tunxura zuciyarta,ta kasa kuma bacci sai data kira ummanta,cikin daren suka qulla abubuwa masu yawa da suke saka ran zasu aiwatar,ko akan widad ko akan abbas din,duk wanda nasararsu ta fada a kansa.

*********Da qyar ta wayi gari da wani irin matsanancin tsoro daya haifar mata da ciwon kai,inda Allah ya taimaketa washegarin saiga su nujood harda hajjaaa sunzo mata,ta samu tadan sake,daga qarshe hajjaa ta tafi tabar mata nujood ta tayata kintsa sashen da sauran gyare gyare,wannan ne ya sanyata tadan warware,saidai komai a darare takeyinsa,koda abune yayi babban faduwa yanzu zata firgita,har nujood ta fahimta ta tambayeta

“Hakanan nakejin haka,nima bansan dalili ba”

“Saikiyita kiran sunan Allah da addu’a”

“Inayi,daqyar nayi bacci jiya”

“Zan karbo miki addu’ar yawan firgita a wajen ya sayyadinmu” da haka suka fada wani zancan,tana ci gaba da addu’a cikin ranta duk sanda taji irin hakan,da haka ta dinga samun sassauci cikin ranta.

Dawowarsu daga saudiyyan sai komai ya sake canzawa,gaba daya hafsat din ta tattara sanya idanunta da komai ta aza akan abbas da widad wadda bata sakata a lissafinta ba kwata kwata,don abinda yake gabanta shi ya dameta,saidai duk wata tijara da abubuwan da zatayi tana jinta daga farfajiyar gidan,ko idan guri ya hadasu,ko daga kai ta kalleta batayi bare akai ga jallin tanka mata,tunda bata taba tararta gaba da gaba ta kama sunanta ba tun sanda abbas din yaja kunnen hafsat,ita a yanzun kawai burinta abbas yace ta shirya su koma kaduna,gaba daya ta tsani garin wani muguwar tsana,duk ranar da ba girkinta bane da qyar take iya bacci saboda wani irin tsoro da yake shigarta,da qyar take hana kanta fita a wasu dararen,saidai ta zauna bakin qofar falo tayita kuka tana jin fita kawai takeson yi.

A WANI DARE karfe sha biyu da rabi na dare,har ya shiga sassansa ya kwanta ya tuna kamar yau din da daddare batasha magungunanta na anti natal ba,ya sauko daga gadon hafsat na gefe tana kwasar baccinta ya fito.

Kamar mutum ya dinga hangowa daga nesa,sai ya sauya yanayin tafiyarsa cikin hikima da dabararsu ta jami’an tsaro,bai wani jima ba ya gane widad dince ke nufar qofa,cikin wani irin zafin nama ya cimmata cikin takun da basu gaza biyar ba,saiji tayi caraf an riqota,ta waiwayo suka hada ido,cikin matuqar kaduwa yace mata

“Ina zaki da daren nan?” Kamar jira takeyi ta fashe da kuka

“Fita nakeson yi,banason gidan nan uncle” mamakinsa ya qaru,to duka me yake kawo haka?,wannan shine karo na biyu daya taba ganinta zata fita din.

A tausashe ya kama hannunta yana son maidata ciki,saita kuma saka kuka

“Don Allah uncle” shuru yayi ya zuba mata ido,yadan lumshe idanunsa hadi da budesu

“Muje ciki magana zamuyi” dole ta sakar masa hannun ya riqeta zuwa ciki.

Bakin gado dukansu suka zauna yana dubanta

“Me yake faruwa?”

“Banason gidan nan” ta amsa masa kanta tsaye tana qwalla

“Me yasa?”

“Tsoro nakeji” shuru ya danyi,ya ciro wayarsa yana son kiran dr,saidai yaga dare yayi,amma duk da haka yanajin ya zama dole ya kirata din.

Bugu daya ta daga ya nema afuwan tashinta,tace batama jima da shigowa daga aiki ba sannan yayi mata tambayar

“Kwai matan da ciki yake sakasu jin zaquwa gajiya da tsanar waje” saita fara masa bayani,yana fahimtarta yana kuma nazartar widad dake zaune a gefansa ta cure waje daya,ya karanci bayananta,to amma a abinda yake gani a tattare da widad din kamar nata yanayin ya dan sha banbam da wadda dr take qoqarin masa bayani

“Amma ba komai,with time zata daina ne” daga baya sukayi sallama yayi mata godiya,sai ya miqe yana kallon widad

“Bari na kawo miki mimi,hakan yayi?” Kai ta gyada masa a hankali sannan ya juya a nutse ya fice,ta bishi da kallo tana sauke ajiyar zuciya,rabon da yarinyar ta kwana a wajenta harta manta,gaba daya uwar ta hanata kwana a wajenta.

Yana buda qofar hafsat din na farkawa,ta bishi da kallo ganin ya shigo ne daga waje,ina yaje?,badai satar kwana aka fara yi mata ba?,saita miqe ta zauna tana kallonsa sanda ya duqa zai dauki mimi daga gadonsu dake gefe,don yau din a nan bacci ya daukesu,sai yace ta barsu kawai

“Bacci take fa”

“Na sani,zata tayata antynta kwana” ya amsa mata ba tare daya kalleta ba,wani abu ya darsu a ranta

“Me ya samu antyn nata?,naga yanxun ita daya take kwana bata ko nemanta ko?”

“Basai wani abu ya sameta zasu kwana wajenta ba ai,tunda yaranta ne itama” ya amsata yana rufe yarinyar da dan qaramin lallausan bargonsu,wanda zamansa a dakin ne kawai yasa bargon ya tsira da mutuncinsa ya kuma dade da kyansa.

Bai sake ce mata komai ya juya ya fice,sai ta bishi da kallo qaramar dariya tana qwace mata,ashe har yanzu da sauran abun nan bai gama sanewa ba,tanason wannan aikin tabbas!, jaddada shi takeson ayi kafin a wuce zuwa matakin gaba,bata qaunar hada inuwa daya da yarinyar kwata kwata.

Sai da kwanciyar tace tayi mata sannan ya tashi yana kallonta

“Ki shirya kayanki jibi zamu koma” wannan shine albishir din da yafi faranta mata rai,duk da ason ranta bataqi ma yace gobe zasu tafi ba,amma babu komai,goben ai a wajenta zai kwana,bata da damuwa.

[04/05, 1:57 pm] +234 916 551 4595: *H U G U M A*
*Arewabooks: Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button