A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 14

Sponsored Links

Part 02

Page 14

Tun daga ranar sai ya zamana duk sanda sukazo kadunan gidan hajja take sauka abinta,don a yanzun ta yiwa gidan hajiya qaura,mugun kunyarta takeji saboda cikin da yake jikinta,ranar da hajiyan tayi mata addu’ar Allah ya raba lafiya kamar zata mace a wajen saboda kunya,taso qwarai ma ya dinga barinta kaduna,amma yaqi,saboda hajiyan nayin fada duk sanda yazo babu ita,bugu da qari shi kansa bazai iya wadan nan kwanakin tana wani gari yana wani ba,a haka rayuwar taci gaba da juyawa,har suka share watanni uku,mugun nufin hafsat din bai cimma gaci ba yadda takeso take kuma tsarama ranta,saidai a wasu abubuwan da dama ubangiji kan yiwa bawansa talala ya barshi da zabinsa.

*_B A Y A N W A T A U K U_*

Sanye take da wata farar gown ta wani cotton material dake da wani irin ado mai qyalli na golden din zare,ta bude sosai daga qasan rigar,hade take da mayafinta mai dan yalwa,tana tsaye gaba madubin dakin nujood tana shafawa fuskarta farar powder,nujood din na saman gadonta daga bayan widad din,hannunta dauke da littafin da widad din ke karantawa,tana tsaka da karatun abbas yayi kiranta kan cewa zai shigo.

Yadda widad din keta qalqale jikinta yasa nujood ta kasa yin shuru

“Ni banga amfanin wannan qaqale qaqalen da kiketa yi ba,just yaushe kikayi wanka ma?,wannan skin din naki da baya riqe dauda kwata kwata?,a wannan kyan da cikinki ya sakaki kikayi indai baso kike ki matso muninki ba don Allah kibar face dinki haka” murmushi ya qwacewa widad din ta juyo tana kallonta

“Uncle abbas ne fa zaizo,ke waya gaya miki ana wasa da lokuttan da za’a kebe da miji,kin mance kishiya gareni?” Dariya sosai nujood ta kece da ita sai itama widad din ta saki dariyar,ta tashi ta zauna sosai saman gadon

“Ni wanna kishiyar taki ita da zero duk daya,kinsan Allah tun bankai haka wayo ba nake tunanin uncle abbas me aji,dan gayu wanda bai rasa komai ba…..me ya gani a tattare da wannan wai?,wai kinsan tun asalinta qazama ce?,da sallah abba yayi yayi muje gidan uncle abbas muqi,ya rasa dalili in gaya miki,baisan idan munje wuni muke da yunwa ba,bata iya dafa mana abinci saidai ta hadamu da kayan tarkace,ci banza ci wofi,ga uban wanke wanke da wankin undies da zata hadaka dashi” sauke hannuwanta data goya widad tayi tana jinjina kai,qazantar hafsat din ita kanta tana matuqar daure mata kai,harta kama jikinta,don ko kumbarta ka kalla kasan akwai burbushin qazanta a tattare da ita

“Allah ya kawo mata sauqi”

“Ai wannan ba zata daina ba har ta mutu”

“Banason wulaqanci,mamar yaran masoyina ne fa” widad ta fada tana jifan nujood da hararar wasa,saita fidda ido

“Wai yaushe kika zama rasa kunya ne?,komai naki uncle abbas,baki da aiki sai maganarsa?” Fararen idanunta ta juya kafin ta saukesu akan nujood

“Kin manta shine rayuwata?,a kansa na fara sanin soyayya qauna kulawa da tattali,a kansa na fara sanin rayuwa, ga kuma d’a ko ‘yarsa a jikina” baki sosai nujood ta kama tana gwalalo ido

“Na shigesu,widad yanzu kinfi qarfina,Allah yasa dai nima gab nake da auren nan bare ki sani a uku” dariya suka sake qyalqyalewa da ita

“Wai nikam……mamar mimi tasan da cikin nan?,banji har yanzu ta nuna kowanne reaction ba” baki widad ta tabe,har zuciyarta bata qaunar zancan matar,ita a yanzun ta mijinta kawai takeyi

“Idan nace miki muna iya sati daya bamu hadu ba zaki yarda?”

