A Rubuce Take Book 2 Page 27
Part 02
Page 27
Yamma lis suka sauka a bauchi saboda gudun da yaron nasa ya tsula bisa umarnin ogan nasa
“FAAZ hotels zaka kaini” ya fada a wani galabaice,kamar yau ya fara doguwar tafiya a mota
“Yes sir” ya fada yana karya kan motar tasu ya dauki titin da zai sadasu da hotel din.
Karon farko gabansa yayi mummunar faduwa sanda suka isa gaban hotel din,abind aya jima baiji ba kenan,duk irin hatsarin aikin da zai shiga kuwa,zuciyarsa ta dinga masa saqe saqen munana abubuwa,tana ayyana masa adadin xuwan widad wajen,kamar wanda allurarsa ta motsa ya zunkuda cikin zafin nama ya buda murfin motar ya fice,bayan ya yiwa yaron umarnin ya zauna cikin motar ya jirashi,yanzu zai dawo su wuce gida.
Cikin rashin nutsuwa yake takawa zuwa makekiyar qofar hotel din,hannunsa cikin aljihun wandonsa yana qarewa qofar kallo,duk da irin qwarewarsa a wajen aiki,duk da qwarewarsa wajen iya bincike amma a yau kamar an bude kwanyarsa an kwashe dukka wannan qwarewar,komai ya kwance masa,a haka ya isa ga security din dake zaune daga bakin qofar.
Sallama yayi masa ya bashi hannu suka gaisa,ya gabatar masa da kansa gami da nuna masa ID card dinsa,ya jinjina kai
“To na shiga ciki ne na sanar da manager zuwanka?” Kai ya girgiza da sauri ransa yana masa suya,yau wai shine zai gwada aikinsa akan widad?,yau shine yazo bincike hotel akan widad?,halittar da duk duniya babu ta biyunta a wajensa?.
“Ba buqatar haka,personal investigation ne,tambaya daya ce kawai zan maka,idan akwai buqatar shiga cikin sai na sanar maka”
“To officer ba damuwa” .
Wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana rawa,ya buda hoton widad sannan ya miqa masa yana hadiye wani abu mai tauri a wuyansa,zuciyarsa kamar zata fashe
“Zaka iya shaida wannan fuskar?,ina nufin ka taba ganinta a nan wajen naku?” Cira kai yayi daga kallon fuskar,ya shaidata sosai,matar da yayita jiya mamaki da yaji tana hausa,don bai zaci ta iya hausa ba
“Tabbas jiya ma na ganta”
“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” ya furta yana saurin dafe qarfen qofar sanadiyyar jiri da yaji yana niyyar kayar da shi, idanunsa suka rufe na wucin gadi,da qyar ya samu ya daidaita kansa jin security din yana tambayarsa lafiyarsa lau?.
“Na gode” ya fada yana karbar wayar daga hannunsa,sannan ya juya da wata irin tafiya yana nufar motar.
Koda ya shiga sai ya saka kansa tsakiyar hannayensa yana jin kamar ana masa laguden tashin hankali,wani saqo can qasan zuciyarsa na gaya masa qarya ne,amma wani abu mai qarfi yana taso masa daga wani guri da baisan ina bane,yana gasgata masa abinda yake son ha zarga din
“Idan hafsat kishiyace,bata qaunar ta,zata iya mata sharri,shi kuma wannan security din fa?,meye hadinsa da ita da zai mata sharri?,ga shaidu da suka tabbatar kuma da haka?”
“Sir…….sai ina?” Muryar yaron ta kutsa tunaninsa
“Kaini gida”ya furta ba tare da ya iya daga kai ya kalleshi ba.
Farfajiyar gidan babu kowa,sai lawal dake zaune daga bakin gate yana yiwa hafsat CID din shigowar abbas din,ko karbar key din motar bai iya tsaiwa yayi ba ya wuce sashensa,yace lawal ya sallami yaron da kudi masu nauyi ya karba key din ya bayar cikin gida a ajjiye masa.
Kansa a sama ya wuce sassan widad,hakanan yaji ko sassan nata bayason kallo bare ya hangeta.
Da murnarsa ya kirga kudi ya bashin,ya karbi key din ya wuce sashen hafsat kansa tsaye baki har kunne,lallau yau ya warke,aljihunsa zai jiqe.
Tana jin muryar sa ta fito da gudu gudu daga kitchen tana watsa hannaye idanunta a waje,irin na mutumin dake jiran wani kyakkyawan albishir
“Ya ake ciki?” Dariya yadan saki
“Da alama komai ya kankama fa,sassansa ya wuce yana tafiya da qyar,ga key dinsa nan”
“Ma sha Allah,miqomin shi,ina zuwa” ta fada tana karbe key din,saura kadan ta fadi saboda yadda zaninta ke hardeta ya fice daga falon.
