A Rubuce Take Book 2 Page 13
Part 02
Page 13
*W A S H E G A R I*
K’arfe shida da mintuna na saafiya ya baro masallaci,bayan ya gama ‘yan addu’o’insa.
Daga bayansa yaji tafiya,kafin ya waiwaya an ambaci sunansa,tuni ya gane muryar sai ya rage tafiyar da yakeyi yaja baya kadan hadi da waiwayawa.
Karasowa mutumin yayi fuskarshi qunshe da murmushi ya miqawa abbas din hannu,maimakon ya bashi hannun shima sai ya rusuna yana gaidashi cike da matuqar girmamawa.
Kin amsa masa yayi har sai da sukayi musabahan,duk da har yanzu abbas bai miqe tsahonsa ba saboda bashi girma
“Ban sani ba ko yara sun gaya maka saqona” yayi murmushi
“Eh abba…..sunce kazo zamu gaisa”
“Eh…..to ma sha Allah,na sake dawowa amma ban samu ganinka ba dai,mu qarasa gidan,inason magana da kai” tare suka jera da mutumin,suna tafe suna dan taba hirarrakin da suka shafesu,har suka isa cikin gidan.
Bayan gaisawa da ma’aikatan gidan,kai tsaye suka wuce setting room dinsa.
Sunansa abban ya kira yana duban fuskarsa
“Nazo jiya sau biyu kamar yadda na gaya maka,saidai duk zuwan da nayi din na iske rikici ne da hayaniya tana fitowa daga gidan har harabar gidan nan,ya akayi kabar gidanka yake neman zama haka?,me yake faruwa?” Gyara zamansa abbas yayi yana sunkuyar da kansa,abban kamar mahaifi yake a wajensa,babu abinda zai boye masa,don haka ya gaya masa komai.
Shuru yayi na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya
“Ba yadda za’a yi ka ajjiye mata biyu a guri irin wannan sannan kayi zaton samun kwanciyar hankali,muddin kanason zaman lafiya saidai ka raba musu muhalli,wannan shine kawai hanya daya da zaka samu dai daito akan irin wannan matsalolin,daya bataga ‘yaruwarta ba bare wani abu ya biyo baya” kai abbas yake jinjinawa yayi, masa godiya sosai,lallai shawarar abban tayi masa qwarai,ya kuma bashi mafitar da shi a kansa ma bai kawo hakan ba
“Amma…..ita hafsatu meye ya dawo da ita kaduna idan ba zallar neman fitina bama?” Abban ya fada cikin mamaki, saboda fes yasan halinta ya kuma san abinda ya wakana wancan karon,abbas din yayi qasa da kansa,yama rasa wacce irin amsa zai bawa abban,Allah shine masanin gaibu,kuma shi daya yasan yadda yakeji a qirjinsa game da dabi’a da halayyar hafsat din,shi kadai yasan irin haqurin da yakeyi da ita
“Kada ka damu,kaci gaba da addu’a,sannan kaci gaba da jajircewa,Allah ya kawo mafita ya shige gaba”
Ranar bai fita aiki ba,gaba daya sai yaji bashi da kuzarin fita aikin, widad din ta gama kashe masa jiki da xuciya da soyayyarta,a irin abinda take masan,yaso ace gidan nasu kamar daa ne sanda suke daga shi sai ita.
Rashin fitarsa aiki ya sake harzuqa hafsat din qwarai,ta sake birkicewa sanda ya fiddo kaf kayansa dake dakin widad da wanda yake dakinta,ya kuma raba komai yace kowacce ta dauka,ranar kamar zata ara hauka
“Wallahi na yarda…….yarinyar nan mallaka da asiri takeyi mai matuqar qarfin da yafi nawa” hankalinta ya tashi sosai,tana ganin abubuwan kamar suna fin na baya lalacewa da jagwalewa,ta rasa inda zata tsoma ranta ranar taji dadi,tanason tayi waya kuma tana shakkar kada ya shigo ko wani ya jita,dole ta dinga hadiyar bacin ranta ita kadai zuciyarta kamar zata fashe.
To tun daga ranar abbas din ya fara neman wani gidan ba tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna.
Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya.
Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada
“Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood” ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna.
Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta.
Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat.
Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba.
Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita
“Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru”
“A dawo lafiya” ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice.
Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya
“Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba” ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin
“In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi” ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana.
Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali.
Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne.
Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka dadi,ta ware sosai abinta,har zuwa sanda abbas dake setting room sunata hira da uncle muhsin,irin hirar da suka jima basuyi irinta ba ya tashi tafiya,ta miqe ta yafa mayafin abayarta ta fice don suyi sallama.
Idanunsa qur bisa qofar,kamar daman jiran isowarta yakeyi,ta yaye labulen ta shigo a hankali,saiya miqa mata hannunsa,ta kama a hankali ya jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinyarsa.