“Haba dai?” Juyawa widad tayi tana zizarawa idonta kwalli

“Bata da aji gaba daya matar,da farko kallon mamata ma nakeyi mata,bana iya.musu ko qanqani da ita,ta cutar dani taso gurgunta rayuwata ta hanyar yin amfani da quruciyata,to a yanzun kuma meye yayi saura tsakanina da ita,ina kishin uncle sosai,shi yasa bana hada inuwa daya da ita,har muzo bauchi mu gama zamanmu bama sake haduwa sai a mota idan zamu koma,to me zai hada ni d……..” Maganarta ta katse sanda kira ya shigo wayarta,ta duba fuskar wayar tana murmushi

“Uncle dina ya iso…..”kafin ta daga wayar kiran ya katse,dai dai nan hajjaaa ta turo qofa tana gaya mata tayi ta fito ga uncle abbas dincan a setting room

“Saina dawo” ta fada rana zira wani plate white shoes na fata daya dace da qafarta

“Allah ya kiyaye hanya Juliet matar romeo”

“Babanki ne dai” ta amsawa nujood ta fice tana dariya,itama dariyar ta saki tana bin widad din da kallo,gaba daya rayuwarta da uncle abbas din burge nujood take,wata qauna da soyayya yake bata irin wadda bata iya boyuwa,duk inda kayi musu kallon farko zuwa.na biyu zaka fahimci hakan

“Ashe dama uncle din nan dan duniya ne” ta fada qasa qasa a fili tana dariya, saboda ta tuna sanda yake zuwa gidansu,tsakaninsu dashi gaisuwa,sai qarancin fara’a da kuma tsare gida da yake dashi,amma fa duk da haka dama can din shi mai kirki ne da yawan kyauta.

A nutse tayi masa sallama da sassanyar muryarta wadda ta tanadeta musamman sabodashi,kasa amsa sallamar yayi,saima ya miqe tsaye cak yana jiran isowarta.

Hannuwansa ya bata duka biyun,ya kuma jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki,ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana tura kansa cikin mayafinta da kyau,tare da shaqar daddadan qamshin da take fiddawa.

Ya jima a haka shi da ita suna jin dumin jikin junansu,kwana biyu tal amma yana jin kamar ya shekara ba tare da ita bane

“Ka zauna uncle” tayi qarfin halin fada,saiya dago fuskarsa ya hade da tata

“I missed you har bansan yadda zan kwatanta miki ba”

“I missed you too uncle” ta fada tana qanqameshi sosai,sai ya saki murmushi tare da ajiyar Zuciya gaba daya,yana jin dadin yadda kullum widad din ke sake zama cikakkiyar mace data karanci abinda yafiso da wanda bayaso,tamkar yana mata sharinga wani part na qwaqwalwarsa ne.

Ita ya fara zaunarwa sannan ya zauna a gabanta,ya dauko dukka qafafunta ya dora saman cinyoyinsa yana matsawa a hankali hadi da sauke mata wani narkakken kallo kamar zai cinyeta.

Kusan ta saba da irin wannan yanayin,duk da yana azama zuciyarta wani sabon naiyi ne,amma ko tace ya koma saman kujera ya zauna bazai zauna ba,yakance yana matuqar jin dadin hakan,duk da tana zaune sai data rusuna da dukkan girmamawa tace

“Barka da yamma yallabai”

“Barka kadai yallabiya maman biyu” saita zaro ido

“Uncle…..kanason na mutu ko?” Kai ya girgiza da sauri

“No…..idan kika mutu babynuncle……na tabbatar a ranar nima zan biki,just kawai ina sha’awar twince dinne,amma tunda bakiso shikenan” ya fada yana dariya cikin ransa,ta wani bata fuska kamar shine mai bayarwa ko kuma yace lallai twince din zata haifa.

“Ya bakaso dasu mimi ba?” Ta sake tambayarsa

“Ban qarasa gida ba,daga sokoto direct nan nayo…..ba zama ma zanyi ba,ki koma ki dauko abinda zaki dauko mu wuce gida” fuska ta narke masa sosai tana kallonsa

“But uncle…..a wajen mummyn mimi ya kamata ka sauka,kuma ma ka manta…..gobe fa na gaya maka zasu wuce kano anty madeena ta haihu,inason na bisu,i missed ummu alort,nayi missing kowa,abba na….su Aarifa da kowa”

“I know…..i know,bance kuma ba zakije ba,amma ina buqatar ki cike ragowar kwananki,kwana daya nayi miki aka kirani sokoto,kin tuna?” Baki ta turo masa gaba,a kwanakin gaba daya ciwon mara ne yake damunta,abunka da rashin kan gado fa rashin sanin makama irin na masu haihuwar fari saitake ganin duka takurarsa ne ya jawo mata,don kamar wanda aka qarawa qaimi a kanta,baya iya daga mata qafa a dukka kwanaki biyun da zaiyi a wajenta,shi kansa yasan tabbas tana qoqari,wannan ya qara mata matuqar kima da martaba mai tarin yawa a idanunsa,abinda wadda ta linka shekarunta ta gaza qanqanuwa da ita tana iyayi,kai bama ita ba,hatta da muhsin yanzun ganin girmansa yake qwarai da gaske

“Uncle a daina tuna baya fa”

“Wannan tuna bayan ya zama dole ai” ya fada yana lumshe ido,yana zagaye lips dinta da suka dan qara tudu kadan da yatsun hannunsa

“Nidai nidai”

“Baki zuwa?,sai naje na kaima mummyn mimi kwanan naki” ya dauka zatace bata yarda ba,don ya gama sallamawa kan yadda take kishinsa,saidai kishi ne irin na hankali da sanin ya kamata,wanda zakayi zaton wasu shekaru gareta masu yawa,amma sai yaji yace ta yarda.