Ba abinda ya iya cirewa daga jikinsa banda takalminsa,sassan fes wanda yake da yaqinin gyaran da widad din tayi ne randa zata fita a girki,abinda ya sake dagula masa lissafi,da qyar ya iya zama saman kujerar.
Duk inda ya kwaso lissafin sai ya wargaje masa,yaji har cikin zuciyarsa yana qyamarta sosai,haske da tagomashin data samu cikin zuciyarsa wani qaqqarfan abu yana shirin tasowa ya lullubeshi fes!!! Ta yadda ko burbushinsa ba za’a samu ba.
Sai data dan tsaya ta saita nutsuwarta a bakin part din nasa sannan ta tura qofar tayi sallama,bata ko duna yanayin shigarta ba dake a jikirce,wata rigar kamfala da sukayi anko ce ash color da aka yiwa dinkin half bubu,ta daura zanin atamfa a sama,sai dankwalin kamfalar a kanta data masa wani dauri kamar na ‘yan talla.
Sosai kamfalar ta fidda duhunta,don dama daqyar tayita,don kala ce dake nuna baqinta,wannan yasa bata cikason abu ash ba.
Da qyar ya bude idanunsa ya watsasu a kanta yana amsa sallamarta,sai yaji kansa ya sake sarawa,ya zuba mata ido harta iso gefansa hannun kujerar da yake kai
“Sannu da zuwa daddyn mimi”
“Yauwa sannuku”
“Ya hanya?”
“Alhmdlh ya yaran?”
“Lafiya lau,sun gaji da jiranka sunyi bacci,yau kayi delay na dawowa,hala ka tsaya wani waje ne?” Kai ya girgiza mata,haka kawai yaji baiso tasan damuwarsa,tunda dama asalan basu saba haka da ita ba,batasan damuwarsa ba,shi daya yake cinye kayansa yayi solving dinta,saiko hajiyarsa Allah ya jiqan rai,ita kuma ba kowacce damuwa yake gaya mata ba,saboda kiyaye lafiyarta
“Sokoto to bauchi kinsan tafiyar ba kadan bace” saita gyada kai
“Ummmm,kuma fa hakane” daga haka shuru ya biyo baya a tsakaninsu,tanason taji ya sake cewa wani abu, tanason taji koda kalma guda daya daga bakinsa amma yaqi magantuwa,daga bisani ma sai ya miqe yana shirin shigewa bedroom dinsa
“Baka buqatar komai?” Bayajin zai buqaci wani abun,amma kuma idan baice komai din ba bazata qyaleshi ya huta ba,a yanzun kadaice kawai yake buqata ko zai samu sararin yin tunanin mafita ga gagarumin ibtila’i ko musibar data afko rayuwarsa
“Ki kawomin black tea”
“In sha Allah” ta fada da wani yanayi da sam bata saba ba,hakan ya sanya ma abun bai wani karbeta ba.
Ta gama shirya komai tsaf sai zaman jiransa da takeyi,tayi shiga irin wadda tasan yana tsananin so,tayi kewarsa kwana dayan nan kacal,ya shiga rayuwarta da yawa,ko yaya suka nisanci juna dukkansu saisun galabaita,ta samu wasu satar amsoshi da yawa a group dinsu na hanyoyin da zaki sake tsayewa mai gida a rai da takeson ta gwadasu a yau din,ita ta yarda da kanta,ta kuma yi imanin ta tsaya a rayuwar uncle din nata yadda ya kamata,amma kullum tunaninta da burinta shine taci gaba da tsaiwa a wannan matakin ba tare data cutar da abokiyar zamanta ba.
Har aka idar da magariba tana sake gwada wayarsa amma still a kashe,sai abun ya soma bata tsoro,tayi Shuru saman abun sallah,cikin zuciyarta tana addu’ar Allah yasa lafiya,ta qiyasta wasu awanni,indai suka shude bai iso ba,bai kuma bude wayarba zata magantu,ba zata iya jurewa ba.
Har isha’i shuru,don haka bayan ta idar da sallar isha din saita zura slipper dinta ta dora babban hijab saman qananun kayan jikinta sabbi fil data saka sabodashi,ta fito farfajiyar gidan tana neman fahad.
Da motarsa ta fara yin ido hudu,mamaki ya cikata,sai taja burki kawai tana kallon motar,yaushe ya shigo?,shine tambayar da takewa kanta,amma saita bawa ranta qila tana tsaka da sallah ne yanzu yanzu shi yasa bataji ba.
Muryar fahad taji a bayanta,saita waiwaya
“Yaushe daddy ya shigo ne?”
“Kai ai ya kusa awa biyu inajin”
“Ok inajin ya leqo ina ciki” ta fadi yana qoqarin danne damuwa da mamakin nata dai,sai tayi gaba tana cewa yadan duba mata affan a falo kada ya tashi ya fara koke koke.
[18/05, 6:54 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)