A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 25

Sponsored Links

Part 02

Page 25

Kasa cewa komai yayi,sai zuciyarsa dake wani irin tsinkewa,sun jima a tsaye a haka har affan ya fara kuka,sai ya miqa mata yaron ya juya ya koma dakinsa yana jin wani yanayi mara dadi cikin ransa,yanason bata haquri ya kuma lallasheta ya kasa,sai bayan ya zauna cin abincin dare yake sake jadda mata

“Ina tsananin sonki,ina kuma tsananin kishinki” bata da amsar bashi,amma batasan wanne irin kishi ko soyayya bane daya rikide yake son komawa ZARGI.

Tun daga ranar data fuskanci haka saita daina doguwar waya don kada ya kirata bai sameta ba,hakanan ta daina nisa da wayarta,idan zaiyi kira dubu zata daga,don don kiyaye faruwar wata matsala da take gani kamar tana shirin kunno kai,da tayi hakan sai taga kamar abubuwan sun ragu,kira dai tana jurar dagashi,to amma ta barwa ranta hakan shine maslaharta.

Ya koyi dawowa gida akai akai,sabanin baya da abincin rana kawai ke dawo dashi,a yanzu sai yazo gida sau hudu biyar kafin lokacin tashinsu a aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri.

Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima

“Zai tayaki zama har na dawo” da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai.

A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu’ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa’a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida.

*R U B U T A C C I Y A R K’ A D D A R A II*

Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne.

Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa

“Allah rayan…..rayan ‘yar nan” sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara’a sosai,shi yasa take sonta.

Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu

“Sannu da zuwa daddy” ya daga kai da murmushi yana kallonta

“Yauwa sannu da gida maman yara” ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata.

Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad

“Shigomin da sauran kayan don Allah” sai tayi gaba ta barsu a wajen.

Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran

“Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu” saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane.

Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade.

Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido

“Lafiya yallabai?” Sai ya dage mata girarsa dukka biyun

“Sonki nakeyi” maganar ta bata dariya har sai data murmusa

“So na nawa kuma ranka ya dade?”

“Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba” ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata

“Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa” murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta

“Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa” fuska yadan bata

“Hakan bai gamsar dani ba madam…..bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho” ya fada yana dan shan mur kamar da gaske.

Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya

“Haka kace uncle?,haka kace?” Dariya ya saki

“Wasa naki miki wuddu na” ya dora affan saman dining din yana cewa

“Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi”

“Allah ya nuna mana”ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din.

*W A S H E G A R I*

Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe.

Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan.

“Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?” Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai

“Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya” girarsa ya daga mata

“Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina…….”

“Wayyo uncle,don Allah kada ka fada” ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya

“Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad……” Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau.

Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa

“Lokaci yana tafiya, everything is ready” tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota.

Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet.

Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa.

Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta

“Me kika ce?” Dariya take qoqarin dannewa

“Bance komai bafa” da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta

“Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne ‘yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?” saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi

“Don’t say no…..na riga naji” juyo da ita gabansa yayi

“I love you,ina kishinki sosai” ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe

“I love you too” ta amsa masa a sanyaye.

Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa.

*B A Y A N A W A H U D U*

Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa.

Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace

“Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi” sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta

“Ta wanne guri kuke?”

“FAAZ hotels”

“Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku” ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta.

Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa’a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan.
[17/05, 7:35 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button