Kicin kicin kuwa yayi,ya kasa ya tsare yace ta shiga ta fito yana jiranta,cikin sa’a Allah ya jefo da uncle muhsin,ya goya masa baya ya tayashi koro qaryarta,harda guzurin

“Kada ka yarda gobenma ta wahalar dakai,zasu biyo ta nan gidan su dauketa basai tazo ba”.

A mota ta dinga masa fishi,bai damu ba ya biye mata kawai,ya yita yawo da ita ya cikata da qwalaman kayan toshiyar baki,bakin kuw aya tosu,ta tasa kayanta a gaba ta dinga ci,saidai a yau din bata wani ci da yawa ba taji ta qoshi.

Yau dinma bayan widad din kawai hafsat din ta gani sanda shiga sashenta,mugun kishin da takeji a ranta ba kasafai ma yake barinta take iya mata wani kallo mai tsaho ba,don duk sanda tace zata zurafafa kallonta zuciya na ingizata ta aiwatar da abubuwa masu yawa,wanda ta tabbatar muddin ta aikata hakan sakamakon bazai mata kyau ba,takanji kamar ta samu wani ruwan guba da zai bata mata fuska ta watsa mata,ko tayita dukanta har dai ta galabaitar da ita,ko kuma ta shaqeta har sai ta daina motsi

“Baqar matsiyaciya” ta fada a ranta,tana sake jin qwarin gwiwar ci gaba da jarraba sa’arta akan widad din har sai sanda ta cimma nasara.

K’arfe sha biyu na rana suka sauka garin kano,cikin gidansu,gidan dake da tsohon tarihin a wajen widad,gidan da tayi wata rayuwa ta gata shagwaba da sangarta,batasan me kalmar matsala ke nufi ba,batasan bacin rai ko damuwa ba,a lokacin ko baka sonta bata jin zafin abun saboda zallar quruciya da rashin damuwa da ire iren wadan nan abubuwan.

Duk yadda zuciyarta ke matuqar dauki da son ganin ummunta amma qafafunta da suka dan tasa saboda zaman mota sunqi bata dama,tana hanya kafin ta qarasa su nujood suka dinga wuceta suna mata dariyar sai sun rigata ganin ummu,ta kuwa kebe baki shagwabar ta motsa,hannunta riqe da bayanta dake dan motsa mata lokaci lokaci ta isa falon ummun,dai dai sanda nujood ke dariyar

“Saida kowa ya gama gane miki ita sannan kika iso” tureta gefe ummu tayi ta miqe tana cewa

“Ba wanda ya rigata gani na,ni na fara ganinta,kuma itama ni ta fara gani” sai widad din tayi qaramar dariya tana jefawa nujood harara hadi da cewa

“Munafuki dai baiji dadin halinsa ba wallahi” ta fada jikin ummunta,ummu ta riqeta da kyau,farinciki ya cika zuciyarta gaba daya,widad dinta kullum girma takeyi,kullum kuma alamu suna nuna soyayyar mijinta a jikinta,ta zama wata babbar mace kamar ba ita ba,idan ka ganta zaka musanta shekarunta,ga kuma albarkar aure a tattare da ita,duk da batasan watanninsa ba amma tasan dai ya fara mata nauyi,Allah zai cika mata burinta na ganin dan widad a duniya?,saita share hawayenta cikin dabara ta zaunar da widad din a nutse tana fadin

“Me yasa kikayi tafiyar mota ga qafafunki nan sun tasa”

“Bazan iya jurewa ba ummu,a taho kano a barni?” Saita girgiza kai tana dariya,kai itama ummun ta girgiza

“Ki shiga ciki to ki fidda kayan nan,ki watsa ruwa sai a dumama miki qafar ki shafa man zafi,kici abinci saiki kwanta ki huta”

“Duk ita kadai ummu?” Aafiya dake shigowa ta fada,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna ita da widad

“Wai ashe dai da gaske mun kusa zama iyaye” ta fadi tana kallon cikin widad da wahalar tafiya tasa a yau din ya fito sosai,kamar damar ranar yake jira,kamar jira yake su shigo kano din.