Hannusa guda daya ya dora saman cikinta,kamar yasan me akayi yayi wani zillo,tadan motsa da sauri tana zare ido,don har yau ta kasa sabawa da irin wannan motsin,abbas da yaga irin yadda ta motsa sai ya saki murmushi
“Kin gani ko?,shi kansa yana cewa zaiyi kewar babansa,amma mamansa kamar bata damu ba” ya qarashe maganar yana langabe mata kai kamar wani maraya me neman agaji.
Yadda yayi din ya bata dariya,tadan saki siririyar dariyar data bayyanar da fararen haqoranta dake burge abbas sosai,ta saka hanuwanta duka biyu ta riqe kansa cikin tafukan nata tana dubansa
“Mamansa zatayi kewarka fiye da yadda shi zaiyi……”
“Amma me yasa kika zabi kibar gidan?,kinsan yadda nakeji duk lokacin da na juya cikin gidan naga babu ke a cikinsa?,widad…..duk gidan da babu ke a cikinsa shida kango daya suke a wajena.
,inji a zuciyata kina gidana wata babbar rahama ce a wajena,kallonki yana bani dukkan nutsuwa da zuciya da ruhi suke buqata…..ban taba kasancewa tare dake ba…..koda wata mu’amala bata shiga tsakanina dake baba tare dana samu nutsuwa ba” yadda yake tsara mata kalaman da yadda yake karanta mata su cikin kunnuwanta sai suka kashe mata jiki,ta matsa a hankali ta kwantar da kanta saman kafadarsa tana rufe idanunta gami da jin yadda bugun zuciyarta ya bugawa a nutse,irin bugun da bata samu irinsa ba daren jiya.
Ita kadai tasan irin yadda take fighting da wani mugun tsoro….. tsoro irin wanda bata taba jin irinsa ba….. qunci da damuwa da wata irin qaguwa na tabar gidan,ta matsa a wajen,tana jin kamar tana taka qayoyi a qafafunta duk sanda take taka kowanne sashe na gidanta,amma batasan ya zata gaya masa ba,ya zatayi masa bayani,tunda ita daya takejin hakan,ta sani tana addu’a kuma tana samun sauqi lokaci lokaci.
Sun jima a haka suna shan dumin jikin juna,kafin ya dagata yana duban fuskarta
“Gobe ne kwananki,zanzo na daukeki,babu cin bashi” narke masa tayi,ya dora yatsantsa saman labbansa
“I will bring you back,right?” Murmushi ta sakar masa sannan ta gyada kanta,tashin hankalinta dama yace zata ci gaba da zama har zuwa sanda zasu koma Kaduna.
Kwana daya tak tayi yazo ya dauki abarsa,hajja nata tsokanarsa ko surukuta babu?,bai amsa ta ba illa binta da yayi da miskilin murmushinsa.
Hafsat ta sake sosai ganin widad bata gidan,hankalinta kwancw tana ganin zata ci gaba da riqe abbas muddin suna bauchi saidai idan sun koma kaduna,a can dinma tunaninta ya fara karkata…..me zai hana tayi wani abu a kaine kwatankwacin abinda ke wakana yanzu?.
Sosai shawarar ta zauna mata cikin kai,don a yanzun da take zaune ita daya cikin gidan sai takejin kamar bata da sauran matsala a duniya.
Ba qaramin kaduwa tayi ba lokacin da ta fara jiyo qamshi na fita daga part din widad din,qamshin turaren wuta da na abinci duka lokaci guda,sam sam batasan sun shigo gidan ba,daga ita har abbas din,zuciyarta tayi wani irin nauyi,mamaki ya kusan kasheta
“Wannan wacce irin musiba ce” ta furta a fili kamar zata zunduma ihu,duk ta inda take hangen nasara sai alamun nasarar sun fara bayyana kansu sai komai ya rushe.
Kasa jurewa tayi ta aika yaran su gano mata abbansu yana nan,baya nan din don tunda ya ajjiyeta ya fita yace zaije ya dawo,saidai sun dawo mata da tsarabar lafiyayyen samosa da yaji nama carrot dankali da wadatacciyar albasa.
Samosan yana daya daga cikin abinda take mugun so,qyuya son jiki da rashin maida hankali a koyi girki yasa bata iya ba,duk da suna da komai na amfani a gidan da zata iya yi da kanta,sa’annan son kudi da son abun duniya kuma baya barinta ta siya a wani waje,saidai idan anci sa’a ta fita wani gurin sha’ani ta samu a can taci.
Duk sonta dashi yau din quncin zuciya da kuma tsanar widad din ya hanata ci,duk da yawan wanda ta bawa yaran,suka sanya abinsu a gaba suka cinyeshi tas suka sha ruwa,duk sai suka hau bacci.
[10/05, 9:20 pm] +234 816 283 5575: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*UCE TAKE_*
(K’addarata)