Da sauri ta kwabi Aafiya, saboda ita har ga Allah kunya takeji idan akace ciki ne da ita,sai taji kamar ta nutse

“Ba abinda ummu fa zata miki,tafi kowa ma murna,randa aka gaya mata ko abincin kirki kasa ci tayi” ta fada tana sheqa dariya,don dukkansu sunsan danbarwar boye cikin data dinga yi,sai suka sanya dariya gaba daya qasa qasa.

To wanka da hutu dai baiyiwu wajen widad ba,don gidan nasu cike yake da baqi kasancewar jibi sunan yarinyar da anty madeena ta haifa,baqi anata shigowa,yan uwa da abokan arzuqi gidan a cike yake,wannan ya shigo wannan ya fita,anata hirar yaushe gamo,sai widad din take jin ranta fes,kamar bata da sauran matsala,hatta da wayarta ta mantata a jaka gaba daya.

Jin hajjaa zata fita ziyarce ziyarce danginta da nasu uncle muhsin din sai widad din tace zatace,ummu ta kasa ta tsare tace ba inda zata fita,ta marairaice mata da kyau

“Don Allah ummu ki barni naje,yaushe rabona da kano,koda zamuje aikin hajji kwana nawa duka nayi,da muka dawo kuma ko gidan nan uncle bai barni na shigo ba muka wuce bauchi”

“Ki barta taje ummu,ta dan tattaka ma,tunda acan nasan ba wani waje kike zuwa ba” anty halima dake wajen ta roqar mata ummun.

Yawo sukayi sosai harda tafiyar qafa,kafin su dawo kuwa jikinta ya soma gaya mata,a ciwon mara da bayanta ya sake qaruwa time to time,a haka take cinyewa ganin idan ya motsa yana daukan wasu mintuna masu tsaho sai basake motsa mata ba.

Basu suka dawo ba sai ana gab da sallar magariba,kai tsaye ta wuce dakin da ummu tasa aka gyara mata ta fidda kayan jikinta tayi wanka da ruwa me mugun dumi wanda mutuniyarta latifa ta hada mata.

Tana fitowa daure da towel taji marar tata ta sake riqewa da kyau,saita lallaba ta zauna gefan gado tana cije lebe har zuwa sanda ya lafa mata,ta yunqura zata miqe don ta shirya ta sake ficewa, hankalinta yayi gaba saboda sautin hirarraki da take jiyowa daga falon ummu sai taji ringing din wayarta,ta dafe baki tana mamakin yadda yau wuni sur ta manta da wayarta,suna gama waya da mommynta kiran abbas ya shigo,tunda sukayi sallama ta maidata jakar,tasa hannu ta dauko jakar da aka aje mata saman pillow wanda duka tasan aikin latifarta ne,ta buda ta ciro wayar.

Ido ta zazzaro ganin tarin miscall din abbas kusan guda ashirin,ta bude pattern din tana yunqurin kiransa sai gashi ya sake kira.

Ajiyar zuciya ya fara sauke mata kafin yayi mata sallama,ta amsa tana jin kewarsa a take tana saukar mata

“Kin dagamin hankali sosai,banda yanzun muka gama waya da naadir ya tabbatarmin lafiya da tuni na kamo hanyar kano” ido ta zaro cike da mamaki

“Uncle?,da gaske?,kano fa kace?,don kawai ban daga wayarka ba?” Murmushi ya fidda mai sauti,ko yaya zaiyi mata bayanin girman matsayinta a idonsa ba lallai ta gane ba,saidai kwanyarta ta dauki iya abinda zata dauka

“Wudd…” Ya kirata da sunan da kaf duniya shi daya yake kiranta dashi,ta amsa masa a tausashe

“Matata fa…..da yarona ne suke neman bacemin,yaya zan saka wasa?” Dariya ta subuce mata mara sauti,saita jinjina kai

“Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana”

“Inason hakan musamman ya zamana tare dake zamu mori lafiyar da kuma nisan kwanan” kunya tadan kamata,yadda uncle din yake mata kamar baya tuna cewa ya ninkata a shekaru,ita din sa’ar ‘yar abokinsa ce,ba ruwansa da wanann,kwata kwata baya iya boye mata soyayyar da yake mata.

Wata irin hira mai sanyi sukeyi shi da ita,sau uku latifa na leqota taga waya takeyi saita koma,basu rabu ba har sai da mararta ta tsikareta tace

“Wayyo Allah” cikin matuqar kulawa yake tambayarta lafiya,data gaya amsa yace ta ajjiye wayar taje taci abinci ta kwanta ta huta sosai,gobe sur yakeso ta yini a gida kada ta sake fita,shima a goben tun asuba zai fita shida Samuel zasu sokoto,tayi masa kyakkyawar addu’ar nan tata dake qara masa qwarin gwiwa sannan suka rabu.

Doguwar rigar da tasan ba zata takura ba ta sanya,ta zura hula ta sakawa qafarta socks sannan ta fito.

 

[11/05, 2:59 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button